Follow us on social media

Showing 18001 words to 21000 words out of 79519 words

Chapter 7 - JUYAYI Raunin da Ba Ya Warkewa by Nimcyluv

05 Aug 2026

69

nasa rabon,ganin Asuba na shirin yasa suka gaggauta fita tare da yanke shawarar cinnawa gidan wuta sabida basa su subar wata shaida da zata nuna sune suka aikata hakan,Gaba ɗaya suka watsa gidan petir tare da cinna masa wuta cikin sauri suka shiga motarsu tare barin Estate ɗin gaba ɗaya.
Maƙota kuka banda kuka babu abinda suke gashi babu damar fituwa kaima kayi silar naka ran amma dukkan Harbin da Arm robbers ɗin suke sunaji,Babu abinda ya ƙara ɗaga masu hankali sai wutar dasu kaga tanaci har saman gidajensu suna ganin hasken wutar,A dai² lokacinne aka fara kiran sallar asuba dalilin hakan yasa mutan unguwa suka firfituwa daga cikin gidajansu lokacin wutar ta gama cinye komai sai motocin da suke compound na gidan sune kawai wutar bata taɓa ba,Nan unguwa ta cika da kukan jama'a sabida kowa yasan waye Alhj Mustapha Rano mutum ne kowa mai son talakawansa da kuma son taimakasu cikin lamuransu kowa nasa ne ya ɗauki kuɗi masu yawa ya bawa mutum ba komai bane kana zaune zaice ya biya maka zuwa Hajji bana,Sosai akai baƙin ciki da rashin a dalin mutum kamarsa da ƙyar aka samu mutane suka shiga masallaci a kayi sallah tare dayi masa addu'a shida iyalansa kowa na faɗin "Allah sarki Najma ita tana da tsahun raine shiyasa tunda safe aka miƙata gidan mijinta wannan yarinyar Allah ne kaɗai yasan tashin hankalin da zata shiga" kowa dai da kwai abinda zaice a haka gari ya ɗanyi haske kafin wani lokacin unguwar ta cika da Ƴan jaridu da kuma manyan Ƴan sanda masu faɗa aji.
Ganin babu wata jana'ida da za'ai sabida gama ɗaya gidan ya ƙone ƙurmus haryau da raguwar wuta naci kaɗan² yasa aka rufe gidan gaba ɗaya ta hanyar saka ƙata gwaɗo a gate ɗin gidan zuwa 7 na safe kowa dukkan wata media tasan da labarin mutuwar Alhji Mustapha shida iyalansa gidan T.V,Redio,Wasapp,Facebook,istagram, Da dai² sauransu Addu'a kam sun shata wajan mutane tare da addu'ar bayyana dukkan wanda ya aikata masu wannan ɗan yan aikin,Haka ƴan sanda suka gama bincikensu amma babu wata shaida da zata nuna ga wanda sukai wannan abun.


