Follow us on social media

Showing 18001 words to 21000 words out of 29865 words

Chapter 7 - SO MAKAHO NE Rikicin Zukata by Qwinn minerhly

ni wlh am in luv, pls koda baza ki so ni ba, to pls mu cigaba da zumunci ko kuma na zama freind dinki, sabida bana san na takura Miki, kuma gaggawa ba shida kyau, pls nihal zaki saurare ni?"

Saida gimbiya ta dan nusa sannan kuma ta ɗan zurfafa tunanin ta, sannan kuma ko ba komai fayal ya iya kalamai na kwantar da hankali da kuma saukar da kai, sannan can kuma tace "ahm shikenan yayan noor babu damuwa, zamu cigaba da zumunci kafin muga abinda Allah zai yi."
Nan fayal ya shiga zuba mata godiya yana mata daɗaɗan kalamai, har sai da suka yi sallama, suka kashe wayar.

Nihal dai tana ajiye wayar ta, ta gyara kwanciyar tana ta tunanin rayuwar duniya, can kuma ta koma tunanin me siffar aljanu, wai ita Meya ke damun ta ne, kullum tunanin wanda bai damu daita ba, to meya ke damun ta? Ita da ta dauki alwashin saita rama abinda yayi mata, shine take nema ta kamu da son shi, kai Allah ma ya kiyaye na so wannan mugun me kama da aljanu, to ko dai mummy zan fada wa ayi min saukar Alkur'ani, ko gamo nayi da aljani watakil.
Gimbiya dai tana ta tunanin yaya ashmir har sai da bacci yayi awon gaba da ita, kuma shima a bacci ma mafarki sa take tayi.


Government house
Islam ce a dakin mummy tana wa mummy sallama, zata tafi sabida magrib yayi, mummy sai hada mata sha tara ta arziki take, kuma tace driver ya kaita, Islam tace "mummy wlh da mota ta nazo."
Sai mummy tace "to shikenan doughter drive safe, ki kula da kanki, ki gaida min da mutan gidan, sannan ga wannan ki saka a gaban motar ki, sabida tsaro kuma idan kika saka babu wanda zai tare ki ko da kuwa yan road safety ne.

Islam kuwa zuba godiya take yi.

Noor ce ta shigo cikin dakin mummy, da gudu tayi hugging islam tace "eyya sister kin ki kwana mana, amma ba komai ki gaida su umma da mami."
Islam tace "bazan fada ba, bayan ba kya san zuwa gidan mu."
Noor ta ce "wlh zanzo, amma next time bayan dawo wa daga school sabida yanzu jibi zamu koma."
Islam tace "to babu komai sister sai kin dawo ɗin."
Nan dai Islam tayi musu sallama tana tambayan yaya nasir, noor tace mata "yaya nasir baya nan wlh, bai dawo daga office ba, dazu da mu kayi waya, yake ce min "wlh wasu patient aka kawo mashi su uku, sunyi accident."
Islam tace"Allah sarki yaya Nasir Allah ya taimaka."
Duka suka ce "Amin"

Nan Islam tayi musu sallama sannan suka fito ita da noor, islam tace wa noor "noor raka ni part din yaya ashmir, pls zan yi masa sallama ne."
Noor tace "okay muje"

Nocking suka shiga yi suna sallama, can dai ya fito yace "waye?"
Noor tace "yaya ashmir mune." Nan ya bude musu kofa ya maza ya shige ciki, ya nemi kujera ya zauna.
Noor ce ta fara gaishe shi, ya amsa yana murnushi, sannan Islam ta gaishe shi, to Kasan cewar mummy tayi masa fada akan abinda ya mata dazu, shi yasa ya ɗan sakar mata fuska kadan yanzu, ya amsa cikin lowly voice din sa, noor tace "yaya wai tafiya zata yi shi ne zata maka sallama, bari ni na tafi, da sauri ashmir yace "no yi zaman ki lil sis"
Ita ko Islam dama tsoran sa take shi yasa tayi saurin riko hannun noor, ta marairaice fuska, tace "no sist ki zauna pls"
Noor tace to shikenan bari na kunna mana tv mu kalla, ita so take ta ɗan matsa ta ba su guri.

