Follow us on social media
Showing 60001 words to 63000 words out of 99941 words
ya saukesu akanta ya miqe hannunsa dauke da dannasu yana
sake shigar dashi jikinsa yace “abune da bazai taba yuwuwa ba kike furtawa Meenah shiyasa
nake ganin asarar bata lkcna wajen baki amsa" yana fadin haka ya fice daga dakin ya nufi nasa
ya zauna a gefen gado ya yaye fuskar Mahfuz yayi masa addu'ar da baisamu yayi masa ba ya
kwantar dashi tare da miqewa yasawa dakin key ya cire kayansa ya shiga bathroom ya watsa
ruwa ya dawo yana shiryawa yana kallon yanda yaron keta wutsil²n dinsa na jarirai yayi
murmushi a fili yace “girman rabo Ina Mai Martaba da yakeson yakaimin wannan Soldier da zai
fita daga jikina ya shiga na Meenah ta qinqishemin shi? Da a Ina yakeso na saka wannan
kyakkyawan qwan da bai cancanci qinqisar kowa ba saita rayuwata?" Bayan ya gama shiryawa
yayi sallar Isha da baisamu yayi ba yayi shafa'i da wuturi ya haye gadon ya kwanta tare da
daukan yaron ya dora a qirjinsa yanajin qaunar gudar tsokar tasa har cikin bargonsa, zubawa
p.o.p idanu yayi yana nazarin kalaman Meenah tabbas lamarin yau me girma ne Meenah da
bakinta ta furta masa gara rabuwa dashi akan rayuwa dashi wannan abu yanayi masa ciwo duk
wata matsala ta gidansa bata zuwan musu a kankin kansu saida wasu su qirqireta idan yace zai
dauki mataki a hanasa wannan wacce irin rayuwa ce ne?"
Miqewa yayi ya dauki Mahfuz daya farka a bacci yake neman uwarsa ya fita ya nufi dakinta ya
bude ya shiga ga mamakinsa ya isketa zaune can qarshen gadon ta zuba uban tagumi ya
zubanta ido tausayinta da qaunarsa na qara nunkuwa a zuciyarsa ya haura gadon ya kwantar
da Mahfuz ya sanya hannunsa ya janye mata tagumin ya janyota jikinsa ya rungumeta yana
sunsunar sumarta yanajin wata natsuwa na kwararo masa yace “idan na rasa gatan kowa a
duniya baikamata na rasa naki ba Meenah bai kamata na zamo mara galihun nunawa duniya a
gurinki ba bayan kin kasance mace daya tal dake mulkin zuciyata please na roqeki ki daina jin a
ranki akwai abinda zai rabamu qaddarar mutum Babu me tayashi dakonta ni kece qaddarata
nima nine qaddararki bazan hanaki kuka ba akan abubuwan da suke faruwa Amma dai ki rinqaji
a ranki iyakar rintsin rayuwar duniya ni nakine ke kadai Babu wani tsanani da zaisa na rabu
dake saidai qaddarar mutuwa idan ta gifta saboda haka banson sakejin wadannan kalaman
naki don Allah kinji?" Zamewa tayi a jikinsa ta miqa hannu ta dauki Mahfuz tayi Bismillah ta
Sanya masa nonon ya kama yanasha shikuma yana aikin kallonsu.
Kwanciya tayi badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta hutu shima kwanciya yayi a bayanta
ya maqaleta da haka sukayi bacci washegari da wuri ya fice daga gdan duk cika ta gidan
sarautar idan ka shiga barayin Rasheed bazaka taba cewa sabuwar haihuwa akayi ba saboda
yanda gdan yake a yashe daga ita sai Kumbo Hami suketa harkokinsu Rasheed bai dawo ba
sai bayan Isha lkcn har sun kwanta ya shigo ya kirata ta miqe ta nufi dakin nasa yana safa da
marwa ta samu guri ta zauna shima ya zauna a gabanta ya dubeta sosai yace “nasa anzo an
kama Hajiya Bilki da Dada Hanne....." Dafe qirji tayi da sauri tace “na shiga uku Baffa'am me
sukayi maka?" Share zufa yayi ya miqe yace “saboda a koya musu hankali su fita daga harkata
da iyalina" yana mgnr yana hada kayansa ta miqe ta Isa gabansa jikinta na rawa ta durqushe
tace “wlh wannan abin baikai ka dauki wannan matakin ba Abban Sarki ana barin halal ko don
kunya please kada kayimin haka wani bala'in zaka qara jefani a ciki kasa a sakosu wlh ni na
yafe musu...."
