Follow us on social media

Showing 90001 words to 93000 words out of 99941 words

Chapter 31 - Juhud Complete Hausa Novel by Oum Hairan

17 Nov 2025

1664

wannan account
din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko
digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/22, 8:04 PM] Oum Hairan: Da mugun gudu cikin fitar hayyaci Juhud ta fito daga dakin da take
cikin gigita ta cacumi Rasheed dake shigowa idanunsa kamar garwashi ta jijjigashi tace “da
gaske ko gizo kalamin Ya'isha sukemin Ya Kareem ya mutu....." Zubanta idanunsa yayi so yake
yayi mata mgn ya kasa sai kawar dakai da yayi hawaye suna zubo masa yasa hannunsa ya
janye nata, ganin yanda yake goge hawaye da tissue yasata zama a gurin dabar ta daura
hannunta akanta ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un" Ya Kareem kada
ka mutu dom girman Allah ya kasance mafarki shudadde Wanda bazan qarayinsa ba har abada
wlh na aminta da kai zan dawo gareka na qara Haifa maka qannen Muneefah nasan
shin....shine burinka a duniya....." Dagota Mom tayi tace “kiyi hqr Meenah shirya mu tafi" Babu
wani shiri ta sunkuci Muneefah da taketa bacci abinta baccin asara abin tausayi mota ta debesu
gabadaya harda Alh Garbu suka nufi airport dake abin na manya ne nandanan suka Isa Nigeria
kamar a qasar suka kwana goma na safe suka shiga Daura lkcn an gama shirya Kareem da
Zahrah zaayi musu sallah mazan suka tsaya wajen jana'izar sukuma suka shige ciki.




Addah Abulle tana ganin Juhud ta miqe ta nufeta da sauri ta karbi Muneefah ta rungume ta qara
rushewa da kuka tace “shikenan ya tafi Meenah yatafi yabar Mana duniyar Babu shi din Babu
Zahra wayyoh Kareem dama inada dama Dana dawo dakai duniya nabarka da zabinka da
yarka daya mafi soyuwa a ranka kullum kana fadamin bakajin dadin rayuwa baka tare da
Muneefah ashe ita kadaice rabonka ita zaka tafi kabarni da ita Kareem wayyoh Ni Zainabu na
cuci kaina na cuceka Kareem Allah na gde maka da bakabani saa ba lkcn da malam Mati
yabani magani yace nabaki kici a waina da tuni Babu Aishatu da tuni Ni da kaina na kashe
bayan dana kaicona Ni Zainabu Allah ya isa Dada Hanne da Hajiya Bilki kune kukayita dorani a
keken bera ashe kaini zakuyi ku baro yau na rasa Kareem ban barshi ya rayu da farin ciki ba ya
tafi da jin ciwon nice silar rabashi da matarsa mafi soyuwa a duniyarsa...."
Surutai taketayi kamar wacce ta zautu hakan yasa wasu mata daga cikin danginta sukazo suka
kamata suka tafi da ita daki tana kuka tana kiran Meenah Kareem shikenan Kareem ya tafi
yabarmim duniyar Ina nutsuwata da hankalina yayi na kasa gane nauyin qaddararsa?" Kowa ka
gani a falon kuka yakeyi mutuwar Kareem tabar tambari ba iya Daura ko Katsina kadai ba hatta
arewacin Nigeria baki daya duk Wanda yaji labarin mutuwar ko baisanshi ba sai yaji alhini a
jikinsa duniya tayi rashin nagartaccen mutum me hqr da kawaici kunya da kara wannan dabi'ar
tasa yake soyuwa a zuciyar duk wanda yayi mu'amala dashi ta kusa kota nesa ranar anyi yinin
alhini Juhud kam zazzabi ne ya rufeta sosai bana wasaba hawaye yaqi tsayawa a idanunta tayi
danasanin zabar Rasheed akan Kareem ta zabi Rasheed tabar Kareem Rasheed din ya

tattarata yayi watsi da ita yaqi saurarenta.




