Chapter 11 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

hangoshi ya jingina jikinsa da mota ya sada kai kasa gwanin ban tausayi ta karaso wajensa sai

lokacin ya dago jajayen idonsa da suka gama rinewa ya dubeta yana kokarin kakaro murmushin dole a fuskanshi.

Sahibata an wuni lafiya ya fada a cikin karfin hali sai kokarin bin yanayisa takeyi tabin kwayar idonshi

tana son ta tantance yanayinsa a lokacin.

So yake ya dan kwantar mata da hankali amma ya kasa hakan da kyar ya bude baki yana fadin kinji

hukuncin da iyayye suka yanke a kan mu ko ?

Baba ya kiranine don ya ban hakkuri na daina zuwa wajenki don kakanku ya riga dayayi maki miji ashe ?

Kakana wani kakan nawa wai tsoho shi yayi min miji kome ?

Ki kwantar da hankalinki hindu haka Allah ya nufa damu saidai ina son ki sani wallahi nasoki tsakani da

Allah son da ban taba yiwa wani mahuluki shiba a duniyan nan bayab iyayyena.

Hawayene ya soma zubo mata a lokacin cikin karfin hali da daurewa yace saidai ina son ki rike a ranki

ba zan taba mantawa dake ba a rayuwana muyi hakkuri kaddaran mu kenan hindu.

Kukan da takeyi yayi yawa da zai iya rungumarta a lokacin daya ruguma tayi kukan a jikinshi ta jika mai

kayansa da hawayenta da haka yayi mai dadi a rai saidai ina hakan ba zai taba yuyuwaba a tsakaninsu kuma.

Da kyar yaja kafanshi zuwa wajen motan ya bude ya shiga ya kifa kanshi saman sitiyari na dan lokaci

kafin muryansu fadila yasashi dagowa ya dan dubesu.

Suma hawaye sukeyi haka yasa yaja motar ya tafi kawai yana masu horn suka kama yar uwarsu zuwa

cikin gida suka nufi dakinsu da ita.

Kuka sosai sukayi saboda yar uwarsu suna ganin tsoho yayiwa rayuwan yar uwarsu katsaladan don me

zai yanke wanan hukuncin akanta bayan an daina yayi auren hadi a zamanin nan saboda wayewan kai ?

Haka mama ta shigo ta samesu a dunkule waje daya tsawa ta daka masu akan me zasu mayar mata da

daki wajen makoki ?

Itaba mutuwa akai mata ba zasu zauna suna mata kuka kamar an mutum faridace ta dago a cikin

dauriya tana fadin yanzu fisabilillah an kyauta ke nan ?

Shi tsoho ya rasa wanda zaiyi sadaka dashi sai yaya ai naga su yaya bintu ba auren hadi akai masu ba su

suka kawo wanda suke so ?

Kwab batayi aune ba taji duka a bakinta lokaci guda ta dafe wajen da takeji kamar jini na zuba saboda

zafi mama ta soma fadin mara kunyar banza da wofi kawai ?

To ubanku ga yacan bai isa ya musa dokan baba ba a gidan nan balleke sannu wace tasan ya kamata

akul naji wani ya nuna ko yayi magana cikin gidan nan kan wanan hukuncin wallahi saina sabawa maishi rai a gidan nan .

Dole sukai shiru don sunsan halinta saidata ta fitane suka soma dan kuskus a a tsakaninsu suna bawa

yar uwar tasu shawara .

Ta dawo dakin ta watsasu su fita suje su kama aiki a cikin gida dole suka fita banda hindu data dago

cikin tausayi tanacewa uwar mama don Allah ki barni kaina ke ciwo kamar ya fashe ?

Tayiwa yar wani irin kallo kafin tasa kai tafice daga dakin alamu ya nuna ta barta din ta huta ko don

radadin da take ciki a lokacin.

******************

Tunda yasamu yakai gida da kyar ya faka mota ya fito da Nabila ya hadu a tsakar gidan tana aiki tana

mashi sannu ya shige dakinshi ya rufo.

