Follow us on social media
Showing 33001 words to 36000 words out of 99941 words
sukayi da kallo Ya'isha tace “hmmm wannan mutumin dan rainin hankalin mutumin wlh bashi da
mutumci yanzu duk hotunan da mukayi sun tashi a banza kenan?"
Qwafa Amrah tayi tace “kuma duk baqin cikinsa bazamu fass shagalinmu ba Allah yasa ba
layina bane akai daya cuceni" janta sukayi suka shiga filin itadai yaqe kawai takeyiwa mutane
har takwas taron ya tashi suka shiga gda ta shige daki ta kwanta tana mayar da numfashi.
Da wayar Ya'isha Kareem ya sake kiranta yake tambayarta Ina wayarta ne yanata Kira a kashe
taja fasali tace “Baffa'am ya qwace tawa ta Amrah ce nakesa layin itanma dazun ya qwaceta"
wata iska ya furzar yace “ina Gsky abin nasa ya fara yawa fah banason shigarmin hanci da
qudundunen nan da yakeyi Ina ganin girmansa kada azo ayi babu dadi zan fadawa Mai
Martaba ya dakatar dashi gsky na gaji duk yabi ya takuraki to ko hsihuwarki yayi kikakai yanzu
ai ya qyaleki balle a sama yaganki" itadai batace komai ba saboda itanma duk kawaicinta da
kararta Baffa'am din nata ya fara duba juriyarta.
*************
Satinsu biyu da Candy samarin Ya'isha da Amrah suka aiko neman aurensu da farko Mai
Martaba yaqi amsar batun a cewarsa karatu zasuyi Alh Ibrahim wani amininsa shine ya sameshi
ya bashi shawarar tunda sun nuna auren sukeso yayi musu ba lallai sai mace a gdan iyaye
zatayi karatu ba a gdan mijinta ma zata iya karatunta da farko bai dauki mgnr ba saida Addah
Abulle ta sake samunsa da mgnr Kareem fah ya matsa akan mgnr aure da Momy da ita da Ya
Arman sune suka sameshi suka rinqa nuna masa abin hakan suna nuna masa Kareem namiji
ne Kuma yanada kawaici tunda har ya fito da maitarsa ayi masa kada azo a samu matsala. Badon yaso ba ya amshi shawarar tasu dake dama an gama shirya komai na baikon Rasheed
da Zulaihat hakanan ya Kuma bada maqudan kudade aka shiga kasuwa aka sake yo siyayyar
baikon Kareem da Meenah Meenah batasan meye akeyi ba ranar baikon korasu akayi Katsina
gdansu Addah Abulle acan suka yini suna tantalbadedensu akatsai da ranar aure Rasheed da
Zulaihat wata biyu masu zuwa ya kama bayan azumi da sati uku dake azumin ya rage saura
kwanaki bakwai ne sukuna akasa wata shidda saboda an qiyasta abinne da yanda zaizo daidai
da hutun shekarar Kareem din ayi bikin ysnana ya dauki matarsa su tafi.
Ranar farin ciki gurin Juhud da Kareem kamar su hadiye juna ta waya inda Rasheed yayi yinin
qunci da baqin ciki a qarshe ma daki ya shiga ya kulle kansa yini sur har dare har safiya bai fito
ba Mom ce ta kirata tace taje ta duba Baffa'am dinta tun jiya bai fito ba, bataso ba batason
haduwa dashi tsoronsa takeji batasan da wacce irin fuska zai kalleta ba, hijjab dinta ta dauka ta
Sanya ta fita ta nufi part din nasa tun daga falo ta fahimci akwai matsala kaca² ta tarar dashi
gabanta ya fadi ganin kwalaben wine da wasu qananun kwalabe ta matsa ta dauki daya ta
duba tare da dafe qirji da sauri tace “A'uzubillahi Baffa'am Alcohol kakesha?" Tsorone ya
sarqeta takai hannunta qofar tana bugawa kusan 20 minutes bataji motsi ba murdawa tayi tajita
a kulle ta rinqa bugawa da dukkan qarfinta Amma shiru dube dube ta farayi a falon can ta
hango mukullaye a hade ta dauka da sauri ta fara gwadawa cikin saa na qarshen da tasa ya
bude qofar ta tura da sauri, toshe hancinta tayi saboda warin daya daki hancinta takai dubanta
inda ta hangeshi kwance a qasa cikin amai ta saki qara tana cewa “innanillahi meye hakan
meye ya sameshi?" Matsawa tayi ta shiga jijjigashi Amma kamar tana jijjiga dutse daidai lkcn
Momy da taji shirun tayi yawa ta shigo ganinsa a wannan yanayin yasata sakin ihu tace
“Abdulrasheed meye hakan bakada lfy ka kulle kanka a daki zaka kashe kanka....."
