Chapter 15 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

fadi haka Salisu bakaiwa Dije adalci ba a rayuwanta wace uwace zata yarta ta aikata haka

inba dai rashin hankali ya kama uwar ba ?

Gashi ko anyi gashi mungani sakacinta wai harda barin yarinyar nan ta taka zuwa inda mutumin nan

yake da sunan bankwana bankwanan bura uba ko iskanci ?

Yarinyar da ake shirin daurawa aure ina ita ina zuwa wajen wani inba lakacewan zamani ba da sakaci

irin naku na uwaye ba ?

Kin daiji na fada maki matukar baki fito da yarinyar nan ba inda kuka boyeta kema dole ki bar gidan

nan a gobe wallahi.

To sai me idan tabar gidan ko a daji ka daukotane wau ?

Dama burinka ke nan ai Salisu kai da wanda suke hure maka kunne kuga Dije bata numfashi to ta Allah

ba taka ba wallahi

Gidanka din me Dije tagane take zaune ciki banda kaddaran yayan nan da Allah ya bayar a tsakani ku ?

Na dai fada ya juya ya tafi fuuuu mutane suna kallonshi ita kuma mama sharifa tacigaba da fada mai

bakar magana suna kai farida dakinta basu zauna ba suka bar gidan a lokacin .

Don suje gun yayansu wanda shima zancen ya daga mashi hankali a lokacin tunda maganan kowa ya

shafa a nan.

**** **** ****

Hindatu tana barin gida tunda ta samu ta fita tana amfani da wayanta wajen da akai mata kwatance ta

nufa tana zuwa bata samu matsala ba ta hango saurayin dayazo daga kaduna daukanta.

Kece ko ya tambaya tace eh ya bude mota ta shiga da sauri suka bar wajen kai tsaye hanyar fita gari

suka dauko inda yayi gudu kamar zai tashi sama a lokacin.

Saida ya tabbatar da sun bar garin ya soma mata magana yana fadin yanzu kan mun tsira tunda mun

bar katsina ?

Itama din ajiyan zuciya ta sauke tana kware nikaf din dake fuskanta inda sai lokacin yaga fuskanta ta

soma fadin nagode gareshi.

No ba matsala tace min ke sister dintace ko yake tambayanta saidata daga kai kafin ta samu bakinta ya

dan budu take fadin eeh bukina sukazo .

Okey tace zaria zan wuce dake idan mun isa zaki zauna a dakinta kafinta dawo zuwa jibi nasan bata

wuce nan da kwana ukku zata dawo ai koda yake zakuyi waya da ita ai nasani .

Ita dai bata samu bakin magana ba bayan kai da take daga mashi a lokacin don magananma ya zama

mata lalura a lokacin donshi shima daya fahinci hakan ya kyaleta.

Sun isa zaria inda yakaita gidan da Nuratu din take zaune yayiwa abokan zamanta bayani cewa zata

zauna har Nuratu din ta dawo sukace tayi masu bayani ai ya fita ya kwaso mata abubuwan bukata da Nura din ta lisafa mai kafin yayi sallama ya tafi.

Ajiyan zuciya ta sauke kafin ta tana bin dan dakin da kallo inda yar uwarta ke rayuwanta inda

"karatune ya kawota zaria, din harta baro gidan iyayyenta."

Dakin acan acan dashi dan wadatace dashi haka akwai fridge akwai tv karami sai katifa da akai mashi

shimfida akai sai tufafinta da tace ta duba tayi amfani dasu kafinta dawo.

"Ta gaji da tunane ta mike zuwa bandaki don tayi alwala tayi sallah dake akanta azahar la,asar dukka ta"

gabatar a lokacin daya.

Taso taci wani abu a cikinta saidai ta kasa hakan a lokacin don damuwa da tunane dake addabanta na

halinda ta baro gidansu ciki?

Saboda tunanen gida daya addabeta tasabn a yanzu gida nacan kowa ya gama samu labarin batanta a

lokacin wanda tasan akarshe kan mahaifiyarsu laifin zai koma don tasan halin mahaifinsu da tijara.

Koma meye tsakaninsune yanzu don ta tabbatar da ba zata iya zama da wanda akace an daura mata

aure dashi ba wai tsoho ya rasa wanda zai aura mata sai sulaiman sulaiman fa dan gwaggo mariya ?

Dake cikin gida wajen gwaggo hafsatu suna cin arziki wanda a gabansu ba irin tozarcin da cin mutunci

da gwaggo hafsatu batayi masu idan tijaranta ya tashi take tsayawa tayiwa iyayyensu tas agabab jama a kamar ba abu guda suka fito da ita ba ?

Wai shine kyamusashen tsohon nan ya aura mata duk cikinsu yama fi raina mata wayau da hankali don

kamar ya wullakantane ma take gani.

Data koma gara ta tabbata nan a wajen yar uwarta mai kaunarta data san zafinya wace tayi mata

abinda kowa ya kasa mata sai ita ?

Umurnin yayan nata shine ta kashe wayanta gaba daya har sai ta dawo zasu dinga magana ta wayan

abokoyar zamanta da kuma wanan saurayin idan tana da bukatan magana da ita din.

Tayi wanka tana shirin kwanciya duk da lokacin tsoro yadda zata kwana wanan dakin ita kadai ya

kamata amma me zai sameta tunda haka yar uwar nata take zaune ita kadai a dakin ai.

Inkaga tsoro bakaga abin gudu bane ko inda yafi nan zama dajine a lokacin zata iya kwana ai matukar

"dai ta samu ta gujewa auren kala,in nan na tsohon nan."

Allah sarki maman mu ki yafe min nasan naja maki abinda kike gudu a cikin gidanmu amma dole

takama in hakan don banda zabi bayan hakan da nayi a yanzu din.

Ta dansha yught wanda aka kawo mata tun isowansu donshi kadaine zai iya zama a cikinta lokacin ta

dansha yakai quarter ta aje goran don shima taji bakinta salab bai daukan komai a lokacin.

"Don haka ta nemi wuri ta kwanta ta soma addu,oin data iya a bakinta na neman mafita ga Allah ga"

wanan jerabawan data samu kanta a ciki a haka barci barawo yayi dan halin nasa kanta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/22, 9:22 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Tun bayan tafiyan yan uwan Dije daga ita sai yaranta da suka saura a daki a cikin damuwa wanda gaba

daya sun kasa sukuni a ranan tun faruwan lamarin batar yar uwarsu da gida ya dauki surutu akai kowa na fadan albarkacin bakinsa kan zancen.

"Ga cin mutuncin da baba ya shigo bainan jama,a yayiwa dije din a gaban kowa wanda yan uwanta sun"

kasa kyaleshi a lokacin tunda baiji nauyinsu kasancewa suna dakin ba.

"Haka ya rufe ido yana mata cin mutunci da tonon asiri bainan jama,a wanda yakai sunji ba zasu iya"

kyaleshi ba shima a lokacin suka shiga jifansa da kalamai masu zafi tare da alwashin a gobe din idan shi bai sallami Dije ba su zasu dauki yar uwar nasu su tafi da ita .

Idan shi da yan uwansa basu kaunarta a gidan cikinsu su suna kaunar abinsu har gobe don haka yasha

kuruminsa zata bar masa gidan dama da diyansa.

Wanan yana cikin abinda ya kara kashe masu jiki a lokacin suka zauna a daki suna tunane yadda mama

sharifa ta dage kan wanan karon ba zasu ragawa baba ba tunda ya iya fadan hakan a gabansu gaban kowa nasa kuma sai sun nuna mai mama nada daraja har gobe.

Da wani zataji a lokacin alhinin rabuwa da yayanta da akai mata bazata ko tashin hankalin da yarta ta

"jefata ciki a wanan ranan cikin bainan jama,a ?"

Ko kuma cin mutuncin maigidan a gareta don ya nunawa mutane bata da muhinmanci a wajensa ita

da babu ita a gidan duk dayane a wajenshi yanzu.

Shi kanshi a lokacin idonsa ya rufe ya manta da yan uwanta masu kokari akansu suna kusa don mama

Sharifa ta kasance wani bangon dafawa ga mama Dije a rayuwa.

Daga suturan yara zuwa nata mama shariface dawainiyar wanan idan zatayi sako haka take aiko sako

mai yawa ga mama din abinka ga dan uwa maison ganin rufin asirinka cikin wuri.

Wanda anyi tsegumin hakan har angaji wanda yana cikin abinda yasa ba a gane raunin mama duk

"yadda akaso aganta ba a ganinta hakana ko yaushe ita da yaranta acan acan suke gwanin ban sha,awa."

Wanda tsabatanta ya karawa abin armashi ba a gane cewa tufafin ma kumcene don yadda take

tanadinsu sabo da tsoho idan ta tashi aike haka zata hadowa yar uwar akawo mata.

Haka kuma dan abin birni zata hado matasu kaya guda driversu zai taso daga kaduna zuwa katsina

wajen yar uwarta ya kawo mata sako.

Inda a nan gida katsina kuma mama gambo itama da nata duk sallah yaran kaf saita bisu tayi masu

dinkin tufafi na sallah da mayafaiya da hijjabai na sallah .

Inda Kawu kuma shine dawainiyar cin mu da shanmu a gidan mahaifinmu don haka zai aiko da buhun

abinci geron kunu da marasa da shimkafa a kawo wa yar uwarshi don dai kada ta gani a wani ta kasa hakkuri suke faman kafa kafa da yar uwar nasu.

Wanan duk baisa baba ya gane shi akewa hassada ba mama yake biyema su har aka rinjayeshi akan

mama din ya soma wullakantata a cikin gidan yawa wanda har abin yaso ya shafi diyanta don tana kafa kafane kuma tsohon gidan a zamanin yana tsaye a kanta ita da diyanta yasa suka dan samu sukuni.

Mikewa tayi ta fita ta dauro alwala ta dawo dakin diyan ta suba tana fadin kunci abinci kuwa fadila

dake da dan wayau ta mike tsaye don tabawa kanneta abinci don kananun har sun soma barci a jikin yannensu lokacin.

Idan kin zuba masu fadila ki kawar da kayan waje ki rufo min kofa ta fada a cikin raunin murya da

saurin yar nata ta amsa mata itama ranta babu dadi a lokacin.

"Isha,i ta gabatar kafin ta dora da nafila don har fadila din taga avinda zatayi waje ta rufo dakin tazo ta"

kwanta tana zaune tana fadawa Allah kukanta .

Akan ubangiji yayi gagawan baiyana mata yarta ta dawo gida garesu kafin rayuwanta ya salwanta yadda

wasu ke mata fatan hakan ga yar nata a yanzu.

Sanin zancen da yan uwanta sukayi akanta yasa ta soma kimtsa kayanta da take bukata wanda ita

kanta zama da baba ya fice mata a rai kwata kwata a rayuwanta wannan karon taji bata iya hakkuri da irin halaiyanshi gareta a yanzu garata nemawa kanta mafaka dashi.

Cikin hakane ta jawo ledan dake can bayan gadonta an nadeshi da wani tsohon zaninta an jefa a wajen

har ta jawo ta dauka ledan banzane zata mayar sai kuma tayi shawaran ta bude taga komeye a ciki don dan nauyi da taji a cikin ledan.

Abinda taganine ya bata tsoro da firgici don kudine masu yawa a cikin ledan an nadesu a waje daya sai

dan akwatin sarkan dashima yake cikin nasa ledan dagani daga Dubai abin ciki ya fito don tambarin dake jikin ledan mai dauke da sunan wani shago acan din.

Jikina rawa ta bude taga sarkan gwalce mai dan girma a ciki ga kuma wanan kudin shima a cikinsa

dunkule har wanda yaba ita farida a lokacin duk ta hada a waje daya ta dunkule ta kada a wajen da tasan ba wanda zai iya tabawa har lokacin da hankali ya kwanta su nunawa mahaifiyar nasu.

Rasa me zatayi a lokacin tayi ba dama ta fadawa wani wanan zancen yanzu gida zai dauki magana don

haka ta mayar ta daure yadda yake tayi niyar mayarwa inda ta ganshi saidai sanin a yau tana iya barin

gidan yasa ta jefa ledan can kasan jakar da take da niyar tafiya dashi inda ta hada kayanta din da zata tafi

dashi.

Tana aikin hada dakinta don sanin halin matan gidan matukar irin haka ya faru ko kayi tafiya sai an

samu wanda ya shigama daki a sace yayima bincike a daki don ganin kwam donshi ta kwashe komai wanda yake sirintane ta adana abinta cikin kayan da zata tafi dasu din wanda zatabawa yarta ta biyota dashi daga baya.

Amma kuma damuwa akan wanan ajiyan da bata raba dayan biyu don ko a cikin yayan natane wata

daga cikinsu ta aje wanan abin ba tare da saninta ba don tsoronsu.

Ranta ya bata ba kowa bace face hindatu kwaraima hindatu dince amma a ina tafito da wanan kayan

da kudi haka idan ba karya tunanenta ya bata ba wanan abin zinarece ta gaskiya ba designer bace da akeyi fake barawon zinare ke nan.

Fadila fita da kayan nan kikai min gidan uwale da sauri Fadila din ta dubo uwar nata ta soma magana

tana fadin mama tafiya zakiyi ki barmu don baba yace yau in baki fito da yaya ba zaki bar mashi gidansa.

Ke dauki kaya kikai min inda nace in na tafi na barku Allah ya zama gatan ku fadila ki kula sosai da yan

uwanki don Allah mu sanman ma Salma da take karama a cikin ku.

Mama don Allah kiyi hakkuri kada ki tafi haba fadila kinfi bukatan in zauna yana muzantani a gaban

kowa duk sanda dan abu ya hadani dashi a gidan nan ?

Haka kikaga yanayiwa sauran abokan zamana inba bashi wuri na danyi ba Fadila bai taba sanin ina da

rana a cikon gidan gara in dan matsa in sarara zaifi tun kan a wayi gari a samu bakin cikinshi ya kasheni a dakin nan.

Don Allah kada kowa yasan ina zaki ki dauki buhun nan ba mai tsareki da tambaya balle yaji meye a

cikinsa ki tafi kikai mata kice zan aiko a daukar min daga baya.

Ba yadda yar ta iya ta dauki kayan zuwa gidan makwabta kamar yadda uwar tace mata ta dawo ta fada

mata takai suna tsaka da maganan muryan mijinta a kofa yana sababi da ita.

Inda yake fasin watau Dije kin dauka da wasa nakeyi ko ba zaki fito min da yarinya inda kika boyeta ba

ko ?

To kiji ki sani karki dauka barazan yarki zaiyi tasiri garenine na fada yau din nan in ankai karfe goma baki

fito min da ya ba zamanki a gidan nan ya kare ke nan dije ?

Sai me malam dama ai ko bakace ba zamana ya kare gidan nan a yanzu son banga tsiyar da kuma zai

zaunar dani ba a gidan nan tunda ba a nan aka haifini ba ai ?

Yarinya kuma bakai kadai ka haifa ba balle ka nuna yatkace kai kadai abin bai dameni bani nafika shiga

damuwa tunda kai kana da wasu yaran bayan wa yan nan niko su nake gani don sune nawa ?

Ta rufe ido abinda bata taba yi mashi ba ya bita da kallo kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya fice

daga gidan yana kutawa.

Ya dan jima da fitane take fadin kuje ku duba min farida kuga yadda ta kwana jin hakan yasa yaran suka

mike suka shirya zuwa duba yar uwar tasu da ta kwana a bakon wuri a daren jiya din dukl da a gida take ba waje ba ?

Suna fita ta dauki jakkarta data kara hada wasu kayanta a ciki ta fice don babu kowa a lungun suna

cikin gida ana gulma wanan ya bata daman fita daga gidan.

"Tayi sa,a har kayanta data bada ajiya ta tsare mai Napep ta saka ta tafi tabar unguwar ba tare da wani"

ya sheda hakan ba.

***** ***** *****

Yau da zazzabi ta tashi wandaz kukan da tayi a cikin dare ya haddasa mata hakan tayi kuka tayi nadaman

fitowa daga gidansu da tayu.

Tayi data sani yafi duba a rayuwanta bata taba kwana wani waje ba tare da yan uwarta ko uwarsu a

kusa ba sai gashi yau ta kwana a zaria inda babu kowa nata a gidan haya kuma inda ba wanda ta sani.

Tana jinsu suna ta shirye shiryen fita zuwa school saidai ba daman ta fito daga dakin don ba wanda ta

sani balle ta fada mai damuwanta na zazzavin dake damunta din a lokacin.

Allah da ikonshi wata makwabcinyan Nuratu din ce ta shigo tana tambayanta yaya ta kwana ta amsa

da kyar tana makyarkyatan dari hakan yasa ta fahinci bata da lafiya.

Itace don zaman lafiyan da sukeyi da Nura din ta kaita asibiti akai mata allura aka basu magani ta biya

kudi suka dawo gida .

Wanan boyan Allah ta kula da ita sosai don suna dawowa ta hada mata tea mai kauri mai kuma zafi ta

tsureta ciko tausaya mata saida ta sha fiye da rabi ta koma ta kwanta.

Barci ta wuni yi don aluran da akai mata harda na samun barci a ciki sai yamma ta tashi taji jikinta ba

kwari a lokacin .

Wanda wanan kawar tayi waya da Nuratu din take fada mata halinda yar uwar nata ke ciki saidai ta

kwantar mata da hankali da tace mata takaita asibiti an duba ta yanzu haka tana barcine ma .

Sosai hankalinta ya rabu biyu don a nan katsina inda suke ga mama dije suna zaune ana karyawa

kwatsam suka ganta tashigo da kayanta gidan kawun nasu.

Inda hankalinsu ya tashi da ganin hakan nadama sosai ya kama Nuratu din tana gudun kada

shawaransu yakai ga kashe auren kanwar uwar nata azo a kuka da ita daga baya.

Ga kuna wayar kawarta data samu cewa wai hindu din na kwance rijib ba lafiya a can zaria din inda ta

boyeta dole ta shiga cikin damuwa itama.

Meya faru na ganki a nan wanan lokaci bayan bakin gidanku basu ko watse ba Khadija yayansu yake

tambayan mama hakan ?

Makin ta bashi amsan tambayashi sai kuka ta fashe masa dashi inda hankalinsa ya kara tashi sosai da

ganin halinda yar uwarsa ke ciki.

Lalashi ya koma yi yana fadin haba Khadija ai sai zargin da mijinki ke maki na kinsan inda yar nan take

ya dauka gaskiyane ?

Yanzu da kika taso kika bar mashi gidanshi a wanan lokacin da ake ciki na zafin abinda ya faru sai suyi

zaton munsan inda take ai mu muka boyeta dama ?

Dakatar da kukan da takeyi tayi a lokacin tana zayane masu abinda baba din ya shigo ya fada mata da

safen nan na sai tabar mashi gida a ranan .

To yaya kafin yai min wullakanci tunda bansan inda yarinyar nan ta shiga ba