Follow us on social media
Showing 51001 words to 54000 words out of 79519 words
والذاكرين آلله كثيرا والذاكرات أ عدالله الله لهم مغفرة واجرا غظيما.
.....Wani yawun takaici ta haɗiya tare da runtsa idanunta ta shiga kukawa da numfashinta daya ɗauke,yay mata abinda ba tayi zatu ba,yayinda wani shashi na zuciyarta ya cika da kunyar abinda yay mata a gaban mutane,lumshe idanunsa yay sosai ƙamshin dake fita a jikinta ta yafi dashi,ƙara ƙasa yay da kansa zuwa wuyanta tare da tura hancinsa wata ajjiyar zuciya ya sauke wacce take nuni da zallan abinda yake ransa da kuma yanayin dake gangar jikinsa,sosai feelings ɗinta ke neman zautar dashi ya tare da dagula masa lissafi,ware idanunsa yay tare da mannasu akan fuskarsa,a sanyaye yaɗan murza waist ɗinta haɗi da juyata suka shiga fuskantar junansu,yadda ya sanya hancinsa a wuyanta hakan ya ƙara ɓata mata rai zuciyarta ta shiga ta fasa idanunsa ya ƙanƙance kaɗan hakan ya tabbatar ɓacin ranta yaje ƙarshe dan abune mai wahalar gaske kaga idanunta sun sauya,wani huci ta fita mai zafi tare da fincikar numfashinta wanda ya ɗauke sanadiyar murza waist ɗinta da yayi,kasa ɗago kai tayi saima wasu siraran hawaye da suka shiga zuba daga cikin idanunta,yadda hawayen ke fita ta cikin idanunta ya sashi sasauta riƙon da yay mata,hannunsa yasa ya tallafu haɓarta tare da zuba oval face ɗinta idanunsa,bakinsa ya masu daf da kunanta yace"meye na kuka bayan mun kusa cima burinmu?"still bata buɗe idanunta ba haka kuma ta gagara cewa komai sabida wani abu daya tsaya mata a maƙoshi,kalamansa jinsa take tamkar ruwan dalma a zuciyarta.
"Meye?"
Shine abinda ya ƙara tambayarta a karu na biyu,bakinta ta shiga taunewa haɗi dasa hannu ta toshe bakinta ganin kuka nason ƙwace mata,kai ta shiga girgizawa tare dayin baya,ganin yadda ta ruɗe ta fita hayyacinta yasa yaja baya zuciyarsa a cunkushe ya juya yabar wajansa,wata ƙatuwar ajjiyar zuciya ta sauke tare da dafe ƙirjinta dake ɗagawa,a hankali taja jikinta zuwa wani ɗan luku da babu kuwa durƙushewa tayi a wajan tare fasa kuka mai ciwo,kuka take sosai kukan dake nuna zallar damuwar dake ƙwance a ranta,kuka take mai nuna abinda zuciyarta ke muradi d kuma son kasan cewa dashi,kuka take wanda yake nuna tana cikin kewa da buƙatuwa,ƙara ƙanƙame jikinta tayi tare da cusa kanta tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kukanta mai cin rai.