*Oum Hairan*
[7/22, 6:51 PM] Oum Hairan: *JH016 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada
ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*
*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or
card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba
94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*
Gabadaya gidan ya rude Big Cele babu lfy Mai Martaba dakansa yazo suka daukeshi da likitan
gdan suks nufi asibiti dashi suka fara bashi kulawa sosai likitan ya kadu dayin hoton zuciyarsa
da yaga ta kumbura jininsa ya hau fiye da misali tashin hankalinsa ya nunku ya fito Yana sharce
gumi iyakar saninsa Abdulrasheed ba mutum ne me shiga sabgar mutane ba balle su Dora
masa damuwa to meye yaja asalin damuwar tasa?
Da wannan tunanin ya fito ya sami su Mom a zaune suna ganinsa suka miqe ya sake share
gumi ya dubi Mom yace “dama Rasheed yanada heart issue ne?" Da sauri suka kalleshi Mai
Martaba yace “aa bashida ita" iska likitan ya furzar yace “to mgn ta gsky akwai abinda yasa a
ransa da yakecin zuciyarsa har yayi mata Ramin da ciwo ya shigeta hoton da nayi masa ya
nuna cewa zuciyarsa ce ta kumbura jininsa yayi mugun hawa fiye da misali nikam lamarin ya
firgitani meye damuwarsa meye yasa a ransa da yake neman salwantar da rayuwarsa akansa?"
Goge gumi Mai Martaba yayi ya dubi likitan yace damuwa Kuma a Rasheed din to wacce irin
damuwa ce wannan nikam bansan irin yaron nan ba zurfin cikinsa yayi yawa" Mom ce tace
“kuma ba akan yarinyar nan bane da yace bayaso kasanshi fah da baqar gaba idan yaqi abu
zai iya komai akansa Mai Martaba ka duba lamarin Rasheed fah da Zulai......" Daganta hannu
yayi yace “dakata Ayshatu indai akan wannan ne to zan tanadi likkafanin suturarsa don wlh
bazan watsawa zuminci baqar toka ba ko zai mutu saina daura aurensa da Zulaihat......."
Kwanansa goma a asibitin duk sanda zasuje dubashi daya ganta saiya lumshe idonsa bazai
bude ba harsai ta fita a dakin maganar duniya bazai kulata ba tun abin na damunta har ya daina
damunta da zugar qannensa da suketa famfata akan kada ta kuskura ta bashi qofar da zai gane
tanajin tausayinsa zai kaita ya baro ne qila ma ba aurenta zaiyi ba Kuma ma yaushe zata saki
saurayi ta kama tuzuru tuzurun ma me Shirin auren wata a fari ba itaba, quruciya da wauta da
rashin mafadi ya hanata gane kuskuren da take qoqarin tafkawa Wanda ita kadai takeda ikon
canzashi hakanan akaci gaba da tafiya har yaji sauqi aka sallamoshi kwanansa Tara da sallama
ya tattara nasa ya nasa yabar gdan batare da kowa yasan da tafiyar tasa ba koda ala fada mata
ya tafi Saida yaji babu dadi a ranta Amma zugar su Ya'isha ta hanata saukar da kanta a gefe
Kuma da sabon haukanta na dokar da Kareem ya kafa mata cewa indai namiji ba muharraminta
bane to ya haramta mata mu'amala dashi wannan dalilin yasa tanason taje ga Baffa'am din nata
Amma babu dama gani take kamar Allah ma fushi zaiyi da ita ta karya dokar mijinta.
