Chapter 10 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

maimaita kana ya kara duban kudin da matar nasa ke mika mashi sabbin kudi yan naira dari

biyar mikkakunsu a hannunta yasa hannu ya karaba yana juya kudin .

Kafin ya soma fadin ban yarda da zancen gefe ba inma zaizo ya zo nan kofan gidan yayi zance da ita

shine magana ta bayan haka kuma zan zauna da baba idan na samu lokaci.

Amma yazo ya sameni in fara sanin ko wayeshi tana kallo ya soka kudin a aljihunsa har yakai kofa

kome ya gani sai kuma yaciro kudin ya kirga dubu goma daga ciki ya miko mata yace ki rike wanan wajenki.

Ta karba a sanyayye tana mamakin mijin nasu da iya abinda zai fada ke nan kan zancen da Farida bata

bata shawaran rage kudin nan ba haka zai dunkule ya dan tsankwara mata ya tura saura a aljihu.

"Alh Rufa,i din yazo sunga juna da baba inda ya gane aiba wani wahalan ganewa yake dashi ba a cikin"

katsina don dan kasuwane da sunansa ya danyi fice.

Yayiwa mama bayani zaiga baba ya fada mai tun wanan ranan ya tsiri zuwa ranan lahadi da kuma ranan

alhamis ranan da yake ganin yana free itama alhamis din ta free wani lokaci.

Aka fara yan tsegumi a gidan kan wani ke zuwa wajen hindatu din hira ga abin arzikin da duk zuwa

yake zo mata dashi gidan.

Wanda ba iya lungunsu ba har saurab part suna lasa hakan idan yayi tafiya ya dawo haka zaizo mata da

tsaraba mai yawa yasa a shiga mata dashi gida wani lokacin baiko tsayawa ta fito zai aje ya wuce sai dare yazo hira.

Ganin haka yasa aka kulla cewa gwaggo Asiya ta sauko ta lakaci arziki inda ta soma jan hindu din a

jikinta don dai taji me suke ciki a dakin nasu.

Yaran da hankalinsu da wayau amfanin ilimi ke nan kuma don sun gane nufin gwaggon nasu kuma

matar ubansu.

Sun fahinci bada zuciya daya take wanan abinda take masu a yanzu ba matar da har shegantasu ta

tashiyi a gari itace yanzu lokaci guda zata dawo ta nuna tayinsu tana wani jansu a jiki ko abu suke nema da sauri zata dauko daga dakinta tace masu gashi.

Itama mahaifiyarsu taja masu kunne sosai kan shige masu din da gwaggo din keyi a yanzu don haka sun

kasa sake jikima da ita.

**************

Yanzu kan iyalansa sun san da zancen neman aurensa inda sun dauka wasane a yanzu sun san da

gaskene don ko bai boye masu ba don har sunanta sun sani Hindatu.

Kishi kan saidai a bayanshi a nuna a gabanshi ba a isa a nuna hakan ba tun bayan ciwa Nabila mutunci

da yayi kowa ya kama kanshi a gidan da zancen .

Amarya ko yar aiki don yar aiki za a dauko muna yanzu tunda tasan abinda zata zo ta tarar ai tunda

bata neman na kanta sai mijin wasu.

Yake fito daga daki yana fadin ashe neman na kai yana da dadi ni aka tauye min rayuwa aka hadani

daku ?

"Ai gara ita nina ganta nace ina so takuma nuna tana ra,ayina auren soyayya zamu dani da ita ba matar"

cushe bace ita.

"A cusha maka abu haka ba ma,ana ka zauna da mutum don dole yanama iskanci a gida don bai saba cin"

arziki ba itako ko wayana kira mu gaisa sai tayi min godiya saboda sanin muhinmamcina bata sameni a bagas ba ?

Cewan da yayi cusa masa akayi shine yaci mata rai ta shige daki tana kuka bai mata ba ta yafa takai

karanshi wajen mahaifiyarshi.