A can wajan amarya Fannerh sosai abin yay armashi sunsha rawa tare da cashewa,kana aka yanka cake saida komai ya lafa za'a yanka cake ɗin Lili aka shafa a kaga bata wajan,dariya suka saka Yusrah ta buɗe baki tace"ai kawai mucinye shi daman bai isheni ba tana can tabi mijinta daɗi soyayya Allah dai ya bamu masu sunmu"dry Fannerh tayi tare da faɗin Ameen dai ƴar uwa ga wannan sakalyar ta tsaya son masu wani"da sauri Yusrah tace "kai haba kice ƙaddarar soyayya ta faɗa mata,wama take sone?"taɓe baki Fannerh tayi kana taja tsaki tace "Yaya Fahad wai fa,inda yake dajin kai gashi nan ko kallo bai isheta ba,bama ƙya gabansa,aikin banza ayi mutun ko zuciya babu na fahimci wannan farar fatar da sajen ke ruɗarki"wani tari ne ya suɓucewa Yusrah tayi saurin ɗaukan ruwa tasha,numfashi taja tare da faɗin "Don't tell me guy ɗin da nagani a gidanan?"Afnerh wacce tun ɗazu ba tai magana ba sbd ɓacin rai da kuma baƙin cikin maganganun Fannerh,sosai ta zubawa Yusrah idanu tana son gane mood ɗinta amma ta kasa saima cewa da tayi "to Allah ya ƙyauta" tana faɗin hakan taja bakinta tayi shuru tare da lulawa duniyar tunani,murmushi Afnerh tayi tare da faɗin "he's mine tabbas Fahad nawa ne kuma zan tabbatar maku da hakan idanma wata na tunanin sonsa wlh tayi ƙarya" Babu wanda ya kulata bare tayi tunanin zasu tankata,Khalisat dake gefe wacce tun ɗazu take sauraransu tace "abun babu sauƙi mutuniyata gske zansu naga wannan guy ɗin"gira ta ɗaga mata tare da faɗin "zaki ganshi soon,amma zaki zaucewa sbd ƙyansa am telling u"gaba ɗaya suka rankaya zuwa cikin gida.
A parlour suka tarar da Mama da Momma sai kuma wasu mata guda biyu tare da wasu maza wanda shekarunsu masu huce irin 35 ɗinnan ba,zama ƴan matan amaryar sukai tare da gaida baƙin,Mama ce ta kalli su Afnerh tace.
"Wannan Yayan mahaifiyar Fahad ne,Sunansa Khalid wannan kuma cousin ɗin Khadija,Mamy kenan mahaifiyar Lili sunzu bikine a matsayinsu na iyayen amarya wanda zasu maye mata gurbin Mahaifiyarta,bayan ta gama bayanin mazan ta kalli matan tace"Wannan kum surukan Fannerh ne basu jima da sauka ba shine suka shigo tare da kawu lefe kamar yadda sukai alƙawari,Wannan yayar Fauwaz ne Suwaiba,wannan ma yayarsa ce sunanta Lawiysat" Sunna kai Fannerh tayi tare da ƙara gaishe su,baki suka haɗa wajan amsawa tare dasa mata albaka sosai suka yaba da hankalinta,sallama sukai masu tare da ficewa suka nufi motar dasu kazu da ita.
Fairus ne ya nisa yace "ni ina ƙanwar tawa ne da kuma ɗana,naga ban gansu ba" Mama ce ta kama zancen tare da faɗin "Yarona baya gari dan banjin yana nan za'a auren,Lubna kuma su Yusrah zan tambaya tana ina"munyi tunanin tun dazu tana cikin gida ai bama tare sun fita da Yaya Sufyan" daga bayanta taji ance "wane Sufyan ɗin? Malamai ku tashi ku nemu min matana" ya faɗa yana haɗa ransa.
Khalid dake matsayin Uba wajan Lili tunda yayan mahaifiyarta ne yace"aa barsu aiba zata ɓata ba,tunda muna nan ai zamu ganta"baki Mama ta buɗe zatai magana taji Lili tayi sallama,gaba ɗaya suka ɗago kai tare da zuba mata idanu,cikin rawar Murya Mama tace "Mamana meye kike kuka?"da gudu Lili ta faɗa jikin Mama tare da fasa kuka ta shiga dukan Mama kamar mahaukaciya,Cikin damuwa Mama ta ƙanƙameta a jikinta tsam har saida ta daina bige-bigen, cikin damuwa tace "Mamana daina kuka dan Allah hakan yana baƙanta raina,tashi kiga ƴan uwan mahaifiyarki sbd dake sukazu nan" girgiza kai Lili tayi bakinta na rawa tace "Mamana i want to see Booby zuciyana ciwo zan mutu Mam ki kiramin Boobyna" Maganar kamar saukar ruwan sama haka Sufyan yaji wani takaici ne ya kamashi cikin saurin ya buɗe baki zai magana sai kuma ya fasa ya fice daga cikin gidan.