Aikuwa Yaya ashmir yace wa Islam "tafiya zakiyi , baza ki kwana ba kenan, Ko sabida school ne?
Islam ta fadada murmushin ta, tace "yaya wlh dama bada shirin kwana nazo ba, kuma gobe ina da lecture na safe.
Ashmir yace "alright ba damuwa ga wannan sannan ki gaida mutan gidan, ya bude wata yar drawer ya dauko sabbin yan raffers na dubu dubu ya ajiye mata, sannan ya mike ya nufi bedroom ya na cewa noor da take ta kallon wani American series a tashar mbcmax yace "lilsist idan kun fita ki kulle min kofa kinji?" Noor ta ɗago kai tace "alright broder".
Nan dai ashmir ya shige dakin sa.
Ita ko islam suman zaune tayi dan wlh ashmir ya tafi daita, kuma wlh komai nasa birgeta yake yi, ga kyau.

Noor dai sai da ta ɗan tabo ta sannan tace sist Islam ta shi muje pls, dare yana yi.

Bayan fitowar su a dakin yaya ashmir saida noor ta raka islam, har parking space din gidan sannan, ta bata kudin da yaya ashmir ya bata, suka yi sallama taja motar ta tafi.

Noor ce acikin dakin ta, tana kwance a kan haddan royal bed dinta, tana lullube da bargo.
Kawai sai wayar ta ya hau rigging.

Sai da yayi ringing kusan so uku, zai yi na hudu shi ne ta ɗaga, acan ɓangaren kuwa taji yana cewa "Assalamu alaikum dafatan kina cikin koshin lafiya sarauniya ta, kuma hasken zuciya ta, kina magana da Alh adamu rano, wanda kuka hadu dazu da rana, a wani special guy's boutique.
Dan Allah sunan ki nake son sani don naman ta dazu ban tambaya ba, wlh saving ma da nayi sai my love na saka."

Noor tace "sunana noor" a gajarce.

Yace "masha Allah nice name"
Ya shiga mata bayanin kanshi da kuma sana'a sa
"Sunana Alh Adamu Rano, Ni dan Asalin garin rano ne, amma ina zaune a cikin kano, a unguwar hotoro GRA, amma iyaye na suna can rano da zama, ni dan kasuwa ne, ina kasuwanci kayan na maza da na mata, babu abinda bana siyar wa, kama daga less, shadda, atamfa, material, gizna, yadi, kamfala, takalma, mayafai, jakukuna, da dai rauransu. Sannan ina da mata ɗaya da yaya biyu, sunan mata ta fauziyya, yaya kuma inada, ayman shine babba sai kanwar sa me suna amany.
Fatan zan samu karɓuwa a gurin ki hajiya noor, kuma wlh auren ki nake so nayi?"

Ajiyar zuciya noor tayi sannan ta nusa a tunanin ta, tabbas ta san sunan Alh Adamu Rano sananne ne kuma ya shahara a harkan kasuwanci, dan akwai wasu yaran shi da suka taba kawo masu kaya suka siya har gida wato dai ordern kayan suka yi.
Amma ita Allah ma yasa ni, baza ta iya auren me mata ba wlh."

Can dai ta nusa tace ....



Made by
Qwinn minerhly
Mr. Yusuf
❤️❤️❤️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤







*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖


*Writer*✍️✍️✍️✍️
*Na Qwinn minerhly*


_Short_ _and_ _romantic_ _story_ .





Page 65_70


Noor ce ta taho a guje, tana kiran sunan nihal...

kawai taji ta bangaje wani bata sani ba.
Ke!!! Makauniyar ina ce ke? Ba kya gani ne da zaki bangaje ni?

Ban sani ba, waya ce ka tsaya a kan hanya, Ni wlh babu abinda ya min zafi, ko yanzu ka kuma tsaya wa a hanya, sai na bangaje ka, ehe.

Duk wannan maganar, bata san da wa take ba, shima bai sani ba.

Aikuwa kamar ance su juyo, suka juyo at desame time.

Sai lokacin kowan nan su yaga ɗan uwan sa.


Shi dai yarima adnan bai san lokacin da ya zaro ido ba, ita kuma sai taji ba dadi domin taga babba ne, zai yi age ɗin big bross.

