Follow us on social media

Showing 9001 words to 12000 words out of 52443 words

Chapter 4 - SAHRA HOT LOVE So Mai Haifar da Hawaye by habiebahlurv

31 Jul 2026

81

magana da abbanki shine ma yace inyi komai yabar komai hanuna shisa kikaji baice maki komai ."" gyada kai tayi takoma ta kwanta zuciyarta fal tsoro kenan da gaske ranar asabar zaa daura mata aure da safwa? Auren da ba kawaye , ba dangi bawanda yasani saikace auren mara asali..a hankali taji hawaye na sauko mata tanajin zuciyarta kamar zata fashe"

saboda irin zafin datake mata.

Vote me on wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv * SAHRA *

*Hot Love *

10....

It's Friday today Abj.

"Karfe shida dai2/alarm din dake kan site drawer yashiga kara , a hankali yafara bude fararen lumsassun idon sa dasuke matukar rikita y'an mata yasauke kan wata babban enlargement dake gaban mirror dinsa yasaki kayataccen murmushi wanda bararen hakoransa suka bayyana. ""My lil sis, my happiness, my everything."" Yafada cikin cool voice dinsa yana lumshe i'don, Sauko da white leges dinsa yayi kasa snn yatashi yacire white pyjamas din jikinsa yadaura towel yashiga bathroom. Ruwa mai zafi yatada cikin bathtub yashiga ya kwanta after like 20 minutes yafita daga cikin bathtub din yayi wanka yadauki wani towel yadaura yafito. Gaban mirror dinsa dake shake da perfumes da lotions masu matukar kyau da tsada yaja stool ya zauna yana shawafa, bayan kamar minti goma yatashi yanufi wani guri da'aka rubuta my wardrobe . wani abu ya danna sai kofan tayi sliding gefe kayanshi suka bayyana, daya daga cikin site din yanufa wanda suit ne jere jikin hanger dazasukai kala dari. Wani baki ya dauka yaje gurin glasses da Rolex watch wanda zasukai kala hamsin shima ya dauka yadauki takalmi bakin cover shoe wanda duk takalmansa na companyn Prada suma zasukai kala sabai'n. Rufe gurin yayi yadawo cikin bedroom din yafara shirin sa cikin natsuwa. Bayan kamar minti biyar yagama dressing dinsa yazo gaban mirror yatsaya yana kallon kansa , murmushi gefe yayi shida kansa yasan yahadu matuka i'ya makura. Farine sosea na gaske don hatta tafin kafarsa dana hanunsa baka banance haskesu dana jikinsa, yanada tsayi da faffadan kiran kirji, yanada manyan lumsassun ido hancinsa dagone gakaramin bakinsa da kowace mace zatayi burin tajishi cikin nata lol. Kara applephone dinsa dake kan gado yayi , cikin takunsa na i'sa da kassita da nuna shi din wani abu ne yakara sa bakin gadon murmushi yay expecting lips dinsa gani wanda ke kiranshi ""my happiness "" shine sunan daya bayyana ,dagawa yayi yasa kunne batare da yayi magana ba still bai bar murmushin ba. Daga dayan bangaren budurwan yarinyace mai kimanin shakaru 18 tana sanye da wasu designers English wear tayi parking dogon gashinta kafarta tana sanye cikin designer high hill"

dark blue wanda yayi set da kayan jikinta. Shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka tace

