Follow us on social media

Showing 129001 words to 132000 words out of 222800 words

Chapter 44 - RAGGON MIJI Angon Mai Kunya By MAMAN MAMY

26 Aug 2026

118

murmushi ta share hawaye tace "nagode yaya "

Ya kalleta ya fita, bawai dawoma abincin zeba dan kawai tade ci natan shi bata abinci yake ba yasamu ya gama da hjya tukun,

da shigarshi gidan hjya yaganta fuskarta kumbure ,ya duka gaisheta"hjy ina kwana? "

tace"bawannan ba saki nawa kaimata?"

yayi shiru ya sadda kai gabanshi na faduwa,

Ta daka mai tsawa "bada kai nake ba shin baka saketa ba kenan?"

yayi shiru kanshi kasa de yana durkushe, tace"wlh khalil ka rako maza duniya, sammm bakai kama da namiji ba, matarka ta zagi mahaifiyarka ka kasayin komi akai da wani ne wlh seya ci ubanta sannan yatura ta gidan ubanta"

"katashi kaje ka saketa tunda sena koya ma yadda ake nuna bacin rai "

cikin kaskantar da kai yace "hjya dan Allah kiyi hakuri wlh yarinyar nan baita kadai take ba tana da iska, tunda ta dawo dede nabata labari take kuka tanaso tazo ta baki hakuri kiyi hakuri dan girman Allah"

Hjya tai banzar dariya "hehehe he! khalil nifa na haifeka nafika sanin duniya nawa kake yanzu, to wannan karyar batai ba sakarai solombiyo bawan mata, katashi kaje ka saketa saki ukku zaka mata ringissss dan kai daita har abada wlh"

yayi shiru ranshi na zafi tabbas jamila batai ba amma he love her kuma tausayinta yake dagayin aure se saki, kuma shi yatsani ma saki kuma bayason yabawa wata danshi ko diyarshi dan baya da tabbacin zata rike shi amana tundade jamilar yarinya ce kuma tanasonshi maybe ta gyara, yanajin tsoro kar yakuma samun wadda tafi jamila hauka shide yasan yayi missing yayi missing mace me tsada,

Murya sanyaye yace "hjy ayi hakuri de aduba ajanye maganar sakinnan she's very young kuma kiduba baatashi yi mata aure ba amma akabani ita, iyayenta bazasuji dadi ba, kiyi hakuri hakan baze kara faruwa ba ,kiyi hakuri kodan cikin jikinta taci albarkacin shi Allah mafa yatsani Saki hjy "

hjya ta zaro ido "Allah ko ustaz alaramma ash sheik khalil, toni ina ruwana da iyayenta aida nasan basu yi mata tarbiyya ba da bazanje ba, tobari kaji wlh tallahi seka saketa dole karabu daita ko kazaba koni koita shasha "

Khalil ya dago fuska Yakalleta yace "haryanzu hjy baki lura ba? Baki fahimci abinda ke faruwa ba, ni bawani so na musamman nakewa jamila ba,akan wanda nakewa faseelat hjy ki tuna baya mana yakamata ace kin dau darasi Dan Allah kiyi hakuri karki matsa na saketa kinga fa siyama na wurinsu abun ze zama matsala, zanwa jamila magana zata zo tabaki hakuri kuma bazata kara ba "

Hjy tace "aikoni nadauki darasi amma nariga nagama daukar shi daga gun jamila de, kuma su sako min siyamar seme shikadai ne autan maza kai seka saketa fa seka Saki jamila dole yarinya mayya marar tarbiyya me zaai daita yo wlh danma cikin jikinta ya tsufa da se abarar dashi dan gudun hada zuria da mahaukata "

Hawayen bakin ciki ne suka zubowa Khalil ya share hawayen yace "nide hjy kimin uzuri akan wannan kimin alfarma kibarni daita,dan Allah "

Ta tabe baki ta dora hannu a gemu tace "to ita kazaba kenan to Allah yayi maka albarka kayi dede katashi kabarmin gida katafi can gun matarka karka sake dawomin anan inde ba sakinta kai ba "

Ta juya ta shige daki khalil yabita da kallo, sosai yaji tausayin kanshi yasa hannu ya share hawayen fuskarshi ya mike ya bita daki yana zuwa ze shiga da karfin tsiya tace "karka shigominnan ka koma can wurin matarka kada insake ganin ko meka ma dakai anan"