Maidugori road.
Tunda aka kaita da idanunta ba zata taɓa cewa taga Faisal ba, any tym tana flat ɗinta dake cikin makeken gidansu Faisal ɗin banda sallah da wanka babu abinda yake tayar da ita a haka har dare yay mata,Daren da yayi mata tsayin a cikin daren ranakun rayuwarta gaba ɗaya ta gasa bacci sai juyi take a tsakiyar bed ɗinta tym to tym gabanta na faɗuwa ƙirjinta na bada sauti tsoro da fargaba haɗi da kuma dana sanin abinda ta aikata ya gama ziyartar zuciyarta,Taci amana ƴar uwarta amana mafi muni tafi kowa sanin shaƙuwa da kuma soyayyar dake tsakaninta da Faisal tabbas idan labarin soyyayar Faisal da Lili zata bawa mutum tana iya yini da kwana bata kammala ba,Idan rubuta labatin zatai kowa zata iya rubuta Episode 50 a haka saidai ya tashi a season tabbas ta zama butulo kuma maci amana cin amanarma ta ƴar uwata ta jini ina zata kai wannan haƙƙin wanne hali Lubna zata faɗa ta sanadiyar hakan? Allah shine kaɗai ya sani domin abune mai wahala mutum ya ganu gaskiyar abinda ke zuciyar Lili duk da hausawa sunce bayanin zuciya a tambayi fuska to ita ko face ɗinta baya showing abinda yake ranta tana da zurfin ciki fiye da tunanin mutum da wahala mutum yay mata abu kaga ta nuna baƙin cikinta ko damuwarta kenan hakan yana nufin na haddasawa Lili baƙin ciki da kuma damuwa a ranta wanda bazai taɓa gogewa ba,Wasu zafaffan hawaye ne suka ƙara sauka daga cikin idanun a lokacin data tuna bawai Lili bace ta wargatsa aurenta sannan kuma ba ita bace ta jewa da Dad akan tana buƙatar a haɗa auren Faisal da kuma Najm ba,ƙara juyawa tayi a kan bed lokacin da komai ya fara dawowa cikin brain ɗinta haƙiƙa tayi wawta da kuma sakalci toshe bakinta tayi jin kuka na neman ƙwace bata,Mai yasa ta aikata hakan meyasa ta rusa rayuwar Lili cikin sauƙi haka tunawa da lokacin da Lili ta shiga ruɗu tayi a lokacin data fahimci kamar Boobi yay rapping ɗinta bata san cewa duk Najma itace sila ba🙀.
Wanni ɓangare na zuciyarta kuma yana tuna mata zallar soyyayar data kewa Faisal a lokacin da idanunta suka fara ganinshi a lokacin ta fara ƙaunarsa a ranta ƙunar da bata taɓa yiwa wani ɗan adam ba face iyayenta,Sosai take mutuwar ƙauna da kuma son Faisal har tana jin zata iya komai domin ganin ta mallakesa ya zama nata ita ɗaya,Ta jima tana danne soyyayar Faisal da kuma muradin kasancewa dashi sabida ƙanwarta Lili ba tasu ta fallasa a sirin zuciyarta sabida Lili domin tasan koda zata rasa ranta zata iya haƙura da Faisal ta mallaka mata shi a matsayin masoyi shiyasa tabi komai cikin ruwan sanyi yau gata a ɗakin masoyinta Faisal kuma a matsayin matarsa amma saidai tana jin kamar ta aikata babban kuskure ganin idan bata cire tausayin Lili a ranta ba zaija mata itama ta rasa buri da muradin ranta yasa ta tattara komai ta ajjiye a gefe ya zauna Faisal babu wanda yake mata gizu cikin idanunta a haka bacci yay gaba da ita bacci mai cike da mafarkai mara kan gado.

Misalin 7 na safe ta fitu daga flat ɗinta cikin shigarta ta alfarma sai baza ƙamshi take,Tafe take tana ɗan ƙifta ƙananun idanunta sabida yadda ta kejin gabanta na faɗuwa a haka ta ƙara flat Ammi domin gaidata,Tun daga nesa ta kejiyo kukan Ammi sama² cikin sauri ta ƙarasa shiga cikin parlour mutuwar tsaye tayi ganin Faisal yashe gaban Ammi ko motsi ba yayi gefe guda kuma family Doctor ɗinsu ne yake du basa,Ɗaya ɓangaren kuma Papa ne zaune akan sofa ya zabga uban tagumi yayinda idanunsa suka sauya kala daga fari suka koma jaa sabida tension ɗin da yake ciki haƙiƙa rashin Aminin nasa ba ƙaramin ɗaga masa hankali yay ba da kuma da gula masa lissafi yayi ba.

A hankali ta ƙarasa shigowa ɗakin lokacin hawaye ya gama wanke mata fuska duk da bata san abinda yake faruwa ba,Ganin Najma a cikin parlour ga ƙara Ammi sautin kukanta domin ta tabbatar idan ta samu labarin mutuwar iyayen nata ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba ko kuma itama zuciyarta ta buga ayi mai gaba ɗaya dan haka suka yanke hukuncin ba zasu faɗa mata ba sai komai ya dai² ta.
Zama tayi ƙasan carpert ɗin tare dasa hannu ta shafi sumar kansa a lokacinne wasu hawayen suka ƙara sakkowa daga cikin idanunta zuwa kan fuskarsa,Ammi ce ta goge nata hawayen tare da faɗin "ba kuka ya dace kiyi ba addu'a ita ya dace kiyi a dai² wannan lokacin ki sama ranki cewa akwai ƙaddararsa babu wanda zai ɗauki ƙaddarar wani ya ɗurama kansa,Dukkan abinda ya faru da mutum hakan a tsare yake wajan ubangiju so take it easy kiyi addu'a wa mijinki da kuma iyayenki da suka aura masa ke kiyi godiya garesu ki bisu da addu'arki mai albarka".
Shuru Najma tayi tare da zurfafa bran ɗinta wajan yin tunani amma ta gagara tunanin komai zuciyarta da kuma ruhinta mijinta kawai suke fata gani a yanzu curewa waje guda tayi tana mai jin dama daga ita sai shine kawai a duniyar inama ace yanzu iyasu biyu ne babu su Ammi da babu abinda zaisa taƙi kwanciya cikin mijinta ɗumin tayi missed daddaɗan ƙamshinsa haɗi ɗumin jikinsa da kuma sweet saliva ɗinsa lumshe ido tayi ta ƙara cure waje guda tana jin kamar lokacinne yake sucking bakinta tare da zuba mata daddaɗan miyun bakisa mai garɗi da kuma zaƙi.


