Chapter 9 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

rainawa kikayi ba ?

Kada muyi haka dakai please idan na karbi kudin ka tun yanzu mama zatayi min fadan hakan kada muyi

haka dake please ya fada.

Ta mika hannu ta karba tana fadin tagode amma don Allah kada ka batani da rike kudi don hakan ba

"dabi,an mu bane gidanmu."

Ya gamsu da bayaninta yace gashi kuma zaki auri mai kudi sai yaya ke nan kuma kunya ya bata ta bude

motan ta fito suna tsaye sai hiransu sukeyi shima fitowa yayi yana kiran sunan farida .

Suka juyo yayi mata hannu tazo yace bansan sunan yan uwan naku ba tace Fadila da Aziza kuma dukkan

ku mahaifiyarku dayane tace ga kama kana gani a zahiri.

Ya mika mata kudin dake hannunshi yana fadin naso in jiraku sai kun fito amma kuma ana nemana a

gida yanzu dole zan koma ki kula min da amaryata don Allah suka kwashe da dariya gaba dayansu.

Yaja mota ya tafi suna mashi godiya yayu masu horn yabar wajen kallon juna sukayi Fadila ta soma fadi

kai amma yaya kinyi dace wallahi.

Dame fa ta tambaya a cikin gatse yar uwar tace da saurayi mana yaya ki mutu yace yana da mata kina

min maganan nayi dace can ?

Dan ihun da Farida ta sake yasa suka maida hankalinsu gareta ta soma fadin wai har dubu talatin ya

bamu fa watau kowan mu dubu goma goma ke nan fa .

Nima gashi ya ban take nuna masu kudin karbi ki boye a jakkarki har mu fito faridan ta hada dana

wajensu ta saka a jakka suka shiga gidan inna gambo din.

*************

Hjy ku diba min yaron nan don Allah kamar fa bayaji baya magana tunda muka dawo sam baiyi magana

ba fa na zata zafin ciwone yasa ya daina magana ?

Karban yaron sukayi suna buga abu kusa da kunnensa ko motsi yaron baiyi ba salati sukasa lokaci guda

hjy hafsatu na fadin wallahi baiji kamar ya kurmancene fa ?

Innalillahi hjy larbata fada tana mikewa tsaye zuwa inda suke sun kewaye yaron ta dan duka kadan

tana fadin babana shiru babana shiru yaron bai juyo ya dubeta ba ta dago tana fadin akwai matsala gaskiya.

Kuka sosai Gwaggo Asiyan ta sake tana fadin shike nan an sabautani an kaini an baro yaro yana min

lafiya yarinyar nan ta kwaso cuta ta yaba mashi yanzu ga abinda ya biyo baya ?

Subbahanallahi Asiya lafiyanki kuwa ita yarinyar waya yaba mata cutar zaki bata jerabawan ki da

shirka dan shashanci.

Wallahi hjy da yarinyar nan bata dauki wanan ciwon ba da bai shigo lungunmu ba yanzu gashi an bar

min da da wahala yaron ya koma min kurma ?

Wallahi ki tubawa Allah don ko ke baki wuce hakan ba idan Allah ya tashi jerabaki kibar zancen nan a

nan tun bai fita mutane sun raina maki wayau ba ?

Magana haka sai kace ba musulma ba don Allah ku daina hakan bakyau wanan yana bata zama har

tsana yazo ya shafi yara kinga ya tashi ga manya ya koma ga yara kuma ?

Suka bata magana kafin ace kwabo har part din ya cika da matan cikin gida kowa da abinda yake fada

an kira baba yace gashi tafe yana kasuwa.

Su baba yahayane suka dauki yarom zuwa asibiti tare da hjy laraba da inna hafsatu part din mu ta

dawo ta kafa zage zage a cikin shiya.

Haka baba ya dawo ya sameta tun daga kofa yake fadin wai menene meya samu baba din kuma ?

Yaya an cuce dama ana bakin ciki da yaran nan gashi yaro ya koma min kurma yau ta fashe da wani

irin kuka mai tsuma zuciya.