Ana azumi ana shirye²n sallah ana na biki gda ya dauki harami sosai komai na bikin Baffan nata
ita dasu Ya'isha suke shiryashi Basu Katsina Basu Kano siyayyar ashobin biki da kayan sallarsu
kwanaki sunsta tafiya soyayya tsaksninta da Kareem tanata qaruwa dare rana yammaci suna
maqale a wayar daya Sanya aka kawo mata sabuwa dal suna tsara yanda bikinsu zai kasance.
A haka aka cinye azumin ana gobe sallah tana falo tana waya Ado drive ya shigo da sallamarsa
suka gaisa ya miqa mata wata leda yace “gashi inji wani soja a waje yace akawo miki" Saida
gabanta ya Fadi da akace soja Mom ta zubanta ido tace “soja Kuma Amina Ina kika samo
soja?" A sanyaye tace “bansani ba Mom" karbar ledar tayi ta bude ta dauko kwalin dake ciki
wata rantsattsiyar wayace Sumsum me matuqar kyau da tsadar gaske Mom ta juyata sosai a
hannunta ta dubi Juhud data zuba tagumi tana kallon Mom.
Sake zaro kwali na biyu tayi wasu fitinannun turaruka ne masu masifar qamshi a ciki sai
tarkacen Sweet da chocolates sai wata takarda qarama dake a ciki miqa mata takardar sukayi
taqi karba saima miqewa da tayi Mom tace “ungo ana Kira ki daga kije me zaace miki" noqe
kafada tayi tace “Mom....." Hannun Mom ta Dora a bakinta tace “shitttt Amina banson gardama
da fada da Wanda baka sani ba ai gara kayi da wanda ka sani ko banza akwai sanayya"
Hannu tasa ta karba tanabin number da kallo hannunta na rawa ta danna wayar ta Kara a
kunnenta yaja ajiyar zuciya daga yanayin saukar numfashin ta gane wayene nan take zuciyarta
ta hau kai kawo a qirjinta. Bai bata damar tunanin komai ba yace “baki tausayin me tausayinki
ko Meenah?" Shiru ce ta ratsa ta juya ta dubi Mom ta nufi qofar dakinsu yafi minti biyar kafin ya
qara qutawa yace “banyi tunanin wannan sakayyar daga gareki ba inaji a Raina a baya idan
kowa ya juyamin baya ke zaki kalleni da idanun Rahma ashe ban fahimta daidai ba Meenah
meye aibuna da kika kasa maye gurbin rashin cancanta da cancanta a tunanina ko ban
cancanta ba ya kamata ki kama hannuna ki dagani matsayin gwaninki....."
