Follow us on social media
Showing 9001 words to 12000 words out of 29865 words
Chapter 4 - SO MAKAHO NE Rikicin Zukata by Qwinn minerhly
ɗaura da cewa "yauwa akwai wani companies da zamu buɗe nan da 3months, kuma muna so ku ma ku halarci gun, don haka ke gimbiya zanwa director na school ɗinku waya akan karban excuse, kuma ina so ki fara shirya shiryan komawa school daga yau because nan da 4 days zaku koma , really"? Nihal ta girgiza kai tace " haka ne abba kuma insha Allahu zan fara shirye-shiryen." yace "yauwa my princess take care of yourself," tace "insha Allahu dad."
Nan ya dawo da duban sa ga adnan yace "yarima da fatan ka fahimci abinda nake nufi," adnan yace "am sorry dad, but pls kayi hakuri at that time inada wani schedules da freinds ɗina so pls dad am sorry ba lallai na samu daman halarta ba.. shutup my friend!!! Mai martaba ya faɗa cikin tsawa, ya cigaba, adnan wlh ka kiyaye bacin raina, sakarai kawai, kai kullum sai shashanci da abokai, to wlh na kusan ɗaukar mataki akan ka stupid, mara hankali, na kawo magana mai mahimmanci kai ka kawo min shiririta, to bari muga nawa za'a ɗauka, to baka isa ba.
nan fa adnan yayi ta sosa kai alamar mara gaskiya yace "don Allah abba kayi min gafara na tuba kayi hakuri wlh bazan sake ba," aikuwa nan dad yace "yimin shiru, ko dan uwarka tana goya maka baya shiyasa kake iskancin da kaga dama ko?" Yarima yace "am so sorry dad," gimbiya tace "pls dad kayi masa afuwa tunda ya tuba kaji dad? Sai anan mai martaba ya gyada kai yace alright shikenan amma a kiyaye gaba, suka ce insha Allahu, nan suka miƙe suka fice suna wa mai martaba sallama.
Bayan sun fito yarima yace wa gimbiya "lil sis sai ina kuma"? Tace "wlh brother zan ɗan fita ne yau," yarima yace mata "alright sai kin dawo lil sis," tace masa "to shikenan bro bye". tayi wucewar ta.
Tana isa part ɗin ta, ta ɗauki wayar ta, ta kira noor, achan ɓangaren noor ta ɗaga waya haɗe da cewa "wow besty kamar kinsan ke nake tunani yanzu", nihal tace wlh kuwa besty gani nan yau zan cika alkawarin da na daɗe ina ɗauka, noor tayi charaf tace "ba dai gidan mu zakizo ba? Gimbiya tace "yeah besty am coming right now. nan kuwa noor ta kurma wani uban ihu tace "kai amma naji daɗi wlh, gimbiya da tayi saurin kawar wayar daga kunnen ta sabida kar noor ta toshe mata kunnuwa ta daina ji dasu, tayi maza ta mayar tace "kai noor meye na ihu kuma? Noor tace "bari kawai sis ko nayi maki bayani ba zaki gane ba", gimbiya tayi murmushi tace "eh ai ganuwa sai ku, iyalan Elizabeth", dariya noor tayi tace "lah abun harda su zagi to wlh karki bari yan elegant su ji ki," nan kuwa gimbiya tayi murmushi tace "hmm wlh ko sunji Ni babu abinda zasu iya min," noor tace hhhh to ai shikenan, sai kinzo ɗin dai, gimbiya tace "alright saikin ganni, ta kashe wayar ta, ta fada bathroom tayi wanka, ta fito ta tsaya, ta shafa cream, ta gyara gashin ta, ta feshe jikin ta da turare, ta nufi dressing room ɗin ta, ta je ta ɗauko wani tsadaddan less red nd black, tayi simple ɗaurin ɗwankwali, ta ɗauki wani alkyabba baƙi mai santsi bugun Dubai ta ɗaura akai, wow tayi matuƙar kyau wlh gimbiya kenan, an iya ɗaukan wanka, ta ɗauki wani heel red color ta saka, faɗar irin kyan da tayi ma ɓata lokaci ne, domin har wani haska gun takeyi.