Rufe mata baki yayi yace “ke zaki iya yafewa saboda bakisan ciwon kanki ba nikam ban yafe ba
Yana fadin haka ya shige bathroom yabarta sake da baki wannan mutumin kwai dan neman
jarfa anason kashe wata yana neman zunguro sama da kara
Tananan zaune ya fito daga wankan Yana tsane ruwa ta sake dubansa zatayi mgn ya nuna
mata hanya yace “jeki ma hadu da safe inason zanyi yan nazarce nazarce" miqewa tayi jikinta a
mace ta koma dakinta ta ishe Kumbo Hami tana sallar Isha ta zauna bayan ta idar ne take
tambayarta meye yake faruwa ta kuwa zayyane mata komai tayi shiru na dan lkc sanna ta dago
tace “banji dadin kaisu qara da yayi ba shima hakan qarin wata fitinar ce daya qyalesu watarana
sai lbr"
Miqewa tayi ta Sanya Sarki junior a gadonsa tana cewa “nima abinda naso ya fahimta kenan
yaqi bani hadin kai koroni ma yayi Kuma tunda yayi niyya Babu me hanashi" da wannan tayi
addu'a ta kwanta sukayi baccinsu itadai da zullimi ta kwana aikam abinda take gudun ne ya faru
da safe Yana fita Hidaya da Khadija sukayiwa gdan tsinke suka rinqa zaginta sunacin
mutumcinta Meenah babu baki sai hawaye kawai da takeyi suna tsaka da wannan tujarar ne
Kareem yazo musu barka don shi sai ranar ma yakejin lbrn haihuwar gurin Fadila aikuwa ranar
Khadija da Hidaya sunji a jikinsu domin dukan mutuwa yayi musu kamar shine sojan daqyar Mai
Martaba ya qwacesu barkar da baiyi ba kenan ya fice daga gdan rashin mutuncin gdan ya fara
girmewa tunaninsa ace Babu Wanda ya isa ya fada aji anbi an tsangwami yarinya akan abinda
bashida tushe balle makama aikam ranar hatta Addah Abulle Saida taji kunyar irin rashin
albarkar da Kareem yazo ya zazzage mata a gdan akan rashin zuwa taga Dan da aka haifawa
Rasheed yan uwansa kuwa gda gda ya rinqa binsu yana ci musu mutumci Yana fada musu ai
ba Meenah suke qi ba Rasheed suke qi tunda shine ya dauko Meenah Kuma yakeson kayarsa
sannan ba Meenah kadai ta haifi Mahfuz ba Rasheed shine silar zuwansa duniya saboda haka
shine basaso"
Basu wani dauki mgnr da muhimmaci ba ba Kuma su risuna ba sukaci gaba da dabdalarsu rikici
yaqi qarewa cikin wannan family har ranar suna akayi sunan babu wani armashi kamar abin
arziqi dangi suka hadu ranar Meenah Saida ta gwammace ita dama mutuwa tayi da wannan
baqin cikin data riska wannan Rana a qarshe baa gama sunan da ita lfy ba sai a gadon asibiti ta
qarashe sunan jininta yayi mugun hawa hawan da Rasheed bai taba tsammani ba ya shiga
tashin hankali matuqa da yanayin da yaga matar tasa a ciki, da dare aka sallamesu suka dawo
gda kanta na ciwo sosai da Rasheed da Mom da Kumbo Hami sunata rarrashinta da kalami na
kwantar da hankali bacci ya dauketa washegari badon yaso ba ya shirya yabar garin ya koma
wajen aiki yabarsu cike da kewar juna................