Haka suka yini yinin koke² da dare kowa ya nemi guri ya kwanta itakam koda ta kwanta kasa
rintsawa tayi rayuwarta da Kareem zamantakewarsu da yanayin salon qaunarsa me tsayawa a
rai shudaddiya wacce bazata dawo ba tanayi mata yawo a kwanya saidai kawai lkc zuwa lkc ta
dauke hawaye, wajen 10:30 taji ana taba qofar dakin data shiga ta kulle kanta ta miqe a
wahalce ta bude ta dan ja da baya a tsorace ganin Rasheed ne jajayen idanunsa akanta ya
miqa mata Muneefah da tayi bacci tasa hannu ta karbeta ta juya ta nufi cikin dakin taji muryarsa
data shaqe da alamun yaci isasshen kuka yace “Duk da bansan irin radadin da kikeji a zuciyarki
ba na rashin masoyinki uban yarki nasan kinajin fiye da abinda nakeji tabbas akwai daci daci
mafi dacin daci rabuwa da abinda kakeso a lkcn da kake tsananin buqatarsa yaune kika farajin
kwatankwacin abinda naji lkcn dana rasa hanyar dawowa gareki kwanyata ta daina fadamin
daidai aka rinqa nunamin ke cikin wani yanayi dana kasa ganewa har yanzu and end aka
nunamin ke wani mutum ya hankadaki cikin wani dogon rami Wanda na yanke shawarar binki
mu mutu tare Meenah bayan na biki bansake sanin komai da hankali zai tuna ba sai bayan
shekara bakwai dinnan Amma ko a cikin yanayin zautuwar qwaqwalwata ban mantaki ba duk
wani furucina kece bansan ya ake tunani ba Amma idan na zauna kece kikemin gizo da siffofi
mabambata"
Numfashi ya sauke ya juyo idanunsa na zubar hawaye yace “meye kike tunani ranar da Allah ya
Amsa addu'ar masoyana ya dawo dani hayyaci na laluba naga bakinan na tambayi kina Ina
akacemin kina matsayin matar wani waninma qanina Meenah taya zan iya yafewa kaina bata
lkcn da nayi na nakasa rayuwata saboda ke? Nakasa yafewa kaina kema na kasa yafe miki
girman cin amanar da nakeji a Raina kinyimin domin bana mantawa kintaba yimin alqawarin
zamu rayu tare zamu mutu tare ya akayi tun Ina raye kika zabi rayuwa da wani bani ba?"




Duk da kalamansa sun kashe mata jiki Amma yanayin da take ciki yasata juyowa a fusace tace
“qaddara Abdulrasheed dukkanmu akanta muke rayuwa Babu Wanda ya isa ya tayani dakon
tawa kamar yanda Babu Wanda ya tayaka Babu Wanda ya taya Ya Kareem Allah madaukakin
Sarki ya sardanta ku biyun daka kuna cikin qaddarata kaine kakeja da lamarin ubangiji ni bana
jayayya Ya Kareem ma baitaba jayayya ba kullum nunamin yakeyi bayin kansa bane girman
rabone da hukuncin Allah saiya Sanya Muneefah tsakaninmu Kuma na dade da sanin tun baya
ma shine akan daidai kai kana rayuwa ne a doron son zuciya saboda haka Baffa'am tun da
sauran mutuncinka a idanuna ka fice cikin rayuwata kafin na keta alfarmarka na shiga nayi fata²
da qimarka Meenah daka sani a baya ba ita bace yanzu yanzun Aminatuh ce a gabanka me
taqama da asali kyawun nasaba arziqi da ilimi kada ka manta bayan tafiyarka na samu
shahadar zama Barrister Aminah Haroon Moddibo so nasan yancina banason kowa cikin
rayuwata ta yanzu"