Nan ta fito bayin ta na biye da ita, tana takun ƙasaita kamar hawainiya, ta nufi part ɗin mum ta mata sallama, mum tace ga wannan ki kaiwa yata noor, gimbiya ta duba taga wani haɗaddan alkyabba ne, shigen irin na jikin ta amma shi wannan yafi stones, da kyau, kuma shi peach ne zallah sai sheƙi yake, aikuwa gimbiya tace wow mum yaushe kikayi ordern irin wannan?, yayi kyau sosai, mum kuma wlh jiya Anty fanan, (ƙanwar maman nihal ce, tana zaune ne a dubai,ita da mijinta da ƴaƴanta). Jiya ta turo min da irin su sak wai a satin nan aka sake su a Dubai, shi ne nace zamu yi ordern sa da yawa, aikuwa mum tace "eh nima shekaran jiya nasaka order, yau kuma ya iso, ku biyu dama na saka wa order keda noor, kuma kalan ɗaya ne, babu bambanci," nan nihal ta rungume mum tana murna tace "mun gode mum sosai," mum tace "ki gaishe min da hajiya nuhaira, noor tace "zataji kuwa insha Allah, to shikenan saina dawo mum, mum tace a dawo lafiya, tace "Allah yasa Amin.
Tana fitowa bayin ta suka yafa mata baya, suna isa haraban gidan, wajan parking space aikuwa motoci ne a parke agun sunfi a ƙirga, nan kuwa gimbiya ta ɗaga masu hannu, tace "dawa za kuje ? common get out of my side!!! Ba daku zani ba, da kaina zanyi drive yau ku koma, har ku tayi poiting bodyguard ɗin ta aikuwa suka zube suna mata kirari, ɗaya yace to ran gimbiya ya daɗe wani mota zaki hau a buɗe miki marfin ta? Batare da tace komai ba, tayi poiting ɗin wata haɗaddiyar mota (AUDI RS5) nan kuwa aka buɗe mata shi, ta shiga ta bashi wuta tayi ficewar ta, ta ɗau hanya, sai government house, aikuwa tana zuwa get aka buɗe mata, kasancewar akwai number gidan sarauta ajikin motar, aikuwa gimbiya tana shiga ta nufi main parlour taga babu kowa, Kasan cewar yanzu mum suka bar parlon, ita da ashmir, don ashmir ne ma yayi mata sallama ya tafi, a cewar sa yayi baƙo, wani freind ɗinsa ne yazo ziyartar sa, aikuwa yana miƙewa, mum ma ta miƙe.
nan kuwa gimbiya ta nufi part ɗin mum ta gaishe da mum, tayi murna da ganin ta, tace "welcome to U mu daughter, I miss u a lot, nan gimbiya taje tayi hugging ɗin mum, sannan ta duƙa ta gaishe ta mum ta amsa da fara'a tace "yasu hajiya Fulani da sauran mutan gidan? Gimbiya tace kowa lfya mum, "mum tace a gaishe ki, aikuwa tace ina amsa wa, nan noor ta shigo a guje ta rungemi gimbiya tace ur highly welcome my lovely friend, gimbiya tace thanks my luv, mum tayi murmushi tace "to uwar surutu zaki rakata can part ɗin, ta warware gajiya ko kuwa? Noor tayi dariya tace "mum yanzu zamu tafi ai, don naga nihal bata saki jikin ta anan ba, sai ka ce wacce ta je gaishe da surukarta, nan gimbiya ta daɗa sunkuyar da kanta domin wani kunyar mum taji ya sake shiganta, aikuwa mum ta wurgi noor da thow pillows ɗin da suke jere a akusa da gadon ɗakin, nan kuwa noor ta ja hannun nihal suka tafi, mum tace "jaira da kin tsaya ai, parrot kawaii."
Nan fa mum ta fara tunanin ilham a matsayin surukar ta, aikuwa da taji ɗaɗin hakan sabida tana matuƙar son yarinyar, dama tunanin noor ya zama gaske.
