Follow us on social media
Showing 147001 words to 150000 words out of 222800 words
a kirji yana hawaye,
gidansu umma ma duk basu cikin walwala har 10 tayi umma taji bata iya bacci ta tashi ta nufi dakin lady, Lady na waya da Hussein dasuke matukar son juna yanzu, umma ta shigo lady takashe kiran ta meda hankalinta kan umma,
Murya sanyaye Umma tace"waikinsan gidansu faseelat ne? "
lady tace "eh nasani"
umma taji dadi tace "yawwa kitashi kisa hijab can zamuje yanzu bari naje na dauko mayafi na"
ta juya tabar dakin, Lady ta tashi ta dora after akan kayan baccinta tafito, umma tafadawa daddy suka tafi gidansu faseelat,
suna zuwa sukai parking suka fito suka tsaya bakin kofa sunata knocking, can zuwa abulkhair ya bude gidan unguwar dun dum dan babu nepa, sede hasken farin wata,yagade mata ne yayi tunanin kawayen ummi ne,
abul yace "inawuni "
Umma tace "lpy lau ya me jiki an sallamosu ne"
yace "dasauki suna asibity "
umma tace "wace asibity suke room nawa? "
Yace "turai, aminity ward room 9"
umma tace "to nagode sosai "ta kalli lady tace "mutafi asibitin "
suka juya suka tafi abul yameda gida ya rufe,
akan hanya suka sai kaza me dawafi da drinks suka tafi asibitin,
Bawani wahala suka gane dakin suka tura suka shiga da sallama bakinsu, ummi kadaice ta rage itama tana salla, da lady da umma hankalinsu bakaramin tashi yayi ba ganin halin da faseelat ke ciki,
idon faseelat akulle umma takarasa kan bed din dasauri tana kara ganin barnar da danta yayi,
jin kamshi na daban faseelat ta bude ido taga umma, tafara hawaye,
Umma tace "sannu faseelat Allah yabaki lpy"
Faseelat tariko hannun umma murya shake tace "umma! ya sakeni ko? "
umma tace"me kike cewa ne? Yazaai fahad ya iya sakinki yana sonki sosai baze iya rabuwa dake ba "
Tace "ban ganshi ba har yanzu bezo wurina ba, Dan Allah umma kikiramin shi inason ganinshi "
Umma tace "ki kwantar da hankalinki yananan zezo "tasa hannu tana share mata hawaye,
ummi da tundazu ta sallame tai shiru tana kallon gadon da faseelat ke kwance tanajin takaici kamar me,
lady ta matsa tace "sannu anty "
faseelat ta daga mata kai tana cigaba da hawaye,
ummi ta tashi tana linke carpet tace "sannunku da zuwa "
umma ta juya wurinta tace "ina wuni yame jiki Allah yabata lpy"
ummi tace "amin "
Itama lady ta gaida ummi, shiru dakin nawani lokaci sannan umma tace "Dan Allah ummi kuyi hakuri akan abinda fahad yayi baa cikin hayyacin shi yayi haka ba, shi kanshi yana cikin tashin hankali don koda yazomun da labarin kuka yakeyi ,nasan yanacan cikin tashin hankali, kuyi hakuri Dan Allah wlh ni kaina abun yabatamin rai sosai don faseelat kamar diyata na dauketa, yaran ne ka haifesu baka haifi halinsu ba"
ummi tace "ihhhm bakomi"
umma tace "kuma wlh naji dadi sosai da kuka dauketa, sede ina rokon da kuyi hakuri kubarmishi ita karku rabasu, don ita haske ce arayuwar dana, tana duk wani kokari na gyara mishi rayuwarshi badan ita ba da yanzu bama tare dashi, ina rokon da kuyi hakuri akan abinda yafaru kubarmishi ita Dan Allah "tahade hannayenta biyu,
umma ta bawa ummi tausayi tace " da nasa araina dole ya saketa saboda wannan abunda yayi kuma ba yaune yafara dukanta ba, amma na hakura saboda ke kuma zanyi iya kokarina naganin takoma dakinta, sede bazan bashi ita hakanan ba se yagane kuskurenshi "
Umma tace "nagode sosai ummi kuma naji dadin hakan don ko dauketan da kukayi yau kadai ma ya razana shi na tabbata wannan zesa yagane kuskurenshi nagode da kika min wannan alfarmar "