Da ƙyar Mama ta lallaɓa Lili akan da kanta zata nemushi,jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta kota kan Khalid dake matsayin yayan mahaifiyarta bata biba bare Fairus ya saka ran zata kulasa shida ke matsayin cousin na Mamynta,sallama sukaiwa Mama tare da nufar hotel ɗin da suka sauka,Amarya Fannerh da ƙawayenta suka nufi ɗakinsu yayinda Afnerh tayi zamanta a parlour tunaninsa yabi ya addabi zuciyarta yadda zata mallakesa cikin ruwan sanyi take nema yayinda gefe guda na zuciyarta ya cika da tsanar Lili wanda ita kanta bata san dalilin hakan ba,miƙewa tayi ta shige ɗakinsu.
Lili na shiga bedroom ta huce toilet ruwa mai zafi ta haɗa tayi wanka tare gasa jikinta,al'wala tayi kana tayi brush ta fitu jikinta ɗauke da ƙaramin towel,wajan dressing mirrow ta nufa tare da juna handrayer ta busar da gashin kanta,buɗe ƙofar akai aka shigo ɗauke sallama,ganin Mamace yasa ta saki fuskarta,wajanta ta ƙarasa hannunta ɗauke da kaya,zama tayi kan stool ɗin dake gefen dressing mirrow,bata kalli Lili ba ta shiga zuba wani magani a glass cup sannan ta siyaya madara ta ruwa tasa spoon ta juya fuska babu walwala ta miƙawa Lili danta san halinta daƙin magani,ganin yadda Mama ta haɗa rai yasa ta amshi magani ba dan tana so ba,saida ta shanye tas sannan Mama ta miƙa mata wata zuma nanma ta amsa wannan karan hadda tanɗe baki sbd daɗin zumar,Hucewa Mama tayi ta nufi toilet ɗin Lili ta haɗa ruwa mai zafi tare da zuba turare a ciki kana ta dawo ta ɗauki wani ƙwabaɓɓen yellow abu a ruba ta shiga shafawa Lili a naked body ɗinta,Mama irin mutananne da babu ruwansa da batun kunya indai akan harkar gyara ne kanta a waye yake tana da sauƙin kai sosai shiyasa mutane keson zama da ita,bayan ta gama tace"nan da 30mins kije ki wanke jikinki sannan ki shiga ruwan zafin dana haɗa maki,idan kika fitu wannan lotion ɗin shi zaki shafa ga boner ki juna ki zuba turare ki tsuguna ya ratsa jikinki sosai"tana faɗin hakan ta juya zuwa wajan Fannerh.
Duk yadda Mama tace tayi saida tayi,hakan yaza mana kamar an sauya mata halittar jikinta banda ƙamshi babu abinda ke fita a jikinta,skin ɗinta kam har wani yellow yake sabida gyaran da yaji ta zamana kamar ƙwai ko ina shaning yake musamman fresh skin ɗinta,a gaggauce ta gabatar da sallah tare da hawaye bed ta rufe jikinta da duvet lkc kaɗan bacci yay gaba da ita sbd gajiya.
Bayan Mama ta kammala abinda take tayi wanka ta shirya cikin kayan bacci,dabarar yiwa Fahad MSM ta email ɗinsa ta faɗu mata,cikin sauri ta ɗauki wayarta tare dayi masa tana gamawa ta kashe bacci fal idanunta hakan yasa ta ƙwanta nan bacci itama ya ɗauketa.