Garin yaya ya koma kurma kuma bangane ba matar baba hassan na mashi bayani ta mike tana fadin

ni ban kula ba tunda muka dawo yaron nan bai magana ashe ciwon ya rike mai makoshi .

Wallahi an cuceni waya cuce ki ni shine ban gane ba ai kinata fadin an cuce ki an cuceni mana yaya ita

salma data kwaso ciwon gashi ta mike amma ni an barni da nakasan da ?

Haukan bamza ke nan kuma da Allah zakiyi jayayya kikan fara shirmenki ke nan wanan abin ba daga

Allah bane ita Salma a ina ta samo ciwon ina ba lungum gidan nan da yaran nan basu kyandan nan ba ?

Cikin wanan fitinan yan matan suka dawo suka samu ana fitana a gidan nasu suka tsaya suka fahinci

akan me ake wanan rigiman haka ?

Mama Dije da imani ya kasheta komai bata samu fadi ba a lokacin haka kuma ta kara tabbatar da

Asiya jahilace bata wasa ba.

Ashe ilimi yana da dadi ga mutum don kuwa da Asiya tana da ilimi da batayi wanan abinda takeyi din ba

"a bainan jama,a ."

Haka suka dawo da bayani da likita yai masu idan anyi nasara bai gama kashe mai dodon kunnesa ba

zai dawo da jinsa ko kuma ya dan iya fada amma a cikin bebanci irin na kurame.

ZAIINAB IDRIS MAKAWA

"[11/17, 9:57 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI

HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS

"MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Ganin tashin hankalin da gwaggo Asiya ta saka mama yasa ba wace tayiwa uwar hira game da fitansu

don mutane sai shigowa sukeyi yin jaje .

Kan abinda ya samu yaron wasu idan sunyiwa gwaggo Asiya jaje sukan dan sato jiki zuwa wajen mama

su bata baki akan tayi hakkuri Allah yana kallonta.

Don saida yakai baba Alu yazo ya tsaya a tsakar gidansu yaiwa Asiya din tas akan irin shirmen hauka da

takewa mutane ya nuna mata shima tsohon kwanune idan ta matsa matakin da zai dauka ba zai mata dadi ba.

Dole tayi shiru ta koma daki tana gumjin kuka cikin bacin rai don tasan baba Alu sarai zai iya daukan

matakin da yace kuma hakan ba zai mata dadi ba.

Gashi a ranan baba ya bata mamaki don bai goyi bayanta ba kan borin da tasoyi ta dagawa mama

hankali ta shafa mata kashin kaji a cikin gida.

Don mutanen gidan su tsani mama akan tana bakin ciki da yaya mazan da Allah yabata har ukku reras

yasa wanan abin ya samu danta baba hamza ke nan mai sunan mahaifinsu baban mu watau kakan mu.

Ashe zance bai kare ba don ko da safe hargowan maizogale ya tayar da mutanen gidan da tazo da fada

kan me baba Alu zaice kada a fadi gaskiya.

Mamanmu tana daki bata fito ba saidai duk zagin da maizogale din ke aika mata a kunnuwantane sai

inna halimane ma tayi magana a lokacin take fadin haba inna maizogale.

In abu ya faru a barwa Allah mana wani ya isa yaiwa wani irin haka ita kanta salman ai bata wuce

"hakan ba a wajen Allah bacin rai karyasa ku,,,,,"

Ke rufamin baki kinji halan namu san komai bane akanki don kina tsaye kamar icen kabari yasa ai ta

barki bata shiga shirginki gidan nan don tasan ke din ba kanwar lasa bace tsaye kike dake da iyayyenki akan aure gidan nan.

Amma dai inna banyi tsamanin haka gareki ba gaskiya da girmanki zaki biyewa haukan Asiya da

shirmen banza kun taba ganin inda wani yayiwa wani wani abin irin haka ?

Dallah ja can kaime ka sani an riga an kammalaka waje daya kasan sherin matane meye mace bata iya

yi a duniyan nan akan kishi ?