ummi tace "bakomi "
su faseelat najin abinda suke fada sede ita abun be mata dadi ba ashe dauketa sukayi, yanzu se yaushe zata ganshi? jin datayi umma tace yana ta kuka yasa taji tausayin shi ta riga tasan fahad na sonta sosai wannan dukan da yamata Har cikinta yafita kokadan besa ta rage digon son da takema shi ba,
Faseelat tace "umma dan Allah kikiraminshi inason ganinshi "
umma tace "kiyi hakuri kinji ,kibarshi yakara gane kuranshi, hakan zesa kobaya cikin hankalinshi baze iya dukanki ba, kuma ze kara sanin darajarki "
faseelat tai shiru,
ganin har 11:30 yasa umma tacewa ummi zasu tafi ta fiddo kudi boundles na 1k ta aje musu,
Ta shafi fuskar faseelat tace "kiyi hakuri kinji yata gobe inanan zuwa me kkso nazo miki dashi? "
faseelat ta girgizakai,
umma tace "kifada min me kkson ci ni da kaina zan girka miki "
Faseelat ta yamutsa fuska ahankali tace "komai inaso "
umma tai murmushi tace "to ki kwantar da hankalinki kiyi bacci "
taiwa ummmi bankwana ummi nata godiya suka fita daga dakin,
ummi ta kalli faseelat tace "shasha ashe duk sunsan kin mutu sonshi,mutum ya nakada maki duka amma kinata nemanshi har uwarshi taji haushi amma ke ko ajikinki marar zuciya"
faseelat ta juyar da fuskarta ummi tace "Allah yakawomaki sauki"
khalil ko abinci kala kala aka kawomishi wanda sede ya tsakura yabarsu saboda bejin dadin komi hankalinshi kuma yakoma ga hjya yasan iyanzu tana cikin tashin hankali, musa yazo sukai ta fira sama sama se 9 sannan ya shiga gida,
suma su hjy sunanan har 10 ganin ba yau zaa sallamesu ba yasa mamar jamila tace wa su hjya sutafi gida, hjya tace ita zaabari akai akai tatafi taki dole suka hakura suka tafi sukabarta rungume da lil khalil ,
da khalil da fahad da hjya da jamila, duk bawanda ya rumtsa,
Baccin asuba ne ya dauke fahad sede bewani dade ba yafarka ,
karfe 7 aka sallami su hjy suka dawo gida,
Karfe takwas fahad ya fita daga gida wanka kadai yayi ya sauya kaya ya nufi gidan su faseelat sede ya makara don har sunbar gidan yana kulle kamar jiya, ya bata fuska yanajin kamar yayi kuka ya cize lips ya juya ya tafi gidan umma,
umma na kitchen don sotake karfe tara tabar gidan,
ya shiga yayi kwance kan kujera don gabadaya bejin dadin jikinshi,
umma tagama komi ta fito da niyyar hawa sama tai wanka ta ganshi kwance hannunshi saman kai,
ta dawo tai tsaye kanshi tace "lpy me kazo yimin nan? "
fahad ya tashi zaune kanshi na sara mishi kamar ze kuka yace "Dan Allah umma kiyi hakuri wlh nayi nadamar abinda na aikata,"
umma tace "to ni aiba fushi nai ba, don kai kaiwa kanka ,don haka katashi katafi wadanda kawa laifi yakamata kabawa hakuri bani ba"
yace "umma nayi zarya gidansu akulle narasa yadda zanyi "
Ta tabe baki tace "to dama ya zaai ka iskesu tunda kaja musu jinya hakuri zakai har tasamu lpy insun barmaka ita to ,katashi katafi fita zanyi akwai inda nikeson zuwa "ta tafi tabarshi dafe da kai fahad ya rasa yadda zeyi kwana guda jinshi yayi kamar shekara,
umma nagama shiryawa ta sa me aikinta ta kaimata girkin da tayi da lemun da tahada a mota sannan tafita ta nufi asibitin,
abul da omer basunan suna school ,dakin daga ummi se Mubarak da ishak,
umma ta shiga tana ta faraa lokacin har ummi takama faseelat tayi wanka ta sauya mata kaya,
Bayan ta zauna suka gaisa ,