Yayi tsaye cikin rashin abunyi, itako ta shige bedroom, yayi kusan 15mnt a tsaye sannan ya juya ya fita jikinshi a mace,

Tuki yake yana neman mafita koda yaje school kasa komi yayi dole ya koma gida, ya samu jamila nata kokarin yin girki his favorite shinkafa da wake da salad da yaji,

Beko tsaya amsa sannu da zuwa da take mishi ba ya shige daki ya haye gado,

Wani mugun zazzabi ya rufeshi yaja zanen gado ya rufa,

Jamila ta biyoshi tazo tai tsaye murya sanyaye tace "yaya baka lpy? Me yasameka? Inkawo maka magani kasha sannan ka kwanta"

ya yaye zanen yanajin haushinta yace "ba dama haka kikeso ba to ga irinta nan seku kasheni ku duka ku huta "yakoma ya rufa

Ta fiddo ido waje "yaya bangane ba fa mekake nufi "


yamata banza tagaji da surutu ta koma kitchen,

masassara yake amma tunanin mafita yake tunani yayi yaje yasamu kawu manu suyi maganar yaje yabawa hjya hakuri maybe adace,

Dan gaskiya beyiwa iyayen jamila adalci ba in ya saketa daita kanta jamilar saboda tana da gaskiya itama,da wannan shawarar ya tsaya anjima ze koma dukda de yasan ba saurarenshi zatai ba amma ze gwada saa,


atanadar min barka da salla ta fan's 🤣zan zuba ido jiran jin alert ran salla jibi 🤗😁

[8/18, 4:40 PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰







By







*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*






✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
*
We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
*Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




6⃣9⃣




*wannan page din goron barka da salla ne ga duk masoyan raggon miji ina maku barka da salla Allah ya memeta mana ya amshi ibadun mu*





Jamila tayi rarrashi tayi magiya yaci abinci ya mata banza tai kuka har tagaji uffan bece mata ba ,seda lokacin salla yayi sannan ya tashi jikinshi rau ya fito jamila ta biyoshi tsakar gida,

Fuska a kumbure taje ta rike kan mashin dinshi da yake niyyar tadawa tace "Dan Allah yaya kafadamin meke faruwa in kuma tun lefin jiyanne sena sani tundazu kashigo inata bakin kokari na kamin banza"

Ya daga ido yana mata wani kallo,

Ta sadda kai kasa yace "daace kinada hankali da nafada maki problem dina amma baki dashi don haka kibarni da matsalata I will fine my solution"

Ta daga ido ta kalleshi tana nuna mishi ka tausayamin ya kauda fuska ,

Ta daga kai kurum ta sakar mishi mashin ta koma cikin daki,

yaja tsoki ya tafi masjid, bayan Sun gama salla ya wuce wurin kawu manu,

Tunda ya Kalli fuskar shi yasan da matsala yana zaune kan dandamalin gidan shi khalil na gefe a zukunne kai kasa yafara yiwa kawu manu bayani tun daga farko har karshe, daga karshe yace "Dan Allah kawu kabata hakuri maybe ta hakura kuma Dan Allah ka nusashsheta ta gyara saboda gaba,ni nasan in aka cigaba ahaka duk wacce na auro abinda zeta faruwa kenan"

Tunda khalil yafara magana kawu manu ya rike baki cikeda alajabin lamarin,

Bayan khalil yayi shiru ne kawu manu yaja numfashi yace"da farko de zanfara da baka hakuri ka kara hakuri akan nada, hjy uwace bazaa gaji da yi mata biyayya ba ,zanje na gwada saa dan kasan tanada wuyar shaani zanyi bakin kokarina na fahimtar daita kuma zan bata hakuri saboda yarinyar bata kyauta ba idan Allah yasa ta hakura shikenan "


Khalil yace "to nagode kawu Allah yasa ta hakuran "

kawu manu yace "Amin sede zan bari se zuwa dare Sannan naje wurin tan lokacin takara hucewa"

Khalil yace "nagode sosai kawu gobe zan dawo inji yadda kukayi"

ya tashi ya tafi kawu manu yanata tunanin maganar yana jinjina halin hjya da yarintar jamila,

shifa khalil be wasa da cikinshi tun akan hanya ya fara jin yunwa dan haka yana isa gida ya shige daki ya jawo tray da jamila ta ajiye yayi sarving kanshi yaci abinshi jamila nata bacci abinta ya kalleta aranshi yace,"da kinsan abinda ke faruwa kila ko barawon bacci baze dauke ki ba "

Ya tashi yasha ruwa da magani ya fita yabar gidan don karma ta farka ta ganshi tafara masa shagwaba da ta saba.


