Chapter 12 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

Asiya ke tambayan gwaggo hafsatu

din akacene ma watau lokacin karamin abune.

Ai a lokacin Dije tana dijenta ita kikeso da gani ga haske ga kyau ga kurciya yaran nan kaf dinsu ina ba

wanda ya biyota a cikinsu gaskiya.

Ta soma basu labari har yadda akayi aka kwace dukiyan hannun shi mijinsu duk ta basu labari tunda

basu gidan lokacin duk da wanan ba shine karo na farkon basu irin wanan labarin ba gareta.

Waceni in zauna inbawa miji kudin gadona yasa gaba ya turmuze daga baya yace bai sanki ba yanzu

gashi hakan dai bai hana ya karo mata kishiyoyi ba bako daya ba har biyu kudin kuma ancisu har abada sun tafi.

Wai shirmem banza banda hakkuri babu abinda ya saura yanzu ai tana kallo anayi yadda akaga dama

da miji kuma ita yar dadin miji ta dauki dukiya ta danka mashi ko ?

Yanzu aiga auren yara ya taso ko cibi banga sun aje a kofan daki ba balle uwar daka wanda za a baiwa

shike da wahalan nemowa daga baya kana fama da abinda kaciyar da mace ka koma kuma yimata kayan daki don tsiya.

Fitowan baba ibrahim yasa sukai tsit a lokacin don basu zaci yana gidan ba suka baje aka saka faifan

dan uwansa a wajen dole kowa yayi tsit sai gwaggo hafsatu ce kecewa ashe kana cikine yau baka fita ba.

Ina ciki yanzu dai zan fita ya bata amsa yasa kai ya fita wanan zance da yaji a bakinsu ya matukar

damunshi a lokacin.

Inda ya kasa hakkuri da zancen a ransa saida ya samu baba sukai magana a kai kuma a gaban tsohon

gidan ya nunawa baba bai kyauta ba abinda yaiwa mama.

Yanzu ga hakan ya zama abin gori da dariya a gareta wajen abokan zamanta da sauran matan gida sun

zauna suna gulmanta kan ta dauki dukiyanta ta taimaka mashi a baya.

Ya cinye yanzu kuma ya samu ya bata tukwicin kishiya kuma ta koma banza a wajenshi yace ko za a

kirasune zai iya maimaita abinda kowa ya fada gabanshi

Ina kadai ji maraye dama wanan nake duba maka kana ganin Allah ba zai tambayeka bane kan dukiyan

yarinyar nan idan nayi rantsuwa ban kaffara na tabbatar da bata taba tambayan ka kudin nan ba har yau din nan ya kamata ka dubawa yarinyar nan hakana ?

Ka samu naka ka haye ka rufe ido tana kallo kanaci da wata da yayanta itako ko oho saidai bakin ciki ya

kasheta watau kayiwa kanka hisabi.

Duk da yaji zafin zancen bai nuna komai ba a gaban tsohon gudun bacin ranshi ya dai bada hakkuri akan

zai duba ita mama me zatayi ds kudi a nasa tunanen inma kashin kudune ga auren yaran ai shi zaiyi shida zai dauki dawainiyar gado da kushin aishine mai kashe kudi ga auren nata bai wuce tarkacen mata da ake tarawa yarinya ba ai.

Ranan gaba daya gidan basu gane kanshi ba don ko ya hade kowa yana sha mashi toka a gidan wanda

basu gane dalilin hakan da yakeyi ba.

*** *** *** *** ***

Tunda akai wanan cancen ya kasance tana dari dari da duk yan uwan nata don zuciyarta sai garari yake

ko dawa wanan tsohon yake shirin hadata a cikin yayyun nasu oho ?

Gashi yaki magana da kowa kan zancen illa abinda yake yawan fadawa yayansa shine da baba ibrahim

da baba Audu su gyarawa yaransu wajen da zasu zauna da iyalinsu don aure zai masu ba fashi.

Jikokin nasa maza basu dauki zancen da gaske ba don sukan karatu sukeyi a lokacin wani zancen aure

kuma za a kawo masu yanzu da suke shirin taka duniya a tauye masu rayuwa.