Ƙauyen Yola.
Tunda aka shimfiɗe Fahad bai farkaba har zuwa yanzun da ake kiran sallar magrib yana shirin kwana a kwance kuma cikin mawuyacin hali domin ɗagawar da ƙirjinsa keyine kawai zai tabbatar maka yana da rai.
Duk wata kulawa daya dace a bashi ayi musamman mustapha shikam Babu Habu kira yake "ka gama kiwansa ya samu lafiya yazu yay kidnama ɗinka wallahi ko sisina bare kuma shanuwana ato,Mutane babu tsoran Allah a ransu musamman mutum mai ƙuriyar fata ka gani satsaɓar shan jinin mutuna har ƙure yake" Ai kamar ance Baba Habu ya Juya yana juya ya gansa tsaye akan ƙafafunsa ga yadda surar jikinsa ta bayya musamman muɗaɗɗiyar damtsen hannayensa ga yadda ƙirjinsa ya ƙara faɗi yawataccen gashin ƙirjinsa yay luff sai gyalli yake nipples ɗinsa sunyi tsini tare da yin red,Da gudu Baba Habu ya saki sandar hannunsa tare da kurma ihu haryana faɗuwa cikin sauri ya shige ƙaramar bukkarsa yana faɗin "Wayyo kayimin rai kidnma shanuwa biyar gareni🤣...
*Nimcyluv ce😘*



*NIMCYLUV MARUBUCIYA*
_Assalamu Alaikum_

Hey Guys I hope all of you are fine?,So I want to thank you all for supporting me thank alot may Allah bless you all.

I knew most of you are following my new book JUYAYI (the secret issue) right?.

So I have a wonderful and amazing game for you guys but only wattpad readers can join the game.

Madam if don't have wattpad appilication I want to say sorry for yourself because you miss it, it gonna be 💃🏻👯🏻‍♀️.. Understand? .


I'm so sorry naƴi intertement ne GAME ɗin dai kashi biyu ke akwai WRITERS akwai READERS muda kanmu zamu zaɓi wanda za'ai Game ɗin dasu daga writer zuwa readers, dukkan maiso zai iya yin searching ɗina a Wattpad *Nimcyluv* sannan yayi following ɗina ta yadda idan akwai announcement zai gani cikin sauƙi.

Kada kayi tunanin shira zamuyi da mutum idan hirana ne muna dasu kala².

Akwai
Coffee with heroine in english, wanda MaimunaAbdullahi ke gabatarwa da hausawanmu da kuma yare. @⁨+234 816 712 0325⁩

Sai kuma.
Zauren MissMeemah on wattpad da ake gabatarwa iya hausa zallah @⁨Kitty😘⁩ .

Ina fata zakuyi following ɗinsu, Game ɗina zaizo maku as happy new year idan kinsan baki da wattpad yana da kyau kije ki ɗauko a play store domin har gift zaki iya ci a wannan game ɗin.

Ina buƙatar jin ra'ayinku ta hanyar yimin messages 08119237616 Writer or Reader duk kuna da damar bada gudunmawarku a wannan tafiyar🥰🤗.

Nasan ba lallai ku fahimci wacce game bace amma indai za kuyi following ɗina zaku iya fahimta ngd sosai da kuka samu damar karanta saƙo na thank for dat.