Da daddare kawu manu yaje gidan hjy tanajin sallamar shi ta daure fuska don tariga tasan maganar da yazo yi mata,

Ba don taso ba tai masa maraba tace ya shigo ciki,

Yace Tom ya shiga suka dan gaisa kowa yayi shiru bayan wani lokaci sannan yace "dama wata magana ce ke tafe dani, khalil yazo ya sameni yamin bayani akan abinda yafaru tabbas babu dadi amma Dan Allah kiyi hakuri kima yarinyar uzuri kuma yakamata ace kin dena shiga harkar yara don ba abinda ya jawo hakan se yawan damuwa dasu da kikai, dan Allah de kiyi hakuri kibar maganar sakin nan ko dan tsohon cikin jikinta taci darajar iyayenta"

tunda yafara magana hjya ta cije baki akagare take yagama yana kai aya tace "wato khalil kara ta yakai wurinka?to yayi mishi kyau manu yakamata kagane ni na haifi dana dole nadamu dashi inason kayana, batun Saki kuma sefa ya sake ta saboda ba macen aure bace duk macen dake wulakanta maka mahaifiya ai ba mace bace amma dayake khalil sauna ne yana sonta ahakan ,to ko yanasonta dole ya rabu daita ciki idan ta haifa akawomin zan rike kayana iyayenta kuma matsalar su ce"

Kawu manu ya girgiza kai yace "nasani hjy amma dukda haka bekamata kina tsaurarawa ba yakamata kisan matar shi ma tana da hakki akanshi na kulawa daita wlh hjy idan baki gyara ba kowacece ze auro haka zatayi"

Tace "wani abu ne dan naso hira da dana ko kwana yake gidana?duk wacce ya auro idan tsari na be mata ba se ya saketa ga mata nan rututu kamar awaki fara ja baka koriya seya zaba "

kallonta kawai yake yace "nasande inada kima a idonki idan har dasauranta na rokeki ki kyale yarannan tare ki rabu dasu ki hakura da maganar sakinnan"

Hjy tai shiru, ya cigaba da cewa "kiyi hakuri dan Allah insha Allah wannan baze kara faruwa ba, yara se hakuri "

Hjy tai nazari takasa manta masifar da jamila ta mata kuma tanajin nauyin manu saboda yana kula daita da yaranta,

Ta kalleshi tace "manu wlh zuciya ta bazata iya hakura da wannan abun haka ba, khalil de beyi mata ba na hakura nabarta saboda kai amma dole yakara aure nanda dan karamin lokaci kuwa"

Ya riga yasanta sarai ahakan ma yanaganin ta mishi alfarma ya bude baki yace "to Allah yasa haka shine mafi alheri ,kuma Dan Allah akara hakuri da harkar yara "

Yatashi tsaye yace "zan tafi se Allah yakaimu"

Hjy tace "to nagode kwarai Allah yabar zumunci agaida mutanen gidan"

Manu yajuya ya fita ta tabe baki kasa kasa tace "ai bazata zauna tanajin dadi tana iskanci ba aure zeyi Allah yasa asamu wadda zatai ta cin uwarta shegiya marar daa"

kawu manu kau tuni ya tafi ,yanata jinjina maganganun da sukayi "

Duk yadda khalil yaso ya share jamila kasawa yayi dan taki ko cin abinci shiko besan abinda ze taba lpyar unborn cikin dare yakasa bacci ya tashi ya sameta falo zaune tayi tagumi yunwa nacin ta cikin ta nata motsi amma taki cin abinci,

Be tsaya wurin ta ba ya nufi kitchen ya zubo abinci ya dawo, ya zauna kusa daita ya kira sunanta "jamila! "

ta kalleshi ido tafff da hawaye yace "nayi laifi kiyi hakuri kici abinci karki wahalar da kanki da yaron dake cikinki"

Jamila se hawaye tace "yaya miye kake boyemin? Hjy ce ko? ta ce ka sakeni? "