umma taiwa faseelat ya jiki sannan ta tambaya kotaci abinci, ummi tafada mata bata ciba, ta zuba farfesun kayan ciki da tayomata ta tada ta zaune tasa hannu ta rika bata abaki,
agidan hjy kau anata zaman gaisuwa dan ta tabbatar khalil ya mutu don beje batsari ba kuma baya kt hakan ya tabbatar da ya mutu tunda safe su kawu manu sunje inda akai accident din sunga yadda motocin sukai hakan yasa sukadawo suka zauna ansar gaisuwa,
mata anata zuwa yiwa hjya gaisuwa da barka lokaci daya,
Anata kiran fahad da wayoyin Suka isheshi da kara seya kashesu gabadaya donshi bata wani aiki yake yanzu ba,
yana zuwa gidan mommy ya tarar da Aisha main palo tana zaune tana kallo ga amira da tai kukan anty har tagaji kwance kan cinyarta,
amira na ganinshi ta tashi ta haye sama da gudu,
Aisha tabishi da kallo duk ya fita hayacinshi,
Fahad ya zauna gefen Aisha ya kwantar da kanshi akan cinyarta yasaki kuka me taba zuciya,
Aisha ta rungumo kanshi tana share mishi hawaye idonta tafff da kwalla tace "kayi hakuri yaya kadena kuka "duk atunaninta gudunshi da amira keyi yakewa kuka,
Yana kuka yace "meyasa zasumin haka? meyasa zasu dauketa daga gareni ina tsananin sonta bazan iya jure rashinta akusa gare niba "
Aisha ta tsaya da share mai hawayen tace ".....
[8/22, 2:56 PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣4⃣
*ban manta daku ba,kuna raina,lady ,maman zainab, Aisha habib, Firdausi,sede kundena comments why?*😒
*soupnas* comment dinki nasani farin ciki keda *maman nour* comments dinku yana kayatarwa kucigaba da gashi 💃🏼, *maman nour* wai ina kawalliyarki *earmeenatuwa*🤣
Aisha tace "bangane ba yaya? "
Yana cigaba da kuka yace "iyayen faseelat Sun daukemun ita sun tafi daita"
Aisha farin ciki ya mamaye zuciyarta batasan lokacin da tasaki murmushi ba tace "Allah yasa daga can ai can"
Jin abinda tace Fahad ya tashi zaune yana mata kallon mamaki yace "me kk cewa ne Aisha? kina farin ciki da abinda yafaru ko? "
Aisha ta zumburo baki tace "to da so kake nace Allah yasa su medo maka ita? Saboda ita kamanta duk wata soyayyata idonka ya rufe akanta se kuma nakijin dadin tafiyarta, wlh naji dadi Allah yasa susa dole ka saketa ,hakanan batasan ya zaman mu yake ba tayi duk yadda tayi taja hankalinka har ka aurota ni ba abinda zance sede nace Allah yaraka taki gona "
Ranshi ya baci sosai da dane da seya mazge bakin amma ya dau alwashin barin dukan matanshi ya ciza lips yace "toko Allah baze amshi adduar ki ba saboda bame kyau bace, faseelat tananan dawowa gareni nida ita mutu karaba, don we love each other insha Allah we will die together"
Aisha dake jin haushin maganar shi kamar me ta turo baki gaba ,
Yaja tsoki yace "stupid bansan time din da zaki dena kishin hauka akan faseelat ba, ita kullum tana girmamaki tana sonki ke kuma ba wacce kika tsana kamarta"
ya tashi tsaye ze fita Aisha tace "bazaka jira ni mutafi tare ba? "
Beko waigo ba yace "batare mukazo ba kinsan hanyar gidan inkinso zuwa "
Yajuya ya bar gidan,
Aisha taja tsoki tace "so yake nayi addua sumedota kome?wlh yaya ya raina ni da yawa wai yagama cemin yanason ta har kuma yayi tunanin zanyi wata kyakkyawar addua can"
Mommy da tundazu tana kan dining tana jinsu tafito da cup ahannu tana kyalkyata dariya,
Tace "ke kuma dan ubanki waya ce kice mishi haka keda yazo ki rarrasheshi "
Aisha tace "mommy ba abin dariya bane wannan yazaai yazo yana fadamin wai he love her inba raini ba"
Mommy tace "to seme dan yace yanason ta tuntuni ina fadamiki kidena fiddo mai kiyyyar ta a fili kirika nuna kinasonta"
