Follow us on social media

Showing 54001 words to 57000 words out of 79519 words

Chapter 19 - JUYAYI Raunin da Ba Ya Warkewa by Nimcyluv

05 Aug 2026

74

kaya iri ɗaya ne a jikin jariran ga kuma yanayin halitta ɗaya abune mai wahala kasan anyi sauyin beby,nayi hakanne kuda sun ɗauke to bafa duk yaranta suka ɗauka ba,na salwantar da ran yarinta bisa farin ciki ƙanwata sbd Dr ya tabbatar ba zata sake haihuwa ba,tun cikin daren na tafi Matata na shaida mata kada ta kuskura kuda wasa ta ɗauki Nono ta bawa yarinyar domin bansan mai gaba zata haifar ba,cikin sa'a ba'a ɗauki beby ko guda ba sai kawai na share aka raɗawa yara suna inda nina zaɓi sunan Lubna sannan na zaɓi sunan ƴarta Afnerh, a lkcn da Mamana ta tabbatarmin ba zata auri Faisal ba saina yanke shawarar haɗa aurenta da ɗana Fahad a ranar da aka ɗaurawa ƴar uwarta aure da Faisal a ranar da daddare aka ɗaura auren Fahad da Lubna_


_Ban baka ita sbd yin kaina ba,a'a na baka ita sbd kasan cewarka jarumin namiji wanda zai zama jagora a rayuwarta,tabbas idan Mamana tayi kuka a dalilinka bazan faɓa yafe maka ba,na maka ita amana duk wahala duk daɗi kada ka sake ka rabu da ita kuda na kwana 2 ne,bare sakin aure,wannan wasiyyace_


_Wasiƙa ta biyu kuma kada ka sake ka buɗeta sai lkcn daka rasa mafita kumai ya tushe maka sannan zaka buɗa, wannan wasiya ce daga gareni_


_Alhaji Mustapha Rano_
_Sun/Dec/2020 10:30pm_
~MSRN~



Musty na kawowa nan yana ya tsaya tare da jan numfashi,ninke wasiƙar yay tare da maidata aljihunsa,wajanne yay shuru kuwa da abinda yake tunani a ransa,Uncle mijin Mama ne yace"to masha Allah kai Sufyan sai kayi hqr tunda ba'a akan wani auren,daman shi aure nufin Allah ne kuma matar mutum kabarinsa,kuda ka aurenta idan ba baronka bace dole wani dalili ya tasu wajan zaku rabu da juna,Idan babu damuwa sai a maye maka gurbinta da ƴar uwarta Afner"
Alhji ne ya amshe maganar tare da faɗin "Ai wannan ba abin damuwa bane da Lubna da Afnerh duk abu ɗaya ne,na amshi tayinka a matsayina na uba a wajan Sufyan" babu kunya wannan karan Alhji ya amshi auren Ɗansa Sufyan na mutane suke shaida ɗaurin auren *Sufyan Sulaiman ƙusawa da Afnerh Tijjani wambai* akan sadaki dubu ɗari cif,ana gamawa aka shiga raba alawa da goro nan akayi photuna taro ya ƙare,Fahad sun gaida da Khalid da kuma cousin ɗin mahaifiyarsa Fairus sun gaisa sama² sbd babu sabu a tsakaninsu musamman Fairus,zaman babbar rigarsa ya gyara tare da watsa wayoyinsa cikin aljihu,yana tafe yana kaɗa key ɗin motarsa,cikin nutsuwa da kamala yana gaf da shiga cikin gidansu sbd inda yake zaune masu wajan sundawo iyayen Fauwaz,yaji hankaɗesa tare da shaƙar wuyansa,cike da jarumta yasa hannu ya kaiwa Sufyan mari,zafin marin da ƙarfinsa yasa yay saurin sakin Fahad,cikin ɓacin rai Sufyan yace.