Nan fa adnan ya fara sausauta murya yana cewa "ahm ƙanwata idan baza ki damu ba, ina son magana da ke pls."

Noor ta cuno baki tana cewa "ina jin ka,"
Adnan ya ce "no ba a nan ba, mu samu guri mana mu zauna pls"


Ba tayi masa musu ba, suka samu guri suka zauna, nan dai yarima ya fara rattabo zance, shi wlh son noor yake da gaske.
Noor dai ta gano shi ne yayan nihal shiyasa taji duk kunyar sa ta kama ta, da sauri ta rufe fuska. Shi kuma ya tsaya yana kallon ta, yana murmushi.



Shi ko yaya nasir yace dawa Allah ya haɗa sa idan bada minal ba, ƙawar su noor.
Nan ya je ta same ta yayi mata sallama, har suka fara ɗan taba zance, ita ko ta saki jiki da shi, domin yana mata yanayi da yaya ashmir.
Nan suka yi ta hira har da kyalkyala dariya.



Shima yaya fayal yace tunda ashmir ya naka sa da ƙasa to gwara ya koma a yi yar gida, domin shi kar ya tashi a zero, wai shi kuma amira yake so, nan ya lallaba ya tafi gurin ta.

Nan ya je ya samu amira suna ɗan taba hira, amma ita fuskar nan ba yabo ba fallasa, wai ita ala dole ashmir ya shaka mata bakin ciki.



Tuni ashmir ya sake nihal yana cewa "servant ɗin ki ne ni da zaki wani lafe a jiki na, ko kuwa dan aikin ki ne ni? taji faɗadd'an kirji harda wani lumshe ido, to kwalelen ki, yafi karfin ki, sai my dream girl, ita kadai zata more wannan faɗadd'ar kirjin."

Nihal kuwa tuni wani tuƙuƙi ya turnike ta, aikuwa ta ɓata rai, sannan ta murguɗa masa baƙi, tace "eh ai daya ke ba ni nace ka riko ni ba ehe, me yasa baka barni na faɗi ba, ai ba jikin ka bane nawa ne, ta kuma murguda masa baƙi."

Ashmir kuwa wannan ɗan bakin ya so cafke yayi ta tsotsa kamar lolly pop sai de babu dama, nan ya ci-gaba da kallon yadda take motsa bakin, yana murmushi.

Sannan yace "kedai faɗi gaskiya yarinya, kishi ne ke damun ki, domin kinji nace kirjina na wata ne.
Ya fada yana kashe mata ido ɗaya.

Nihal kuwa kasa cewa komai tayi sabida takaici.



Yarima adnan ana can ana ta zuba wa noor hira, ita kuma sai dariya take yi, nan taji ya kwanta mata sosai, amma bata nuna masa ba, sai de ta saki jiki da shi sosai.




Yaya nasir ma tuni ya zaiyana wa minal sirrin zuciyar shi, ta ko yi na'am da shi, domin ita a tunanin ta, nasir zai maye mata gurbin ashmir, domin ashmir yayi mata nisa, nan suka yi sharing contact.



Shi kuwa fayal yana can yana tausan amira, sabida so yake ya fara tausan ta, ta hakura da ashmir, kafin ya fallasa mata sirrin zuciyar sa.


Ita kuwa islam ƙanwar amira, tun ɗazu aka tafi daita gida, yau sun shiga tashin hankali ita da mamin ta, yau sun tabbatar da yarda da boka aikin banza ne, yau mami ta fara istigifari a rayuwar ta, tana wa yar ta fatan Allah ya kawo mata wani mafi Alkhairi.



Tuni mutane suka fara watsewa a sannu a hankali, inda ashmir yace shi da kanshi zai kai amaryar sa gida.

Ita kuma minal kasancewar a gidan su noor zata kwana, shi yasa nasir ya dauke ta suka yi gida wato government house.

Itama noor adnan yace "shi zai kaita gida da kansa."

Inda fayal ma ya dauki Amira ya kaita gidan su wato Zooroad.

Nan kowa ya watse

Ashmir ne a harabar gidan sarauta, ya sauke gimbiya nihal sannan ya duƙa saitin kunnun ta, ya raɗa mata "ki kular min da kan ki, kar ki bari komai ya taba min ke, kiyi mafarkina, ki kwana da bege na, masoyi ya ta."