*Wattpad@Nimcyluv*
*Sat/Dec/26 9:23pm*

```💖THE SICRET ISSUES``` 💖
*JYY*
*10-11*
Wattpad@Nimcyluv


*Happy new year*
Dear 2021
Be the best new year please, There's so many traggicc happen in.
2020
I hope that in coming 2021.
No killings
No viruy
No War
Spread peace and love, we hope that.
2021 will be the best year to come 🙌🏻. *Happy new year to all my Fans and Fam🤾🏻‍♀️*

......Fahad kam sam bai fahimci abinda Baba Habu yake faɗa saima ƙara zuba masa shanyayyun idanunsa yay zuciyarsa fal mamakin abinda ya kawoshi yay yasan kaf a tarihin rayuwarsa bai taɓa saman ƙauye ba,Musamman wannan ƙauyen daya fahimci zallar fulanine a cikinsa lumshe tsumammun idanunsa yay tare ds cije lips ɗinsa sosai kansa keyi masa bala'in ciwo ga kuma yadda zuciyarsa keyi masa zafi.
A hankali komai daya faru iyayen masu sonsa da ƙaunarsa ya shiga dawowa cikin brain ɗinsa dama ƙwayar idanunsa,Babu abinda yake damunsa a rai wanda har yanzu yake masa sauti cikin dodon kunnan wato lokacin da ƙarar harbin bindigar ya tafi da ƙarar mahaifinsa wanda ya tabbatar zuwa yanzu ya rigasa gidan gsky.
Me suke so?..waya turusu har suka nunawa iyayensa wannan zallar rashin imani da tsusayin,Hannu yasa ya shafi kwantaccen gashin ƙirjinsa wanda yay baƙi siɗik sai ƙyalli yake,A hankali ya ɗura hannun nasa a saitin zuciyarsa tare da murzawa jin yadda take buga masa kamar zata fito waje ji yake kamar yayta kurma ihu amma bazai iya ba sabida baison raunisa ya bayyana har haka,Yasan iyayensa a yanzu ba kuka suke buƙata ba addu'arsa kawai yake buƙata zuwa yanzu baya da burin daya huce ya gano wanda sukaiwa iyayensa haka.
Jin an taɓa kafaɗarsa ne yasa ya buɗe gajiyayyun idanunsa tare da ɗurasu akan fuskar Mustapha ko kallan 2min baiyi masa yaja idnunsa ya kulle tare da ɗan jingina bayyansa da bukkar dake kusa dashi "I most go" shine kawai abinda ya faɗa cikin zuciyarsa,"Ga motarka can nasa an petir an zuba maka a ciki" maganar Mustapha kenan wacce ta ƙatse masa tunaninsa,Ware manyan idanunsa wanda wuka ƙanƙance a yanzu yay tare da mannasu a kan Mustapha'n ɗan lumshe ido yay tare da jinjina kansa alamar "Thank you" raɓawa yay ta gefensa tare da bin hanyar da yake tunanin itace wacce zata sa dashi da waje,Cike da kwarjini haɗi da haiba mutanan ƙauyen ke kallonsa musamman ƴan mantan da suke zaune a wata ƙasan bishiya ɗauke da ƙoƙwan nono a gabansa,Ƙara tamke fuska yay tamkar bai taɓa dariya ba koda yake ni kaina bana ce na taɓa ganin dariyar Fahad Mustapha Rano ba.
A hankali yake tafiya tare da bada faɗi cikin isa da kuma gadara wacce ta riga ta zama jinin jikinsa a haka ya ƙarasa inda motarsa take ajjiye tsaf da ita sai ƙyalli take da alama tana shan wanki wajan Musty.
Yana zuwa yasa hannu ya buɗe motar tare da shiga ya zauna a kan kujerar drever,Lumshe gajiyayyun idanunsa yay tare da fitar da wani huci mai zafi tunawa yay da files da kuma takaddar da Dad ya bashi ne yasa yay sauri juyawa ya kalli gefensa baƙar jakar ya gani ajjiye a gefen kujerar cikin sauri yasa hannu tare da ɗaukan jakar ya buɗe files ɗin ya ɗaukko ya shiga dubawa.
Wasu zafaffun hawaye ne suka taru a cikin idanun ba tare da sun zubu ba,taune jajayen laɓɓansa yay yana jin wani zafi da kuma ciwo a cikin zuciyarsa sosai yake baƙin ciki da kuma takaicin rayuwarsa a kan idanunsa an kashe masa iyaye amma baya da ikon hana faruwar hakan,Sosai yay mamakin ganin files ɗin ashe duk ƙadarurin Dad ɗinne hatta A.T.M ɗinsa wajan guda 10 tare da Pin ɗinne kowanne a rubuce jikin wani files hatta Banks ɗinsa da suke ƙasar waje ko wanne da bayaninsa.