Aisha ta mike kafarta akan kujera tace"bazan iyaba niba wacce natsana kamarta Allah nagani da nasota kafin nagane hainta ta take ita ,ni wlh har mamakin zuciya ta nayi duk yadda natsaneta ranar da ya nakada mata duka seda naji tausayinta "
Mommy ta zauna ta kurbi tea tana murmushi tace "kin shirya zaman gida ko? Tunda kinsan ba zuwa zeyi daukar ki ba "
Aisha tace "hmm zezo ai Wadda ake makalewar batanan kinanan zaki ganshi "
mommy tai dariyar manya tace "amma kinyi kuskure karki kara irin wannan "
Aisha tace "to"
Fahad gida yakoma yayi kwance zuciyar shi na kuna yarasa ina zesa kanshi ba arziki da yunwa ta cishi ya tashi ya hada tea yasha,
akai akai yakan leka unguwarsu faseelat amma gida kulle, har dare yagaji yakoma gida,
Aisha taci wanka tana jiran yazo daukarta har 9:30 shiru bezo ba ta tashi ta dauko gyale mommy ta kalleta tace "ina zaki? Bakince ze dawo ba kijira shi "
Aisha ta yafa gyale akafada tace "mommy baze zo ba tunda har aka kai wannan time din bezo ba tafiya zanyi maybe yanacan ko abinci beci ba "
mommy tace "aiko baki isa ba ki samu wuri ki zauna, har se randa yaga dama yazo da kanshi daukarki "
Aisha ta turo baki gaba tace "Dan Allah mommy kibarni in tafi wlh hankalina duk baa kwance yake ba, yaya yana bukata ta yanzu "
mommy tace "yanzu kikasan haka ai, kicire gyalen nan "
Aisha ta turo baki ta tafita daga dakin mommy nata kiranta taki amsawa, daga karshe mommy tace "zakizo kisameni ne "
Aisha ta fita tasamu napep ta haye yakaita bakin gidansu, ta kwanwasa baba tsoho ya bude ta shiga ciki,
Ta kitchen tabiyo ta shigo gidan, fahad na kwance akan gadon faseelat rungume da kayanta ta shigo dakin,
Dukda yaji kamshinta amma be nuna ba, tana sanye da riga da wando na Sari ta haye gadon idanunshi a lumshe ta riko hannunshi tana cewa "yaya kaci abinci kau? "
yayi banza ya kyaleta tace "yaya kayi hakuri da abunda yafaru plsss katashi kaci abinci kar ciwo yakama munkai"
Fahad ya bude ido yana kallonta ,ta langabe kai tace "plsss katashi kaci abinci? "
ya yamutsa fuska yace "Aisha plss leave me alone ba ruwanki da naci abinci ko banci ba just go to ur room "
kamar zatai kuka tace "yaya da ruwana mana yanzu in wani abu yasameka fa?bansan ganinka cikin wannan halin na damuwa kayi hakuri katashi kaci wani abu "
Yace "bazan ci ba ko dole ne, kitashi kibani wuri, damuwa kuma zan cigaba da zama acikinta har lokacin da farin cikin rayuwata zata dawo gareni "
Aisha ta tashi tafita daga dakin tana kuka, fahad yaja tsoki yace "u don't love me da kina sona da kinso faseelat"
Aisha tafada kan bed ta cigaba da rusar kuka, ita ba maganganun nashi ba suka fi kona mata rai aa yadda yabi ya rude harda sukin cin abinci saboda mace, ta sha kuka har tagaji, har 2 takasa yin bacci shima ba baccin yake ba idonshi biyu,
Kanta na ciwo Ta tashi ta shiga kitchen ta hado mishi tea me kauri ta dawo dakinshi, yana kwance yanata kallon silin tazo ta zauna akan gadon murya dishe tace "Dan Allah yaya katashi kasha ko da tea ne ba don ni ba "
yayi mata banza tai ta magiya hardasu kuka sannan ya tashi zaune ko kallon fuskarta be ba ya mika hannu ze amshi cup din, taki bashi ta kai cup din bakinshi seda yashanye shi tasss sanan ta dauke cup din,
Tai murmushi ta share hawayenta tace "nagode da ka daure kasha "ta ajiye cup din a bedside table ta tashi zata bar dakin ya riko hannunta yace "anan zamu kwana"
