Follow us on social media

Showing 150001 words to 153000 words out of 222800 words

Chapter 51 - RAGGON MIJI Angon Mai Kunya By MAMAN MAMY

26 Aug 2026

185

yafaru "

umma tai karaf tace "alhaji dan Allah ka kyaleshi karka shiga wannan maganar kaje kaji kunya kaima kasan sunada gaskiya gwara ya saketan yafi tunda beda hali "

Fahad idonshi cike da hawaye yake kallonta,
daddy yace "a, a bahaka yakamata ba, zanje nasamu abban nasu in roki yafiyarsu, ka kwantar da hankalinka kaji "

fahad de bece komi ba ya tashi yafita tun kafin yakai gida zazzabi ya rufeshi yana zuwa ya shiga wurin Aisha ya kwanta ya kudundune jikinshi na mazari, Aisha ta rude tai ta kuka ta kira doctor ba dadewa okaton yazo ya dubashi jinin shi yahau yabashi drugs da shawarwari ya fita, dakyar Aisha tasamu yasha maganin da aka rubuta mishi badadewa bacci ya dauke shi dan cikin magungunan akwai na bacci acikinsu kwananshi ukku ba bacci saboda rashin faseelat, Aisha na zaune gefenshi tai tagumi tana kallon fuskarshi duk yabi ya rame har baki ma yayi ba wata kwanciyar hankali duk harijan cin nan ya tafi 🤣yau kwana ukku ba tabi 😅,

awurin aikinshi anyi neman wayoyinshi amma switch off ba karamar asara suke yiba mutane sunyi zarya gidanshi sede baba tsoho yace bayanan, don fahad yabashi umarnin fadin hakan,


Yau akayi sadakar ukkun khalil su hjya suna cikin tashin hankali har yau, jamila duk tabi ta zube ta rame duk kibarnan ta tafi hartafi lokacin da take budurwa rama, hjy ma ta kanjame don bata bacci rashin ganin gawar nema yakara tada mata hankali, zakuyi mamaki innacemaku hjy ce kebawa jamila abinci abaki don mugun tausayinta takeji tana ganin kamar itace takashe mata miji, kullum lil khalil yana hannunta ,

bayan yan gaisuwa Sun wuce da marece sosai mamar jamila sun hadu falon hjy tafadawa hjy yau zasu koma gida kuma tareda jamila zasu tafi,

Hjya tafashe da kuka tace"dan Allah zulai kubarmin yarinyar nan awurina wlh yanzu ba abunda nake kallo naji dadi se ita da danta, ina rokon kubarmin ita tazauna anan nawani lokaci ,zuwa lokacin da zansamu natsuwa nida kaina zan medo muku ita na rokeku "

Maman jamila tace "hjy zamu tafi daita ne don amata wanka, kuma anan zata karamiki damuwa tunda har yanzu taki dena kuka ga danta dabata damu dashiba,dawainiya zata miki yawa ki kula daita ki kula da danta, gwara mutafi daita can "

hjy tace "wlh bata karamun damuwa, wanka kuma zansamu unguwar zoman da zata mata wanka, kula daita da danta bawani abu bane wurina, nide ina rokonku wannan alfarmar"

dakin yayi shiru na wani lokaci jamila na kuryan hjy kan dadduma tanajin komai hawaye suka kara zubomata wai hjy ce kuka tana rokon abar mata ita inama ace lokacin da khalil yana raye ta nuna mata wannan soyayyar ba yanzu ba,

Baban jamila yace "toshikenan hjy ga jamila nan zata cigaba da zama anan kamar yadda kika bukata, Allah yakara mamu hakurin rashin khalil "

Maman jamila tai shiru dan taso tatafi da yarta takula daita sosai ,

hjy tafara godiya "nagode sosai Allah yabar zumunci"

sukace "amin "

Maman jamila ta tashi tashiga ciki tasamu jamila dake zaune ta zauna tace "jamila zaki zauna nan din? "

jamila ta daga kai tana matse baki,itakanta jamilar tausayin hjy takeji saboda Halinda tashiga, lalle mutuwa waazi ce gasu ba sulhu sun dedeta,

maman jamila tace "to amma ki kula da kanki sosai don dinkin jikinki ya warke kuma ki daure kiyi hakuri jamila khalil de yatafi baze dawo ba addua kawai zaki rika masa "

jamila tace "to mama"

maman jamila ta tashi tafita hjya nata godiya suka tafi garinsu,


Unguwar zomar dake dora musu ruwa itace ta cigaba da yiwa jamila wanka kuma tana bakin kokarinta,

