Follow us on social media
Showing 219001 words to 222000 words out of 222800 words
bayanan da akagabatar nagode"
Alkali yayi rubuce rubuce yace"kotu ta daga kara se nanda 3days"
Akatashi mommy nata danasani suka tafi gida ,
Fahad ko besamu yaje ba don baze iya jura ba,
Tunda akamedasu oteka prison sukarika dirkar die hard seda aka sauya mai wuri,
Bayan 3 days aka dawo alkali ya tambaya ba me abun cewa ,
Ya dago ya kalli Su oteka yace"shekara nawa kukai kuna wannan aikin?"
Oteka yace"may be 10yrs kuma mu Sana'a ce mukeyi bawani abuba"
Alkali ya kura mai ido yace " zaka iya gane mutum nawa ka kashe?"
Yace"yawane dasu ai kila sunkai 50 ko 60 hakade"
Alkali yace"subhanallah"
"Nasani kowa yasani acikin bible ba inda aka halatta wa cristian kwace da kisan juna da ketawa mata haddi da nakasa masu lpy kuma bawani littafi naku dayace haka ,kuna matasa kuna da karfi ku tsaya ga fashi da makami a matsayin Sana'a ,bawani littafi acikin littattafanku dayace kuyi haka ,kun aikata laifi kuma kunsan laifine kunada hukunci kamar yadda sharia ta tanada"
Ya kalli takardar gabanshi da yagama tsara komi yagama nemo komi yace "sakamakon hayar yanfashi da mommy tayi Wanda hakan ya sabawa sharia kotu ta Yanke mata hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu da horo me tsanani zata biya kudi nera millions 20 ,itako cellular zatayi 10yrs a can domin itace me kawomasu costumers kuma ta turasu sunyi fashi agidan kishiyarta tasa suka kasheta,zata biya kudin da suka kwato da kudi 5millons abawa yanuwan matar ,oteka ,tiger,die hard sun dade suna aikata aika aika ,sunshiga gidaje da dama sunyi barna zasu biya kudin da suka amshe agidan kuma kotu takwace duka kudinsu,sannan kotu ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar bindigewa"
Su oteka suka fara raba ido jin mutuwa kusa,
Die hard ya fashe da kuka yana begging "Dan Allah kuyi hakuri wlh natuba inason musulunci Dan Allah kubarni na rayu"
Alkali yace"sakamakon die hard ya fadi gaskiya beba kotu wahala ba ya kuma yi ikirarin yanason musulunci bazamu hanashi damarshi ba don haka kotu ta masa sassauci ta yanke masa hukuncin zama gidan yari na tsawon rayuwarsa batare da horo ba"
"Zaa iya daukaka kara kafin nanda 2weeks"
Ya buga guduma aka mike mommy nata kuka cellular die hard kuka Su oteka sunata raba ido da alamu zuciyar bazata sauko ba,
Su ramlat suka rungume mommy dazaa wuce daita suna kuka zasu rabu da mahaifiyarsu,
Fahad da yasamu yazo se hawaye yake mommy taje ta rungumeshi tana kuka tace"kuyi hakuri ku yafemin"
Sunata kuka akajata akai prison daita,
Samm fahad yakasa natsuwa hukuncin be masa ba ya daga karai cikin kwana ukku kacal ,
Umma taita fada shide he can't forget mommy alheri ,haryanzu gidansu faseelat ba natsuwa,
Bayan 7days akashiga wata kotun nan kuma aka yankewa mommy hukuncin 1yr ko tabiya30 billions ,
Hakan yayiwa fahad dadi anagamawa suka rungume mommy shida kannenshi sunata kuka,
Umma kam taji haushi aida yabari taje taga rayuwar gidan yarin da yadda take takara tsoron Allah,
Bayan 3days fahad yabiya kudi aka sako mommy tadawo gida tana jin son fahad fiyeda yaranta,
Aka biya fahad kudinsa 50millions dollars,
Aka amshe kudinsu oteka aka bindigesu ,die hard kuma yana prison yayi joining musulunci yana cigaba da istigfareee,
Sabeer de yasamu aiki a marocco ,daddy ya samarwa fahad aiki a abuja awani diamond company amatsayin accounter donme matsayin ya rasu shi yasamu,
Mommy kullum kunyar fahad takeji abunda ta masa ganin bayanunawa yasa ta saki jiki itama,
Jarabawar data samu fahad tazama alheri agareshi domin kudin da yarasa ya samu linkinsu gashi yasamu wani aikin Wanda yafi nada.