"""yayana!."" Yanajin muryanta haka yawara manyan idonsa yace ""kuka kuma!?."" Girgiza kanta tayi kamar yana gatanta tace ""am not crying Yaya...amma pls kafito dawuri kokana so sallan jumma'a yawuceka!?."" Dasauri yashiga girgiza kai yace ""ganinan fitowa yanzu!."" Daga haka yakatse wayar yasata cikin aljihun suit din na ciki yafito daga bedroom din bayan yayi scanning thumb dinsa kofar tabude. Gidan cike yake da securities da soldiers girman gidan zaikai hacter daya manyan plat gudu uku ne wanda yafi sauran biyun girma yanufa securities nata gaidashi. Palo yashiga da sallama wanda girmansa zaikai 100/100 ga manyan Sofa's dakomai na more rayuwa ba'abinda babu ciki. Tana hangosa tatafo da gudu ta rungume sa tana dariya , dagowa tayi ta kallesa sosea tace "" kayi kyau yayana, amma matsala daya rashin mata. "" sanza fuska yayi zuwa na tausayi yace ""baby basune basaso naba matan ...duk sunki aure na."" Dukan wasa takai mishi a kirji tace ""gaskiya Yaya ban yarda ba, kai ne baka sonsu..amma nasan abin yi.."" Takareshi tana kama hanunshi sukayi dining. ""To mekike shirin yi.?"" Ya tambayeta yana zama. Tsayawa tayi da saving dinshi datake tadaura hnnta saman kirjinta tace ""kawata zan hadaka da i'ta tunda kakiyin aure, dama tacemin tana sonka!."" ? Wara manyan idonsa yayi yace ""kam batada kunya nitakeso?, mezanyi da karamar yarinya yar 18 Allah yakiyaye."" Yamaida hankalinsa kan tea din da yake had'awa. ""To nidai kayi aure ko infadawa abba cewa wata tace tana sonka kai kuma kace"

"bakaso .."" Hararan wasa yay mata yace ""kifada!, ai nagirma ..bamemin n dole!."""

Kuyi hakuri yau naje unguwa ne shisa kukaji shiru.

Beenaf/beelurv * SAHRA *

*Hot Love *

11....

"Zama tayi kujeran dake gefen nashi tafara feeding dinsa bayan tayi saving nashi. ""Wow!..testy.."" Yafada yayinda takai mashi spoon daya. ""Baby amma ke kikayi breakfast dnn ko?."" Yakara fada yana karban second spoon. Dariya baby tayi tace yaa Aliyu ..bani nayiba mami ce tayi sai takoma ta kwanta don tace bcc bai isheta ba."" Cikin minti shabiyar yakare breakfast din yatashi yana goge bakinsa da tissue yace ""lil sis zanshiga ingaida mami.."" Yakare yanayin hanyar bedroom dinta, kamo hnnushi tayi tace ""yaa aliyu! Mami tace bcc zatayi inka gama shirinka kawai katafi. Naga a'lama kanaso kamakara ne yau."" To shknn zokirakani..yafada yana makaleta one site dinsa suka fice. Wasu manyan motoci kirar Bentley guda hudu aka shirya mashi na tafiya, kai tsayi gurin motar suka nufa ga securities din dazasu tafi tare nn tsatstsaye har an bode mishi wanda zai shiga. Juyo da i'ta gabanshi yayi yay mata kiss a goshinta yace ""baby zantafi, mekikeso insayo maki."" Murmushi tayi tace ""bakomai yayana, amma yau i'nafatan kasamo mana mata yanda kayi kyau dnn kamar ango.."" Tai maganar cikin zolaya . jan dogon hancinta yayi yace ""kai baby adduan ki bazata ciba, ni bayanzu zanyi aure ba, saina girma!."" Yakare maganar yana langwabar da kai kamar karamin yaro. Dariya baby tasa tace ""u a now in 33/34 years kacemin saika girma yaya?, koninan 18 nagirma aure zance abba yamin.."" Taboye fuskanta a kirjinsa."""

"Dagota yayi yana dariya yaja hancita yace ""baby bakida kunya ko?."" Girgiza kanta tayi still tana"