Amma da sunayen su baban namu ya fito akan su gyarawa diyansu inda zasu saka matansu sai kuma

zance ya juya ya koma zancen tsegumi a gidan baki daya.

An dauka kamar ko yaushe za a samu matsala da baba Audu sai gashi ya bawa kowa mamaki shinema

ya soma gyaran wajen duk da yayansa da suka isa aure maza sun kai ukku a lokacin gabanshi indai aure

irun na kasan hausane a baya da akewa yaro aure da shekara goma sha to nasa suna batun haura ashirin a lokacin.

"A bangaren hindatu kuma suna nan radam a waya da sahibinta Alh Rufa,i saima ince kamar an kara"

zugasune a yanzu kan soyayyansu din.

Duk da yasan tunda mahaifinta da kanshi yace ya hakkura da ita tabbas hindu din rabon wanine ba

nasa ba amma irin karfafa masa zuciya da takeyi kan ba zata zauna ba koda sun aura mata wani.

Haka yasa yake biye mata don ba asan inda jifa zai fada ba sai ranan daya sauka a kasa wanan yasa ya

kasa cire ransa a kanta.

Haka kuma bai fadawa kowa halinda yake ciki ba yabar zancen a zuciyarshi abin yana nukurkusanshi shi

kadai a rai.

Don kuwa duk akaji zancen nan akwai kunya a gareshi musanman a wajen matansa ga Nabila tun ranan

data kyalla ido akan hundatu ta daga hankalinta.

Dan dama dama ita barakha don ta iya tako sosai baka saurin gane bacin ranta a lokaci daya sai idan

abu yakai intaha zata nuna lalai ranta ya baci ga abin.

"Alh Rufa,i ya kula hindu tana da kurciya sosai haka kuma badon kudinsa ko wani abu ita da iyayyenta"

suke sonshi ba sone take mashi na tsakani da Allah.

Don yasha aunata tana kyatare wanan gwajin mafi yawan lokuta zai mata alheri amma taki amsa tace

idan ta karba mama zatayi mata fadan maiyasa ta karbo.

Wanan yasa yake kaunar yarinyar ta kasance daga cikin matanshi sai gashi wanan tsohon mai bakin

akidar mutanen baya ya kawo masu cikas a tafiyansu.

"Yasan halin irinsu da ra,ayin rikau wanan yasa bai nuna kudi ko karfi ba wajensa dole yaja baya ya"

tsurawa sarautan Allah ido gashi son yarinyar sai kara dabaibaye zuciyarasa yakeyi a kullum.

"Ita kanta mahaifiyan Alh Rufa,i din jin irin bayanin da yayi akan yarinyar yasa ta kwanta mata a rai don"

yadda Nabila ta tayar da hankali kan wanan auren yasa taso hana hakan ga dan nata.

Yanzu ko ta fahinci akwai wani abindake damun dan nata don wanan rama daya dauko yi tun bayan

kwanciyashi asibiti.

Idan kuma anyi magana yace ba komai har yakai maigadantama yaga hakan wani yammaci daya shigo

ya gaidashi bayan ya wucene yake fadin hjy meke damun dan hakane ?

Bakiga raman da yakeyi bane a tsaye ki tambayeshi fa kada wani abu yazo ya sameshi daga baya kuma

a koma da an sani ?

Anya kwa ba matsala da ga wanan neman da yakeyiwa yarinyan nan yanzu ya kamata ki tambaye aji

meke damunshine wai ?

Yadda mijin nata ya bata shawara haka akayi da yazo gaida ita ta tsureshi da tambaya yaya zancen

yarinyar da yake nemane wai me ake ciki da zancen taji shiru.

Dan shiru yayi kafin ya dago ya soma fadin yana nan hjy saidai gaskiya akwai matsala don iyayyenta

sun nuna kamar suna son hadata aurene da dan uwanta.

"Ai shine abinda ya saka,ka damuwa ashe kake rama ai kaima kasani yana da wuya su bari wanan yar"

tayi aure a bare dole sai gida saidai idan itace taki hakan.