Nihal ce ta ce "yaya ashmir meye haka zaka wani kusanto ni, fuskar ka gab da ni kuma kai ba wani abu zaka ce min ba."

Nan ashmir ya sosa kansa yana jin wani takaicin kansa, au dama duk wannan maganar ba a fili yake yi ba, a she acikin zuciyarsa yake maganar.

Hmmm yarinya ni kike wa tsiwa ko, wlh zan kama ki, za kiyi bayani. Oya wuce gida, take care, ki gaidar min da mum.

Nan ta wuce jiki a sanyaye, ita wlh ta dauka ko wani magana mai dadi zai gaya mata, ashe wai babu abinda zai ce mata.

Sai da yaga wucewar ta, sannna ya shima ya shige motar sa, ya tafi.


Government house

Ashmir ne a kusa da Mum, yana mata tausa, yana daddanna wa mum kafar ta. Sannan mum tace "son yau ka bani mamaki fa, to dama kana son nihal ne, ko kuwa?

Hmm mum, ai itace wacce nake so, itace wacce kwanaki ta hargitsa ni, mum wai ya akayi su dad suka yanke wannan shawarar ne, kai amma dai daddy ya gama min komai mum.

Mum tace "ni dai a tunani na, ranar da suka haɗu akan maganar bikin buɗe companies, to a ranar suka yanke wannan shawarar."

Kai amma naji dadi mummy, ance biki nan da 3 months, kin ga kafin nan nayi closeup na aiki na a jamany sai na dawo nan kasa ta.

Mum tace "yayi kyau, son na taya ka murnar samun wacce kake so.

Dadai nan noor ta fado dakin tana cewa "yaya ashmir dama kana son nihal ban sani ba, kai amma naji dadi, yaya congrat. Smilling yayi mata, sannan yace thanks lil sis.


Nihal ce tayi wanka ta sa ka wani light sleeping dress, ta daure gashin ta, ta feshe jikin ta da turare, sai ta nufi part din mummy, tana zuwa tayi hugging din mummy sannan tace "mum sannu da hutawa"
Mum tace "yauwa nihal sannu, ya gajiya, dafatan kin karbi zabin daddyn ki, hannu bibiyu, dan ɗana ashmir ba duk kai ba, wlh doughter kinyi dace da samun miji nagari, ina taya ki murna daughter.

Nihal kuwa sadda kai kasa tayi bata ce komai ba. Amma mummy ta gane ta karbi zaɓin daddyn ta.
Bayan ta dawo daga part ɗin ta ne ta kwanta, domin yin bacci, amma sai tunanin yaya ashmir take yi, da abinda ya wakana a tsakanin su, Ita dai tasan tana son ashmir, idan tace bata son shi tayi ƙarya, hmm to kodai shima yana so na ne, naji harda wani cewa take care. Cike da tunanin sa bacci yayi awon gaba daita.


Haka kowanne su, ya kasance a wannan daren.


Bayan komawar kowanne su bakin aikin sa, su noor kuma sun koma school.


Can na hango noor sai waya take da adnan ɗin ta, anata soyewa, kasancewar yarima adnan, ba karamin so yake wa noor ba.


Nihal ma kuwa waya suke da yaya ashmir, sai tsokanan ta yake, ita wlh idan yayi wani abin ma har mamaki yake bata, kamar ba shi ba.


Minal kuwa chat suke da yaya nasir ɗin ta, suma yanzu soyayya suke sosai.


Alh kabeer ne ya zaunar da iyalin sa yana masu magana......


Mrs Yusuf
❤️❤️❤️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤







*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖


*Writer*✍️✍️✍️✍️
*Na Qwinn minerhly*


_Short_ _and_ _romantic_ _story_ .




Page 70_75

Alh kabeer ne ya zaunar da iyalin sa.
suna tattaunawa tsakaninsu, inda yake cewa "kuyi hakuri yaya na, babu komai rayuwar duniya ce, idan banda son kai irin na yaya, taya za'a yi gida bata koshi ba, ka kwasa ka kaiwa na waje, amma babu komai, kuma Abinda nake so da ku shine kuyi hakuri ku dangana, Allah zai baku mafi alkhairi."