Ita Dije din ta kammalani kuma inna ?

In bata kammalaka ba kazo kana wanan maganan abin kuka ya samemu yaro ya nakasa ta dalilinsu kace

wai kada ai magana a barwa Allah.

"Toshike nan sai kuje kukai kara duk kotun da kuke ganin za,a daukan maku mataki baba ya kashe"

zancen nan bai kamata kizo kuma yau ki tayar da zancen nan ba ?

Inya kashe zance ya dauki mataki mana amma zai kashe zance yace ayi shiru ga gaskiya ana gani yace

"ba za,a fada ba ?"

Inda taje akai mata hakan ai kowa yasan hanyan shima mu zuba da ita a gidan nan tunda abin ya koma

haka yanzu.

Abindana guda ke nan tun farko ina kani dai maraya kaga aikin maguzawan irin nata ko ai mai hali baya

fasa halinsa maizogalece fa ?

To bari kiji wallahi duk wani abu ya samu yarinyar nan ko diyanta ki rubuta ki aje ga shedu nan sai

"munyi shari,a dake a garin nan ."

"Ahhaye nanaye shari,a ai mun saba ba farau ke nan ba Alu kasanni na sankafa Alu ?"

Ya ja tsuki yana fadin kije Allah ya fiki yafi sherinki kuma duk abinda zakiyi Allah zai kare hadizatu da

"zuri,anta insha Allahu."

Gaskiya da baku son a fada don ta cika maku gida da yaya mata data samo a wajen yawon banzanta

tana cewa yayan kune.

Don baku da hankali kun kasa tsayawa ku duba yaran nan ba zubin gida suke daukowa ba zubin wasu

kabilune don kanku ya kulle ?

"A,a a,a dama sherin da kukewa yarinyar nan ke nan kuka hadata da mijinta ashe kowa garin nan yasan"

dan kwara mahaifin hadiza ansan kamaninsa kuma kaf dinsu shi suke kwasowa .

"To wanan maganan bamu zakiyiwa bayani ba shari,an zaki fada a inda ta samosu ya juya gunsu baba"

"dake fada yace kai musa kira min magatakarda yanzun nan a daukaka shari,a akan zancen nan sai matar nan tayiwa kotu bayanin inda zancen nan ya fito ?"

Tana zarton zancen wasane don haka ta tsaya tana mayar da bakaken maganganu ga tsohon da yake

kani ga marigayin mijinta.

Sallaman magatakardane yasa jikinta ya soma sanyi tsohon yace a ka daiji irin munanan kalaman da

take fadawa sarakuwar mu don tana kishi da yarta ?

Don haka ina karanta akan tana neman bata min sunan gidana da kuma na sarakuwata data hada kishi

da yarta.

Aishi ba mahaukaci bane irinka tunda yasan fadan gida duk abinda yazo bakin mutum yana fadawa dan

uwashi ?

Bako da irin wanan maganan mai karfi da zai iya tasowa shekaru aru aru ba ?

Magatakarda ya fadi hakan cikin dakewa ya daure fuska yace dolene aje kotu a nemi inda zancen nan

ya fito abawa mai gaskiya hakkinshi .

Kai ibrahim ka biyuni a baka sammaci a kawo wa dukkansu da uwar da yarta dole a zauna kotu kan

wanan zance don ayi maganin abin.

Haba don Allah ana baka kana roko wanan fa fadan gidane ba kuma yau aka saba hakan ba tsakaninmu

dasu gidan nan shima ya sani.

Kudi tsohon ya lalubo a cikin aljihunshi yana fadin ga kudin kara malam na komai da komai sai muji kira

daga gareku ni Ali zaka saka ina karan Asmau maizogala ya juya zai bar wajen.

Haba malam Ali kada kai mun haka mana don Allah munyi fiye da hakama bakai karana ba sai wanan

zai hadani har kotu dakai don Allah ?