Bai sake fitowa ba sallah ma ranan a daki yayi magariba ganin haka har dare tara da wani abu barakha

ta nufi dakin ta sameshi don Nabila ta fada mata yana ciki tun yamma daya dawo kila baida lafiyane ?

Haka yasa ta mike ta sameshi a dakin yayi zaune a inda yayi sallah bai daga ba sai faman tunane da

yakeyi a wajen .

Ta turo kofa tashigo tana fadin yauko lafiya baban Imran ance tun dazun ka dawo gidan nan gashi ko

sallah a gida kayi ?

Lafiya ya dago da kyat yana bata amsa ya mayar da kanshi ya sada kasa ya fita batun ta a wajen ta

danyi jimm tana bin yanayinsa da kallo kafin ta nisa tana Allah ya sauwaka toh ta fita.

"Ya mike ya hau gado ba,a jima ba Nabila tashigo dakin tana fadin lafiya kuwa yaya itama ya amsa mata"

da lafiya abinci fa ta fada tana kallonshi yace banjin cin komai a yanzu.

Ta mike daga zaunen da take tana fadin aida kaci dai zaifima sauki da kwana da yunwa tunda an gama

tun dazun ?

Ba zan iya ciba yace mata ta rausaya tana fadin Allah kyauta tafice nan suka zauna a falo suna zancen

kome ya sameshi ohho ?

"Zai wuce wajen sana,anshine kila ko kuma wani sukai fada dashi kila kuma baida lafiyane yaki fada dai a"

to ai sannu bai rage mutum idan ya fada Nabila take fadan hakan cikin jin haushi.

Keko maza basu faye fadan matsalansu ba ai tundai shi da bai damu da yazauna yai hira haka da mace

ba sai idan yaga dama ?

Kaima basai ka kama kanka ba a haka wai har mutum ke neman kara aure kai baka iya dana gida ba

balle ka karowa mutane tension kuma ?

Ke wai meya dameki da zancen aurensane koda yake yi abinki kune amaren dole ki nuna kishi a kai ai ?.

Sai naga a nan babu zancen su amare ai kowa ta kansa yakeyi tunda kowa mijin dai yakeyiwa dariya

barakha ta kwashe dashi tana fadin wai kinji haushinane ashe ?

Naga ba abinda ya dameki da auren da zai kara tunda kema ai zuwa kikayi kika samu wata kema dole

"azo a sameki ai ita din hakane tunda yana da ra,ayin aure a rayuwanshi."

Ai ashe shine haushinki yasa baki nuna kin damu don nazo nashigo rayuwanku da so kike abar maki

gidan ke kadai kiyi yadda kuke so yi ko ?

Ai gaki mun zama biyu ko yanzu sai wata tashigo mu zama uku ai hakan ba laifi bane sai kowa ya wala

yadda yakeso ko ?

Kai imran zo ka dauko min ruwa a fridge muryan mijin nasune cikin ko in kula da cacan bakin da sukeyi

a lokacin ya fito yake fadawa danshi .

Tsit sukayi lokaci guda karshema mikewa ita Nabilan tayi ta dauki yaronta dake kwace yayi barci zuwa

daki ta shifideshi .

Wasa wasa har washegari bai fito ba haka yasa barakha komawa dakin ta sameshi ya dunkule a waje

daya take fadin .

"Haba yaya Rufa,i inma baka da lafiyane ai kaje asibiti da wanan kwanciyan haka tunda bamu saba"

ganinka kana kwanciya haka a gida ba ?

Zan tafi ya bata amsa donya samu ta rabu dashi don maganansu kara mai takaici da bakin ciki yakeji a

lokacin tundai Nabila da yake ganin ita taja mashi haka har mahaifiyarsa tayi mai mashi baki aka samu wanan matsalan .

**************

Yaya ki tashi kici wani abu tun safe kina kwance kinki cin komai shi tsoho daya haddasa hakan yana can

yanzu yasha fura yakai sau goma a cikinsa baisan kina nan bakici ba ?