_Kuyi hqr da wannan_
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 viaí ½í±‰í ¼í¿¼ 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan
account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton
katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/4, 8:56 PM] Oum Hairan: *0028* Kwananta sittin da haihuwa Kumbo Hami ta koma Mali inda
ita Kuma taci gaba da rainon danta cikin kulawa da tattali a hankali lkc yaketa tafiya qaunarta da
Rasheed tanata qara gaba inda aiki ya riqeshi kusan watanni biyar sannan ya waiwayosu ranar
anyi qara'in rayuwa kamar bazaakai gobe ba yayi musu sati biyu ya shirya domin tafiya wani
aikin hadin gwiwar qasa da qasa zuwa Togo yaso tafiya da ita Mom tace gara yaje yaga yanayin
gurin tukunna inyaso sai yazo ko ya aiko tabisa.
Hakanan suka rabu bason ransu ba wani abin almara tunda ya tafi wayarsa bata shiga da farko
sun dauka yanayin aiki ne tafi tafi da tafiyarsa ya dauki wata biyu babu waya babu aike, sosai
hankalin Juhud yaqi kwanciya hakanan wata faduwar gaba ta aureta Mom ma tana cikin
damuwar rashin jin labarin dannata hakanan take daurewa tana kwantarwa da Meenah hankali,
tafiya na qara tsayi har aka tafi wata shidda Babu waya Babu amo Babu labari. Qa'idar aikin
nasu yace watanni shiddan ne gashi sun wucce nan fa Mai Martaba ya tashi takanas yaje
barikinsu inda ya dawo cikin matsanancin tashin hankali suna ganinshi Meenah dake zaune ta
dora kanta saman cinyar Mom tana aikin kuka ta miqe tana cewa “Mai Martaba kaganoshi Yana
cikin qoshin lfy?"
Sunkuyar dakai Mai Martaba yayi yana kwance rawaninsa yace “lamarin akwai daure kai fah
naje barikinsu duk sojojin da aka tura Togo sun dawo tsiraru ne suka mutu Amma shi bai dawo
ba dana matsa da bincike ma a data na aikinsa tun sunada wata biyu da tafiya wani mugun
ciwon kai ya sarqeshi shine dalilin da yasa aka bashi hutu da zummar zai dawo gda tsayin
watannin nan bai dawo ba....." Yanke jiki Meenah tayi ta fadi qasa sumammiya gabadaya
sukayi kanta Mom ta dauko ruwa ta fara yayyafa mata daqyar ta dawo hayyacinta ta miqe
zaune ta dubi Mai Martaba cikin gushewar hayyaci tace.
“Me kakeso kacemin Mai Martaba mijina ya taho gda daga filin daga Kuma baizo gidaba to Ina
ya tsaya Kuma wayoyinsa basa shiga tun satin daya tafi?" Gumi Mai Martaba ya sharce yace
“shine abinda nima nake tambaya kada ki tashi hankalinki na sanar da duk Wanda ya kamata
na sanarwa wannan isue din Kuma sun fara bincike daga yau insha Allahu komai zaizo da
sauqi...." Cikin kuka tace “ta yaya zan kwantar da hankalina bayan rayuwata tana cikin garari
nikam don Allah ku fitomin da mijina wlh inason kayana" daqyar suka samu suka lallasheta
shima ba shiru tayi da kukan ba kawai surutan ta daina hakanan aka duqufa babu ji Babu gani
nemansa ta kafofin sadarwa na Internet da duk wasu hanyoyi da zaa samu bayaninsa Amma
shiru Babu amo Babu labarinsa.
Gabadaya hankalin gdan sarautar Babu na kwance wannan baqon alkaba'i daya fado musu
Babu zato ya girgiza zuciyar kowa a gdan daga yara har manya hatta wadanda ke nuna
adawarsu irinsu Hajiya Bilki a zahiri suna nuna alhininsu tare da jefar da maganganu na zargi a
fakaice suna alaqanta batan nasa da Juhud da take kwance cikin halin jinya bata kwana uku da
lfy saboda tashin hankalin da take ciki duk ta qare sai qasusuwa gashi kullum lkc qara tafiya
yake babu wani amon labari tun daga sama ga manyan sojojin da suka baza idanunsu a
kowanne lungu na Africa domin ganoshi zuwa gwamnati da itama take hobbasa wajen ganin an
samo bakin zaren saidai kullum labarin daya ne baya canzawa daga inda yake.