Noor suna shigowa part ɗin ta, gimbiya ta zuba mata duka a baya, noor ta zuba ihu tace "shi ne zaki na kasa min baya ki cuci mijina ko? Gimbiya ta rike baki tace oh sweet luv am sorry but kinsan baki kyauta min ba ko? Kin san ai zanji kunyar mum, kika faɗi wannan maganar, kuma kinsan da kunya ko", noor tace "to meye? Ai babu komai, mum ai social mum ce karki damu", ta ɗaga mata gira ɗaya, nan gimbiya tayi murmushi tace "daɗi na da yan jarida, iya zance da zaƙin baki, noor tayi dariya, tace, "am coming few minutes," nihal ta gyada mata kai, noor na fita ta je tayiwa Peter bayanin abubuwan da zai kawo masu ita da bakuwar ta, aikuwa ta taho kenan ta hango yaya ashmir da abokin sa suna tahowa, aikuwa ta ƙarasa ta gaishe da su, abokinsa me suna fayal yace "wow lil sis amma fa kin girma sosai, so beautiful, ashmir yayi murmushi yace "to aku is okay don naga alama idan kuka haɗu da noor sai ku yini kuna surutu domin ita ma gwanace, noor ta turo baki tace "yaya fayal ka ganshi ko? Kullum sai yace min parot, fayal yace rabu da shi, kin san ai shi kurma ne baya magana, ga shegen miskilanci, ai kan yakarasa ashmir ya doka masa wata uban harara, yace nayi gaba idan ka gama zuban ina ciki, yayi tafiyar sa, kasancewar fayal yasan hali, shi yasa yayi murmushi ya dafa lil sis yace "don't mind ashmir, haka yake kullum, shi baya son yawan magana, but lil sis sai anijima bari naje na samu mutumin nawa ko"? Nan noor ta gyaɗa mishi kanta haɗe da murmushi, tace "yauwa yaya fayal bye", ta miƙe ta dawo cikin part ɗinta ta samu ilham na kallon laptor ɗin ta, ta ƙaraso tace "sorry my luv na barki ko? Gimbiya tace no ba komai ai ina kallon pics dinki ne a gallary, tace ki ce kinga brothers ɗina guda biyu? Nihal ta girgiza kai tace "no ban kai nan ba but ai zan gani ko ba yanzu ba, aushsh nayi mantuwa, noor tace "me kika manta? Nihal tace "no ba damuwa yana cikin mota mum ce tabani saƙo na kawo miki, noor tayi murmushi tace "Allah sarki luvly mum ɗina, aikuwa naji daɗi wlh, ilham tace "eh idan na tashi tafiya sai ki karba yana mota, noor tace "okay ba damuwa," to daman tun ɗazu Peter ya zo ya ajiye tire tire na kayan kwalam da makulashe,
Noor ta matso masu da kayan lasawa, tacewa ilham "pls ki matso kici abinci", gimbiya tace "wlh bana jin yunwa," noor tace "wlh baki isa ba kawai ki matso ko dambun nama kici, pls my luv" ilham ta matso tace "kai! ni wlh kin takura min" noor tace "eh naji ɗin amma sai kin ci, ke bari ma ki gani da kaina zan baki a baki," ta ɗebi dambun nama a ƙaramin spoon ta kai saitin bakin gimbiya tace ahm, to sanin halin noor da kafiya shi yasa bata musa ba, ta buɗa baki, aikuwa noor ta zuba mata a baki, suna cikin haka ilham tace "yaisa na koshi" noor tace "saura yurghourt ta tsiyaya mata shi a cup ta bata shima ta sha.
Can noor tace "wai besty lafiya kuwa kike"? Gimbiya tace "mai kika gani"? Noor tace "wlh da ganinki akwai abinda yake damunki", ilham tace "wlh babu komai sist", noor tace "lallai ma yaushe muka fara ɓoye wa junan mu abu"? Nihal tayi murmushi sannan tace "ai bamu taɓa ba, kuma ba zamu taɓa ba, insha Allahu."
Tace "sister kinsan dai bana soyayya ko"? Noor ta girgiza kai alamar eh,
Ta cigaba da bata labarin wannan haɗaddan gayan da ta haɗu da shi a palace, har izuwa mafarkin shi da tayi da kuma yawan tunanin shi da take yi.
Ta ɗaura da cewa "ni abinda nake tunani shi ne, maybe sabida ina so na rama abinda yayi min ne shi yasa nake yawan tunanin shi ko besty?"