"wlh kayi gaggawar rabuwa da my lovely bbyna idan ba haka ba,ka siyawa kanka tashi hankali wlh bazan taɓa bari ka mallaketa ba bare kayi tunanin ƙwanciya da ita"tunda ya fara magana Fahad ya lumshe idanunsa saida ya kammla sannan ya buɗesu tare mannasu a kan Sufyan murmushi kawai yay danshi kansa yana mamakin yawan murmushinsa yana jin zuciyarsa wasai,yayinda nauyin kansa ya tafe dukkan wata damuwa tayaye ba tare daya san dalilin hakan ba,juyawa yay zai tafi Sufyan yay saurin shan gabansa yace "Ka saketa nace,idan ba....,"
"Kadaman shirme ban waje naga lafiyar iyalina naji ɗumin jikinta"yana faɗin hakan ya juya tare da shigewa cikin gidan,bango ya kaiwa naushi tare da faɗin "i will kill u Fahad wlh zakai ladamar abinda ka aikata,wlh nizan fara sanin Lili before this is my promise"a zafafe ya juya tare da shiga mota ya bata wuta.


Yana shiga cikin parlour yaga mutane sbd baison takura ya gaidasu a taƙaice yay flat ɗin Mama,yana zuwa ya ganta gaban wadrope tana fitu da kaya,a hankali ya ƙarasa wajanta tare da rungometa ya shiga juyi da ita a parlour'n,Mama wacce tsoro ya kamata amma ganin Fahad yasa ta saki ajjiyar zuciya,Tsayawa yay tare da lafewa cikin Mama,wular kansa ta cire ta shafa kansa cikin farin ciki tace "Yaro na wannan farin cikin na mene,tnx God kazu akan kari kafin Uwata ta huce,Lili kullum cikin kuka take ita Yayanta bata da aiki sai kiran sunanka"Lumshe idanu yay tare da taune jajayen laɓɓansa yana jin wani sanyi na ratsa jikinsa,zame jikinsa yay tare da zubewa a ƙasa yay (Sujudur shukkuri)ya daɗe yana wa Allah kirari kafin ya miƙe tsaye fuskarsa fal farin ciki ya shiga zaiyyanawa Mama abinda ya faru,kuka Mama ta fara saida tayi mai isarta yana kallonta bai hanata ba,"Allah sarki ya sadaukar da yaran ƴar cikinsa akan farin cikina,wannan sadaukarwa ba kowane zai iyayinta ba,Allah ubangiji ya jiƙansa yay masa rahama Ubangiji ya ƙyautata ƙarshensa halinsa na gari ya bisa,Rabbil izzatu ya haskaka kabarinsa"da Ameen Fahad yake amsawa a zuciyarsa jin Mama nason tasu masa da miƙin dake Fama dashi yay saurin cewa "Mama na gaji bacci"ya faɗa yana ƙwaɓe fuska,hararar wasa ta watsa masa tace "ok bari nazu na goyaka"dry yay wanda ya bayyanar da fararan jerarrun haƙwaransa masu ƙyau da tsari,murmushi daya haifar da lumawar Beauty points ɗinsa,sajen gemunsa ya shafa tare da jan gemunsa yace "laa bance ba,saidai kijira Ɗana wannan bayan nasa ne"baki ta saki tana mamakin rashin kunyarsa.
"Yaran zamani nifa sirikarka ce,yawwa akwai event after magrib"shuru yay kafin yaja numfashi yace "no Mama banson tarin bidi'ar nan,a hqr dayi ayi walima da saukar alkur'ani"jinjina kai tayi domin ta gamsu da bayaninsa,kan bed ɗinta ya faɗa daman Mijinta ba nan yake ƙwana ba,duvet yaja ya rufe jikinsa tare da lumshe idanunsa,daman ya gawa Mama kada ta sanarwa da Lili komai,babu daɗewa bacci yay gaba dashi.


