Follow us on social media
Showing 99001 words to 99941 words out of 99941 words
Rasheed ya dauketa sukaje har Jos suka shiga rugarsu abin mamaki bata taba
ganin rugar data samu ci gababa kamar rufar Wandu an gyara musu ita harda makaranta da
hanya ga wutar NEPA ta aminta mutane duniya sukeyima bauta Wai yau itace Baffa Ribado da
Baffa Bangel suke kuka suna bata hqr akan abubuwan da suka faru da irin sharrance
sharrancen da suka rinqa yi mata.
Murmushi kawai takeyi tana share hawaye lkc bayan lkc da dare ne bayan komai ya lafa take
tambayar Ina Hammah Manga nan aka zauna ana bata labarin Wai an kasheshi a dalilin
kidnapping din wani Dan siyasa da sukayi sojoji sukaje sukayi barin wuta akansu ko gawarsa
baa tsinta ba.
Sosai ta jinjina lamarin tare da yimasa fatan rahama ta kwana dayanta a dafe wai saigashi sune
harda soya mata manshanu da tatso mata danyar Madara Baffa Moddibo yayima Sarki da
Muneefah kyautar saniya aikuwa Sarki yace saidai a daukar masa abarsu dake ba wata babba
bace Rasheed da taya bera Bari yasa aka daureta aka sanyata a mota sunata yi musu dariya
suka dauki hanya cike da jin dadi zuciyar Juhud yan uwan da suke qyamarta yau itace suke
qauna sunata Sanya mata albarka da abubuwan alkhairin da suka samu ta dalilinta.
Cikin wata biyun da sukayi suka juya Lagos hada kan yayansu suka tafi daga Muneefan har
sarkin aka Sanya a makaranta taci gaba da rainon cikinta suna qara samun shaquwa da kula
da juna da haka cikinta ya isa haihuwa ta dawo Daura Kwananta uku da komawa kuwa ta
sunkuto yaranta uku wannan abu ya tsuma dangi ita kanta tayi mamaki saboda cikin nata ba
wani shararren girma yayi ba sannan ko a hoto biyu suke cewa da ita sai gata da uku duk maza
nan fah wannan family ya kacame kowa mgnr haihuwar yakeyi ranar suna yaran sukaci sunan
Babban Haroon mai bi masa Abubakar sai Abdulkareem qaramin aikuwa ansha shagali kamar
baa taba yiwa wannan Fam Haihuwa ba kama daga Daura Mali da Jos kowa yayi bajinta su
Rasheed harda kyautar kujerar hajji yayima mutum uku Baffa Moddibo da Baffa Ribado da
Baffa Bangel saboda murnar wannan haihuwa.
Bayan komai ya lafa yaso su koma Lagos ta kafe Saida tayi arba'in sannan suka koma da qarin
me raino daya Ladi itama mutuniyar kirki sukaci gaba da rayuwarsu cikin gdyr Allah da
amincewarsa Rasheed kullum likkafa ci gaba takeyi yau matsayin General Rasheed Gen
Mahfuz yake amsawa inda makarantar Meenah kullum take qara habaka abin gwanin birgewa
da hamdala shekara biyu Meenah ta qara haihuwar ya mace daga kanta tace ta gama abinka
da yan bokon qarshen zamani suka fita India aka juyar da mahaifar gabadaya ta dawo taci gaba
da kula da yaranta.
Sannu a hankali maqiyanta irinsu Fadila Dada Hanne Hajiya Bilki da wasunsu na boye sai gashi
duk sun zama yan koranta idan taje Daura har zuwa sukeyi gaisheta musamman Fadila data
zame mata kamar aminiya yanzu duk duniya bata da qawar data wucce Meenah hakan ya
samo asali ne daga yanda Meenah ta shiga ta fita taga sun daidaita da mijinta ya mayar da ita
dakinta cikin yayanta, itama Addah Abulle daqyar bayan auren datayi Mai Martaba ya dawo da
ita dakinta inda ta dauki soyayyar duniya ta dorawa yaran Meenah guda biyu Muneefah da take
yar danta da Kuma Kareem qarami da yaci sunan danta duk wani tanadinta nasune sauran
jikokin gdan har tsiya sukeyi mata wai ita ta fiye son kai, itadai Meenah saidai tayi dariya tana
mamakin yanda komai ya wucce kamar ma baayi ba idan tai tsai sai kawai taji hawayena
tsiyaya a idanunta da zaran ta tuna yanzun muma duka wataran shudaddu ne gushewa zamuyi
a manta da tarihinmu mu dusashe kamar baa haliccemu ba, a wannan ritsin tsoron Allah yake
qara ziyartar ruhinta takanji duk duniya tayi mata zafi kullum addu'arta Allah kada ya jarabci
yaranta da irin jarabtarta Allah ya Basu qaddara me sauqin dauka ya Sanya musu albarka cikin
cinsu da shansu da motsinsu a kowanne yanayi yabawa mijinta qarfin gwiwar nemo halal a ko
Ina take.
_Tammat bi Hamdullah_
_Tabbas komai yayi farko zaiyi qarshe yau dai Juhud yazo qarshe Ina gdy ga ubangijin bayi me
kowa me komai daya bani ikon farashi da kammalashi lafiya kamar yanda na tsara._
_Kurakuran dake ciki ubangiji ya yafe Mana badon halinmu ba amfanin ciki Allah ya bamu ikon
amfana baki daya._
_Bazan rufe ba sai nayi gdy gareku masoya da baku qasa a gwiwa wajen qarfafamin gwiwa da
kudadenku da lkcnku tabbas Ina alfahari daku Ina fatan ubangiji ya sadamu a dausayin zumunci
na masuyin soyayya dominsa._
_Kada ku manta next book dina _*YAFI ZAMAN AURE!*_ _yananan tafe da irin tasa rikita
rikitar very soon insha Allahu._
_*Oum Hairan*_
. *************************⬇**********************
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************