Na yaba da tarbiyan yarinyar tun ranan farko dana gansu asibiti din nan nayi nazari yarinyace ta kirki

sosai saidai naga hankalin matanka ya tashi matuka da kyau yarinyar tun a ranan hjy Nana ta kirani tana min korafi.

Tunda ta nuna min bayan yarta take duk kokarin nan da nake masu amma ashe ita bata ganin haka ita

da yarta ?

Yasa naji ina son kayi auren don ashe ba karamin hakkuri kakeyi da wa yan nan marasa kan gado ba ?

Harni Nana zata kira ta nuna min yarta tafika muhinmanci a wajenta nasan haka dinne dama amma ana

kara ai kamar yadda ni nake kara mata ko wani lokaci.

Har tana nuna min mun hade kai da yaya bilki muna son aiwa yarta kishiya ita bata zaci hakan agareni ?

Ranshine ya baci sosai din jin abinda kanwar mahaifiyar nasa tayi mata sai lokacin yake fadin nima ta

kirani hjy bandai fada maki bane har tana fadin idan banson yartane in turo mata da abinta ita tana son abinta dama ke kika matsa ayi hadin nan.

Don karatu taso yarta tayi amma kika nace da sai an hadamu kaji sherin dan adam ko zata iya komai

nasani indai akan diyane.

Yanzu dai ka nemi shiri da iyayyen yarinyar nan ko zasu yarda in basu yarda ba kuma sai kayi hakkuri ka

zauna da matanka su biyu hakana ?

Hjy ba zan iya zama dasu haka ba basu da ranan sauya halinsu gaskiya so nake in karo masu wata a

gwada a gani kuma ko abin zaiyi sauki.

Idan da alheri a cikin auren yarinyar nan Allah ya baka ita baba in kuma bamu ya sauyama da wace

tafita zama alheri a garemu sai kasa hakkuri da dangana a lamarin kuma .

Insha Allahu hjy nagode ina nan dai ina ta kokari inga na samo kan abin don ita yarinyar ma wallahi

itace abin tausayi yanzu ai hjy.

Don cewa tayi koda sun mata auren ba zata zauna ba sai ta fito ta aureni kinga abinda ke ban tausayi da

ita wallahi.

Ba za akai can ba ai da yardan Allah in rabonkane ita sai ka aureta insha Allahu sosai yaji dadin

zancenshi da mahaifiyar nasu koba komai ya fadawa wani matsalan ya dan samu relief.

Yasan koya rasata Aziza na nan tana jiranshi ko yau yace ya shirya zata yadda a daura masu aure dashi

to matsalan aziza din bai son irin rayuwan karyan nan nata shine kadai yasa bai mayar mata da hankali ba.

Haka kuma halinsu ba daya bane da hindatu don ita Aziza tun bata shigo gidan nasa ba take aikawa

matanshi da bakaken magana akanshi.

Shi kuma baya son tazo ta hanawa rayuwanshi kwanciyar hankali tunda ta fara da haka yasan ita kanta

barakha hankalinta yafi kwanciya da hindu don Aziza daba shiri a tsakaninsu tun yanzu da bai aureta ba.

Tafiyan daya danyi zuwa kasan waje shine har ya dan samu relief a wajen wanan zancen don hakan

zaisa ya soma mantawa dasu gaba dayansu saboda harkokinsa da yayi mashi yawa a can din.

"Saidai ba haka bane ashe so bala,ine don kuwa ya kasa mantawa da hindatu din ko yaushe tana makale"

a zuciyarshi.

Itama a bangaren hindatu din tun bayan daya fada mata zancen tafiyan take a cikin damuwa don tana

gudun yazo bayanshi zancen aurenta da tsohon ke shirin shamtanta ya taso.

Don abubuwan da take ji game da zancen bukinsu a bakunan mutanen gidan dake jiyo karaya da

gaskiya suna yadawa.

Inda Gwaggo Asiya ta samu kafan jan hindu dinna jiki tana nuna itace mai kaunarta a yanzu don yadda

take nuna mata kowa bai kaunanta a gidan.

Badon komai don taci riba biyu take hakan na farko don ta samu ta musgunawa Dijr ta bata mata rai

idan ta hurewa yarinyar kunne.

Saina biyu yanzu tana dan samu tana lakata daga yarinyar ana ci da ita a boye ba tare da sanin

iyayyenta ba duk ake wanan.

Haka kuma don bakin wayau taki yarda wani nagidan yasan da shirinta a wargaza mata shirin nata

alkawari ta daukarwa kanta akan dije din da sai ta fitar da ita gidan taga bayanta.

Kamar yadda wasu ke fadin tubbuke ince har saye ba aiki bane ga mai karfi to daga dijen har yayanta

sai ta masu tabo a rayuwansu yadda sukai mata danta ya nakasa .

Nakasan daba warkewa ita mata haka zatayi masu tabon daba waraka har abada donshine take ta

wanan nuna soyayyan ga yarkishiyar nata.

Wace itama yace a wajenta inga zumunta don kakansu guda aida mahaifin yaran da ita mai imanice da

tunane da kishinta zai tsaya akan uwarsune kadai a gidan.

Amma tunda rashin imani ya shiga ya hade da kishi sai ya zamanto idonta ya rufe ga gina ramin

mugunta data daura aniyan yiwa yar kishiyar nata a lokacin.

Sarai mama ta fahinci wanan sabon halakan daya shiga tsakanin hindu yarta da kishiyan nata wace tun

shigowanta gidan nan ta nuna bata kaunarta har cikin ranta.

Amma yanzu ta koma jan yarta a jiki wanda tasan wanan shirin bana girma da arziki bane donshine take

yawan jawa yayan nata kunne akan abokiyar zaman nata wace tasan badon Allah ko zumunci haka ke gudana ba.

Amma abinka da dan yau yarinyar a lokacin tana ganin ai duk gidan babu mai kaunata irin gwaggo

Asiya din wace ke nuna mata kula akan damuwanta yanzu.

Shima mahaifin nasu ya dan zargi wani abu amma da yaga bai fahinci komai ba kawai ya watsar da

zancensu gefe daya yana facing din matsalan gabanshi.

Gwaggo mariya yar gidace itama don kuwa dakinsu daya da gwaggo hafsatu mijinta mutumin

jalingone aiki ya kawo iyayyensa katsina suka zauna a unguwar lokacin.

Amin dake tsakanin uban mijinta da mutanen gidanmu yasa suka dauki yarsu suka bashi wanda a

yanzu sun hayayyafa a tare tana da yaya kusan bakwai dashi a raye.

Haka kuma rayuwansu gaba daya da yan uwansa ya dawo a katsina wasunsuma basu san danginsu ba a

Yola saidai a tarihi suce sun yan yolane asalinsu.

Wanda da akai rabon gadon gidan kakanin mu ta dawo nan suka ja yan dakuna biyu a inda ta samu

tana zaune da mijinta da iyalanta.

Din mijin nata baida karfi tallakane talas haka kuma take hakkuri irin na matan hausawa take zaune

"dashi ana tara zuri,a."

Da yake diyanta suna cikin gidane sun samu taimakon yan uwa irinsu baba Audu don yaranta biyu ya

dauki dawainiyar karatunsu don a hannun gwaggo hafsatu suke tare da yaranta tun tasowansu.

Itama sun samu wanan sakon tsoho na su gyarawa babban dansu wajen da zai saka mata shine ake

kokarin jan daki a dan filin daya rage a bangare daya na gidan.

Nan tsegumi ya taso ba manya ba har yaran gidan akan danwa tsoho zai dauka ya manna a cikin talauci

don har iyayye maza sunyi wanan tsegumin a tsaksninsu.

Wanda tsegumin ya koma kunnen tsohon yayi murmushi yana fadin kaiya an fada maku haka zasuyi ta

tabbata a cikin talauci har abada ?

Ina komai da nazarine mariya macece mai hakkuri ga biyayya hakama yaranta duk sun kwasota mijinta

bai taba nuna mu din ba yan uwanshi bane akan me ba zamuyi masu kara ba ?

Tabbas nayi niya don shi kanshi mijinta kamar amana yake ai a wajen mu tunda mahaifinsu a hannun

mu ya danka amanan iyalan shi a garin nan.

Wanan zancen da tsoho yayi yasa kowa yaja bakinshi yayi shiru don kada zance ya taso ace a bakin

mutum akaji haka kuma ga gwaggo hafsatu dake farin ciki akan abinda kanin mahaifinsu yayiwa yar uwarta din na nuna itama dangice a gidan ai har yanzu.

Gida dai kan ya rikice tsoho ya bar yayansa a duhu yaki zance da kowa abu dayane shine duk wanda ya

kira yace ya gyara waje ko ya soma shirin auran yarsa yasan dashi a cikin wanan badakalan na auren tsohon.

Dole baja ko rai ya baci mutum zai hau shiri badon yaso ba abu daya baba Ali din yayi inda ya sanarwa

diyanshi maza da cewa ya hutar dasu ga kayan gadaje da abincin gara da za akai su dai taimakawa diyansu mata da kayan tarkacen daki su taimaki uwayensu dashi.

Wasu sunji dadin wanan maganan irin su baba ke nan masu matacen zuciya amma irinsu baba Audu

cewa sukayi shi har wani kayan kwarau zai iyawa yara na zamanin nan na fita kunya za adai karba a kara amma shi zaiwa yarsa kayane na zamani .

Itama gwaggo hafsatu da yartane za aiwa auren wanda kusan abinda yaci hindatu shine zai cita taso

tayar da kura amma ganin hutsun mijinta ya goyawa abin baya yasa dole taja baki tayi shiru tunda dama da bazarsa take rawan iskanci a gidan ai.

Don gaskiya baba Audu din hutsune na gaske irin na bugawa a jarida din nan baya tsoron hurhura ko

gemun mutum idan abu ya hadaka dashi haka zai tsaya yai ma tas a gabanka.

Amma sai akaga yayi shiru dole duk wani mai jayayya da zancen tsoho ya kyale aka kawo ido akasa tare

da soma shirye shiryen dole akan zancen kamar yadda yaba umurnin ayi din.

Mama gambo itace take kwantarwa mama da hankali na ta zuba masu ido ta fita zancen kowa su zasu

san abinda zasuyi insha Allah ai yazama dole su taimaka mata tunda bata dashi ita a cikinsu.

Ga tsegumin babban gida dake zuwa yana dawowa gareta inda har gwaggo Asiya ta kasa hakkuri da

gulman dake cinta ranan take fadin.

Ke yaya kowa na shiri kin ki motsawa akan yata ko don kinji baba Alu yace ya daukewa diyanshi maza

kayan daki yasa kike tunanen harda kayan aiki na uwa zai taimaka maku dashi ?

Shifa baba Alu rigimace ta tsufa kawai yake damunshi koshi malam da yana da zuciya irin yaya Audu

aida ya motsa yayiwa hindu abin kwarai nagani na fada tunda itace yarsa ta farko da zai wanke ?

Gashi kowa na shiri mu nan kunyi shiru daga ke har malam din ba mai wani motsi karfa kusaka aiwa

yata dariyan daki kinsan mutane da gulma ?

Murmushi mama tayi kawai tana fadin Asiya ke nan abindake ga mutum bashi zai kaiwa yarsa ba wani

"motsi zanyi tunda bandashi ban wani sana,a kuma kowa ya sani a gidan nan kuma ?"

"Kafin gwaggo din tayi magana inna halima tace kai amma Asiya na rabaki wallahi shi sha,anin aure aiba"

"a mai wani shiri abin sa,ane daga Allah ranan dai yazi kila sai kinyi mamaki rabu da irin su yaya masu barwa Allah lamarinsu ?"

Kajiki da wani zance don Allah aiko Allah yace ka tashi ya taimake ka wa yaya ke zuwa buki a garin nan

da zai nado kayanshi yakai mata ?

Yaran na daki sunyi tsamo tsamo suna sauraren wanan abin wanda suma ya soma damunsu gaskiya din

ko wani part na gidan suka shiga sukaga irin shirin da akeyi hankalinsu yana tashi suyi magana a tsakanin su dama.

Sai gashi yanzu kuma har su gwaggo sun fara fitowa fili suna magana a kai wanan yasa suka soma

tsegumi a tsakaninsu kan zancen.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/20, 10:04 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2-