Ajjiye files ɗin yay a gefe ya ɗauko takaddar daya basi guda biyu ne ashe ba ɗaya ba,Guda ɗaya ya fara ɗaukkowa yaga ansa.

_From Mustapha to my lovely son Dr Fahad._

Wani wahalallan numfashi ya sauke tare da ƙara dafe saitin zuciyarsa wacce take ƙoƙarin fasa ƙirjinsa ta fitu,Ɗaya takaddar ya ɗauka tare da dubawa itama rubutu akai a jiki kamar haka.

_From Mustapha Rano to Mamana i wish u all the best zanyi kewarki,Insha Allah ko bayan babu raina ba zaki kukan maraici ba kina da yaya wanda yake tamƙar uba a wajanki Mamana kina da gata gaba da baya Booby yana tare dake i love you._

Kansa ne ya buga da ƙarfi yayinda zuciyarsa ta shiga tunanin sunan da yaji an ambata na "Mamana" wace haka tunawa da itane taya jikinsa ya fara rawa jijiyoyin kansa suka shiga miƙewa idanunsa ya sauya kala har wani ruwa² yake sabida tension bakinsa na shaking yayinda teath ɗinsa suke haɗewa suna bada wani sauti ƙas...ƙas...ƙas cikin hawalalliyyar murya yace "Liliana.. She is not OK" ya Kai maganar muryarsa na creating.
Yaya akai yabar gidan ba tare daya tuna tana ciki ba? Meya aikata yanzu yaci amanar da Dad ya bashi kenan jiyayi gaba ɗaya duniyar tayi masa girma gaba ɗaya yaji ya tsani rayuwarsa domin idan zai manta da ita tamkar zai manta da kansa ne ko kuma ya manta wasiyar Dad ɗinsa she is to yought she can't life without mentor "Where is she now?" itane tambayar da yaywa kansa ne cikin sauri ya buga kansa da jikin ƙofar motar lokacin daya tuna acikin gidan ya barta shida kansa ya kaita ɗaki ya kwantar saida ya tabbatar ya rufe mata ƙofar ɗakinta sannan ya huce ɗakinsa.
Cikin sauri ya ɗauki wayarsa wacce take cikin jakar yay daining numberta abunda yaji yay matuƙar ɗaga masa hankali wajan 10 miss calls yay abu ɗaya ake gaya masa shine "a kashe take" notipications ne suke ta shiguwa wayarsa ganin haka ya shiga B.B.C news sbd yana buƙatar sanin wani abu.
News farko shine wanda yafi ɗaga masa hankali ya sashi cikin shiga firgici wanda bai taɓa shiga irinsa ba,labarin mutuwar iyayensa da kuma wutar da aka sakawa gidansu yasa yaji zuciyarsa tayi irin bugawa wanda hasa yay saurin sa hannu ya danne zuciyarsa.
Zai jure komai na rayuwarsa amma banda ita domin zannan ƙaddararsa haɗe yake da tata,Rashin kamar tsawar numfashinsa ne ko kuma tawaya a rayuwarsa,idan duk duniya za'ace ta mutu shikam bazai taɓa yarda da hakan ba, she's a life tabbas da bata numfashi da tuni numfashinsa ya daɗe da ɗaukewa.
Buga ƙofar da a kaine ya dawo dashi hayyacinsa wani ajjiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke tare da ɗaga rinannun idanunsa wanda suka gama yin jaa ya mannasu a kan Musty.
Cikin daƙushasshiyar muryar mara sauti yace.
"i have to go now".



_Abuja private hospital_
A hankali yasa hannu tare da ɗura akan handle ɗin ƙofar ya murɗa ya shiga bakinsa ɗauke da sallama Momma wacce take zauna gefen bed ɗin marasa lafiyar ta amsa masa sallamar cikin muryarsa mai cike da jarumta.
Kallonsa tayi ganin bashi da niyar magana yasa tace"Sufyan me Dr ɗin yace?" ɗago kai yayi ya kalleta cikin muryar damuwa yace"he have noting to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login