Inda mahaifiyar ta hau fada tana fadin tun yarinyar bata shigo ba ya fara ciwa yar uwarshi fuska haka

"inagata shigo gidan haka zai nuna mata cewa su din hadasu akayi dasu bashi ke ra,ayin aurensu ba ya aura ?"

Tasa kanwarshi ta kirashi bai bata lokaci ba sai gashi a gidan ya zata wani abune da yar uwar nasa ta

kirashi tace ummah tana son ganin ka yanzu yaya .

Sam ya manta da sunyi hakan da Nabila din sai gashi ya iso saidai yana ganin Nabila din zaune a kasa

"yasha toka ya murde fuskanshi suka soma gaisawa da hjynsu da fuska ba fara,a a lokacin."

Meya hadaka da matarka tambayan data jefo mashi ke nan bayan sun gama gaisawa din dashi .

Saida ya dan dubo Nabila din yace ita bata fada maki bane ummah magana tayi ni kuma nabata amsa

daidai da abinda ta fada ai.

Koma meye tace ai bai dace kace zakai mata gori ba yanzu don kafi kowa morewa wanan hadin balle

ya zamo abin gorantawa a gareta yanzu.

"Amma ummah ai,,,, kai dakata don Allah ka saurareni banson shirmen banza daga Nabila har barakha"

sun wuce ka zauna kana masu gori don an hadaka aure dasu ?

Diya nawa ko wace ta haifama da zaka zauna kana masu gori akan haka ummah aini ba gori nayi mata

ba cewa da tayi zatazo cin bamza .

Shine nace ko taci banza auren soyayya mukayi da ita dakatar dashi tayi tana fada har tana ikirarin

cewa zata iya hanashi kara aure idan ya kawo mata diban albarka.

Ka dauki matar kuje gida ta fada ka matsa ka bata min rai zakaga abinda zai biyo bayan hakan don sai

inje gidan su yarinyar in hana a baka ita komai kake takama dashi kuwa .

Hakkuri dai yaba hjy din sukai mata sallama suka fito a mota shi kuma ya kafawa Nabila din nasa dokan

da mutukar tasa ya bata da uwarshi ita kuma sai ta dandana kudanta a hannu.

Wanan yasa taji tsoro bata iya tanka mashi ba don batayi zaton ran mahaifiyar nasu zai iya baci haka

ba saida taji irin fadan da uwar tayi mai a gabata tun nan cikinta ya duri ruwa sosai.

A gidama taresu yayi da abokiyar zamanta yayi masu gargadi mai kaushi yana fadin kunsan dai ban

tauyeku ba a zamantakewan mu daku ?

Baku mi wani abu najin dadin rayuwa a gidan nan kun rasa ba duk da bakanta min ran da kukeyi kuwa

ban tauye ku da komai na rayuwa ba da har kuke son ku hanamin jin dadin rayuwani ?

To wallahi matukar kukace haka zamuyi daku sai dai gaba dayanmu mu zauna acikin bakin ciki kuwa

tunda haka kuke so ayi ?

Nikan yaya ina ruwana da zancen ku tunda bakiji wani abu ya fito daga gareni ba ban isa in hanaka kara

aure ba ai tunda nima auroni akayi aka kawo barakha ta fada cikin son ta gwale yar uwar nata.

Kun daiji na fada maku ba zan yarda da mace tana hadani fada da uwata ba aure koba hindatu ba

matukar ba mutuwa nayi ba sai na kara aure a gidan nan.

Karshe dai suka bashi hakkuri ya bar zancen don tagane tayi kuskure kuma idan taje jan capacity

karshe kanta abin zai iya komawa gara ta rufawa kanta asiri ta zauna lafiya yadda kowa ya taushe zuciyarshi badon yaso ba.

Anyi haka da kamar sati hindatun ke fada mai mahaifinta yana son ganin shi yayi mamaki inda ya zata

ko zancen aurenne zasuyi dashi don shi a shirye yake saiya mayar da hankali ya gyara gidansa ke nan su tare tare da ita .