Shiru yayi saboda numfashinsa da yake sarqewa yaja numfashi sosai sannan yaci gaba da
cewa shekaruna 37 bantaba ji ko a wasa ina muradin rayuwa da wata mace matsayin mata ba
sai a wannan gabar da qaddarar ta hadani dake tabbas da nasan cewa kedin zaki zamo
masheqin rayuwata da ban fara jin tausayinki a farko ba" jikinta ne yayi sanyi da kalamansa
zuciyarta ta karye bai Bari tace komai ba yace “bansan meye laifina ba don nace inasonki wlh
tallahi duk duniya babu namijin da yakeyi miki irin son da nakeyi miki Meenah ba iyakar farin
cikina zan fansar gareki ba har rayuwata da mutumcina duk zan iya sallamasu dominki na
rantse da Allah idan ban sameki ba matsayin mata to kuwa shima Kareem bazai sameki ba
saidai muyi ragas gara ki fita waje ki auri wani Amma a gdanmu ki auri qanina ki rayu dashi gani
Ina bulayi Ina bazan iya ganin wannan baqin cikin ba, yess kince yanada nagarta nasan haka Ni
banida nagarta Mazinaci ne ni yanzu Kuma soyayyarki ta mayar dani mashayi Kuma a haka
zakizo ki rungumeni ki rayu dani dole idan kinqi bani hadin kai don Allah zaki bani don dole
Meenah kiji a ranki ni mijin mace daya ne Kuma kece ko babu aure zamu rayu tare"
Cikin tsananin fusata da kalamansa tace “ya Isa Baffa'am bantaba ganinka matsayin
qasqantacce ko marasshin daraja ba wlh ko lkcn da nasan kana zaman dadiro da arniya mara
Imani banji na tsaneka ba Amma yanzu kalamanka suna aika saqo cikin zuciyata duk da
kasancewata mara galihu na shaida niba banza bace kamar yanda kakejin izzar sarauta a cikin
jininka nima inajin izza a nawa jinin saidai Ni bansan ta meyece ba da wannan nake son sanar
dakai na gode da kulawarka gareni Amma bazan taba kwarewa Mai Martaba baya ba saboda
jin ya isa dakai yasa yaji a ransa nima ya isa Dani ya zabamin Ya Kareem batare daya nemi
shawararmu Ni dakai ba to danme Ni zan nuna masa nidin ba halattaciyar ya bace?
Numfashi taja taci gaba da cewa “bari kaji Baffa'am bazan taba canza zabi ba domin ba zabina
bane na ubangiji ne saboda haka bana buqatar kalamanka ka adanasu ka fadawa Aunty
Zulaihat ita zataji dadinsu Kuma zasuyi mata amfani Amma Banda Aminatuh"....... Qit ta kashe
wayar gabadaya ta cillah a wardrobe tana jan tsaki Baffa'am din nata ya fara kai hqrnta qarshe
to waima anayin so dolene da zai takura saita qaunaceshi bayan tariga tayi kyautar zuciyarta ga
waninsa?.
Komawa tayi ta zauna a hankali Kuma take auna kalamanta sai takejin babu dadi duk da cewar
gsky ta fada masa, turo qofar akayi aka shigo ta dago ganin Muntaz yasata miqewa ya zubawa
qirjinta iso yana murmushi wayarsa tayi ring ya miqa mata yace “kin tara kayan dadi baby
Amma na hqr na fahimci babu rabona a wannan gurin gonar manya ce" tsaki tayi ta karbi wayar
ganin sunan dake kai yasata miqa masa ya matsa da sauri yace “ai baki isaba yarinya dole ki
Amsa wayar nan bazaki jamin masifa ba" jifa tayi da wayar ta shige bathroom bugun duniya taqi
budewa Saida taji ya cewa “taqi karba fah tama shige bayi tabarni shanye kamar maratayi"
Bata fito daga bathroom dinba Saida taji shigowar su Ya'isha ta fito tana goge idanunta da suka
canza kala, da dare ma daya kirata a tata wayar da yasa aka tura masa number tana ganin
numbersa ce ta dannata a silent ta koma ta kwanta washegari ta kama idi tun asuba suketa
shirye²n tafiya idi sai bakwai suka gama suka fito sunata baza selfie Suna Shirin fita ya shigo sanye da kakinsa hularsa a hannu ya sauke idanunsa akanta tare da
kwantar da kansa a jikin qofar yanajan wata wawuyar ajiyar zuciya me qarfin gaske qwarjini yayi
mata ta kasa motsawa daga inda take su Amrah sukayi masa barka da zuwa ya dagansu hannu
tare da nuna musu hanya suka fice ta daga qafarta daqyar zata bisu ya cafko hannunta ya