Ya girgizakai yace "niban fadi haka ba yanzu de kici abinci"

Ya debo a spoon zekai bakinta ta kauda kai tace "bazanci abinci ba, nakoshi yaya kafadamin mike faruwa "

Ya ajiye cokalin yace "wai ya kkso ne kefa kika dauko fitinar nan miye amfanin tada hankali ?ainasa kin shirya ma abubuwan da zasu faru to hjy ce taita fada nabata hakuri ta hakura shikenan kici abinci"

jamila tace "nasan I made a very big mistake amma Hakan baze kara faruwa ba Dan Allah kamanta komi kakara bata hakuri kuma "

Ya debo abinci yakai bakinta yace "namanta just eat the food"

Ta bude baki taita amsa seda ta cinyeshi tasss sannan suka nufi bedroom tai brush tana kwanciya se bacci shiko idanunshi biyu yanata tunani,


Da safe lpy lau ya nunawa jamila ya tafi school be je ko gaida hjy ba, anayin breakfast ya tafi wurin aikin kawu manu ya sameshi, kawu manu yafada mashi yadda sukayi da hjya,

Yace "inaga kai auren shine maslaha tunda ta hakura da maganar sakin kuma kanada halin yin auren "

Zufa tarika karyowa khalil ya cire hularshi yafara fifita cikin tashin hankali yake cewa kawu manu "kawu da akwai matsala wlh nide harga Allah bazan iya rike mace fiyeda daya ba saboda ba nauyin ciyarwa ne kadai ze rataya awuyana ba Dan Allah ina rokon kasake koma wa ka rokar min ita kai kadaine yanzu Wanda zaka taimakamin"

Kawu manu yace "to sede nabaka hakuri khalil dan bazan iya komawa wurinta ba kariga kasan halin mahaifiyar ka "

Khalil yayi shiru kanshi kasa yanata hada zufa,

Kawu manu yace "kaje kamata bayani kila ta fahimceka "

Khalil yace"to nagode sosai kawu ni zantafi agaida mutanen gida"

Ya tashi ya tafi, tashin hankali kenan bema san ta ina zefara ba, memakon ya koma school se ya nufi gidan hjy, da shigar shi ya tarar tana baccin tohon gira ze juya ta bude ido "kai dogore dawo nan "

Khalil dake ta zufa kamar ya hadiyi kwado ya dawo ya zauna kasa ,

hjy na kwanciyarta tace "ainasa bazaka zo gaidani ba tunda zan rabaka da matarka,shine kaje kakai karata shi kawunnaka yafada ma sakona ko? "

Khalil ya daga kai tace "to dole kai daya ko ka saketa ko ka kara aure,

Dubara ta rage taka tashi kabarmin gida marar tunani, kwana biyu nabaka kagama duk shawarar ka"

Khalil yayi zaune dakyar ya samu yace "Dan Allah hjy kiyi hakuri wlh bazan iya auran mace fiyeda daya ba "

Tace "shikenan hakan yafi sekaje ka Saki waccan bakar dagar"

Ya dago ya kalleta yace "amma hjy.... "

Ta katse shi "amma me? Amma baa kyauta ma iyayen ta ba ni ta kyauta min? ni wlh khalil se naita ganin kamar anmin musanyar ka har atabani ka kyale, toni bazan bari ba katafi ka saketan tunda kai raggo ne baka iya auran mata biyu "

Ya buda baki ze magana tace "get out from my house karka sake zuwamin wawa marar kishin zuci"su hjy antuno school 🤣

sumi sumi khalil ya tashi ya fita ta bishi da harara tace "idan ka saketan zan nemo maka ustaziya wadda ko hoda bata shafawa in zata fita saboda tsoron Allah 🤣ai akwaisu "


Haka khalil ya koma school yanata tunani, sama sama yake komi beiya tunkarar amininshi da maganar ba,

Wan safe yakasa zuwa gidan hjy, hjy nata zuba ido har dare shiru, ta cika tai fam,

wansafe khalil bejeba again kuma befadawa jamila komi ba sede duk ya rame saboda zullumi da tunani bakomi ya hanashi zuwa gidan hjy ba se tsoron abinda zefaru,har dare shiru hakurin hjy yakare kodayake dama bashi gareta ba,