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/18, 9:32 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Bani dai batsa sai fadakarwa idan bai karaki ba zai kara wata kuyi min hakkuri hausan mu ke nan na yan

kebbi masu fahinta suna fahinta kuma su karu.

"Bani fatan inyi shari,a da alkalami gobe kiyama kan rubutu donshi bani rubuta abinda babu a tafiyan"

rayuwan dan adam musanman nan arewa .

"Kuyi hakkuri ni yar kauyece Allah ya nufa sai kun sanni ta rubutu fadakarwa mukeyi ba bata al,umma ba"

komai daren dadewa wata rana wani zai amfana daga fadakarwan mu insha Allah nagode.

Ku bamu hakkin mu ba laifi bane don munce a bamu rubutu yana cin rayuwa ko nawa kuka bamu ba

zaku iya biyan mu ba .

Maraya nace akirakane don maganar yar wajenka da labari yazo min ta fara tsayawa da wani yaro a

kofan gidan nan.

Hakan ba laifi bane din takai munzalin ta tsaya din da samari dubaga yadda muke bada auren yaran mu

a gidan nan.

Daba don karatun nan na zamani da sukeyi ba lalai da yanzu ko wacensu tana dakin mijinta harma an

kaiga rabo idan Allah ya bayar.

Don ka bata umurni kuma ban mamaki dubaga yadda wasu yan uwanka suke son su bata muna tsarin

tarbiyan gidan nan da muka taso a cikinsa.

Sanin kankane a baya dan gidan nan sai ya aje mata yar gida daga cikin dangi kafin ya fita ya auro ta

"waje son ra,ayinsa."

"Sabanin ku da tsoho yace a barku ku kawo daga wajen tunda kuna ra,ayin hakan zamani ya sauya da za"

a wuce da wanan akidar tamu da mukeyi da farko a cewan tsohon mu.

Hakane baba ya fada yana gyara zama yace da kyau amma ni sai nake hango hakan kamar kar a barshi

ga baki daya a gidan nan duba ga yadda zumunci tun yanzu yake ta rauni a tsakanin ku.

Wanan baisan darajan wacan ba wacan mace tana duba ai diyanta diyantane da mijinta kaga nan gaba

abin ba zai haifar muna da mai ido ba a zurian nan.

"Don haka har inkai kaba yaron dake zuwa wurin ba,indiya umurnin ya soma nemanta ina son ka dakatar"

dashi daga zuwa inda take .

Domin tana cikin wa yanda nake son yiwa hadi a bana a cikin gidan nan gida bai koshi ba ance ba a

kaiwa dawo inji manya.

Saida baba ya gyara zama a lokacin ya iya furta to baba insha Allahu za a dakatar dashi din da yarda

ubangiji.

"Maraya nagode Allah yayi maka albarka a kullum ina maka fatan alheri dakai da zuri,anka irin duba da"

"biyayyan da kayiwa iyayyenka Allah ya shiryama zuri,anka suyi maka fiye da hakan ya kara amsawa da amin baba."

Kana cikin yayan gidannan da nake alfari dasu duba da iri biyayyenka a garemu wanan yasa nake maka

uzuri cikin lamarinka.

Sai magana ta biyu naji dadi kwarai daka dauki shawaran dana baka akan iyalinka wanda nasan ka gyara

a yanzu sosai fiyema da tsamanina labari yana zuwa min a gidan nan akan komai nako wani lungu da sako na cikin gidan nan duk da suna ganin an raba gida amma ai bamu rabu ba a ganina ?

Hakane baba nagode watau maraye da kake ganin yaran nan matane Allah ya baka da farko kuma ka

rugumesu kana kaunan abinka fiye da masu yayan maza bakaji dadin da nake jiba a lokacin ?

Musamman yadda ka samu mace mai imani da rikon aure sai dai kuma kash shigowan wanan yarinyar

sai tayi kokarin dusar da komai daga gareka .