Malamai kuwa da suke aiki da addu'ar Allah ya fito dashi sunfi dari suma kullum amsar daya ce
a qara hqr lamarin daya Sanya Juhud a wani hali ga shayarwa gashi ko abincin bata iyaci dole
tasa sarki yanada shekara daya da wata hudu Mom tayi masa yayen dole aka dorashi akan
abinci aka qyaleta da damuwa daya gabadaya ta quntata kanta kullum bata da aiki daga sallah
karatun qur'ani sai kuka
Mai Martaba da yayansa maza musamman Kareem daya dawo daga Saudia ya gama
karatunsa kullum basa Kano basa Abuja basa Lagos Basu kotono Basu Togo Basu Burkinafaso
tafiya kullum qara miqawa takeyi Abu ya tafi shekara guda, watarana suna falo suna zaune
Meenah na rungume da Sarki junior Amrah da Fadila suka shigo suka zauna aka gaisa suka
jajantawa juna Dada Hanne dake zaune ta rafsa tagumi ta dago tana kallon Juhud tace “lamarin
nan da ban mamaki Mahfuz batan Abdulrasheed kamar batan toka a ruwa gsky abinnan da
lauje cikin nadi Anya ba mutuwa yaronnan yayi ba"
Duk Wanda ke falon Saida ya dago karma Juhud taji labari da kaduwa tasata zamewa daga
kujerar ta sauko qasa tayi dabar tana kallon Dada Hanne. Harara ta watsa mata tace “eh Mana
biri yayi kama da mutum to nidai tunda abinnan ya faru nake biyar malamai da yan bori idan
suka hau bori suka jirge sai suce ai saqale kurwarsa akayi akayi bandarsa" gabadaya hankalin
kowa sai ya dawo kan Juhud da itama take jujjuya mgnr a kwakwalwarta Dada Hanne tace
“kuma fah cewa sukeyi makusancinsa ne yayi masa wannan abin kawai saboda yanason cin
gado to nidai naga kaidai Mahfuz bazakayi wannan abu ba itama Mom din yara bazatayi ba
saura da me dama Kuma ku hudune magadan nasa....."
Miqewa Kareem yayi yace “don Allah dakata Dada kada kizo Mana da surkullen hauka cikin
wannan lamari ke Ina kika taba ganin anyi bandar mutum banda sakarcinku na mata? Kuma ma
meye Rasheed ya Tara da har zaayi tunanin kasheshi don gadonsa haba dallah ku rinqa auna
mgn kafin kuyita Mana" Yana fadin haka ya miqe zumbur ya dubi Addansa daketa harararsa ya
dubi Mai Martaba da Mom yace “wlh daukan alhakin Meenah zakuyi indai kuka zargeta yarinyar
nan batada wani abu da ta sani game da batan mijinta haba ai abinda zai yuwu ma dagaji
ansanshi" ficewa yayi daga gdan idanunsa nakan Meenah da keta jan zuciya tunda mijin nata
ya bata take cikin masifa komai Yana neman koma mata baya gdan an qara tsangwamarta da
Mom kawai takejin dadi sai Kareem daya mayewa Sarki junior madadin bsbansa komai ya
tarkato Sarki.
Ana haka Mai Martaba yaga zaman ya fara tsayi Abu ya tafi shekara biyu ya Sanya Kareem ya
nema mata admission bayan sun biya mata an zana mats jamb lkcn da sukayi mata mgnr
karatun fir qi tayi tace ita bataso daqyar Mom da Kareem sukasha kanta ta yarda ta fara zuwa
Alqalam University Katsina bata jima da fara zuwa ba abubuwa suka fara canzawa Dada Hanne
da Alh Aminu suna zuga Mai Martaba baiyi furuci ba Amma gabadaya ya janyewa Meenah
tallafi babu Wanda yasan dalili Mom ce taci gaba da dawainiya da karatun nata ita da Kareem.