Tunda aka sanar masu an ɗaura Auren Lili ta fashe da kuka haddasu birgima a ƙasa,rarrashin duniya su Fannerh sunyi tayi burus dasu,saida tayi mai isarta sannan ta miƙe tare dayin bedroom ɗinsa,cikin nutsuwa take tafiya amma kana ganinta kasan bata hayyacinta tana ƙoƙarin buɗe ƙofa ta shiga cikin bedroom ɗinta taji anyi saurin riƙeta tare da haɗata da jikin bango,tsoro ne ya kamata ganin Sufyan tsaye a gabanta kafin tayi magana ya haɗata da jikinsa tare da matseta ya shiga sauke numfashi,bakinsa ya ɗuran daman kunnanta yace "Lovely bbyna nayi missed naki,finally komai ya ƙare" ya yana tura halshensa cikin kunnanta ya shiga latsa,runtsa idanunta tayi da ƙarfi tana jin wani abu yana yi mata yawu a jiki, sam bata jin daɗin abinda yake mata ji take tamkar wuta ake watsa mata a jiki.





Najma pov
Ba ƙaramin hauka Najma tayi ba lkcn data tabbatar da Faisal ya mutu tayi kuka kamar ranta zai fita,da ƙyar aka lallaɓata hqr amma har zuwa yanzu bata da burin daya huce taga bayan Lili,wannan shine burinta tashi take ƙwana take tashi,yayinda kuma gefe na zuciyarta yake tunanin tarin kuɗin da mahaifinsu ya mutu ya bari wanda dana da tabbacin kuɗin sunnan kuma ta ɗauki alƙwari mallakar dukiyar gaba ɗayanta,hakan zai bata damar aikata abinda tayi niya ga kuɗin mahifinta gana mijinta daya bari,sosai take farin ciki da samun cikinta wanda take fata ace namiji zata haifa wannan shine zai bata damar yin abinda taga damar yi acikin gidan,a kuma ranar data haihu tana arba'in zata bar gidan ta shiga duniya neman Lubna mustapha Rano babbar maƙiyarta a duniya.




*** ***
Tsoro da fargaba sune suka cika zuciyarta yayinda take jin wani baƙin ciki ya cikata,tsoransa ya bayyana a ranta tasan abinda yake ba haram bane amma zuciyarta da ganggar jikinta sunƙi aminta da hakan,tana jin kamarta aikata ba dai² ba,jikinta ta shiga ƙoƙarin janyewa amma ta kasa sbd yadda ya ƙara matseta a jikinsa,cikin salo yake ƙoƙarin tura hannunsa cikin rigarta,numfashinta ne ya shiga ɗaukewa cikin fitar hayyaci ta fasa wata uwar ƙara wacce ta karaɗe gidan gaba ɗaya.


Yana tsaka da baccinsa mai cike da nutsuwa baccin daya daɗe bai samu irinsa ba,yaji sauƙar ƙara a cikin kunansa,runtsa idanunsa yay tare da dafe kansa daya sara masa a lkcn wata fargaba ta saukar masa a zuciya,yayinda yaji gudun zuciyarsa ya ƙaru ba kamar ɗazu ba,addu'a yay tare da sake lumshe idanunsa yaja duvet ya ƙara lulluɓe jikinta, “Booby” yaji saukar muryarta kamar a mafarki,muryar da har abada bai taɓa manta sautinta ba,a suƙwane ya diro daga kan bed ɗin gaba ɗaya manta ko riga babu ajikinsa,da gudu ya ƙarasa isa parlour'n zuwansa yay dai² da ƙarasuwar Mama,Momma,Fannerh,Afnerh,Yusrah,Uncle Alhaji,Khalid,Fairus..
Sassauta riƙon da yay mata yay tana ganin hakan ta ƙwace jikinta da saurin still idanunta a rufe bata san wake gabanta,a haka ta shiga tafiya da sauri harta faɗa jikinsa ba tare data san waye ba,a tare suka sauƙe ajjiyar zuciya,laɓɓanta ya mannu akan tsinin jajayen nipples ɗinsa,lumshe idanunsa yay a hankali tare da zagaye hannayensa ya rungometa tsam a jikinsa,kuka ne ya ƙwace ba ta shiga dukan ƙirjinsa tare da girgiza kanta tunanin Sufyan ne,ganin abinda take ya tabbatar masa bata cikin hayyacinta,a sanyaye yasa hannu ya tallafu haɓarta tare da tura mata babban ɗanya tsansa a cikin bakinta.



⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️ayi comments,ayi comments ko a wanne grp kake kayi comment zan gani kuma a shirye nake dana duba,wlh rashin comments zaija maku nayi sati banyi update ba,wattpad,wasapp,telegram,facebook,ai comments😍😅😅wlh hankali ƙwance zan tafi FADATA nayi ƙwanciyata.

Juyayi fans
Sarauta place
Akafta🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️.

*💖JYY💖*






*40-41*






```NIMCYLUV🤏🏼```





*_@Telegram_* https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ




```Wattpad```
https://my.w.tt/jN2GLY5RKcb











Ajjiyar zuciya ta saki tare da shigewa jikin Booby still tana dukan ƙirjinsa ba,lumshe idanunsa yay tare da ƙara matseta a cikin jikinsa yana jin yadda gudun zuciyarsa na ƙarauwa fiyeda da,sai yanzu ya tabbatar da bugun zuciyarsa da take bugawa da tunaninta bawai zumunci bane,soyayyace da kuma zallar ƙauna mara algus,ƙaddara babu ta inda bata haɗa mutum sai yanzu yasan ƙarfin ƙaddara yafi gaban haka,yarinyar daya ɗauketa matsayin ƙanwa uwa ɗaya uba ɗaya yau itace ta zama matarsa,matarsa ta sunna ta ina zai fara aƙwai tazarar shekaru masu yawa a tsakaninsu,ƙara lumshe idanunsa yay yana sauraran yadda take tsotsar yatsan sa kamar ta samu sweet,hannunsa yasa ya shiga bubbuga bayanta harya samu ta saurara da kukan sai sauke anjiyar zuciya take har zuwa yanzu taƙi yarda ta buɗe idanunta,sannu a hankali bacci ya shiga fisgarta jinta samu nutsuwa,Sufyan tunda ya kifa kansa a jikin bango bai ɗago ba,sai sauke numfashi yake da sauri idanunsa sun kala Tare da sauya kala,Mamace tace.
“Yaro na”
Maza ɗauketa zuwa ɗaki naga bacci ya fara ɗaukanta da alama wani abun ya bata tsoro"kasa ce mata komai yay sai cije lips ɗinsa da yay,ɗaukanta yay cak tare mannata da ƙirjinsa yana jin yadda numfashita ke dukan ƙirjinsa,cikin sauri ya nufi ɗakin Mama da ita yana zuwa ya sawa ƙofar key,derect toilte ya nufa da ita yana zuwa ya haɗa ruwan zafi a cikin bathtube yana gamawa ya sakata a ciki.
Sauri buɗe idanunta tayi tare da ƙwaɓe fuska tsaye ta ganshi gabanta ya riƙe waist tare zuba mata narkakkun idanunsa wanda suka janye sbd baƙin cikin abinda Sufyan yay mata,da sauri ta miƙe da cikin ruwan sbd mamakin ganinsa a lkcn da matayi tsammanin ganinsa ba,yazu a lkcn da komai ya ƙare yazu a lkcn da zara fara rayuwa da mutumin da bataso bata ƙauna,kasa cewa komai tayi sai kuka data fashe dashi tare da faɗawa jikinsa ta ƙanƙameshi tare da cizonsa,runtsa idanunsa yay yana sauraran yadda take cizonsa haɗi da kuka,sosai kukanta yake taɓa zuciyarsa,ganin abinda bana ƙare bane yasa a hankali yasa haka tattusan hannunsa ya tallafu haɓarta,tsumamman idanunsa ya zubawa innoncet face ɗinta.
Lumshe idanunsa yay naji wani abu a ransa wanda bai gama tabbatar da menene shi ba,hawayen fuskarta ya shiga goge mata tare suma rarrashinta ta hanyar bubbuga bayansa,ɗanya tsansa ta tura cikin baki ta shiga tsotsa tare da sauke ajjiyar zuciya ta nayi tana sakar masa cizo,saida ta gaji ta sakeshi tare da sauke manyan idanunta a kansa cikin muryar kuka tace.
“Boobyna”
Gira ya ɗaga mata ba tare da yay magana ba,sai yanzu ya fahimci zallar ƙuruciya a kan fuskarta,sam bazai iya ba,yana da tausayi yana jin tausayi mata masu ƙanan shekaru irin nata,tayaya zai iya rayuwar aure da ita harya sauke haƙƙinta dake kansa abunda kamar wahala,a hankali ya lalubar kallamar.
“My sunshine bby”
Turo baki tayi gaba tare da ƙwantar da kanta a jikinsa tana ji kamar zai ƙara guduwa yabar ita ɗaya,a yanzu bata jin zata jure rashinsa,tayaya zatar ruhinta da kuma bugawar numfashi taje ga son ranta? Wannan shine tamvayar da take ranta,cireta yay a jikinsa yace.
"oya wanka i will be back soon" kaita jinjina ta suma cire kayanta a gabansa yay saurin fita tare da dafe kansa.