Noor ta ɗan yi ajiyar zuciya da jin labarin ilham sannan tace "a gaskiya besty Abinda na lura da shi a cikin story ɗinki kamar kin kamu da soyayya ne".
What wlh ba gaskiya tunanin ki ya baki ba, taya zan so wannan mugun mutumin, wlh bazan so shi ba, kina nufin ya bugu banza? Ko kina nufin ya zagi banza, kuma ya sha? To ki buɗe kunnan ki kiji ni, wlh sai na rama abinda yayi min ko waye shi.
Noor tayi murmushi tace "Besty baza ki gane ba ne, but amma na barki shike nan, idan tayi tsami ma ji.
"Kai nifa wlh ka fara bani haushi, a ce mutum ba dama a fara zancen budurwa ko aure sai ya ɓata fuska wai shi baya so, sai ka ce wani dutse."
"Cewar fayal"
Tsaki ashmir ya ja sannan yace "kanka ake ji."
Fayal yace "kai ma ɗin kanka a keji."
Ashmir yace "comm'on pls mu bar wannan zancen, ni tambaya ce ma dani."
Fayal yace "ina jin ka freind".
Saida ya ɗanyi jimm sannan yace "pls wai meke sa mutum ya paya tunanin abu, ko kuma ka faya mafarkin abu?"
"Cewar ashmir"
Fayal yace "amma kafin na baka amsar tambayar ka, zan so naji akan me kake yawan mafarki da tunani?"
Ashmir yace "na tambaye ka, kai ma ka tambaye ni, so pls bana son haka, babu ruwan ka da sanin wannan, idan zaka bani amsar tambaya ta to, idan kuma baza ka bani amsar ba to shike nan."
Fayal yayi murmushi idan da sabo ya saba da halin ashmir.
Sannan yace "okay! Pls ka maida wukar, sannan kuma ga amsar tambayar ka."
A gaskiya abinda yake jawo yawan mafarke mafarke da kuma yawan tunanin abu, ba komai bane illa kasa ka abun a ranka,domin idan ka saka abu a ranka, za kaji ka faya tunanin wannan abin har ma da mafarkin sa.
Pls freind ka faɗa min meke faruwa ne?pls ashmir.
Ashmir ya kwashe komai daya faru tsakanin shi da wannan yarinyar ya faɗa wa fayal, sannan yace nifa freind na kasa gane komai,brain ɗina ya toshe.
Fayal yace "frend akwai mafita but saika bani haɗin kai tukun, sannan sai ka yarda da cewar ka kamu da soyayyar wannan yarinyar ne, sai kuma mu samu mafita."
Is okay pls, bana son yawan comments, ni babu wani soyyaya, na rasa da wacce zanyi soyayya sai da fitsararriya, to bazan iya ba, kasan me kake faɗa."
Murmushi fayal yayi sannan yace "gud, wlh wannan kafiyar taka yana birgeni muje zuwa, amma kar a sake azo nemen shawarata wata rana, kuma ka tashi ka raka ni zan tafi.
Fayal ya mike, ashmir ma ya mike haɗe da cewa "naga alamar kayi fushi ko to sai kayita yi bazan baka hakuri.
Besty yaushe zamu je saloon gyaran gashi? "Cewar noor"
Gobe sai mu je saloon ɗin, sabida kinsan nanda 4days zamu koma ko?
"Cewar gimbiya"
To shike nan besty Allah ya kaimu goben,
"Ameen"
Besty tashi ki rakani zan tafi, "cewar nihal"
Nihal tun yanzu zaki tafi ?
To ai noor magriba yana daf dayi kuma kinga na yini maki da wuri nazo fa.
To shike nan muje ki sallami mum saimu tafi.
Nan suka miƙe gaba ɗayan su, suka nufi part ɗin mum, nihal tace "mum zan tafi,"
Mum tace "my princess har zaki tafi?"
Nihal taji daɗin sunan sabida haka mum ɗin ta ke ƙiran ta.
Tace "Yes Mum zan tafi magrib ya kusa".
Mum ta miƙo wa nihal wata ƙatuwar leda haɗe da cewa "ga wannan my princess, ki gaishe min da Hajiya Fulani."