Ranar Asabar aka gabatar da Henna day yayinda abin yay armashi amare aka tsara masu jan lalle na salatif har zuwa saman ƙafarsu,faɗin ƙyanda Henna ɗin yay ɓata lkcne dake gaba ɗayansu farare ne,haka aka haɗa da traditional wedding aka kama amare,Lili kam kuka tasa akan ita babu mai fesa mata wani turare abarta da abinda ta keji,kowa yay mgn tai burus dashi hatta Khalid saida yazu shiku albarkacin kallo a wajanta bai samu ba,wajan ƙwanansu uku amma ko gaisuwa bata haɗasu ba,saida Mama tazu da kanta sannan ta bari aka kamata kamar yadda ake kama sauran amanare,kuka ta fashe dashi kowa na wajan yasa mata dry ƙanƙame Mama tayi ta shiga rera kukanta"Haba Uwata ta kaina ya isa haka,baza a ƙara ba"ta faɗa tana bubbuga bayanta har saida tayi shuru,ba'a tashi wajan ba sai bayan isha'i.
Jikin kuwa a gajiye suka shigu cikin gidan,a gaggauce Lili tayi wanka ta gabatar da komai nata kasan cewar ba sallah zatai ba domin tun safe period yazu mata,tana gamawa ta ƙwanta tare da lulluɓe jikinta.
Daman yadda tsarin yake sai anyi ɗaurin aure da yamma kuma ayi mothers day,da daddare kuma ayi dinner Sai award for the best couple.
Juyi yake kawai akan bed zuciyarsa taki nutsuwa sai azalzalarshi take yaje gareta,musamman idan yaji mararsa ta murɗa masa,amma idan ya tuna gobe iyanzu ta zama mallakinsa sai kawai ya share,a hankali yake murza mararsa data kumbura ciwo yaci ƙarfinsa,ganin idan bai bawa kansa taimaƙon gaggawa ba kamar yadda ya sama zai iya samu matsala,tashi yay tare da zare dugun wandon jikinsa yay cikin toilet,yana zuwa ya haɗa ruwan zafi tare da cire sauran kayan jikinsa ya shiga cikin ruwan,a hankali a ɗura hannunsa saman mararsa ya shiga jijjigawa,wajan 20mins da fara ya ɗan saki ƙara hakan ya tabbatar masa daya samu sauƙi daga sexcy pain ɗin da yake,wakan sarki yay sannan ya fitu jikinsa ɗauke da towel,kan bed ya faɗa ya daɗe kafin bacci ya ɗaukesa.
Ceremony
Yauta kama Sunday ranar da za'a ɗaura aure,tun safe ta shige ɗaki ta ɗinga kuka ko abinci taƙi ci a wannan karan ba iya Booby take kira ba,hadda Mamy da Daddy haɗi da Faisal😢ita kanta mama zuciyarta tayi rauni hakan yasa ta shige ɗaki ta fara kukan rashin yayan nata,da ƙyar mijinta ya rarrasheta wanda yay shiguwar cikin dare,misalin ƙarfe baƙwai mai makeup ta ƙarasu inda aka tsarawa amarya Fannerh yayinda Lili tace bata buƙata a barta,girgiza kai kawai Sufyan yaya tare da miƙewa ya nufi ɗakinta,a ƙwance ya sameta sai sakin ajjiyar zuciya take,tana ƙwance daga ita sai towel iya waist ɗinta,numfashin sane ya ɗauke na wani lkcn sosai skin ɗinta da kuma ƙamshin dake fita a jikinta ya nemi zautar dashi,"lovely bbyn nine baki so ko auren yau kikemin hakane ba zakiji tausayina ba?"luff tayi tare da lumshe idanunta ba tare data tankasa ba,haurawa yay saman bed ɗin tare da birkitota ta faɗa jikinta,saurin dafe ƙirjinta tayi haɗi da suma girgiza kanta,wani shu'umin murmushi yay mata kafin ya sunkuyar da kansa zuwa wajan kunnanta,iskar bakinsa ya shiga wura mata tare da tura halshansa cikin kunnanta ya shiga lasa,runtsa idanunta tayi lkcn hawaye ya samu damar zubuwa daga cikin idanunta,cikin rawar murya tace"banso pls kabari"cikin da ƙushewar murya yace"ni inaso bari kawai na mallakeki a nan tunda kinki fita a shiryamin ke nima na samu damar shiryawa naje a ɗaura mana auren"da sauri ta ƙwance jikinta tace "zani wallahi zani"tana faɗin hakan ta zari hijab ɗinta tayi ɗakin da ake makeup ɗin,ya daɗe zaune yana maida numfashi kafin ya miƙe ya nufi ɗakinsa.