Shigewa tayi daki ta banko qofar ta murda mata key ta haye gado ta zubawa yarta ido tana
mata tunanin rayuwarta ta gaba babu bangonta na farko kwanciya tayi bacci ya qauracewa
idanunta kamar yanda ya qauracewa idanun Rasheed sosai yake jujjuya kalamanta ya rasa a
ma'aunin dazai sanyasu ta fada masa kalamai masu wahalar gogewa a zuciya tabbas shima
saida ne daga yanda ta watsar dashi da lamuransa na rayuwa yasan tabbas da gaske ba
Meenan daya sani a baya bace, to Amma meye yasa ita ta kasa gane tayi masa laifi me girman
daya dace duk hukunci ya dauka akanta?
Busar da iska yayi ya gyara kwanciyarsa tare da dauko takardar da Mai Martaba yabashi dazu
dazai shigo bayan ya fito daga dakin Meenah yace Kareem ne yabashi yace abashi kafin ya
rasu. Tashi yayi ya kunna haske zuciyarsa na bugawa ganin yanda takardar ta bushe da jini ya
warwareta ya fara karantawa da larabci yayi rubutun fassararsa kamar haka. _“Assalamu Alaika ya dan'uwa mai albarka na rubuta maka wannan takarda ne a lkcn da Raina
yake tafiya ga ubangijin daya halicceshi, badon komai ba saidon inason na qara baka hqr akan
laifin da kake tunanin nayi maka na auren matarka Allah yasani ban aureta don cin mutumci ko
tozarci a gareka ba, Ni Abdulkareem Mahfuz na zabeka na mallaka maka amanar yata qwaya
daya tilo ta zama taka dama nasan takan ce don Allah Abdulrasheed kada kabari Meenah da
Muneefah suyi kukan rashina musamman Muneefah ita kadai gareni Kuma na mallaka maka ita
halak malak"_




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account
din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko
digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/23, 7:30 PM] Oum Hairan: Matse takardar yayi a tafin hannunsa jikinsa Yana tsuma zuciyarsa
nayi masa wani zugi ya miqe a gadon ya rinqa zagaye dakin nasa a tsarinsa na gaskiya ji

yakeyi kamar bazai iya sake zama da Meenah ba yanajin ciwon abubuwan da suka faru a baya
so yanzu ya zaiyi da wannan nauyin da Kareem ya dora masa a halin yana gargarar mutuwa?
Tambaya ce da yakasa amsawa kansa ita dole akwai sarqaqiya cikin wannan al'amari komawa
yayi ya kwanta ya kasa bama kansa mafita sai zafi da zuciyarsa takeyi kawai. Abu daya da yasan ya zame masa dole shine daukar amanar Muneefah da Kareem ya damqa
masa to Amma ta yaya zai karbeta a gurin mahaifiyarta bayan yasani yanajin yanda shaquwa
take tsakaninsu ko giyar wake Meenah tasha bazata bashi yarta ba, da wannan tunanin ya
samu bacci ya dan daukesa da safe yana fita falo ya ishe kowa suka gaisa yanata raba idanun
ganin Meenah Babu alamarta hakan ya tabbatar masa tana dakin daya isheta jiya yaja fasali ya
dubi Amrah yace “shiga ki daukomin Muneefah" miqewa tayi ta nufi cikin dakin ta tarar Meenah
tayima yarta wanka tanayi mata kwalliya ta zauna suka gaisa tace “Big Cele yace akawo masa
Muneefah"
Bataso ba saidai batada ikon hanawa ta gama shiryata Amrah ta riqema yarinyar hanu suka fito
ya dauketa suka fice daga falon Mom tana kallonsa batace masa komai ba, kwanaki bakwai din
da Meenah sukayi suna karbar gaisuwa ta fahimci abubuwa da yawa sosai Addah Abulle tayi
laushi batada aiki sai kuka tunda ta haifi Muneefah bazata iya cewa ga ranar da Addah ta dauki
yarinyar ba sai cikin kwanakin nan da taketa nan nan da ita danma Rasheed ya hanata sakat
akan yarinyar duk wani motsin da Muneefah zatayi tana gareshi.