Wani ƙyaƙƙyawan mari Alhaji ya kaiwa Sufyan cike da ɓacin rai ya ƙara ɗaga hannu da niya ƙara marinsa Khalid yay saurin riƙe hannunsa tare da faɗin "haba Alhaji wannan ba shine hukunci ba,dani daku kunsan cewa yana cikin hali na ɓacin rai da kuma kishi bai kamata ayi masa hakan ba,kai Sufyan kayi hqr kaje ka rungomi matarka sai Allah ya shiga lamarinka samakaƙon biyayyar da kayiwa iyayyenka"ɓacin rai yasa Alhaji yin shuru tare da girgiza kai,Momma ce ta kada baki tace "Sufyan kaban Mamaki hakan yana nuna zaka iya tarayya da matar wani ko,kasan cewa Lubna yanzu mallakin Fahad ce ba wakai ba,meye duk wannan abunda kake? Ba zaka iya sauya hukuncin ubangiji ba,wlh ka kiyayen na gaya maka"tana faɗin hakan ta shige flat tana jin ranta babu daɗi akan abinda ɗan nata ya aikata domin Uncle ya zayyane masu komai,cike da tashin hankali Afnerh tayi ɗakinsu yayinda Fannerh ta nufi ɗakin baki inda Mijinta ke jiranta,Yusrah ma bayan mahaifiyarta tabi tana jin zuciyarta a sunkushe,Uncle da Alhaji da Fairus sukayi waje,guri ya rage daga Sufyan sai Khalid.
Kallon Sufyan Khalid yay kafin yay murmushin gefen baki yace "nasan zuciyarka cike take dason ɗaukan fansa ko baka faɗa ba,ninan zan taimaka maka wajan faruwan ƙudirinka"da saurin Sufyan ya kallesa yana mamakin abinda ya faɗa idan bai manta ba shiɗin ɗan uwane wajan Fahad ko yace Uba gaba ɗaya,amma tayaya zai taimaka masa wajan cikar burinsa,kafaɗarsa ya tafa yace "ka ganni wlh bana da imani babu abinda bazan iya aikatawa ba wajan cikar muradina,kai na taƙaice maka har akan kabari nasha ƙwana sbd wani ƙuduri nawa,dukkan wannan dukiyar da nake samu akwai JUYAYI a cikinta,kawai haɗin kanka nake nema"murmushi Sufyan yay tare da faɗin "tayaya zan mallaketa kafin shi?"shuru Khalid yay kafin yaja kunnan Sufyan ya raɗa masa wani abu,dry suka saka a tare kafin su fice daga cikin gidan.
A sanyaye Mama ta tura ƙofar ɗakin da Afnerh take ciki sannan ta tura kanta tare da rufe ƙofar,ta daɗe tana kallon kafin ta ƙarasa inda take ƙwance tana kuka,hannu tasa ta jawota jikinta tare da share mata hawayen idanunta cikin muryar mai daɗi da kuma ƙyaƙƙyawan Lafazi tace "ashe ƴarta ba zata iya ɗaukan ƙaddara ba? Ashe ba zaki tawaƙƙali ki rungumi abinda yazu maki ba,ki sani ko Fahad ya soki ba zaku taɓa kasan cewa abu ɗaya ba,ke dashi jini ɗaya ne jinin dake gudana a jikinsa shine ke gudana a jikinki,Yarinta cikar imanin mutum shine yadda da ƙaddara,damu dake dama kuwa babu wanda ƙaddara bata tare dashi ina roƙanki Allah da Annabi ki rungumi aurenki kada ki bari ki faɗa fushin Ubangiji,Aure kimane daraja ne, kuskure kaɗan zaki ki shiga fushin Allah dana mala'ikunsa,Yarinta kiymin hakan a matsayina na uwa a gareki" kuka Afnerh ta fashe dashi tare da rumgume Mama cikin muryar kuka tace "na yarda Mama wlh na Amince zan zauna da Sufyan har lkcn da Ubangiji zai ɗuramin sonsa,dan Allah Mama ki tayani da addu'a"shafa kanta Mama tayi tace "Ubangijin Rahama yay maki Albarka Allah ya baki ikon riƙe aurenki da gsky da Amana"shuru tayi ta lafe a jikin Mama tana sauke numfashi wai duk wannan soyayyar dake tsakani za'ace ba itace Mahaiciyarta ba,lallai hukuncin Ubangiji yafi gaban komai.
“Oyya tashi ki shirya ki amshi mijinki ina jin zasu ɗan ƙwana biyu a nan sbd gyaran gida ake masu,wancan sabbi Flat ɗin guda biyu zan buɗe a bawa Fahad ɗaya Sufyan ɗaya,zuwa jibi kayan da mumai order na furniture ɗinku zasu zo"jinjina kai Afnerh tayi tare da miƙewa ta shiga cikin bathroom,Mama kuma ta miƙe tare da ficewa.