"Alhamdullahi tunda ka gane gaskiya a yanzu ka kara kaimi kabawa yaran nan kula yadda shari,a ya bada"

ai wa yaya mata insha Allahu da yardan ubangiji dadin ku yana tafe a kansu wata rana.

Wanan yasa kaga bani son ka kauce kamar ka butulcewa Allah ne idan kayi haka bamu san meye

dalilinsu ba a cikin mu.

Allah yaima albarka ya kara fada ya amsa cikin jin dadi da amin baba suka dan taba hira sukai sallama

"da juna shine kiran da hindu din tacewa Rufa,i mahaifinta yana mashi a lokacin."

Don kuwa washegari tana kwance dakin mahaifiyarsu yasa mata kira tafito yake fafdin yaron nan dake

zuwa wajenki baizo bane kwana biyu.

Sai gobe zaizo baba taba mahaifin nata amsa a kunyace to ina son ganinsa akwai maganan da nake son

muyi dashi inson samune basai goben da zai zo ba.

Ya amsa din yazo ya sanar da ita tun yana hanya cewa gashi tafe ita kuma ta samu mama ta sanar

mata da zuwanshi cikin mamaki mama din ke fadin lafiya dai babanku ke son ganinsa ne ?

A cikin wani yanayi na dan damuwa take fadin nima ban sani ba mama ya dai fada min ince yana

magana dashi ?

Caraf gwaggo Asiya ta tsoma masu baki ga zancen tana fadin kema kinsan akwai magana ke nan tunda

yace yazo din bari a fada mai don ya sani tayi gaba zuwa turakan maigidan wanda kofan falon yake daga waje tana fada mashi ta dan gyara falon cikin munafunci ta fito.

Falone babba da kujeru a cikinsa wanda yake karban bakinsa maza akasarin iyayyen namu duk sunyi

wanan a sassansu da aka basu a gidan.

Kasan an malala mai jan kafet daga can tsakiya kuma katon tv baba ya saka da sauran tarkace iyayyen

mu mata ke gyara falon duk wace take da girki a rana zata shiga ta kakkabe ta sharo a fesa sheltox da turare a rufo .

Koda ya iso bai dan jima ba fadilace baba yasa ta fita tayi mai iso zuwa inda yake tayi gaba tana sallama

shi kuma yana biye a bayanta zuwa ciki.

Ya shigo da sallama yariyar ta fice ya samu waje ya zauna cike da ladabi yana gaida baba din da wuni

sannan ya dukar dakai din saurarenshi.

"Alh Rufa,i nina aika a kira min kai don wani magana daya taso game da zancen neman daka soma a"

gidan nan na yariyar wajena.

Kasan na fadama lokacin dakazi neman izzini cewa ina da magabata na gaba dani a gidan nan son wan

mahaifina yana raye da ransa ?

Baba na fadin hakan yaji wani zazzzafan gumi ya fara kyato mai a jikinsa wanda dakyat ya iya dago kai

ya dan dubi baba din yace hakane baba .

Din haka ina fatan zaka fahinceni a yanzu abinda zan fadama kuma kada hakan ya soshi zuciyarka don

Allah ba komai baba ya fada a cikin karfin hali irinta maza.

Baba yace to Alhamdullahi shekaran jiya ina zaune wanan baban namu ya aika ya kirani yana neman in

dakatar dakai da zuwa wajen ita hindu don akwai wanda zasu ba a nan gidan cikin yan uwanta.

Don haka yau din ya zamana rana ta karshe da zakazo gidan nan da sunan kira a gun Hindu din soboda

kiyayye zancen tsohon kamar yadda ya bukaci ayi.

Ina fatan zakayi hakkuri don Allah ba laifi kai muna ba ko munji wani abin asha daga gareka babu ko

daya abune da bawa keso Allah kuma baison hakan a gareshi mu dauka haka zancen yazo a kaddaranku.