Ta dawo ta kwanta gefenshi ta rungumeshi ba dadewa bacci ya dauketa,shiko yakasa koda rumtsawa sema kukan faseelat da yayita masa yawo akunne kamar lokacin yake dukanta duk da AC dake dakin yayita zufa,
Da safe,
tun 7 ya isa kofar gidansu faseelat lokacin har abba yafita yana tsaye bakin kofa omer yafito cikin shirin shi ze tafi school, fahad ya mika mai hannu ya mishi sallama fuska murtuke omer ya mika mai hannu ya amsa gaisuwar, ya zare hannunshi tun kafin fahad yace komi omer yawuce ya shiga mota yayi tafiyarshi,
fahad yayi tsaye zuciyarshi na kara zafi,can sega abul yafito shima ze tafi school ko kallon fahad beba yawuce warshi, sega su ishak da Mubarak sunfito suma zasu tafi school kasancewar yau Monday abun yabashi mamaki suma basuko kalleshiba ishak ya garkame gida suka juya suka tafi abun su,
dana sani yakara cika zuciyar fahad yara kananu ma Sun dena ganin girmanshi ,ya dade tsaye sannan ya shiga mota ya nufi gida time to time seya share hawaye bakin ciki da suke fitowa ta gefen idonshi,
Ya koma gida yayi kwance, Aisha tayi rarrashin yakasa koda shan ruwa ne har tagaji se yanzu takara gane faseelat ta mata nisa azuciyar fahad gatade zaune dashi amma zuciyarshi tana wurin faseelat seta karajin tsanar ta aranta ,damuwar shi yasa itama tashiga damuwa, yakasa komi se aikin tunani, itama faseelat na can tana fama da ciwo da damuwa amira ma nacan tana kukan anty, fahad akewa punishment amma su duka suke azabtuwa, har Aisha taji gwara faseelat din ta dawo kota samu fahad dinta yasamu natsuwa,
Wansafe tunda asuba fahad yafita da mota a masallacin unguwarsu faseelat yayi salla ana sallamewa yafito yakoma bakin kofar gidansu ya tsaya yasan de dole abba yafita sallar asuba, yana nan tsaye yara yaran sukai tawuceshi suna shiga gida, can zuwa sega yaya omer yana zuwa ya daga mishi hannu yace "assalamu alaikum" yawuce abunshi, fahad bewani damu sosai ba shide burinshi yaga abba, yana tsaye sega abba yazo ze wuce yashiga gida, yayi sauri ya duka yafara gaishe shi memakon ya amsa seya mika masa hannu suka gaisa fahad na zukunne be tashi ba,cikin ladabi yace "abba Dan Allah ina neman yafiyarku kuyi hakuri akan abinda na aikata, nasan ban kyauta ba kuma nayi nadama Dan Allah kuyi hakuri "
abba yace "banji dadi ba yadda ka wulakanta min diya raina ya baci amma ni na yafe maka sede ina bukatar ka rubuta mata takardarta saboda zamanku atare akwai cutarwa "
Fahad da kanshi ke Duke ya dago arazane besan lokacin da ya mike tsaye ba, sannan yakoma kasan yana magiya "Dan Allah abba kuyi hakuri inason ta sosai bazan iya rayuwa batare daita ba, wlh nayi alkawari bazan kara dukanta ba Dan Allah kuyi hakuri wlh itace rayuwa ta zan kiyaye duk wani abunda ze bata mata rai koya taba lpyarta"
Jin abinda yake cewa cikin ran abba yace "nan wurin ba lpy "🤣
Yace "nide nafada maka Dan Allah kakawomin takardanta in kuma bahaka ba zamu shiga kotu "yana gama fadar haka ya shige gida,
fahad yaida yin zaman dirshan awurin yana hawaye da kukan zuci seda gari yayi fayau sanann yatashi ya nufi gidan umma,
umma ko kullum setaje asibity suna zaune a dining sun hallara don yin breakfast yashigo gidan duk sukabishi da kallo umma ko kallonshi batai ba bare ma yabata tausayi,
yazo yaja kujera ta kusa da daddy ya zauna murya na rawa yabawa daddy labarin abinda abban faseelat yace,
yace "Dan Allah daddy kaje kabashi hakuri wlh nayi nadamar dukanta tun daga lokacin da abun