[9/13, 2:21 PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
9⃣5⃣➡➡🔚🔚
*dedicated the whole book to sister Zulaihat Rano* kullum bazan dena miki addua da godiya ba ,sister nagode da kaunar da kike nunamin tun fara jagolgwalo na kike nunamin so , ke kika gogar da rubutuna da nakeyi da kara zube ,kika nunamin kauna har nadena novels baki dena kulawa dani ba ni bansan ta yadda zan nuna miki son da nike miki ba sede in fadi kawai ,kinfi karfin 1dedicate sister kome na zama sanadinki ne insha Allah bayan wannan akwai wasu dedicates din soon or later bazangaji dayi miki dedication ba nagode Allah yakara miki basira da daukaka yakara lpy da nisan kwana i can't forget you in my life❤
*Manzon Allah (S.A.W)yace :-aikin da Allah yafiso shine aikin alheri da aka dawwama anayi komin kankantarsa*
*(S.A.W) yace idan dayanku yayi nuni zuwa ga aikata alheri yanada ladar wanda ya aikata*
Masu tambayar miye faseelat kesha yakesa fahad ihu to ku nemi maman mujaheed me kayan mata zata baki abinda ba ihu ba har kuka seyayi😉 ga numbern ta 08066726866.
Shawara gareki yaruwa Dan Allah arika nunawa miji ana enjoying abun wani komi zakisha inde baki nuna kinji dadi kika kundume GU daya ba umm ba umm bazeji dadi can can ba,a daure adan rika nishinnan😉irin kinajin dadin nan🙈hakan nakara rikitasu shawara ce👌
Don haka suka kwashe suka koma abuja da zama ainda yafara gudanar da aikinshi lpy lau,ya dauki nanny's masu kulada babies.
Da dare ne Suna kwance suna fira jefi-jefi tana kwance kan kirjinshi tana wasa dashi ,yanata lumshe ido yace"ummuna inason nayi wani aikin alheri "
Tace"namefa?"
Yace"inason fidda graduates students zuwa waje karatu domin seda ban lpy nagane Nigeria muna bukatar doctors inaso kudinnan nabiya ma akalla mutane50 school Su karo karatu but ya kk gani miye shawaranki?"
Faseelat tai murmushi me sauti tace"kuma in kai hakan ba karamar lada zaka samuba amma idan akwai abinda yafi wannan lada ai nasan zaka zabeshi kabar wannan"
Yace"eh sosai"
Tace"Nigeria akwai likitoci wasu basa samun aiki domin yawansu kuma government na tura wasu kara karatu wasu ma suna biyan kudinsu su karo "
Ya zuba mata ido yanason yaji inda ta nufa ,
Takara kwantar da kai jikinshi tace"Nigeria tana daga cikin jerin kasashen dake fama da talauci ,akwai marayu wadanda basa da iyaye akwai miskinai wadanda basu da hali akwai mata tsoffi da yara marassa aikinyi akwai likitoci marassa aiki akwai students da sunada degree,nce, PhD,diploma and others kuma basuda aikinyi ,suma suna bukatar temako sosai"
Taja numfashi tace"ni aganina karin ilimin doctors bekai yin jerin wannan aikin ladan ba ,su wannan ta bangaren lpy kadai zasu temaka sukam wadannan an temakesu an ceto rayuwarsu daga kunci da halaka"
Tai shiru tace"I don't know ko kudinka zasukai amma nasan kanada friends da yawa kuma they will help kuma nasan ana bude foundation anasamun temako"
"Meze hana kagina orphanage house kasa yara hamsin din aciki karika kula dasu ka dauki yan aiki da masu kula da lpyarsu da masu koya musu karatu dasauransu kaga ka temaki jamaa da dama"
Yayi murmushi yace"meyasa kika ce hakan yafi wancan lada?"