Khalil ko yanacan yana daukar darasi musa ya girme shi dan yayi 45 amma yanayin yadda yake tafiyar da rayuwa ya burge khalil, yana aiki ne a babbar ruga shima likitan fata ne, bayada wani hali sosai amma kullum dasafe se anfita da Kula da bokitai na kunu wanda ake kaiwa asibity ana rabawa patients marassashi, da yadawo daga asibity yake sauya kaya bayasa kananan kaya, kuma kayansa duk ba tazarce suna da dan shape Iya gwiwa yaiya dressing sosai anan khalil yakara daukar cause din saka hula ashe ba bakin ido ake kaita ba 😬tsakiyar goshi ake dedeta ta,

Shima musa ya karu da khalil dan yalura khalil kosu na magana yana dannar counter dinshi in suka tsagaita wani lokaci yana ganin bakinshi na motsi ,shima yanzu ya dage rikon counter yana tasbihi kuma yakara kula da mahifiyarshi akan baya don yayi mamakin dukda khalil bejin dadin mahaifiyarsa amma burinshi ya rayu dan ya kara kyautata mata bare shi tashi da yakejin dadinta ,


da drugs suka saki fahad ya farka tsakar dare dakyar Aisha tasamu yasha tea tayi iyayinta yakara shan magani yaki wai beso yayi bacci ,idanshi biyu har asuba yakara komawa gun abba,

abba beji wani tausayin shi ba yakara memeta mishi abinda yafada jiya don umarnin alhaji babba ne kuma shi bemasan su ummi sunyi wata magana da mahaifiyar fahad ba yade san tana zuwa amma besan komi daganan ba,

fahad ya koma gida ya dukunkune dan zazzabin da yakara rufeshi fiyeda jiya,

sabeer ya kira wayar fahad many times besameshi ba, tun karfe 7 yayi parking kofar gidanshi yafara knocking gate, baba tsoho ya bude mishi yaganshi tsaye baba tsoho da yasaba ganin shi yana faraa yace "barka da zuwa alhaji "

Sabeer yace "ina kwana baba, mutumen yana ciki kau? "

baba tsoho yace "eh yana ciki sede yace duk wanda yazo ace bayanan"

Sabeer ya girgiza kai yace "OK Allah yasa lpy nizanshiga naganshi"

baba tsoho yace "afito lpy "

sabeer yawuce ciki yatsaya bakin kofa ya danna door bell shiru yadade tsaye yanata dannawa sannan Aisha taji tazo tabude mishi,

idanunta jawur dan tana shan kuka akai akai ta yadda fahad be damu daita ba, ga kuma damuwa da halin da yake ciki "tana ganin sabeer taji dadi ,

sabeer ya kalleta tayi wani kala abun tausayi yace "Aisha lpy kuke "?

Aisha tace "sabeer yaya yadena kula dani baya bacci baya cin abinci baya zuwa aiki baya komi se tunanin faseelat, tun jiya baya lpy har yau nayi iya kokarina yaki shan magani doctor ma yace jinin shi ya hau sosai, yarage damuwa amma yaki,dan Allah kaje kamishi magana koyaji ya rage yiwa kanshi wannan horon"

ta matukar bashi tausayi yace "kiyi hakuri insha Allah ze dawo dede muje naganshi "

Aisha tawuce tahaye step sabeer na bayanta har cikin dakin faseelat da fahad ke kwance cikin duvet,

Aisha na tsaye sabeer yaje ya zauna kan bedside ya dan yaye duvet zuwa kan fuskar fahad yaganshi duk yayi wani wuriwuri dashi,

be wani mamaki ba don yasan yana matukar son faseelat ,sede yaji haushi yadda ita Aisha ke azabtuwa saboda da damuwarshi

Fahad ya bude ido ya kalli sabeer, sabeer yace"yanzu fahad dan an dauke faseelat shikenan Kagama rayuwa, kazauna kana wahalar da kanka da matarka, ka ki yin aiki kaki zuwa office kasan asarar da akeyi kuwa kuma kasan kamfani baze dauki asara ba "?