In akwai inda yafi kotu sai mun shiga kan batawa jikokina suna da kikeson yi a gari gara in daukar masu

mataki tunda shi kun mayar dashi matakalan takawa ku haye ?

Kaima Allah Ali ka tsaya a kashe zancen nan a nan nida tsigar kishi na fada bada wani abu ba Allah na

tuba matan gidan nan kaf akwai wanda yakai yarinyar nan hadiza kamun kai da rikon aure ?

Gaba daya wanda ke wajen saida mamaki ya kashesu ta shiga ban hakkuri tana bin tsohon ita da yarta

suna bada hakkuri .

Baba imani da mamaki yasa yayi tsayuwan baki sake yana mamakin wanan abin don yadda suka juya

zancen lokaci guda alhalin sun jima suna jefanshi da wanan kalman .

"Wanda har yake jin mama ta fice mai arai bai iya wani mu,amulan aure da ita kuma duk da yayi bincike"

baiga gaskiyan hakan ba amma kuma ya kasa sakin jikinshi da ita.

Sai gashi yau da bakinsu a gaban kowa suna fadin wai sherine irin na kishi yasa suke fadawa mama

hakan amma wallahi ba gaskiya bane.

Baba yayi nadama yayi kukan zuci yasa an kira mama da Asiya har halima ya kafa sheda koba a bakinsu

"ba wani ya aibatan mashi yaya zasuyi shari,a da maishi koda zai rasa komai a duniya kuwa."

Washegari ana nan dai sama sama a gidan saiga baba ya shigo da kayan marmari a cikin leda dakin inna

halima yake lokacin.

Yasa ta kira mai salma ya zauna nan a kofanta tayi mai shimfida ya tara yaran yana raba masu kayan

marmarin Allah sarki yarinyar bata taba ganin hakan ba gareta saita fara makewa takasa zuwa wajen baba din a lokacin.

Shima yaji wani iri a ranshi yake fadin zo salmata kinji ba komai zan maki ba lemo zan baki kisha mama

sai aikinta takeyi bata ko dago kai ta kallo inda suke ba.

Ana bata ta hari baba dashi tana mika mashi yaron ya karba shima yazo wajen baba ya mika mashi nasa

rabon.

Wanda inda kafin wanan fadanne saidai ya mikawa inna Asiya ledan ita kuma ta shige dakinta dashi

susha ita da yaranta su kadai a daki.

Fuska ta daure ganin abinda baba yayi ita a zatonta zai saukone idan yaga tayi fushi yadda takeyi a

baya amma ranan sai taga sabanin hakan .

Sai kuma ta koma tsamani neman shiri yakeyi da mama a ranan yasa ya soma nuna kulawa kan yarta

don ta sauko ta yarda dashi .

Hakan yasa ta soma sakin haibaici a bayan fitanshi tana fadin ina ruwan sakarai dama neman tayi akeyi

an dade ba a hadu ba.

Caraf ina halima ta bata amsa da abu cikin duhu ai sirine wanan kuma ba a iya ganewa ai don abin

sirine.

Tunda har gobe ruwa na maganin dauda asha ko ayi wanka son ruwa komai dadewanshi yana da

amfani don da ranan da zai taimakawa rayuwa ai.

Cin danko har dasu kaza yanzu da nake zancena na ambaci halima a wajen nan halima ina baki

shawara da kifita hanyata wallahi don ba dadine gareni ba.

Hanya kan tunda mun hada aisai hakkuri don ki bangajeni in bangaje ki dama mukeyi a gidan nan ba

zan kara saurara maki ba Asiya tunda nagane kin mayar damu bamu san abinda mukeyi ba ?

Ita din wace kika raina din don tana hakkuri tana babba a gidan nan in baki sani ba ki sani randace

uwar ruwa duk a cikin mu .

Muryan mijin nasune ya katsesu da fadin tau tau zaku fara yanzun nan ko wacen ku na kwana gidansu

kuma da sheda a hannunta.