Tace "inka lura wannan din mutane da dama zasu amfanu dukda doctors dinma hakane amma senaga kamar wannan din yafi kuma suma kaga zakai supensoring karatunsu kaga har doctors din zaa iya samu,akwai wani hadisi da manzon Allah (S.A.W)yace dani da mekula da maraya haka zamu kasance a aljanna,seya nuna danyatsan shi na tsakiya da manuniya,akwai wani hadisin da wani yakawo mishi kara yace zuciyarshi ta bushe me zeyi zuciyarshi ta yalwata,se manzon Allah (S.A.W)yace kanason zuciyarka ta yalwata bukatunka Su biya seyace eh se yace kashafi kan maraya zuciyarka zata yalwata bukatunka kuma zasu biya,bayannan kwanaki naji wani waazi na sheikh gombe yace agarin makka wani bawan Allah yayi mafarki da manzon Allah (S.A.W),manzo yace mishi yaje unguwa kaza gida kaza yafadawa megidan shi dan aljanna ne,se mutumin beyi abinda yasashi dinba bayan kwana biyu se yasake yin similar mafarkin manzo yace meyasa bakaje ba ?kaje kafadamishi shi dan aljanna ne,se mutumen ya tsorata seyaje yasamu wani babban malami yafada mishi se suka kara duba siffofin manzo dake rubuce alittafi se suffofin suka zama iri daya da Wanda mutumen yagani kuma dama shedan beiya siffantuwa da maaiki,se suka tafi Neman wancan mutumin dansu fadamai sakon maaiki ,da sukaje se suka samu mutumin driver taxi ne ,bayan sun fadamai yayita murna yana godewa Allah se suka tambayeshi shin meyake gani yakeyi daya kaishi wannan matsayi?se yace banayin komi se farilla domin nakan wuni nakai dare ina aiki dana dawo gida ina hutawa ne kuma bana azumin nafila sede akwai abinda nakeyi da nake tunanin hakan shine sila,akwai wani makwabcina Allah yamishi rasuwa tunda yarasu nake daukar dawainiyar iyalanshi nakan raba musu cefane dede da iyalina yace nawa diyarsa daya aure yanzu bikin wata yataso yace bugabugar danake tayi shine kudin da zanyi mata kayan daki"(Allah yasa nakawo labarin dede nadan manta wani abun maybe)
Fahad yace "Allahu Akbar"
Faseelat ta cigaba da cewa "kaga hadisin can nafarko dama manzo yafadi hakan,shine nake maka kwadayin hakan mijina domin inason kasamu alheri duniya da lahira ,idan har akwai yiwuwan yin hakan nakega yafi wancan din"
Fahad ya zagayeta da hannu ya matseta jikinshi sonta nakara gauraya duk ilahirin jikinsa da jijiyoyinsa tabbas duk macen da zata rika nuna ma hanyar samun aljanna abarso ce abar riritawace ,
Ya lumshe ido ya bude yace"zeyiwu mana don inada kudin da zasuyi wannan ginin kuma su biya maaikata sede bansaniba anan gaba ,insha Allah nasan Allah baze hana abinda zasu cigaba da rayuwa dashi ba ,koda komi nawa ze kare zan cigaba da kula dasu insha Allah ,Allah yasawa abun albarka de ,nagode sosai ummuna shiyasa kullum kike kara mallake zuciyata "
Tai mishi kiss tana murmushi tace"thanks"
Yace"zanyi shawara da bro amma awane gari kike ganin yafi ?"
Tace"anan ko tunda anan kake zaune zakafi kulawa dasu in kuna wuri daya"
Ya mata kiss Yace "thank you ,kimana adduar cin nasara da temakon Allah akan abun"
Tai murmushi me kara mata kyau tace"I will surely did insha Allah "
Ya mirginata kasanshi ya fara sucking lips dinta,
Bayan satittika aka daura auren mommy da justice saboda masoyan sun sake kullewa,
Bayan watanni fadilar ya omer ta haihu ta samu boy,lady ta haihu tasamu girl,saffiya girl,salma boy,jamilar khalil ma ta haihu tasamu girl ,radiya boy shi kuma sabeer yafison girl saboda amira se fatouma ta haifi girl yana murna yasa mata amira,
Alokacin ne kuma Su faseelat suka daga saudiya sukayo hajji ta yaye yaranta sunada 1yr5month,
Bayan kwana biyu da suka dawo fahad yafita aiki yadawo da wata amota ,
Faseelat tafito tarbar shi taganshi da wata tai tsaye yafito yabude wa waccan kofa tafito yarinya ce yar kimanin shekara 17 ya amshi jikkar hannunta yanata sakarmata murmushi tana meda mishi,
Faseelat da jitakeyi kamar taje ta shake yarinyar idonta jawur ta kakaro murmushi tace "bakuwa garemu? kishigo"
Tayi gaba suna baya fahad nata kallonta yana boye dariya,
Suka shiga falo tawuce gun fridge ta dauko ruwa da cup ta ajiye kusada yarinyar ,
Takoma ta zauna tanata kallon fahad dake ta kallon yarinyar itakuma kanta kasa,
Faseelat ta samu tace "sannu ko banganeki ba?"
Fahad be kalleta ba yace"budurwata ce itace wadda nakeson aure very soon"
Zuciyar faseelat na harbawa take kallonshi idonta jawur,
Yarinyar tace "ina wuni anty?"