Farida ba zan iya cin komai bane wallahi kuma banjin yunwa ballema ince zanci me nayiwa tsoho da zai

min haka farida ?

A to keya samu wallahi ni ba zan yarda da wanan hadin ba ai shi waya saura wanan a yanzu da zai

kawowa mutane shishigi koda yake barinyi shiru kada mama tajini ?

Wallahi Farida ko za a kasheni ba zan yarda ba ba zan zauna ba ko anyi min auren nan tunda ga wanda

nake so ?

Dako na debe maki wallahi tunda nake gidan nan kina gani kona bayana ban tabawa rashin kunya ba

balle nagabana ?

Hatta ubanku har mu a karkashin baba muke a gidan nan ki soma inkin cika mai kunne kashi wace ba a

isa da ita ba sai ki nuna masu basu isa dake ba ?

Mamace data fado masu dakin girshi take fadan hakan garesu cikin tausa murya inda ta umurci maza

hindu ta mike taje tayi wanka ta dora girki dole ta mike don yin abinda uwarta fada.

Bata samu kanta ba sai bayan magariba inda suka tabbatar da mama din tana wajen mahaifisu farida

ke fadin wai ina wayanki don Allah kira muna habibinki muji yaya yake ?

Haka kawai bawan Allah wanan tsohon da yaki mutuwa kowa ya sheka shiya tsaya gadin duniya don

kwadayin rai zai kawowa mutane katsalandan a rayuwa ?

Bari yajiki ai ya iya jifa da sanda kin sani ya jefe maki kafa fadila ta fadawa yar uwar nata cikin dariya

kafin ta koma fadin Allah nima yaban tausayi bawan Allah ?

Wayan ta dauko ta mikawa kanwar nata tana fadin har wani tsufa yayi da zakice ya tsaya gadin duniya

shidai su baba Audu ne maganinsa dama har ake ganin laifinsu ?

Numbershi ta danna yayi ringing har yana batun katsewa kafin aka daga tayi sallama tana mikwa yarta

wayan don bata san me zatace ba ita a lokacin.

Habibina na barka da wuni an wuni lafiya ta fada yace an dai wuni amma ba lafiya ba habibiya yanzu

haka gani nan asibiti ana kara min ruwa.

Subbahanallahi asibiti kuma to yaya na iya habibiya idan ya kare sunce wani zasu kara saka min sai an

kara min leda ukku kafin a sallamemi.

Takabir din da sukaji tayi yasa hankalinsu ya dawo gareta suna son jin ko meye sukaji tace asibiti kowa

yayi shiru cikin kashe murya fadila ke fadin ta tambayeshi wani asibiti yake suji.

Yace hamdala clinic yake kwance da alama kuma yana jin jiki don maganarshi da bai fita sosai lokacin

yasa tace Allah ya sauwaka tana kashe wayan.

Suka shiga zancen halinda yake ciki nan fadila din ta kawo shawaran suje washegari idan sun fita

islamiya har suje su dawo ba za a sani ba agida.

"Farida tace a,a zance zamu gidan mama gambo da safe mama ba zata hana ba tunda dama tana son"

muje can suka kwabi bakin Saffanah da saura ta tona masu asiri wajen mama din wallahi susa kafan wando daya da ita.

Haka akayi kuwa ita farida tun da safe tacewa uwar yau tana son suje gidan mama gambo su dan

dubota da jiki kada tajisu shiru tunda uwar bata samu zuwa ba kwana biyu.

Dakun kyauta min kuwa idan kuje kwanan nan duk tana cikin raina wallahi suka shirya tsab suka tafi

harda tsarabansu sukaje gidan suka mika sako da sunan zasu dawo zasu dubo kawarsu.

"Asibitin hamdala suka tafi da tambaya suka kai dakin da yake kwance saidai basuyi sa,an zuwa ba don"

kuwa kowa nasa na wajen a lokacin an kewayeshi yana barci sai huransu suke zubawa a dakin.