Kwanaki goma da rasuwar su Kareem bayan komai ya fara nutsawa Meenah da Kumbo Hami
suka fara Shirin tafiya Rasheed baisan me akeyi ba sai a daren da zasu tashi Mom ta kirasa
lkcn bai dawo daga yawonsa ba kasancewar har yanzun bai koma bakin aiki ba yana hutune
take sanar dashi su Muneefah zasu tafi, Saida yaji wata faduwar gaba yace “tafiya Kuma Mom
na zaci sun dawo kenan?" Murmushi Mom tayi tace “basu dawo ba to yanzu haka ma Shirin
kaisu airport mukeyi" tana Fadi masa haka ta kashe wayar ta dubi Meenah da hankalinta take
kan Sarki junior da yaketa kukan sai yabita itama hawaye ta share tace “makarantarka junior
kabari idan akayi hutu zanzo ko na turo a daukarmin kai kaji" daqyar ta rarrasheshi ta samu ta
sulale ta shiga mota suka tafi abin mamaki wai harda Addah ayi musu rakiya ashe dama tunda
suka rabu da Mai Martaba tayi aure batafi wata biyu ba ta kasoshi tanason Mai Martaba ya
dawo da ita dakinta shikuma yaqi.
Ko a airport din daqyar aka karbi Muneefah a hannunta tanata kuka so take ta roqi alfarmar
abata yarinyar take gani ko ta rinqa samun sauqi Amma tsoro ya hanata furtawa saboda ta
fahimci suma dangin uwarta sunason kayarsu da hakadai jirgin su Meenah ya daga sukuma
suka juya domin komawa inda sukafi wayo cike da kewar juna. Wannan tafiya ta zamewa Rasheed tamkar famin tsohon miki a cikin zuciyarsa abubuwa sun
fara dawo masa sabbi duk da cewa izza da dagawar da Meenah ta rinqayi masa ta girgizashi
baitaba tunanin akwai juyin da duniya zatayi Meenah ta rinqa kallonsa watsi dashi kamar tunda
Allah yayita batasan anyi ruwansa ba.

Wata biyu abubuwa suka zama tarihi akaci gaba da cudawa kamar yanda aka saba kowa yasa
abinda yake gabansa a gaba Rasheed ya koma aikinsa gabadaya sun ajeshi guri guda a Lagos
inda kullum tunaninsa zuciyarsa da ruhinsa yake Mali gashi tun a farkon da abubuwa suka
lalace da Meenah ta rinqa kiransa yayi block na numberta itama tayi block nasa koya nemeta
baya samunta wannan tasa dole ya nemi sabon layi dal saboda zuciyarsa taqi sabawa da
rashin sauraro da jin abinda zuciyarsa take muradi saidai rashin saar da yayi daya Kira sai yaji
layukan dukka a kashe girman kansa na masifa ya hanashi tambayar wani cikin yan'uwansa
layinta yabari akan cewa idan ya koma yasan yanda zaiyi ya sata a wayar Mom.
Hakan kuwa akayi bai iya hqrn wata biyun da yayi niyyar yi a Lagos ba ya dauko hanya ya taho
Daura bayan ya huta da dare suna hira da Mom a dakinta tanayi masa fadan zamansa haka
yayi murmushi yace “mom kamar akanki nake duk kinbi kin damu nayi aure" jinjina kai tayi tace
“to ai Rasheed nidai naga cikar kamalar mutum shine hade kansa da iyalansa guri guda kai
Kuma na rasa inda kanka yake kunqi ku daidaita da yar'uwarka Meenah Kuma ka kasa samo
madadi jiya ma Baffanmu yakirani yake tambayata akan lamarinka da Meenah ance mata aure
tace karatu ance ta dawo hannunka tace har abada kaima ya tuntubeka kayi masa shiru wai
meye yake faruwa ne"




Goge gumi yayi ya gyara zamansa yace “ni bawai Meenah ce bazan dawo da ita cikin rayuwata
ba aa Mom abubuwa ne sun kasa gogewa a mind dina Kuma na fahimci kamar itama ba nine a
gabanta ba yanzun" murmushi Mom tayi tace “hakane bakai ba aure ne ma bakidaya bashi
gabanta so Amma idan kaje zaku iya daidaita kanku" shiru yayi yana nazartar kalaman Mom
tace “zanji dadi idan hakan ta faru Rasheed Meenah tanasonka kanason Meenah ga yaranku
guda biyu baikamata ku Bari shaidan ya raba kanku ba babu wanda ya isa cikinku ya canza
wannan qaddarar kama godewa Allah da rabon Muneefah bai kasheka ba Rasheed rabon ya
mace zafi gareshi shiyasa kullum yanada kyau karinqa yima kanka addu'ar Allah ya rabaka da
auren mace me yayan wani a cikinta duk son da kake mata idan rabon nan ya yunquro to sai
dayan biyun ta faru kodai a rabu ko Kuma a mutu"
Jinjina kai yayi jikinsa ya qara sanyi abinda Kareem yayita qoqarin fahimtar dashi kenan ya
kasa fahimta yau kam ya gane Kuma ya fahimta wayar Mom ya dauka ya fice daga dakin nata
ya shiga mota ya nufi gidansa ya shiga ciki Saida ya dangana da dakin baccinsa ya cire
kayansa ya fada bathroom yayi wanka ya dawo ya kwanta gabadaya dakin manyan hotunansa
ne shida Meenah saina yaransa Sarki da Muneefah ya zubawa hotunan idanu a fili yace “lkc
yayi da yakamata da dawo da farin cikina" wayarsa ya dauka ya Kira Abokinsa Kamil suka
gaisa yace masa “cikin satinnan kana free ne?" Amsawa yayi da “eh" yace “ok zamuje Mali ne
jibi" bai boye masa komai ba khamil yayi dariya sosai yace “tsohuwar zuma kishin ya gushe
kenan?" Ya lura tsiya ya shirya yi masa don haka ya kashe wayar ya dauki ta Mom yanabin
contact din ya lalubo number ya danna kira lkcn tana sallar Isha Muneefah ce tana wasa da
wayar ta danna tana gwarancinta yayi murmushi yace “daughter bakin yazo kenan?" Nan