"dariya ""anyway.. Kikoma ciki zamu wuce."" ""To yayana ka gaida min da abbey.."" Saida yaga shigewar kafin yajuyo wurin motocin walwalan fuskanshi yadauke yadawo ai nahin Aliyun shi snn yashiga back sit yay crossing aka mika mishi news yafara karantawa. Tada motocin sukayi sukafice daga gidan bayan megadi soja yabude masu get sukadau hanyar meduguri. **waye Aliyu?. ALIYU MADU INDABO shine cikekken sunanshi, mahaifin shi Alhj Madu Indabo babban soja ne wanda ayanzu yayi ritaya , mahaifiyar shi Haj Maryam. Aliyu shine dansu na fari wanda yataso cikin gata ba'abinda yanema a rayuwar sa yarasa , saida yayi shekaru 17 kafin aka haifa mashi kanwa Aisha ana kiranta da baby. A US yayi karatunshi 1 degree 2,and3 babban doctor ne haka shine shugaban NGO na African gaba daya. Yakasance yana balain kaunar baby bayason duk wani abinda zai bata mata rea dalilinta nema yasa yabaro US yadawo nig..Sam! Mata basu damesa ba, basa gabanshi ko kallo basu ishe saba. Shekaru uku da suka wuce Alhj Madu ya auri wata mata maisuna Haj Nafisa dalilin makale mashi datayi , tashigo da 'yar budurwa gidan mai suna samha wanda batada burin daya wuce Aliyu ya aureta amma sam bataga fuskaba duk da haka bata zubda maka mantaba tananan tama kanta alkawari harsai burinta yacika. Aliyu miskiline nakin karawa baya taba fara'a i'nkaga dariyarsa to lalle yana tareda baby don ko i'yayensu basu ciki ganin fara'an saba. Mutum ne maison addini don kullum karfe uku yake tashi ya gabartar da nafila harsai yaje masjid yagabatar da sallan asuba snn yazo yayi karatun alqur'an sai gari yayi haske yake komawa bacci, haka duk ranar jumma'a a meduguri yakeyin salla a babban masallacin yayan babanshi duk sallan juma'a a canyakeyi. Wnn kenan. Karfe daya motocinsu sukayi paking a babban haraban gidan Al Sheik, gidan da girmansa yakai unguwa guda ga katon masallacin jumma'a a jikinsa. Al sheik dakansa yazo yakarbi dan nasa ya rungume shi don yana matukar son Aliyu ko cikin 'ya'yansa bawanda yakeyiwa son dayake mishi. Babban falon al sheik suka shiga wanda yaji kayan more rayuwa suka zauna . abinci kala2 aka jerawa Aliyu a dining ..alsheik dakansa yay saving dinshi yasashi gaba yanashi suna taba hira, karfe 1:30 dai2 suka fita masallaci don gabatar da sallan jumma'a. Sauri2 abban sahra yake shiri don yakusa makara sallan jumma'a , dakin sahra yashiga ya hangeta can kuriyar gado tatakuru tahada kai da gwiwa tana kuka. Hankali a tashe yakarasa yadagota ya rungume ta jikinshi yana rarrashin ta. ""Meyake damunki habibty..kifada min what's happen to u?."" Kamar wanda yazugata takara fashewa da kuka tace ""abba wai gobene aure? Taya hakan zata kasance?."" Shiru yayi baice komai ba sai rarrashin ta dayakeyi "" abba ka taimaka min.. kayi wani abu kai wllh mutuwa zanyi inna auri safwan bana sonsa!."" Cigaba yayi da shafa bayanta yace ""kikwanta da hankalinki ..insha Allah bazaki aure shiba!."" Shiru tayi sai ajiyan hat datake saukewa haka yafita"

yatafi masallaci .

Yauma zanfita innasamu time zakujini dadare lv u ol.

View wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv * SAHRA *

*Hot Love *

12.....