Fahad da muryarshi ta Marassa lpy yace "I know and I don't care ,idan har basu barmin faseelat ba mutuwa zanyi she's my life bazan iya dena tunaninta ba kona second "

sabeer yadan saci kallon Aisha don shi kanshi yaji haushin maganar yaga tana ta kallon fahad tana hawaye,

Yace ma fahad "to cewa sukai bazasu baka itaba kome? "

fahad yace "naje 2times wurin mahaifinta he's asking for her divorce later nabashi hakuri amma beyiba "

Sabeer yace "Dan Allah friend karika hakuri da yadda rayuwa tazo maka, yanzu kaga Aisha daita dakai bazaa gane marar lpyar ba, ka daure karika shan magani ko kasamu lpy "


"yanzu ka kwantar da hankalinka kabani address na gidansu zanje nasamu mahaifinta nakara bashi hakuri zan kuma nemi alfarmar yafadamin asibitin da suka kaita, kaje kadubota koka dawo dede "

fahad yafada mishi adress din ,

sabeer yace "zanje nasameshi insha Allah zanyi bakin kokarina wurin shawo kanshi amma katashi kasha magani"

fahad yace "magani baze yimin wani amfani ba faseelat itace maganin rashin lpy ta "

Sabeer ya tabe baki yace "Allah yasawwake to, bari natafi gidan nasu "ya mike tsaye,

fahad ya meda kanshi cikin duvet, da hannu sabeer yayiwa Aisha dake tsaye tana hadiyar zuciya magana akan ta biyoshi, ta bishi suna fita kofar dakin, sabeer ya juyo yace "kiyi hakuri Aisha da yanayin shi, karki bari suratan shi su dameki naga kamar baya cikin hayyacin shi, kiyi hakuri ki sa masa ido "

Aisha tai murmushin da yafi kuka ciwo aranta tace aiba yanxu nafara jin irin wadannan daga bakinshi ba, afili tace "Tom nagode Dan Allah kayi bakin kokarinka wurin samo mishi address na gidan nima zanso yaganta koya dan samu sauki "

sabeer ya lumshe ido ya bude yanajin matsanancin tausayinta yace "I will do my best "

ya juya yatafi ita kuma takoma dakin ta kwanta gefen fahad don hakanan take kokari amma zuciyarta matsanancin ciwo take,

sabeer na cikin mota yana tuki hannunshi daya akan bakinshi yana tunanin maganganun fahad,yace"kammmm amma wlh Aisha na hakuri, wannan irin so haka to ko ya zaman nasu yake? nide insha Allah bazan bari matana sugane wacce nafiso ba,"

har yaisa unguwarsu faseelat gidannasu a kulle dayake komi acikin natsuwa yafi hankali seya nufi wasu samari dake zaune can gaba da gidan bayan ya musu sallama yatambaye su kosun san inda zesa mu alhaji maaruf,suka fada mishi ai shagon shi nanan kofar keke, ya musu godiya ya kama hanyar kofar keke don ganawa da abba,














gaskiya duk group din da baa comments zandena turawa aciki kunsamu awani wuri, yan groups dina kuma zanfara removing marassa magana wasu ma tunda suka shigo basuyi magana ba kar in cire mutum yaji badadi shiyasa nafada kurika comments please,

shalele novels group
Shalele value group
shalele boost group
raggon miji fans 123

duk wace batason ganinta awaje tarika comment.
[8/23, 2:42 PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰








By






*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*




✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





7⃣5⃣





*page dinkune yan group dina shalele novels group, kai jiya kun matukar burgeni wannan ruwan comments haka, naji dadi sosai Allah yasa ku dore 😍*


Ba wuya ya gane shagon shi ya shiga ciki da sallama bakinshi,

Shagon ba kowa ciki don safiya ce mutane basu fito ba, abba ya amsa sallamar yana kallon sabeer,

Sabeeer yaja bench ya zauna acikin ladabi yace "abba ina kwana ya mejiki? "

Se sannan abba ya gane ba siyayya yazo ba yace " lpy lau dasauki "

Sabeer ya kara sunkuyar da kai yace "abba ni abokin fahad ne aminina ne sosai, nazo ne nakara baku hakuri akan abinda yayi wlh yayi nadama sosai yana cikin tashin hankali yanzu haka ma baya lafiya, Dan Allah abba amishi hakuri kar a rabasu domin yana sonta sosai kishi ne ya rufe mai ido har ya mata haka "