Nan kuwa suka sunkuyar da kansu, Islam sai hawaye take, umma kuwa cewa tayi "ai babu komai Alh kasan ance matar mutum kabarin sa, dan ga dukkan alamu, ni dai naga kamar amira ta, ta samu mijin aure, don naga akwai wanda yake yawan kiran ta, kuma na tambaye ta, tace min abokin ashmir ne, kaga kuwa mu Allah ya musanya mana da mafi Alkhairi sai dai ko su wance. Ta fada tana kallon mamin islam."

Aikuwa bata ce mata komai ba, don yanzu ba kamar da ba, ta rage zafin kishi, sabida ita yanzu damuwar ta, Allah ya fito wa yar ta da mijin aure, duniya ta koya mata hankali.

Nan kuwa ya ƙara yi musu nasiha, yana cewa Islam ma kar ta damu, insha Allahu, Allah zai kawo mata mijin aure.


Ita kuwa amira yanzu ta saduda ta karbi zaɓin Allah, ta amince da yaya fayal, yanzu soyayya ake zuba wa.




GIDAN SARAUTA
yarima adnan na hango a fada, shi da mai martaba, kansa a sunkuye, yana ta magiya yana cewa "dan Allah daddy ka shige min gaba, akan maganar yarinyar nan, wlh ina son ta, kuma yanzu na shiryu na daina shan komai, bana bin abokan banza yanzu, pls ranka shi dade ka gafarce ni."
Cikin fushi mai martaba yake cewa "yi min shiru, kai ne babban ɗana kuma kai kaɗai ne namiji, kuma kaine magajina, amma sai dai baka da hankalin da zaka iya daukar al'ummar mu, ka gaza, kayi rauni, kuma yanzu kazo ka ce min, wani kana son yar gidan manya, wato kaje ka tozarta ni ko, ko kuma kaje ka kunya ta ni, domin muddin kaje ka watsar da amanar yarinya ai kaga ka kunya ta ni, sabida tsakanin mu da waɗannan mutanen sai dai addu'a sabida nagartattun mutane ne, dan haka ko zan shige maka gaba akan wannan maganar to sai na kafa maka sharudai da kashedi.

Cikin sauri yarima yace "wlh na yarda daddy, komai kace na amince zan yi.


Nan Mai martaba ya dinga jero masa da shuruɗan sa, shi kuma yana gyada kai, yana cewa "na amince daddy."



After three months


Nihal na hango, sanye take da wata atamfa pink nd black, wow abinka da farar mace sai tayi wani irin kyau, dama gashi amarya ce, an fara karbar gyaran jiki, sai sheki take ga wani kamshi da ke tashi a sassan jikin ta.

Waya take yi, sai wani zumburo baƙi take, tana yatsine fuska, ni fa wlh ka dame ni, taya zaka wani ce in dinga yawo da mayafi a cikin gida don kawai mun fara baƙin biƙi.

Okay, to ba zaki yi ba kenan, hmmm yarinya ki bini a sannu fa, zanyi maganin ki.

Nasan yanzu ma a haka kike babu mayafi ko? To ki jira ki ga abinda zan yi.

Kittt taga ya kashe wayar.


Ɗan karamin tsaki taja sannan tace "kayi ka gama, an fada maka ni baiwar kace.




Anty fanan ce (kanwar maman nihal) ta shigo part din gimbiya, tana cewa "ke nihal meye haka kike yi, tun dazu mijin ki yazo, amma ko shirin zuwa baki yi ba ko, to wlh ki shiga hankalin ki, domin kiris ya rage ya zama mijin ki yarinya, tashi na shirya ki, ki je gun sa."

Nan ta shi tana ta wani zumburo baki, ita ala dole an takura mata, wai to ya akayi ma yazo gidan su, dama ashe dagaske yake, daya ce mata zata ga abinda zai faru, ashe zuwan zai yi, kai yaya ashmir halin ka, sai kai.

Hangota yayi a cikin garden din gidan tana tahowa, tuni ya shagaltu da kallon ta, sanye take da wani hadadd'an material, kirar dubai, baki da orange color, yayi mata matukar kyau.


Har ta iso gun bai sani ba, turaran dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login