_1 week letter_
Ankai Amarya Fannerh gidan gida mai kyau da tsari,tare suke zaune da iyayen mijinta saidai flat ɗinta daban nasu daban,komai yana tafiya cikin farin ciki bata da matsala da kuwa.
Wajan Sufyan da Afnerh babu yabu babu fallasa tsakaninta dashi gaisuwa idan ya fita tun safe sai dare zai dawo yayinda kullum suna tare da Khalid suna haɗa muna furcinsu,babu wanda yasan abinda suke aikatawa.




Ƙwance take tsakiyar makeƙen royal bed ɗinta ta lumshe idanunta tare da dafe ƙirjinta,yau tun safe ta kejin tsoro da faɗuwar gaba wanda bata san dalilin hakan ba,ƙara curewa take waje ɗaya tunanin yayanta wanda yazu ya zama mijinta a yanzu,tana mamakin yadda har yanzu bai taɓa tunanin yin wani abu da ita ba,me hakan ke nufi kodai bai sonta ne? Shuru tayi jin babu amsa ita kam sosai take jin zuciyarta da gangar jikinta suna muradin wani abu wanda ta kasa sanin menene,tsakinta da Fahad saidai da daddare yaɗan matseta a jikinsa ya shiga cakuɗa mata gashin kanta a haka har bacci ya ɗaukesa,saidai tana lura dashi duk dare saiya haɗa tea mai lemon tsami yasha haka zaita juyi,taita tambayarsa mene saidai yay mata shuru ko kuma ya jawota jikinsa har bacci ya ɗaukesa,numfashi taja tare da ɗauko wayarta tace ta shiga cikin wattpad tayi searching sunan Sarauta (nikam nai dry nace wannan sunan nada banne kamar yadda zai fitu a special book ɗina wanda zuwa yanzu komai ya kammala,salonsa dana banne kamar yadda kuke ganin Juyayi,da Jiddah, wannan za kuyi kuka harku rasa hawaye🤣"
Ganin bai bata result

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login