Sukai sallama suka shiga bayan sun gama shawara da zasu koma farida tace don me tunda sunzo ai

gwara yasan sunzo din atlist zaiji dadin hakan koba komai.

Suna shiga suka gaida kowa cikin ladabi na irin tarbiyan da suka samu daga mahaifiyarsu girmama

"babba yana cikin abinda suka taso dashi a gidansu wanda hakan yaiwa hjynsu Rufa,i din dadi sosai har suke tambayan daga ina suke basu ganesu ba ?"

Keko mama kila amaryace taji ango ba lafiya tazo gaidashi mana barakha ke fadi cikin zolayan Nabila

data hade rai tun shigowan yaran dakin.

Don ta fahinci bakin fuskane daga family din don kowa baisansu ba sai ga maganan barakha kuma daya

bata mata rai a lokacin.

Haka yasa taja tsuki tana juyawa daga kallonsu wanan ba abinda zata gwada masu don duk wace ta

haifo yaran nan haka masu kama daya tasan ta haifo matan gwaunoni a nan ?

Shi ko yaya yayi ya zakulo wanan yaran haka oho namiji akwai shige shige kanwar hjy din ke fadin ku

tashi gashi can a kwance barci yakeyi tun dazun an masa allura.

Suka daga zuwa bakin gadon yan dakin da sukai tsit sai manya ke magana duk suka bisu da kallo suka

karasa bakin gadon still matar dai ta dazun ke fadin bai tashi bako ?

Idona biyu mama ya fada a hankali cikin yanayin ciwo a bakinsa tare da furta habibiyata kune tafe

yanzu yau ba school ne halan ?

Ya jikin naka habibi ta fada a lokacin tana mai kura mashi ido na dan lokaci matar nan tamike zuwa

wajensu tana fadin wacece sarakuwar tamu a cikine ?

Sukai dan murmushi banda hindu din da idonta ya cika da hawayen tausayi don wanan tsohon kakan

"nasu ya jefa rayuwansu cikin halin hau,ula,i a yanzu da basu san makomarsu ba ?"

Saffanah ce ta aje ledan dake hannunta a gefebshi inda yake fadin meyasa why zaku wahak da kanku

bayan zuwan da sukayi din .

Still dai murmushi suka danyi a wajen na dan lokaci suna tsaye suna kare mai kallo sai faman sannu da

suke mai yake fadin amma gida ba a san kunzo ba ko ?

An sani mama tana gaidakai tace Allah ya sauwaka farida ta fada nagode ku gaiyar min da ita don Allah

acewa mama nagode suka amsa da to sukace zasu wuce.

Nan abokan wasa suke tsokanarta da lalai amarya Rufai don kai muna tsiya ka kwaso wanan yar

buzuwan ko ?

Ba yar buzuwa bace larabawa dai ya samu ya basu amsa da kyar suka fice yana kwance yana binsu da

kallo yana jin tankar hawaye zai fito mai a lokacin.

Itakan hindu din da kuka ta fita dakin a lokacin don ta kasa rike hawayen dake ta kokatin zubo mata tun

suna kanshi tsaye shima ya gane hakan yasa yacewa farida su tafi.

Sun da jima da fita ya juyo yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin bare min lemu insha barkha ta mike

tazo zata dauki lemon Nabila ke fadin ga lemu can dasu yaya suka kawo mashi tun dazun .

Wanan nake son a bare min ya bata amsa da hakan a taikace yana nuna lemun da yan matan suka

shigo dashi din nan uwar ke fadin keko nabila akwaiki da jan magana to wanan dai din yake son sha bana su yayan ba.

Ai dole ta fada tana mikewa tsaye cikin takaicin gwaletan da yayi din indonta itace fita da ledan lemun

za ayi gaba daya daga dakin ma a lokacin don haushi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/20, 7:15 AM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Tun daga wanan ranan baya zuwa gidan balle asan suna tare har lokacin haka kuma ana cin arzikinsa a

cikin gidan har lokacin.