"Karfe biyu mutane suka fara shirin fitowa daga masallaci bayan an i'da sallan anyi addua da tunatarwa, tashi abban sahra yayi dakansa yanufi gurin alsheik . guri suka samu a gefe cikin natsuwa abban sahra yashiga kora mishi bayani akan damuwarsa harda dan guntun hawayen sa yak'ara da cewa ""ka taimaka kadaura mata aure koma dawaye ne bayan komai ya lafa sai a raba aure, ni wancan yaron ne banaso ta aura ."" ajiyan zuciya alsheik ya sauke ya dafa kafadun abba yace"" ka kwantar da hankalin ka, insha Allah matsalanka yakau..bari ina zuwa."" Yafice bayan yabada umarnin kar kowa yafita sujira shi. Bayan kamar minti talatin yashigo dawasu samari bayanshi hannyensu rike da manyan kwalaye dakuma takardu. Lokaci daya gurin yayi shiru bayan jawabi da alsheik yafara gabatarwa cikin mintu na goma aka daura auren Aliyou Madu Indabo da Sahra Yousuf Aliyou . Razana Aliyu yayi jin sunan da'aka ambata amma alsheik yay masa alamu daya kwanta da hankalinsa. rabon minti da goro akayi daga haka kowa ya watse akabar alsheik.. abban sahra da Aliyu dakuma sadiq autan alsheik mai shekaru 17. Zufane yake ketowa Aliyu ta ko'ina jin bayanin da alsheik yake mishi , bakaramin taba mishi rayuwarsa wnn aure yayi ba , shida baida burin yin aure yauzu ..to wama aka aura masa !?..wace irice!?,,,shin tanada duk qualities din da yake nema gun macan dazai aura ko bata dashi!?. Dafa shoulder dinsa da alsheik yayi ne ya dawo dashi hayyacin sa ""Aliyu ka kwantar da hankalinka, kadauki wnn abu amatsayin kaddara.. Kadubi wnn halin da bawan Allah nn yake ciki ka taimaka in bayan abubuwa sun lafa za'a i'ya raba auren ka auri wanda kake so. Kuma zan kira abban ka nai mashi bayani dakaina ."" Aliyu bai i'ya cewa komai ba sai wani abu mai daci daya tadiye yafara kokarin mikewa. Rikeshi alsheik yayi yamaidashi ya zauna yace ""ka dawo da nutsuwarka mana Aliyu !, kadawo hayyacinka."" Dago idonsa dasukayi jajaye saboda tsabar zafin zuciya yayi ya kallesu duka yace ""i'na cikin hayyacina!, kawaidai abin yazomin wani kalane,, bantaba tunanin haka zata faru dani a rayuwa ta ba!."" Gaba daya sai hausayinsa yakamasu . shafa kansa alsheik yayi yace"" nasani Aliyu amma kayi hakuri ..yanzu ga mahaifin yarinyar zaku tafi dashi a yan zunnan i:nzaku koma abuja tareda matarka zaka tafi! Kuje Allah yayi maka albarka!."" Daga haka alsheik yatashi yafice daga masjid din yashiga gidansa. Jikin Aliyu har rawa yake yagama kidime wa gaba daya baimasan abinda yakeba . d'agashi sadiq yayi suka fita abban sahra ma yabi bayansu batare da bata lokaci ba securities dinsa suka bude mota sadiq yasashi snn yay mishi sallama suka tada mota suka tafi bayan abban sahra ya zauna gefen driver don yin kwancen gidansa. Suna isowa gidan yafita yashiga da sauri harda bigewa da get , Aliyu baiko daga kanshi ya kalli gidan ba hasalima tunda yashiga motar kansa ke kasa maya bukatar ganin komai a yanzu. Abba yana shiga falon ya sauke ajiyan zuciya ganin momy bata ciki, bedroom dinta yashiga yaji tana wanka dasauri yakoma dakin sahra tana kwance kan gado idonta lumshe. Zama yayi bakin gadon yakira sunanta a hankali tashi tayi ta zauna tace ""abba!."" Murmushin yak'e yayi yace ""tashi kidauki hijabinki kibiyoni."" Daga haka yayi gaba jiki a sanyaye tadauki hijab dinta tafito inda taga abba nn falo yakama hannunta suka fita. Tunda taga manyan motocin dake kofar gidan kirjinta yafara bugawa da sauri2 tanajin wani tsoro na shigarta . ""SAHRA! Abba Yakira sunanta kai tsaye, kallon shi tayi hawaye na taruwa idonta duk tarasa ma meyake faruwa. "" kishiga motarnan kutafi!, daga baya i'nkin samu waya kikirani zan maki baya ni..yanzu ba lokaci!."" Kamar sokuwa haka tatsaya tana kallonsa i'ta duk batama san meyake"

"cewa ba. ""Kiwuce kije umartarki nakeyi!."" Jiki a matukar sanyaye kamar wanda kwai yafashewa"

"a ciki haka take takawa, wani guard ne yafito yabude mata kofa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login