Yana zaune shiru kansa a kasa ya kasa wani motsi a wajen sai gumin da yake dan rufe masa jiki lokaci

guda jin zancen yake kamar a mafalki yake wanda zai falko ya iske mafalkine ashe ?

Idonsa ya runtse lokaci guda yana jin bama zai iya dagawa ba balle ya iya takawa yakai kansa wajen

motansa a lokacin.

Don ya kama kwallafawa ransa yarinyar nan ya tsara irin rayuwan da zasu kasance da ita idan ya aureta

bai taba sanin dadin soyayya ba sai akan haduwansa da hindatu gashi kuma iyayyenta sun ravasu a yanzu.

Hakkuri za ayi Alh haka Allah ya tsara lamarinsa ita din ba matarka bace dama ka dauki hakan kaddara

nasoka da hindatu duk bincken da nayi ya nuna kai din mai mutuncine da zan iya baka aurenta amma ubangiji bai nufi hakan ba a tsakaninku.

Insha Allahu ubangiji zai musayama da wace tafita mungode kwarai da irin dawainiya daka dingayi

mata in akwai abinda kake bukata cikin abindaka bata sai kayi magana a maida maka suna nan uwarta nace ta aje dama ?

Sai lokacin ya dago kai a hankali ya samu furta haba baba tsakanina da hindu soyayyace ai duk abinda

na bata koban aureta ba zan iya mata ko wani nata abinda yafi haka insha Allahu.

Sai baba din ya kara jin tausayinshi ya cikashi yarone mai mutunci daya san kanshi tare da sanin girman

manya.

Ya daga da kyat yana mikewa sukai sallama ya yana godiya ga baban din don ya fahinci shima baiso

hakan ya faruwa fin karfine irin na iyayye.

Hindutu na dakinsu kwance cikin zullumi taji Saffanah na kwala mata kira ta fadon dakin tana fadin

naga Alh ki waje yaya kamar ransa a bace yace inkiraki wai kuyi sallama ni kamar kukama naga yanayi don a rude yake min magana.

Kuka kuma meya faru kinkan fara haukanki ke nan saffanah mama take tsawatawa yarinyar a lokacin

"a,a mama bari naje ingani farida ta fada bari kawai inje ita hindu tace ta mike tsaye a cikin sauri ta figi hijjab zata fita."

A daidai lokacin baba ya leko yana fadin ke hadiza yarinyar nan taje suyi bankwana da mutumin nan

don daga yau din nan ba zai kara zuwa wajenta ba kuma ?

Duk wanda ke gidan jin zancen yayi a lolacin kamar saukan aradu a kunnuwanshi sai inna halimane tayi

karfin halin fadin meyayi zafi haka malam ?

"Ko kina da maganane ya bata amsa a hasale ta suke kai tana fadin a,a da naci me zan yafawa kaina"

maganan da bai shafeni ba wanan tsakaninka da yarkace ai.

Ni gani nayi kawai abin baiyi dadi ba gaskiya ta fada tana juyawa zuwa dakinta yaya wani abu akayi da

kabarsu tunda suna son juna mana ?

"Wai ban isa inyi iko da hindu bane hindu dai yatace ina da ikon komai da ita gidan nan a,a kayi hakkuri"

amma ke rufa min baki don Allah .

Ko zanki bin umurnin babane yace bai aminta ba da haka auren gida zai mata so kukeyi ince ban yarda

da hukuncin daya yanke bane kome ?

Baba kuma shi baba da kanshi waya saura wanan auren hadin yanzu kuma don Allah dai zamani yazo

da sauye sauye a yanzu abar yarinya ta auri wanda take so zaifi.

Kuna da wani magana baba zai kafa dokane gidan nan malam ya kyatarene tayi hakkuri duk wanda

malam zai hadata dashi ai dan uwantane dayasan zafinta ?

Amsan da mama ta bayar ke nan a lokacin a gaban kowa don zancen yakai karshe wanda a lokacin

hindatu ta kai ga fita su farida na jiran shigewan babane subi bayanta.

A tsaye ta