Abba yayi murmushinsu na manya yace "u only know about ur friend, yayanta da kannenta suna nan suma duk basajin dadi atare suke jinyar, kishi ai bahauka bane daze mata irin wannan dukan haka, don kishin ma nada kyau manzon Allah (S. A. W)cewa yayi wanda baya kishin matar sa baze shiga aljanna ba, amma shi nashi yawuce akira shi kishi gaskiya "

Sabeer yace "Dan Allah abba kuyi hakuri kudauki wannan abunda yafaru a matsayin kaddara "

Abba yace "mun dauki kaddara kam amma seya saketa "

Sabeer yace "kuyi hakuri dan Allah wlh duk gidannashi ya birkice rashin faseelat, shiba lpy matarshi ma yarshi ma, Dan Allah kuyi hakuri tunda yagane kuransa nasan nan gaba baze sake ba "

Abba yayi shiru sabeer ya cigaba da bada hakuri,

Jim kadan abba yace "nifa nadade da yafemasa tunda ya sameni batun saki kuma bani zebawa hakuri ba seyabari idan alhaji yadawo daga Niger yaje yasameshi idan ya yafemishi shikenan danni haifuwar yara na kawai nayi amma alhaji yafini son su yafini kula dasu danhaka nabar masa ragamarsu seyajira shi har yadawo nanda kwana goma "

Cikin ran sabeer yace "tirkashi yo shi yana kai kwana goman ma "

Afili yace "to nagode sosai abba Dan Allah ina rokon alfarma abani address na asibitin da faseelat take ,wlh yar shi ma kullum kuka takeyi tanason ganin antin ta atemaka Dan Allah "yayi kamar maroki,

Abba ya yamutsa fuska yace "nan ne asibitin turai room 9"

sabeer yace " nagode sosai abba ina kuma kara baku hakuri akan abinda abokina yayi "

abba yace "bakomi "
Sabeer ya mishi bankwana ya tafi,

direct gidan fahad yawuce, Aisha ta budemai yashiga yana shiga dakin da fahad yake ya zauna gefen shi ya furzar da iska ya dan bugi fahad yace "katashi muyi magana "

fahad ya yamutsa fuska jikinshi na fidda wani irin suraci yace "komi zaka fada kafada inajinka kaje baka samesu ba ko? Bashi ne maganar ba "

Sabeer yaja tsoki yace "to wlh zanyi tafiya ta in baka tashi ba nasameshi har shagonshi nabishi amma zan tafiya ta "

fahad ya tashi yana yamutsa fuska yace "inajin ka "

sabeer ya kalleshi duk yadda ya koma yace "look at you hmm, na sameshi nabashi hakuri sosai yace shide ya yafe amma seka saketa da nai ta bashi hakuri yace shi yahakura sede kajira yayanshi da yatafi Niger har yadawo kabashi hakuri in ya hakura shikenan yacemin nanda kwana goma ze dawo "

fahad ya tabe baki yace "kafin kwana goman na mutu ai ,wlh ina cikin hali zuciyata ciwo takemin kamar zata buga"

sabeer yace "kai kasani ai kana mutuwa ni kuma nasamu mata "

fahad ya wurga mai harara sabeer yayi karamin murmushi yace "eh mana ko haramunne?"

fahad ya koma ze kwanta sabeer yace "jira mana inada good news bayan bad one's nasamo maka asibitin da take da room number "

fahad yafasa kwanciyar yace "wace asibity room nawa? "

sabeer yace"turai room 9"

fahad naji ya yaye duvet din yatashi tsaye Aisha na gefe na kallon ikon Allah,

ba bata lokaci ya bude wardrobe ya dauko jallabiya ya zira ya dauki key din mota yayi hanyar fita ,

sabeer yace " kai malam bazaka tsaya muida maganar ba? ko godiya aikatsaya kamin "

fahad ya juyo yace "thanks ,kuma kafitomin daga dakin mata "ya juya ya bude kofa yafita yana sauri,

Sabeer yayi murmushi ya girgiza kai ya tashi tsaye, ya kalli Aisha yace "Allah yabashi lpy ni natafi aita hakuri lokacine "

Aisha batace komi ba, ya fita,

Koda yafita har fahad yabar gidan ya shiga motarshi ya nufi office,

fahad yayi ta sharara gudu cikin mintuna kalilan yaisa turai yana tafiya ahankali jikinshi ba kwari har yaisa kofar dakin,

nan kuma gabanshi yarika faduwa yayi knocking so biyu omer da tunda yazo duba faseelat yakasa tafiya saboda yadda ya ganta yana zaune yana bata abinci yace "turo "