Wanan maganan da baba yayi yasa su natsuwa kowa ya kama gabanshi amma kan na ciki yana ciki a

"zuciyarsu don kishi bala,ine."

"Tana zaune ta idar da sallah magariba da tasbaha a hannunta tana ja tana jiran isha,i farida ta tsuguna"

a gefenta tana aje mata damin kudi da yasa mama din dago kai tana kallon yar nata cikin mamaki ?

Farida wanan kudin haka daga ina mama tun shekaran jiya suke dakin nan na boyesu ganin ranki a

bace yake yasa ban nuna maki ba.

Nan ta soma yiwa uwar bayani akan kudin cewa saurin dake son yarsu hindatuce ya basu bata boyewa

mama din komai ba game da kudin.

Farida garin ya kuka amsa kudin namiji haka bayan ba matsaya akai mata dashi ba kunsan me hakan

ke nufi kuwa farida ?

Magana kuke son ku jawo min bayan wanda nake ciki a yanzu idan Asiya tasan da zancen nan labarin

zaisha banbanne kuma don zata juya zancen tace na soma turaku wajen maza kuna kawo min kudi.

Bama zataji ba mama ni wanan matar a yanzu ban kaunar ganinta balle taji wani abu daya shafeni na

rayuwan mu .

Kada ki soma ko bata matar mahaifinku yar uwar mahaifinkune tana zaman gwaggo a gareku don haka

kishin mu bai shafe ku na fada maku batun yau ba kuwa.

Mama da gwaggon muce da gaske aiba zata nemi shangata mu ba tana neman bata muna suna a dinga

maki kallon banza damu dake ?

Na dai fada maku ku fitar da bakinku a cikin zancen wanan ba maganan yara bane kudi kuma ku mayar

mashi da abinshi.

Kuce nace kada ya kara hakan har idan yana sonta tsakani da Allah yazo wajen iyayyenta ya nemi

aurenta.

Mama baya gari yace zaiyi tafiya zamu kwana biyu bamu ganshi ba mama kada dai mu kara amsa don

ko wanan din wallahi munki karba yace wai mun rainane .

Har nawane kudin nan Farida mu dubu goma goma ya bamu mu ukku talatin ke nan ita kuma yaya

dubu hamsin .

Farida kanki daya kuwa mai sonka tsakani da Allah zaima kyautan irin wanan kudin haka masu yawa

lokaci guda ?

Haka ya nuna da wata manufa yazo gun yar uwarku ke nan badai da aure ba ?

"A,a mama wallahi yace ko yau akace ya fito shi a shirye yake kuma zaizo idan ya dawo yagasu baba"

don ansan yana cikin manemanta.

Dan bin yar tayi da kallo kamar tana nazarinta kafin tace ina ita hindu din tabi sannu irin wanan abin a

budewa mace ido da kudi hatsarine baba ga ya mace .

Kira min ita idan na idar da sallah ta fada tana mikewa dama hindu din hannuta a gaba don irin

hukuncin da uwar zata yake idan taga wanan kudin haka mai yawa.

Fada mai kamar nasiha tasa yar agaba dukkansu tayi masu sannan tace a aje kudin har mijinsu yazo da

sauri farida tace wallahi mama da baki nuna mai ba kawai ki aje kiyi amfani dasu tunda ba zaice a biyasa ba ai koda bai aureta ba.

Farida ina horon ki da kwadayi kudi abin banzane kina ganinsu nan sai su zubar maka da mutuncinka

lokaci guda.

Barin nuna mashi kawai ya sani yafi muyi abu haka a cikin duhu dani daku gara inada sheda kan komai

zaifi.

To mama ki raba biyu mana in yaso saiki nuna mai na wajen mu ki boye wanan din kada a karbe duka

kuma ki tashi baki tsira da komai ba a ciki.

Shawaran yar nata tabi bayan tayi tunane kan zancen da sukayi din inda da mijin nasu ya shigo dakin

da safe ta fito da kudin ta nuna mai tare da bayanin yadda yarinyar ta bata labarin haduwan nasu.

Sunan ya