Ɓangaren ango Fuwaz ba'a magana ya haɗe cikin light blue ɗin shadda wacce taji ɗinki riga da wando da kuma babbar riga,yayensa Suwaiba da lawiysat sai kuma sauran ƴan uwansa,misalin 10:30 abokansa suka shigo tare da ficewa dashi daga cikin gidan domin 11:00 ɗaurin auren,rashin Fahad a wajan ba ƙaramin ɓata masa rai yay ba amma ya share.
Sosai aka shirya Lili cikin duguwar riga ta shadda mai kalam milk ɗinki Bubaa yaji zare,idan kaganta sai kazu ƙara kallonta ta kuma kamar ƴar tsana,Sufyan ma ya shirya cikin ash ɗin shadda mai ƙyau babu babbar riga daman bai fiya sonta ba,amma yay ƙyau har ba'a magana.
Mutane kake gani kota ina babu matsakar tsinke kowa yana cikin farin ciki,musamman angwaye Sufyan da Fauwaz,addu'a aka fara gabatarwa kana aka amshe neman aure daga ku wanne ɓangare,inda Khalid ya zama Uba a wajan Lili ya bada aurenta wajan Sufyan,yayinda Alhaji mahaifin Sufyan ya bada auren Fannerh zuwa ga kawon Fauwaz,Uncle Mahaifin Fannerh ya amshi auren Sufyan da Khalid ya bashi,cikin farin ciki aka fara addu'oin ɗaurin auren,wata muryace mai sautin da amo ta sauka a tsakiyar wajan,malamin ɗaurin aurenne yace"Yarona lafiya dai" idanunsa da sukai matuƙar jaa suka ɗan rage daga girmansu ya zubawa Sufyan,yayinda Fauwaz kuma ya zubawa Fahad idanu yana mamakin dawowarsa,yana tsaye cikin shiga ta alfarma,sanye yake da farar shadda getzner yasha babbar riga sai walwali yake,haiba da annuri sun cika buskarsa hakan yasa kowa ya gagara ce masa ƙala,cikin tausassiyar murya yace "stop the ceremony" wani mugun kallo Sufyan ya watsawa Fahad cikin fusata yace"waye kai? Wanne matsayi kake dashi? Meye dalilinka daza kace a tsaya da ɗaurin aurena?" ya faɗa lkcn dake miƙewa tsaye ya nufi inda Fahad yake tsaye ya harɗe hannayensa,shima cikin ƙaraji da nuna cewa zuciyarsa a kusa dake yace "because she is my wife".