Jiki mace fahad ya tura kofar dakin yana shiga yaga faseelat jikin omer ,zuciyarshi tayi mummunar bugawa, (ana nanfa me hali.....) dasauri yafara a'uziya yana korar shedan aranshi

Faseelat idonta a lumshe suke itakadai tasan yadda takeji abubuwa Sun jagule mata ba ciki ba fahad ga ciwo, kamshin fahad daya kewaye dakin yasa faseelat ta bude ido ta ganshi tsaye kamar bashi ba duk ya rame ya jeme yayi wani iri, tausayin kansu yakamata ta meda ido ta lumshe,


kallo daya omer ya mishi ya daure fuska tamau,

fahad yasamu yakara dedeta kanshi ya karasa ciki,

Ya mikawa omer hannu, omer yabashi sukai musabaha kowa ya zare nashi,

Omer ya dauki spoon yakara kaiwa setin bakin faseelat ,ta kauda kai idonta lumshe,

Omer ya kwantar da ita ya ajiye cup din yafita don in yatsaya bazaa kwashe lpy ba,


Bakowa dakin domin ummi tafita,

fahad yakarasa bakin gadon da faseelat take kwance yana kallonta tayi muguwar rama tayi fayau,

Faseelat kam taji dama da taganshi amma bataji dadin yadda taganshi duk yafita hayyacin shi ba,

Fahad Ya zauna kan bed din yanajin matsanancin tausayin ta ya dora hannu akan cikinta , yace "I'm sorry honey I hurt you, na rabaki da farin cikin ki I'm very sorry kiyafemin " hawaye suka zubomai ,

faseelat bata bude ido ba tai shiru se takara jin kewar cikinta don tunda yana 3wks yafara mata motsi,


Fahad ya riko hannunta ya rungume a kirji ya saki kuka, tabude ido tana kallonshi ba tayi shiru dan tanajin haushin shiba ne tayi shiru ne don kartai magana tayi kuka don inde tabude baki kuka zatai, ganin yana kuka yasa tafara hawaye,

irin muryar marassa lpy tana hadiye kukanta tace "hero kadena kuka,bakamin komi ba, nasani acikin tunaninka bazaka yimin haka ba,kayi hakuri kashare hawayenka banajin dadin ganinsu"

fahad yanata kallonta da jikakkun eye lashes dinsa tunda tafara magana ,yace "we lose our baby "

faseelat ta lumshe ido ta bude tace "Allah ze bamu wani, kadena damuwa "

Fahad be dena hawaye ba na tausayi da kaunar faseelat yariga yasan tana sonshi sosai yanzu dabata yi fushi dashi ba sonta yakara ninkuwa a ruhinshi,

faseelat tace "stop shedding ur tears pls, har yanzu inasonka mijina nayi kewar ka sosai, kewarka tafi ciwon jikina zafi amma na samu lpya da naganka "tasakar mishi murmushi,

Ya share hawayenshi ya duka ya mata kiss a wuya yace "I miss you too kidubeni yadda sonki ya medani ina wahala honey "

faseelat tai murmushi tace "I'm very sorry ina Princess?ina anty I hope suna lpy "

Yakai hannunta dayake rungume dashi abaki ya mishi kisss yana karajin sonta yace "Aisha tana nan lpy, princess bata lpy, yanzu haka bata gida don tsoro na takeji saboda halin da ta ganki aciki, kiyi hakuri honey wlh bansan nayi ba bansan meke faruwa ba sede naganki cikin jini "

faseelat ta lumshe ido tana tunanin yadda yashigo toilet din ya fincikota, tace"i known kadena damuwa na yafe maka since,yakamata ka kawomin amira naganta kona ida warwarewa ina kewarta da surutun ta "

Yace "zan kawomiki ita meyasa baki fushi dani ba ?"

Tai murmushi tce"yazaai na iya fushi dakai, kaine rayuwata hero ina tsananin sonka bazan iya rayuwa in babu kai ba "

Yana tausayin kansu yace "gashi zasu rabamu abba is asking for ur divorce paper ,yan uwanki duk basu son kici gaba da zama dani "

faseelat ta dan bata fuska jin abinda ke faruwa tace"bazasu rabamu ba don inasonka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login