Aka kara kwana arana ta ukku karfe 9:00am ta shirya ta nufi gidan khalil,

ta shiga tanata kwada sallama da karfi,

Jamila dake bacci ta fito hankali tashe jin muryar hjy,

hannun hjy akugu tabita da kallo tundaga sama har kasa turtsetsen cikin jamila yayi sororo a tsaye,

Jamila ta sunkuyar dakai tana hadiyar wani miyau me daci,

Hjy tace "ke dan ubanki me kike jira kinbi kin manne wa dana sekace shine ubanki ki maza ki dauko tsummar hijabinki kibar gidannan yanzunnan mahaukaciyar banza da wofi "


Jamila ta zube akan gwiwa tafara begging" Dan Allah hjy kiyi hakuri wlh sherin shedan ne bazan sake ba "


Hjy tace "wato dagaske da hankalinki kika jemin kikamin dibar albarka, to dan ubanshi shedan din daga yau baze kara Saki kiyi wani abu da auren dana ba maza tashi ki dauko hijab kibar gidannan ki nufi kauyenku"

Jamila tasaka kuka "hjy kiyi hakuri dan girman Allah "


Hjy tace "ai sekiyi "
Fuuuu ta shige dakin su ta dauko mata hijab tadawo ta tillamata ta wurga mata 1000 tace "aje can aiwa tsoffi badeniba "

Jamila tana kuka ta dauki hijab din tasaka tasa slippers ta dauki kudin ta fita daga gidan,

Hjy taja tsoki ta saka keys ta kulle gidan takoma gida tana ta banbami ita kadai,


2:pm khalil ya dawo cin abinci amma gida gar kame da sabon padlock ,yayi shiru yanata tunani gabanshi inba faduwa ba ba abinda yake yi hakanan zuciyarshi tabashi hjy takora jamila gida,

Ya dauko waya yayi dialling number jamila tana ta ringing baa dauka ba , ya gaji ya tada mashin ya nufi gidan hjya,

Ya sameta tana ta hidimar ta hankali kwance,

Tana ganinshi ta tabe baki tace "se yau mijin jamila? Kamanta kana da uwa ta hakkin matarka kawai kake shasha to ni na korar maka ita tana gidan ubanta yanzu haka "

Khalil kamar ze kuka ya samu wuri ya zauna ya dafe kai da hannu biyu,

Hjy ta cigaba da aiyukanta tanayi tana fada,

"wawa kawai mutum kamar ba namiji ba yayi ta abu kamar mace ina amfanin me irin zuciyarka"

Can sede taji kukan khalil, ido waje ta leko daga kitchen taga lalle kuka ne yake, tafita tasameshi tai tsaye kanshi tace"kuka kakeyi kenan saboda ankora ma mata " ta dauko keys ta jefa mai tace "gashinan kaje ka dawo daita tunda tafini agunka, katashi katafi ka dawo daita tunda abun yazama ciwo sena tashi neman maka magani tunda ko wata tsigagga ka auro haka zaka mutu kanta"

Khalil be dauki keys dinba yatashi ya fita daga gidan,

Hjy tabi bayanshi da kallo "kai Allah ya wadaran naka ya lalace mtswww"


Khalil betsaya ko daukar mashin ba ya nufi tasha ya shiga motar batsari tana cika suka dauki hanya


fahad jinya biyu yayi gata faseelat gata Aisha ,faseelat abunma gaba yake karawa memakon asamu sauki,

Yau suna zaune a main palo faseelat tafito tana yamutsa fuska hannunta dafe da kanta , tun a bene yaji kamar yaje ya daukota ,

Saboda Aisha nagun ya danne ya zauna har taiso besan lokacin da ya mika mata hannu takama tazo ta zauna gefenshi, shi yariga yasan yafi ma yawan taba Aisha akan faseelat sede dukda haka yana kiyaye maganar aishan dan ta zauna lpy, ya saci kallon Aisha dake wa amira tsifa tacika tai fammmm fuska daure,

Fahad beko kara kallonta ba ya cigaba da aikinshi a system,

Faseelat ta kalli Aisha tace "Dan Allah anty kiyi hakuri wlh dan banajin dadi ne shiyasa ban sauya mata wani kitson ba amma dama inada niyyar zuwa gobe nai mata "dayake tunda tazo gidan ita ke mata,

Aisha tace " karkidamu"atakaice


Faseelat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login