Faseelat tace "lpy lau ,namiki murna da samun kamarsa Allah yasa alheri "
Ta tashi ta haye sama dasauri jikinta na rawa,fahad yabi bayanta da kallo,
Tana shigewa ya kalli yarinyar yace "u see matata tanada kishi sosai amma see yadda tai controlling kishin dukda kinaganinshi azahiri don haka kije kibawa mijinki hakuri"
Yarinyar diyar manager dinsu tace"uncle nifa bazan iyaba yazomin da wacce ze aura wai dasunan gaisawa don yaraina ni"
Fahad yace"nayi zaton da kinga wannan abun dayafaru zaki koma gun mijinki amma baki dauki komiba I want you to come back after some time matata zata koyamiki rayuwar aure don bakiiya komi ba"
Tace"OK amma karoki daddy kar yamedani plsss "
Yace "u most go back to ur matrimonial home kitashi kitafi tunda bazaki fahimta ba"
Tatashi tafita tana turo baki yaja tsoki why ma ya kawota donyin example da matarshi yabata mata rai hakanan,
Yatashi ya haye sama yana shiga dakinsu batanan yawuce na babies yasamu tana tura kayansu a trolley yana gumtse dariya yace "ina zaki da kaya haka ummuna?"
Tai banza tanata hawaye yaje ya rungumeta ta janye jikinta tazo zata tafi yariko hannunta ta juyo tana kallonshi yace "haba sayyada miyayi zafi haka?"
Ta wurga mai harara tace "kome ma gidanmu zantafi seka kawo ita wacce kakeson dame tafini dazaka je kadaukota bayan kasha yimin alkawari cewa bazaka kara aure ba bazakamin kishiya ba ,tafiya ta zanyi "
Ta cire hannunta tafita ,har garden tai tsaye tana kwalawa yaran kira "abdurrahman ,abdullah ,Aisha amira habiba kuzo mutafi unguwa"
Suka rugo da gudu wurinta ta kama Aisha datafi jidaita tafara tafiya Sega fahad bakin motar ta yanata kallonta yana dariya,
Tazo zata shigarda yaran ya zagaye ta yace "ummuna let me explain plsss"
Tace"just leave me base kace komi ba"
Ya fiddo ido yace "yanzunnan kuwa nagama yabonki ina cemata baki fiddo kishi fili Ashe jira kikeyi tatafi"
Tace"bansaniba "
Ya mata kiss yana murmushi yace"diyar manager ce maybe bakisanta ba amma kinsha zuwa gidansu ,tanada aure mijinta ne zekara aure bayan 5month da bikinsu shine yakawo matar gaisheta itakuma taita dukanta shine yakorota kuma daddynta yace dole seta koma itakuma bataso shine tazomin da maganar shine nace tazo taga mar atussaliha"
Faseelat tace "ita maratussaliha batada kishi ?dazaka rike mata jaka agabana kabude mata kofa kanata mata murmushi "
Yanata dariya yace"amin hakuri jinin jikina ,kisha kuruminki kekadai ce insha Allah cos ba abinda zesa nakaro aure bayan nasan wuyar da mukasha abaya I know my self bazan iya boye sonki ba shiyasa barinshi yafi kuma ni kallon matan nake ma kamar maza ke kadaice mace "
Ta harareshi taturo baki,yace"tunda kunyi shirin fitar mutafi nakaiku wani wuri
Tace"wata exam dince canma ko?"