Mahaifin mu na mijin bahaushene irin mazan da basu wani damuwa da sauke hakkin iyali ba saidai

iyali suyi ta fafitinkan neman abin rufin asiriwa kansu da diyansu.

Gamu har mu shidda manya hudu kanana biyu cikin rufin asirin ubangiji kuma haka mama ke kokari ita

da yan uwanta don suga ta zaunu a dakin aurenta dai.

"Hakane yakan kansace ga al,umma wani lokacin idan Allah ya baka zuri,a mai yawa lokaci guda saika"

zamowa yan uwa liability dole sai an taimaka maka.

Ta kasance itace tafisu iyali kuma mara karfi a cikinsu ganin wanan zance daya soma tasowa na auren

yarta yasa ta samu lokaci taje ta samu yan uwanta da zancen gadonta dama don haka sukai shawaran a adana matashi a hannunsu har wani lokaci.

Khadija ba zan yarda ki sayar da gidanki ba don gaba da yawa abubuwa dama suka iya tasowa gareki

nan gaba idan baki da gidan nan kin sayar kan yar nan yaya zakiyi ?.

Babban yayansu namiji dake aiki a gidan gona yake fadan haka a gareta bayan ya gama sauraren

bayaninsu din da suka zo mashi dashi.

Mama gambo ta nisa ta soma fadin nima nayi wanan tunanen yaya idan ta sayar da gidan nan yanzu

gata da iyali ta tashi a babu ke nan a cikin mu ?

Bama za ai haka ba Gambo kuje zan nrmoki ke ku hadu da hassana azo a zauna muji ya za ayi ya kawo

kudi ya bata masu yawa yace tayi kudin mota ta koma gida.

Ta riga yar uwar fitowa falonshi nan yake fada mata zai duba zancen yayi abinda da duk ya dace ayi

akai amma ba zan bari khadija ta rasa wanan gidan ba a yanzu.

Nima yaya nayi kokarin lurar da ita hakan amma ta nuna min bata da wani dama bayan wanan haka

kuma auren nake gani kamar da muhawara a cikinsa don sai yau take labarta min wai ashe wanda yarinyar ke so iyayyen syn koreshi wai auren gida zasuyi mata da wani dan uwanta.

"Ikon Allah Allah waya saura wanan dabi,an hadin yanzu abinda ke kawo rabuwan kai cikin zuri,a ko"

basu yarda da tarbiyan wanda take so din bane ?

Banjin hakane yaya donshi mahaifin ya bashi baki yashiga neman yarinyar tun farko su dai halinsune

gidan kasan sai su ba a gane gabansu.

Amma ko idan sunyi haka basu kyauta ba don naga aisun daina hadin nan a baya yanzunr zasu tayar

da hakan kuma ko ?

Kuje zan kiraki muyi shawara sukayi sallama ta fito suka sallami mantashi suka bar gidan akwai

zumunci mai karfi tsakaninta da yan uwannata suna tausaya mata sosai itace kadai bata da karfi a cikinsu.

Inda a nan gida kuma faifanta aka kafa a tsakar gidan yaya ibrahim inna hafsatuce ta dauko zancen ta

tana tambaya yau ina matar gidanku ta tafi naga ta fita tun da safe ?

Waya sani ta dai ce zata gidan Gambo nasab ko ba iya can za a tsaya ba sai an kewaye dangi da roko a

dawo gida.

Gwaggo Asiyace ke fadan hakan ga mama din aiko ba haka take ba ni shedace a nan gaskiya inna

halima ta fada tace yaya da zata rasa abu kayi da ita taje wajensu amma taki zuwa.

A toh aiba zata ba tunda an raba gado daidai da kowa tasa gaba ita da mijinta lokacin sun ciye wa zai

dauki nasa ya bata yanzu ?

Wai da gaskene da ake cewa tare suka cinye dukiyanta da yaya ina