*Dan Allah dan Annabi idan har kinsan na faranta maki rai a wannan shafin ina neman alfarmar kiyi share ɗinsa zuwa groups ɗin da kike👏🏻👏🏻,idan kinsan kinyi farin ciki da abunda ya faru da Allah kiyimin Comment mai ma'ana pls,daga ƙarshe ina neman addu'arku ku tayi da addu'a pls🙌🏻ina maku sahihiyar ƙauna masoyana masoyan Juyayi😘*
F@y@l
*💖JYY💖*
*38-39*
```SARAUTA``` 👸🏼
*_@Telegram_* https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ
*Dedicated to*
Yaya Mu'az, Bro Muhammad Ibrahim, N.yareema, Fa'at class, Hassan basiru,Muhammad kareem, Al'amee, ```kuna ƙoƙari sosai Allah ya saka da alkairi😍``` 👏🏻
Not Edited
..A hargitse Sufyan yayu kan Fahad,Fahad na ganin hakan ya gyara tsaiwarsa tare da harɗe hannayensa a ƙirji,Wani shu'umin murmushi yaywa Sufyan,cikin kiɗima Sufyan yace"wat are you try to see?"gira Fahad ya ɗagawa Sufyan tare mutsa jajayen laɓɓansa yace "i knw u alry heard wat i'm say" wani mugun damƙa Sufyan ya kaiwa Fahad tare da faɗin" are u crzy matar da zan aura kake kira da ur wife,a wajan ɗaurin aurena da matana zaka kawumin maganar shirme kace matanka ne"lumshe idanu Fahad yay tare dayin wani murmushin gefen baki wanda ya ƙarawa fuskarsa ƙyau haibarsa ta ƙara fituwa,annurin dake fuskarsa ya ƙara bayyana,cikin lion voice Fahad yace "Ka daina haɗa kanka da macen da take mallakina,she's always mine not urs understand"ya faɗa cikin ƙaraji da kuma nuni da gargaɗi,ganin rigima nasun kaurewa tsakaninsu yasa gab ɗaya aka zaunar dasu,Fahad ne ya ɗaga kai ya kalli mutum dake gefensa wanda ko ba'ai magana ba yasan jinin Mamynsa ne,cikin fahimtar juna Alhaji wanda ya kasance uba a wajan Sufyan yace "Dr Fahad yaya akai Matar da ake shirin ɗaura mata aure da wani kazu kace matan kane,Alhalin kuwa yasan cewa ita single ce bata taɓa aure ba"jinjina kai Fahad yay tare da ɗan tafa hannunsa saiga Musty yay sallama tare da shiguwa cikin parlour,cikin muryarsa wacce take ɗauke tada jurumta yace "Musty karanta wasiƙar nan a fili yadda kuwa zaiji"
Babu ɓata lkc Mutsy ya buɗe takaddar hannunsa tare da gyara tsaiwa yace.
_Na san kuwa zai mamakin yadda Lubna zata kasance mata a wajan ɗana Fahad,Tabbas Lubna matsayin ƴar take a wajena amma a zahiri banine Mahaifinta wanda ya kawota duniya ba,Lubna ƴarce a wajan ƙanwata Fatima ita kanta bata san da hakan ba sai yanzu idan ta samu labari, wata rana kafin raɗin sunan ƴar da mamata ta haifa da kuma twinst ɗin da ƙanwata ta haifa kasan cewar ta dawo wajena da zama kafin arba'in,ta shine daga zaunan na nufi waje tare da shiga mota na amso wani saƙo wajan abokina wanda ya kasance Miji a wajan ƙanwata Fatima,bayan na shiga mota na dawo ina gaf da shiga gida naga wasu mutane sanye da fuska na girgiza sosai ganin gida suke kallo ba tare dason ganni ba,na rufe glass ɗin mota ta kasan cewar baƙina babu mai ganina na gangara gefen titi,abinda naji mutanan suna faɗa yay matuƙar ɗagamin hankali ɗaya daga cikinsu ne ya ƙara faɗin "Dama ɗaya ce garemu dole ne acikin yara ukun nan mu ƙwashe guda biyu,to dole zargi zai shiga tsakanin yaya da ƙanwarsa,kaga zata kaishi ƙara ƙilama a yanke masa hukuncin kisa,daga nan mun gama da ita domin a plan ɗinmu babu ita zamu koma kan matarsa Khadija domin ɗaukan fansa" cikin tsoro na ƙara mai² ta kallamar “Fansa” wacce fansa? Shine abinda nake ta tunanin har lkcn dana rubuta wannan wasiƙar ban samu amsa ba,dan haka Lubna ƴar uwace a gareka Fahad “Afnerh” itace ƴarta amma bama mata kallon ƴar wannan Lubna itace farin cikina jin daɗina,bayan na gama jin abinda suke cewa har suka bar wajan ban kunna mota ta ba,bayan sun tafi na shiga cikin gida ina zuwa na tarar dukkansu suna bacci,ƴarta na ɗauka sannan na shiga ɗakin ƙanwata Khadija na ajjiye na ɗauki ɗaya daga cikin yaranta,kasan cewar