sukayita shirmensu da yarinyar bayan ta idar ta karbi wayar tunaninta ko Muntaz ne ko Urwat
tace “surutu ke gareta Mamana bata rabo da rigima" ajiyar zuciya yaja a hankali taji ya sauke
numfashi yace “hakan yanada kyau ba lallai tayi kamar na Mom dinta ba" qamewa tayi a gurin
jin muryar da batayi zato ba nandanan ta rinqajin zuciya na ayyana mata ta kashe wayar tana
Shirin gimtse layin taji yace “ranar juma'a idan Allah ya amince zan shigo qasar ki fara Shirin
zama amarya domin bazan kwana a garin nan ba saidake matsayin matata kamar yanda yake
rubuce a allon qudura duk wanda yayi karambanin shiga wannan gonar ma saiya fice da kansa
ko Kuma dole ta fitar dashi"




Murmushi tayi tace “tunaninka ne yake baka hakan nikuma inajin a raina qaddarata tayiwa taka
nisa Ya Rasheed so don Allah kada mu wahalar da shari'a kayi zamanka a inda Allah ya ajeka
idanma matsuwa akayi nayi auren naji zan fitar da miji tsakanin yau da gobe Amma kaikam
nagama aurenka" murmushi yayi yace “au haba da gaske Kuma kikeyi? To ai kin manta da Abu
daya ni idan nayi niyyar aiwatarwa yuwuwa yakeyi Meenah badon kanki da kaina ba don
rayuwar yaranmu nayi niyyar abinda na furta saboda haka kada ki manta gyarane kawai Amma
kedin matata ce domin da igiyar aurena uku akanki aka jingine aka dauranki wani.... Oh God
banaso nake tunawa fah ki share kawai sainazo".......
Daga haka ya gimtse wayarsa yabarta da sakin lebe lallai wannan yazo da izala mara gemu
dole ta takansa birki don bataji a ranta wannan tatsunniyar zata yuwu ba.





Ranar kwana tayi tana jujjuya kalamansa da safe kuwa bata sanar da kowa ba ta shirya nata ya
nata ta gudu gidansa Aunty Kharimatu batare da kowa yasan inda ta tafi ba Kumbo Hami ta riga
tasan me ta gudarwa saboda sunyi waya da Mom a haukan ma da takeyi tuni magana taje ga
kakanta ya Kuma amsa har anyi duk abinda zaayi an wucce gurin da sahalewar Mai Martaba. Tana zuwa gdan Aunty Kharimatu suka lalace da hira har dare tayi kwanciyarta dake mijinta
matafiyi ne washegari ma sukaci gaba da harkokinsu har magrib batada niyyar tafiya suna falo
suna cin dambum nama sukaji sallamar Jabir gabanta ya Fadi ya shigo yanayi mata dariya yace
“girman kujera aunty babba kinada baqi a waje fah" harara ta zabga masa tace “munafuki suwa
kak debomin?....." Bata gama rufe bakinta ba sukayi sallama suka shigo idanunsa na kanta ta
kuwa hadiye fara'arta ta hade rai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login