Nihal ta noke tace mum harda ɗawainiya?
Mum tace ke noor gashi rike mata rakata har mota, noor ta karba tayi wa Mum godiya, nihal ma tayi godiya haɗe da cewa mum zataji inshallah, nan suka fice sai parking space.
"A hankali ta dinga hango bayan shi, domin suna da nisa a tsakanin su, sabida sune a gaba, kawai taji gaban ta ya faɗi."
Bayan wa aka hango?
Wai shin ashmir da nihal suna haɗuwa kuwa?
Idan sun haɗu me zai faru?
Ku biyo ni a next page domin jin ya zata kasance.
Taku
Qwinn minerhl
Mr Yusuf
❤️❤️❤️
More comment more typing✍️✍️✍️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖
*Writer*✍️✍️✍️✍️
*Na Qwinn minerhly*
_ina_ _fatan_ _xaya_ _nishaɗantar_ , _daku_ _haɗi_ _da_ _ilmantarwa_ ,
_Short_ _and_ _romantic_ _story_ .
Page 40_45
Shi ko yaya fayal tunda ya ga princess nihal gaba daya ya rasa sukunin sa,duk ya rikice a kan ta, yana kwance a kan 3 sitter din dake parlon sa, sai ya dauki wayar sa ya kira noor, tana daga wa suka gaisa, yace mata "pls noor ki bani num din kawar ki pls lil sis,"
Itako noor tace "to shikenan yaya fayal bari na kirata na fada mata ko, sai na turo maka shi true sms. Fayal yace "yauwa lil sis Nagode kwarai da gaske."
Tace masa "ba komi yaya".
A can ɓangaren yaya ashmir kuwa yana can cikin daki yana ta wani aiki da aka kira sa a waya yanzu a can jarmany wai suna buƙatar taimakon sa na gaggawa ko ta laptop ne, to shi ne ya dukufa yana ta aikin shi cikin natsuwa.
Gidan Alhaji kabeer
Hajiya binta ce ta kira yar ta wato islam, ta zaunar daita ta bata wani turare tace "ungo wannan
Malam na tudu ne jiya da naje ya bani yace "ki shafa a jikin ki yanzu kitafi government house yanzu kije ku gana da ashmir, kuma ki tabbatar ya shafi koda mayafin ki ne kinji na gaya miki,"
Islam tayi wani ihu ta rungume mamin tace "nagode mami ai dama nasani ke ta daban ce, sai na auri yaya ashmir."
Nan ta tashi ta shirya cikin riga da wando damammu ta daura afterdress a kai ta yi wa mami sallama ta tafi.
A dayan part din ne ita kuma Hajiya Hafsah yanzu ta gama waya da aminiyar ta me suna hajiya salame, ta gama zugata akan wai Amira ta tafi government house, ta je tayi kwana biyu sabida zasu fi shakuwa da ashmir, wai ta dinga shishige masa a jiki a sosai, wannan ne mafitan su.
Inda Amira ta ce a bari ita sai gobe ta tafi wai yau zata je saloon tayi gyaran gashi da kuma na jiki.
GOVERNMENT HOUSE
suna kan dinning suna breakfast gaba dayan su amma banda daddy shi baya nan wai suna da meeting a nan government house din shida ministry of education na jahar.
Bayan sun kammala ne sai suka ji ana nocking hade da sallama inda Islam ta shigo cikin parlon ta durkusa ta gaishe da mummy, ta kuma gaishe yaya ashmir da kuma yaya nasir, ashmir a yatsine fuska yace lfya.
Shi kuma yaya nasir cewa yayi " ahh Islam ce yau a gidan na mu? Tace wlh kuwa yaya nasir Ni ce", sai cewa yayi very gud kin kyauta kwarai wlh.
Shiko gogan karamin tsaki yayi ya tashi yace "mummy zan dan shiga ciki" mumy tace "to son a fito lafiya."
Mummy ta ce "Islam ina yan gidan naku da Amira?"
Islam tace wlh mummy duk suna nan sunce na gaishe ku gaba daya.
"Muna amsa wa cewa mummy".
Islam tace "noor ko magana babu yau kin wani share ni"
Noor tace "sorry my sist naga kuna ta hira da yaya Nasir ne shi yasa