A hakadai da dadi babu dadi take gurgura karatun cike da samatsi da qalubalen rayuwa kullum
addu'a takeyi Allah ya bayyana mijinta itama ko ta samu hasken zuciya. Yau da gobe ce tasa
Kareem bawa Mom shawarar kama mata hostel saboda karatun nata na Law yanajan kudi
sosai hakan kuwa akayi suka kama mata hostel ta koma can da zama Sarki junior na gurin
Mom yanata girmansa inda a lkcn Ya'isha ta ta haihu Zahran Kareem ma ta haihu taso zuwa
daidai lkcn suna exam hakanan ta hqr sai bayan Exam akayi hutu ta shirya domin zuwa tayi
barkar ta nufi Daura cike da kewar gudan jininta da sallamarta ta shiga falon Sarki ya taso da
gudu ya rungumeta ta dagashi tana juyashi suna dariya tayi kissing nasa tace “miss you love
inata kewarku"
Lakace mata hanci yaran me shekaru hudu yayi yace “yaushe zaki dawo?" Narkar dakei tayi
tace “saura semester guda Son ka matsu na dawo ne?" Turo baki yayi yace “Addah Fadila ce
tacemin na daina zuwar mata gidanta kada na cinye mata su Jabir Momy wai tace kece kika
cinye Dad Ina ya bata....." Gwabe bakinsa Mom tayi tace “ba nace maka idan na qarajin mgnr
nan a bakinka saina yankaka ba" riqe bakinsa yayi alamun yayi shiru ta daukeshi jikinta a mace
ta nemi guri ta zauna suka gaisa da Mom ta miqe tace “zanje nagano babyn Ya'isha" miqewa
itama tayi tace “nima abinda ya kawoni kenan hutunmu na sati daya ne Kuma tun shekaran jiya
akayi" dungumawa sukayi suka fita suna fitowa Muntaz na shigowa Mom tace “yawwa zo ka
kaimu gdan Ya'isha"
Babu musu yaja suka tafi suna taba yar hirarsu tace “Jiya Hafeez abokin aikin Baffa'am
yakaimin ziyara" murmushi Mom tayi tace “nan ms yazo gurin Mai Martaba yazo ne da wani
shirme wai qa'ida shekara hudu ne idan mijin mace ya bata alqali zai bata damar tayi aure ke
anbaki dama ne? Tsaki taja me zafi tace “shege sai naci kutumar ubansa ni ce masa akayi
mijina bazai dawo bane nifa Mom bantabaji a Raina Baffa'am ya mutu ba Yana raye kawai dai
Allah ne be gama ganawa ba" numfashi Mom taja tace “nima haka nakeji so naga Mai Martaba
ya saduda shiyasa nima na fidda rai da tsammani" shiru ce ta dan gifta suka Isa gdan Kareem
ta jinjina haduwar gdan karo ns farko data sanya qafarta a gdan tun aurensa da Zahrah
kasancewar Zahra mugum baqin kishi takeyi da ita to itama shiyasa taja jikinta.
Da sallama suka shiga aka Amsa musu Dada Hanne na dagowa taga Juhud tayi maza ta dauke
jaririn tasa a bayanta suka gaisa tayima Zahrah barka tana amsawa a yatsine ta aje kayan data
siyowa bebin tana satar kallonsa a bayan Dada tanason jariri a rayuwarta bata samu arziqin
daukan jaririn ba Kareem ya sauko tunda ya fito idonsa na kan Juhud dake wasa da yatsunta
yace “aa Meenah Ina cewa zanzo na daukoki ashe kina hanya" murmushi tayi masa tace “wlh
na matsu nazo naga baby's din da muka samu shiyasa na biyo motan haya" shafa kansa yayi
yace “insha Allahu cikin satinnan motarki zatazo haihuwar nan cema ta dan takemin birki" gdy
tayi ta miqe saboda bata cikason zaqewa a lamarinsa ba ganin haksn yasa Mom miqewa sukayi
sallama ya biyosu har jikin motarsu yanajan Sarki da wasa suks shiga suka tafi shikuma ya juya
suka nufi gdan Ya'isha.........
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 viaí ½í±‰í ¼í¿¼ 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account
din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko
digit number ta