janyota ya shigar da ita jikinsa ya matseta sosai yanda bazata iya motsawa ba yace “barka da
sallah My wife" qoqarin qwacewa taketayi da hannu daya ya hardeta Amma ta kasa
qwaqqwaran motsi ya figi hannunta ya nufi sama da ita ta cake a bakin qofar ta riqe qarfen
benen ya juyo ya zuba lumsassun fitinannun idanunsa akanta yace “idan Kuma nayi amfani da
qarfina nace saikin shiga cikin fah ya zakiyi?" Qasa tayi da kanta ya dagota yace “banson kuka
kawai maimaitamin kalamanki na jiya zakiyi" da sauri ta dago yayi mata murmushi yace “zanyi
amfani da duk wani abu daidai ko rashin daidai domin naga na hanaki samun abinda kike
tunanin shine ya dace dake badon na cutar dake ba saidon sama miki yanci zaifi miki dadi ki
rayu da wanda yasan mutumcinki"
Dagowa tayi ta zuba idanunta cikin nasa tace “kana nufin Ya Kareem baisan mutumcina ba kai
kadaine kasani?" Baitaba tunanin abinda zatace kenan ba ya tsaya cak Yana nazarin me zaice
mata ta juya zata fice ya sake riqota yace ki shirya zaki rakani unguwa" hannunta ta janye
batare da tace masa komai ba ta fice ta nufi masallacin suna idar da sallar ta zille ta nufi wani
bangare na gdan ta zauna tana wayarta da Kareem dinta taji an cire wayar a kunnenta ta juya
da sauri yayi wanka ya canza kaya cikin wata brown gezna yayi mata kyau sosai taja fasali
yace “zaki?" Kallonsa tayi zatayi mgn yace “bama zabi zan baki ba dolene kizo muje" bata kawo
komai ba batayi tunanin komi ba tabisa har inda yayi parking motarsa ya bude mata ta shiga ya
sake mata murmushi yaja motar a guje suka fice Muntaz ne kawai yaga lkcn daya dauketa suka
fice,
Sunyi tafiya me nisa da gidan sarautar ya dauke wata hanya itadai batace masa komai ba wasa
kawai takeyi da yatsunta Yana satar kallonta yayi parking jikin wani gda ya fita ya bude ya dawo
ya shigar da motar ya sake rufewa ya bude mata qofar ta fito tana qarewa gidan kallo koda bata
shiga gdanba tasan an qarar da fasaha wajen gininsa batayi aune ba taji ya dagata cak ya nufi
qofar da take alamta itace ta shiga cikin gdan duk irin tureshin da takeyi da magiyar da take
masa bai direta ba Saida ya danganata da wani daki dake saman ya direta ya kulle dakin ya
cire key din ya jefa a aljihunsa.
Zama tayi a gadon tana kallonsa ya nufi wata qofa ya bude ya shiga batasan inane ba bataji me
yayi ba yadai fito da cup guda biyu a hannunsa sai cake ya aje mata na tea ya dauki coffee din
ya duba aljihunsa ya dauko wata qwaya ya jefa a ciki yasa cokali Yana juyawa idanunsa qurrr
akanta, mamakin yanda bata nuna damuwa ba yasashi cewa “meye ayyanawa a ranki game
dani?" Shareshi tayi taci gaba da wasa da yatsunta" dagowa tayi da sauri lkcn da taji yayi jifa da
cup din ya nufota yanayin nutsuwar takunsa yasa bata kawo komi ba Saida taji ya bajeta a
gadon yabita ya danne da dukkan nauyinsa Yana wani lumshe ido Yana dafe kansa yana tura
hancinsa cikin qirjinta.
Wata faduwar gaba ce da bata taba sanin da irinta ba ta ziyarceta ta dafe kansa cikin firgici tace
“Baf.... Baffa'am meye kake Shirin aikatawa ne me kake nufi da......" Bakinsa ya Dora saman
nata ya dura masa yawunsa yana lasar lips dinta tanajin yanda zuciyarsa take kai kawo a
qirjinsa hannayensa ya dauka ya bude idanunsa da suke wani lumshewa yace “bantaba
sha'awar neman wani abu daga gareki ba kalamanki sukaja miki koma mene kada kiga laifin
Rasheed inason.....jin.....da....di....Meenah...........
*Oum Hairan*
[7/23, 4:47 PM] Oum Hairan: *JH017 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada
ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqin na dake kanki*
*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or
card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba