Chapter 14 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

din suka fita akan zasuje suga yayansu su kara shawara dashi.

Baba sai washe baki yakeyi ya kai ya komo a cikin gidan ana binsa da kallo har yayanshi don ba alaman

zai yiwa yarsa wani abin arziki ga bukin nan .

Gida kan ya soma cika da baki ko wani lungu yan uwane ke zuwa dauke da abin arzikinsu sai oyayyo

"akeyiwa bakin a cikin murna gwanin ban sha,awa a lokacin."

"ZAINAB IDRIS MAKAWA[11/21, 10:19 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Duk inda tabi idonta na kanta kallom da take mata baiwai a lokacin ta soma ganinta ba sai sauyin yanayi

da damuwa da take hangowa ga yar uwar nata haka suka kwana har washegari da za ai kamun amare.

"Tayi sa,a aka barta da yan uwan akan sun tafi dubo anko har da kanwarta sai lokacin ta samu sukunin"

magana ta soma fadin .

Wai hindu nikan ya na ganki hakane kamar kina a cijin damuwa game da auren nan keda ya kamata ace

mun sama a cikin walwala da farin ciki amma sai ki take a gefe kina tunane da ajiyan zuciya ?

Kwalla suka zubowa hindu din a zatonta mama sharifa tasani kuma zata fadawa yayan nata ai irin auren

da ake dmshirin mata a gidan.

Subbahanallahi hindu ya da kuka kuma haka daga tambaya ki fada min meke faruwane wai akan aureb

nan feel free ni yar uwarkice kin sani.

Cikin kuka ta kwashe komai ta sanawa ya diyar anty sharifa din wace ke matakin university a zaria

yanzu.

Suko dai don Allah meyasa zasuyi haka daku basu san an daina irin auren nan a yanzu ba ai lokacin irin

haka ya shude ko a kauye balle gari irin katsina da suke da wayewan kai !

Amma gaskiya banji dadi ba haka kuma zaki zauna kina kallo a daura maki auren ba wani matakin da

zaki dauka ke ?

To anty Nuratu ya zanyi ni mama ta hana min wani motsi tace nabarwa Allah ni ya zanyi itace hope dina

ta kuma ce ba ruwanta ita tunda iyayyena sukace ga yadda zasuyi dani ?

Wallahi anty nasan halin mutanen gidan nan gasu da girmansu idan fada ya tashi har gobe sunawa

junansu gori kan auren hadi na gida amma wanan tsohon ya kafe nace yace shi zai muna.

Nuratu din tayi shiru tana nazarin zancen kafin ta soma fadin bari mu gani ko da abinda zan iya akai

amma gaskiya ba zan iya kallonki a cikin wanan damuwan ba.

Ta yaya za a dauke ka akaika gidan wanda baka so shima bai son ka ka iya zama dashi zamanin nan

wanda kake so din ma ya kuka kare balle.

Kiyi hakkuri dan bani time mugani zuwa gobe zaki iya yin duk abinda nace ko zan iya wallahi anty ta

fada da sauri tana duban yar uwar nata kamar zata shige mata jiki a lokacin.

Gashi dai tana son tambayeta amma kuma ba sata iya ba abu dayane shine tasan zata taimaka mata

tunda tayi niyar hakan a yanzu.

"Banda ita ba wanda yayi niyar taimakonta a wanan halin da take ciki na ha,ula,i na auren dolen da za"

ayi mata kowa saidai yace taje tayi hakkuri.

Batayi aune ba taji tana waya tana sanarwa wani cewa yazo katsina ga gobe ya dauki kanwata don

Allah yakai mata gidansu gwaggo ta tsara mashi duk yadda take son abin ya kasance.

Maishi yace zai shigo insha Allahu su zauna da shiri tagama wayan ta kallo hindu din tana fadin zaki iya

guduwa ko zai kai min ke zaria ya aje har muga abinda hali zaiyi .

Amma fa sai kin daure sosai da wanan yakin don abune dake son dauriya da cijewa a cikinsa.

Zan iya anty indai zaki taimaka min ta fada a dan maraice ga yar uwar nata don a lokacin koma meye

yar uwar tace tayi zatayine a lokacin don idonta da zuciyarta sun gama makancewa.

"Ba kuma don son Alh Rufa,i bane hakan kawai bata kaunan kowaye za a hadata dashi a cikin dangine"

"kawai ra,ayinta shine abarta tayi zabin kanta a lokacin."

"Gida kan ya kicime da shagali duk daba wani bidi,a na raye raye akeyi ba a gidan lokacin amma"

tukwane sai saukewa akeyi a dora wasu mata iyayyensu da yayyu sunata shagalin da annashuwa ana dararaku kamar ko wani gidan buki dai.

Wayan da aka kira misalin tara na safe shine ya zaburar da Nuratu din ta dan dubi hindutu tare da

dauko wayanta ta rubuta mata sako kamar haka.

Kije wanda zai tafi dake yazo yana daidai bakin waffa a zaune mota baka na tura mashi numberki saiki

kirashi don ki tabbata da cewa shine.

Wani sakone ya kara shigowa yake fada mata zai dan sha mai a duba mai mota nanda muntuna hamsin

ta tabbatar data zo wajensu tafi.

Ta sake turawa yar uwar nata sako akan ta dan dakata har zuwa mintuna goma sha biyar saita fice daga

gidan Allah ya tsare hanya.

Goma daidai maza suka taru aka daura aure nan gida ya kiceme da surutai wansu na murna wasu bakin

ciki a ciki kuwa harda farida da akaiwa iyayyenta bazata da ita don sam ba shirin aurar da ita a lokacin sai

gashi tsoho ya bada sunanta an aura mata Ahmad dan gidan gwaggo Hafsatu ita kuma hindu sulaiman dan wajen gwaggonsu mariya wanda hakan yazowa mutanen gidan har yan daurin auren a bazata.

Don kusan daki daya a gida daya sukai aure tsaton baba garba wanda asali kuma dai kakansu daya ke

nan ta wajen uban daya haife iyayyensu.

Farida sai haukanta takeyi don bata masan wai da ita a cikin zancen auren ba a lokacin yasa take ta

taya yar uwarta hindu data zama kamar itace kawarta a lokacin budawa don taga komai ya tafi daidai.

Dakinsu ta shigo inda ta samu iyayyenta a zaune kamar ma kuka mama keyi a lokacin saidai haka ai bai

rasa wani abin ko alhinin rabuwa da yarta da zatayi yasa bata damu ba tunda maganan manya ce ta soma fadin wai ina hindune mama ?

Dakyar mama ta dago tana fadi cikin rashin dadin rai bata dakin gwaggonku Asiya dubata a can kila

can ta shiga.

Ta juya ta tafi bata dakin don kome dakin bata ciki a lokacin tana can tana tausan uwar dakinta dake

bori an aurawa danta Farida a lokacin.

"Ita danta bai isa aure ba a rasa wanda za,a daurawa aure da yayansu sai yayan Dije fakirinyan mace"

dake fama da talaucinta a daki ita da yayanta.

Ta duba ko ina bataga yar uwar ba hakan ne ya soma daga mata hankali ta koma dakin mahaifiyar nata

ta soma fadin mama bafa ganta ba a gidan nan kaf na duba ko ina bata cikin gidan nan.

"Bata gidan nan fa kikace sai kuma ta koma fadin innalillahi wa inna alaihim raji,um wanan kalman data"

ambata mai tsarki yasa hankalin yan uwan dawowa kanta gaba dayansu.

Ba a gantaba ina taje nima ban sani ba farida din ta fada a cikin damu kin duba ko ina kuwa bata nan

dakin gwaggo hafsatune kawai ban duba ba gidan nan don suna ciki suna magana kamar wani abu sukeyi yasa ban shiga ba.

Yaya kardai ace yarinyar nan gudu tayi don taja min magana a gidan nan ?

Gudu kuma wani irin gudu don Allah taje ina da zata gudu wataga aure ya kashe balle ta gudu yaya

gamba din ta fada tana mikewa don zancen yar uwar ya bata tsoro a lokacin.

Ki fita ki kara dubawa dai Farida ba wani gida nan makwabta inda kukw shiga kota tafi can tunda taga

gidan nan ya ciki ?

Ina take zuwa yaya ban saba masu da hakan ba ai ko a xikin gidan nan basu zuwa ko wani part haka kai

tsaye in babu wani dalili farida ta juya zata tafi mummy sharifa ta dakatar da ita da fadin .

Kina matan aure ina zaki fita haka ke kuma nemi hijjab din kwarai ki yafa ta fada a umurce wanan yasa

ta karbi hijjab din mahaifiyarsu dake a hannunta.

Dakata inzo muje mama gamba ta fada suka fita tare suna fita wata kawarta zata shigo ta soma fadin su

amaren fa kice muna dakene kikaki fada sai mukaji har kece ashe ga auren ?

Wani kallo mai kama da harara ta watsawa kawar nata tabi mama gambo da sauri sun duba inda ya

dace ba labarin hindu zance tun sunayinshi iya dakinsu kadai har yanzu yakai sun soma fitarwa suna tambaya ?

Abu ga babban gida kamar jira ake hakan ya faru don kafin ace kwabo zance yabi ko ina na gidan cewa

hindu ta gudu ba aga hindu ba ai ?

Wasu suce uwarta ta turata ta gudu don Sulaiman da aka daura mata aure dashi wasu suce ba gudu

tayi ba wanda ke nemantane ya dauketa ai.

"Haka zancen ya soma aka bar sha,ani buki aka koma kuma gulmab zancen abinda ya faru da yar dan"

uwan nasu akan auren wanda ido ya rufe abin nema ya samu kowa da abinda yake fadi kan zancen.

Lokacin da zance yazowa tsoho kan an nrmi hindu ba a ganta ba a gidan ana kyautata zaton ta gudune

saboda auren ko wanan dake zuwa wajentane ya saceta ?

Ko kuma uwartace ta turata ta gudu a lokacin angonne suna zaune gaban tsoho yana ganawa dasu ana

ta zancen da tsoho da iyayyensu maza .

Koda mahaifinmu yazo zagin mama ya somayi don ya tsaya ga cewan da akayi itace ta boye yarinyar

don bata son auren .

Tsoho yace anya kuwa haka zai yuyu ta boye yarta akan aure baba ya soma fadin meye ba za a iya ba

baba dole Dije tasan inda yarta take hadin bakine abin nasu.

"A,a baba banjin hakane gaskiya dazun zan shigo gidan nan na hadu da wata mace ta saya fuskanta da"

nikaf zata fita.

Har tayi nisa dani sai jikina ya ban kamar bata da gaskiya don yanayin yadda take tafiya saina juya na

bita da baya har ta tare Napep zata shiga a zatona watace amma a lokacin saina gane ai hinduce.

Nima tun dazun naga hankalin su mama a tashe sai daga baya nake jin wai hinduce ta bace ai kowansu

kokarin kare mama dije yakeyi a lokacin don sunsan irin matakun da zai iya dauka a kanta.

Karku damu duk inda taje ai dole ta dawo tunda bata da gidan dayafi wanan sunyi ta shawarwari a

wajen kan matsalan tsohon yana kwantar masu da hankali.

Inda ya umurci da aje dakunan amaren ai masu jere a ranan don ya fasa zancen tarewansu ga gobe a

wanan ranan zasu tare a daku nan su wajen mazajensu.

Abu kamar wasa an daije nan tsalaken titi gidan gwaggo mariya anyiwa hindu jeren kayanta wanda

yan uwan mama sukai mata yayinda wanda tsoho yayi masu nagaba daya aka jerawa hindu a nata dakin da zasu zauna a nan shiyan malam daga gefe guda.

Don farida bata tashi sanin aurenta ba saida surutu yayi yawa akan batar yar uwarta da aketa ba mama

baki mama Gambo ke fadin .

Idan tayi hakane don ta daga maki hankali aiga yar uwarta nan zata tare a nata dakin a yau su masu

fadin cewa wai kece kika turata ta gudu meyasa bamu tura farida ta gudu ba ita ?

Mama ni kuma tambayan da farida din ta watsowa yar uwarta ke nan tace ke mana farida ai dake

cikin wanda aka daurawa aure gidan nan yau .

Wanan abinda ya faru da yar uwarki yasa bamu zauna dake ba tun dazun mun sanar dake komai don

hankali ba a kwance yake ba tun dazun din.

Kuka ta fashe dashi tana fadin yaya don me baki tsaya munyi wanan yakin a tare ba meyasa kika tafi

baki fada min ba alhalin baki abu sai kin fada min kome zaki aikata ?

Tabasu tausayi amma shigowan da inna halima tayi dakin tana fadin gashi can baba Ali ya tura a kira

wanan mutumin dake neman hindu .

Da ance a tura kwalawa suzo dashi amma baba ya hana yace a bari ayi abin a cikin mutunci nan kowa

a dakin ke fadin albarkacin bakinshi kan zancen .

"Alh Rufa,i din yazo kamar yadda akai mai kiran gagawa baiyi kasa a gwiwa ba ya taso yazo inda akai mai"

iso zuwa wajen tsohon.

Don dama basu taba haduwa ba duk zuwa wajen hindu din da yake suna shirin zuwa gaidashine ya

samu sakonshi na dakatar dashi daga zuwa wajen jikanshi.

An gaisa a cikin mutunci duk da tun isowanshi gidan yasha jinin jikinshi da irin kallon da mutanen daya

samu suke mashi .

Alhamdullahi shi din sunan maya ke gareshi balle a rainawa hindu din da take kokarin yiwa iyayyenta

bore don kuwa irin mazan da ko wace mace take fatan mallakane ya zami mijin aurenta .

Matashine shi ga kudi ga ilimi ga wayewa duk sun nuna a jikinsa a baiyane basai ya tsaya fadab koshi

waye ba haka yasa masu niyar mashi tijara a lokacin kwarjininsa yasa dole suka dakata har aji shakuwanshi.

Bayan sun gaisa da tsohone yake dan masa ba a tare da soma fadin kai mai sunan manya kaine kake

son ja da danka ko ?

"Alh Rufa,i din bai gane ba a lokacin din haka yayi murmushi kawai ga tsohon inda tsoho yacigaba da"

fadin duk da wananne karo na farko da muka soma haduwa dakai banganka da wani ruwan rashin adalci ba gaskiya Alh.

To a gaskiya Alh mun kirakane akan wani matsala daya taso a gidan nan wanda hakan bai taba faruwa

damu ba shin menene gaskiyan zancen muke son ji daga bakin ka.

Nasan kasan a yaune muka daurawa yaran mu na gidan nan aure da safe a ciki kuma harda ita hindu da

"kaso ka hada zuri,a damu ta dalilinta Allah bai nufa ba."

Sai gashi kuma a yau din da aka daura mata aure mun nemi yar namu mun rasata a gidan nan a daidai

lokacin da take sgirin tarewa a gidan mijinta.

Jin zancen tsohon na karshene yasashi dago kanshi da yake duke cikin girmamawa da sauri gabanshi

"na faduwa ya soma fadin innalillahi wa inna alaihim raji,un."

Ya subbahanallahi hindatu bata gida kuma garin ya haka ya faru kuma ?

Bata gida tsohon ya kara fadan hakan tun safe mun nemeta mun rasa yasa muke son maslaha game da

lamarin muji a gareka ko kana da masaniya inda take ba tare da kai ruwa rana ba tsakani ?

Ya tabbata baya da wani hubbasa a yanzu banda ya kare kansa ya fito fili ya fada masu tsakani da Allah

kada sunanshi ya lalace a banza kan wanan yarinyar.

Din haka bai tsaya wani boye boye ba ya soma magana yana fadin wallahi Allah banda masaniyan bata

gida kuma bansan inda take ba a yanzu ?

Asalima rabona da ita tun dana dawo daha dubai na samu ba ai auren ba na nemi ganinta don muyi

bankwana tun wanan ranan wallahi ban kara sakata a ido ba kuma.

Don ko waya na rufe layinta a cikin wayana saboda nasan zatayi aurene kada na sabawa sharia in shiga

hakkon aure.

Wanan zancen banza ke nan dole ai kasan inda take kada ka rainawa mutane wayau don Allah a nan

gashi kace ka nemeta kuyi bankwana bayab kasan an dakatar dakai zuwa wajenta ?

"Baba ibrahim ke fadin hakan cikin zafin rai tsohon da yan uwanshi suna dakatar dashi shima Alh Rufa,i"

din ya shaka inda ya soma fadin

Hakane so kuma ba cuta bane inda hankali don nace ina son zuria daku ba wanan zaisa don kun

dakatar dani daga auren yarku na nemi sabawa ubangijina ba.

Nifa musulmine nasan abinda sharia ya koyar a neman aure haka kuma ni ubane don na haifa idan

akaiwa yata haka aiba zanji dadi ba don me zan aikata hakan idan banson ai mun ?

"Look nifa ba jahili bane haka kuma ni bahaushene na gidi kuma musulmi nima nan ina cikin bakin,ciki"

da jin wanan zancen a yanzu a matsayina na mai kaunar yarku ?

Ya kamata kuyi min adalci tsohon nan ya tambayeni tsakani da Allah nafito na fada mashi iya gaskiyata

harga Allah banda masaniya kan batan yarinyar nan a yanzu.

Duk da nasan ta dalilina ta gudu tabar gida amma wallahi bada hannu a cikin shawaran ta gudu tabar

gida da hukuncin iyayyenta ba nimafa ubane wata rana ya kara fadan hakan .

To shike nan idan munje wajen hukuma zakai bayani a can tunda an fitoma da lalama ka nuna baka san

haka ba ai akwai hukuma a gari ko ?

Duk inda zaku kuje zancena dayane wallahi banda masaniyan komai akan bantanta aje gun hukuma din

shima ya fada a hasale.

"Tsohon ne ya dakatar da baba ibrahim da suka fara sa,insa da Alh din yayi mashi dan nasiha mai nuna"

don Allah koda yaka san inda take daga baya suna rokonshi daya dawo masu da ita gida hannunsu.

Hakan baiwa iyayyen dadi ba yadda tsohon yabishi da lalama shidai yayi sallama dasu ya fita ya barsu

"da kamshin turarensa daya dume wajen dashi suna fadan ra,ayinsu a kanshi kan abinda suka fahinta."

Baba na tashi daga wajen taron bai tsaya ko ina ba sai kofan mama Dije inda ya tsaya daga kofan tana

ciki da yan uwanta suna alhinin wanan abinda yarsu tayi .

Saiji sukayi muryanshi daga kofa yana fadin Dije ta amsa da kyat tana fitowa ya soma fadin to ki sani

matukar hindatu bata dawo gidan nan ba yau zuwa gobe kema zaki bar gidan nan ke nan .

Don zamana dake yakare wanan karon tunda na fahinci dakece aka hada kai aka yarinyar nan ta gudu

tabar gidan nan ashe ?

Yanzu ga yaron nam Alh nan yace har nemanta yayi akan taje wai suyi bankwana dashi kuma kika bata

dama ta tafi yanzu ga abinda ya biyo baya bayan kuma kinsan nayi mata iyaka dashi lokacin.

Amma inka