Yayi dariya yana dariya yace"no no wani wuri nace kede just enter ki kalleni kurum"
Yabude motar tashiga sunata tafiya basu zame ba se wata sabuwar unguwa,bakin wani rafkeken gate jiki da wani rubutu yanata danja anrubuta *ummuna charity living house*
Ta bude ido da baki tanata kallon wurin tana murna basu jimaba aka bude masu gate suka shiga katon wurine fangameme da bene hawa hudu da different sections aciki,
Suka fito tanata kallon wurin tana murmushi tace"masha Allah wuri yayi kyau sosai Allah yatabbatar da alheri ya tsare yakuma temaka "
Yace"amin amin muje muga ciki yadda yake"
Suka shiga suna duba wurin ga school ga small despensary,ga masjid mata da maza ga wurin wasa ga garden duk aciki ga bangaren staff , acikin benen ko dakunan dalibai duk room ze dauki mutum hudu,bangaren mata daban na maza daban abun gwanin shaawa,
Suka gama dubawa tanata addua suka koma gida sunata farin ciki,
Ba jimawa akafara daukar maaikata bayan anyi sanarwa agidajen radio da TV kuma kafin adauke su ana musu gwaji daga malaman doctors din gates man,metrons dasauransu,
Seda akagama daukarsu sannan aka bude kawo yara kananu da matasa under 12yrs,
Ba jimawa suka cika maza da mata wadansuma iyayensu na raye suka kawosu danbasu iya rikesu guda hamsin din akadauka dukda wurin naiya daukar dari da hamsin,
Su sabeer ,Hussein hassan rayyan dawasu daga cikin friends sune jagoran tafiyar ,wasu friends na temakawa kuma sunada foundation Wanda hardaga ketare suke samun temako,
Sosai fahad ke kula da yaran Wanda wasu yara dasuke da iyaye da dama basu samu hakaba abincinsu suturarsu karatunsu komi normal ,
Faseelat kuwa takan kai musu ziyara time to time wani lokaci da safe koda rana ko dare abinda takeyi idan taje takan lura dame damuwa tajashi jiki tana tambayarshi har taji bata tafiya seta sasu farinciki kuma takan yi order na kayan makulashe taraba musu hakan yasa da sunji zuwanta zasuyi ta murna suna ihu sosai sukeson ta,
Bayan wani lokaci me tsayi yaran sun wuce matakin secondary suka tura wasu karatu waje wasu kuma anan Nigeria ,komi nata tafiya lpy lau sede anasamun wadanda suka mutu se akawo wasu madadinsu yanzu de abun yabunkasa domin kullum arziki keta shigowa fahad har shima yayi maaikatarshi ta kanshi suna businesses very successful, shiyasa yakara fadada wurin yakuma daukar wasu 50 suka koma Dari ,
Su faseelat an zama hajiyoyi makka duk shekara umara duk time da akaso gata itama yabude mata hannu takan temaka wa marassashi da gajiyayyu shima inde kaje wurinshi to kukan ka yakare,
Mommy ta rasu ,Umma ma tarasu desame day da mijinta don yatashi yaganta amace brain dinshi takasa dauka shima yafadi ya mutu,
Abba ma yarasu saura Ummi hjyar Khalil ko tana raye Khalil nata kula daita ta tsofe tuguf yanata samun lada shima yazama shirgegen alhaji yana tareda jamilarshi tanata haifamai yara,
Bayan shekara 35 su faseelat an manyanta anzama babbar mace fahad tsufa yazo ,ummi ma ta rasu hjyar Khalil ma ,haihuwar faseelat biyar takarayin yan biyu sukazo ba rai setayi Farhana,da musab se auta Mohammed suna kiranshi habib, dukansu sunyi aure saura auta Habib don duk dawuri ake musu aure ,da Aisha da faseelat cikin orphans suka aura amira tayi aure madeena,mazan kuma suna nan Nigeria daya lauya daya midwife da matansu da yara,farhana ma tai aure bata haihuba itada musab ,
Yau jumaa katon makeken falo ne da seya dauki mutum 60 Wanda cikin orphans dinsu wani yagina musu tareda hadin kan sauran yara ,cike yake da jamaa sunzo yiwa ummuna barka da jumaa sunzo sada zumunci ga drinks nan birjik awurin ,anata nishadi faseelat da eye glass dinta makale da ido haka fahad,
Anata firarraki anata harkoki Sega Habib ya sauko daga sama yanata sauri,
Diyar saudat tanabin bayanshi idonta duk hawaye ta rikeshi ya juyo ya dauketa da mari,hankalin kowa yakoma Kansu ,
Yaja tsoki yabar gidan gabadaya tabi bayanshi tana kuka,
Faseelat ta girgiza kai itade bata gane wagga soyayya tasu ba ,yanata bata wahala kuma ansa masu rana,
Bayan ishai kowa yatafi su faseelat sungama dinner suka zauna fira main falo habib na kwance yanata kallon pop na dakin ko abincin kirki beci ba,
Faseelat ta kalleshi tace "habib kadena dakar musu diya inde bakasanta shikenan amma kadena wulakantata haka"
Fahad yace"in bayason ta waya keso ?yarinya nabinshi yana wulakantata sekace ba yaruwarshi ba"
Habib ya tashi zaune yace"ummuna nifa temaka mata kawai zanyi bawani so nake mata ba ni da son raina ne nafison farar mace kamar balaraba me aji da takama bawacce kebin namiji ba tana kuka yasota"
Faseelat tace"hmmmmm !!!"wai me Jan aji me kyau bame ilimi ko addini ba,
Fahad yace"to ita yesmeen baka sonta kenan?"
Ya koma ya jingina da seat yace "temakonta nake abbu amma ai nafi ajinta kudube ni yadda nake mana"
Faseelat da fahad sukayi