Chapter 17 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

son zakuyi sammako ku tafi zaria kaida yaron

nan Amadu ku dawo da yarinyar nan hindatu gida.

Zaria taje baba tana zaria ashe yau ta bugo waya tana sanar da dam uwanta inda take saidai ina son ku

kama bakinku don Allah har kuje ku dawo kafin wani yaji a gidan nan ?

Insha Allahu baba ya fada yana gyara zama tsohon yaci gaba da fadin mota nake son ku dauka shata ta

yadda zaku tafi har ku dawo wani bai sani ba gidan nan ya bashi kudin motan da zai ishesu sukayi sallama aka watse daga wajen akan da safe zasu tafi zaria din.

***** ***** *****

A bangaren hundu kuma saida ta fada ta koma data sani bata fada ba dawowan Nuratu daukan darasine

taganta a hargitse take tambayan meya farune na ganki haka ?

Waya nayi da farida yau me ta fada da sauri tana aje rigan data dauka zata saka a jiki tace kin fada mata

inda kike ke nan ko ?

"Eeh na fada mata ina zaria gidan wata tsohuwa kinga,,,,,amma hindu baki kyauta min ba yanzu idan"

sukai tracking din numberki suka gano inda kike fa kija min bacin rai ga iyayyenmu kome ?

Yaya Nura hankalina ya kasa kwanciyane wallahi banso in zama sanadin mutuwan auren iyayyena

wallahi ko badon keba ai mama tasha alwashin dauko ummi dama .

Baki kyauta min ba da kika kirasu wallahi yanzu za a gane cewa kina wajena ke nan goben nan

zakigansu garin nan sun iso yadda ake nemanki din nan.

Ta mike ta fita wajen kawarta taje ta fada mata abinda ya faru shiru kawar tayi tana tunane kafin ta

samo mafita tace bari mu shiga nan gidan Iya muyi magana da ita a fada mata komai ko zata yarda ta karban muna ita a matsayin gidanta take zaune kinga mun wanke kan mu ai ke kuma kada ki bari su san kina nan su gane wajenki take gaskiya.

Tare suka mike har hindu din zuwa wajen iya tana zaune a dan shagonta da take kasa kayan miya a

unguwa sukai sallama suka shiga wajenta.

Ta saba da yaran sosai a unguwar iya mutumce mai haba haba tana zaune da jikanyanta daya wace

"batafi sa,an farida ba a shekaru."

Sun zauna bayan sun gaisa sukai mata bayanin komai basu boye mata ba inda tayiwa Hindun da Nuratu

fada sosai kan gangancin da suka aikata din a lokacin.

Zata dawo gidan nan a yau koda basu zoba ga gobe nida kaina zan mayar da ita hannun iyayyenta in

masu bayani kan tana shawagine a cikin unguwa na taimaka mata take zaune dani.

Godiya suka soma yiwa tsohuwar ita kuma tanayiwa hindu din nasiha akan karta kara gudu tabar gida

in bata so ta nuna kawai bata so a rabasu yafi wanan gudun mutunci.

Don yanzu inba Allah ya gyara ba sai a dauka ai bariki ta shiga yawon banza kinsan halin mutane da

jifan dan uwa da mugun abu yanzu.

Da dare suka rakota ta dawo wajen iya din kamar yadda aka tsara a dakin tsohuwar suka barta zasu

zauna tare tana fadin dana kowane ai ?

Haka ta kwana a takure aranan tasan daraja da girman gida a wajen da adam duk wanda baida gidan

iyayye koya duba baya da gaba abin a tausaya mashine.

Gashi dai shimfida maikyau tsohowar tai mata amma kuma a takure ta kwana a ranan da safe koda ta

tashi aiki ta kamawa tsohiwar tana saka mata albarka tare da kara lurar da ita irin kuskuren da tayi na barin gida.

Koko da fankene suka karya dashi a gidan tsohuwar wanda daga baya aka dora abincin rana Nuratu

tashigo ta dubata da zata wuce school sukai dan magana irin ta yan uwantaka a tsakaninsu kafin ta fice zuwa makaranta.

Barci ya soma daukanta sakamakon rashin barcin da bata samu da dare a yanzu don tunanen gida

karan wayantane ya tayar da ita a lokacin ta tashi firgigit ta dauki wayan ya Ahmad dinsune a kan layin taji lokacin da yake fadin ta dauka ai.

Kafin ya soma fadin ke hundu kina jina gani a zaria kina wani shiyane in karaso dan shiru tayi jin kafin

yaji tana fadin iya meye sunan unguwan nan ?

Nasarawa GRA ta fada mai da kwatance suna waya har ya iso gidan shida baba haruna sukai sallama

saiga iya din ta fito suka gaisa tasa akai masu shimfida bakin shagonta.

Ruwa da lemun kwalba mai sanyi ta kawo masu sukace sun gode ina ita hindu din kafin ta mike ta shiga

ta kira masu hindu din dake kuka a lokacin.

Nan iya ta soma fadin aifa aikin ke nan tun ranan da nazo da ita gidan nan a mota muka hadu da ita

kasan dole in fahinci ba lafiya ba duk da batace dani komai a lokacin ba .

Saidai mota ya tsaya nan kofan dokane na dai fahinci yarinyar nan bata san kowa ba garin nan nake

tambayanta shine ta fada min ita bakuwace batama taba zuwa garin nan ba.

Shine dalilin da nazo da ita nan ni kuma ban matsa a lokacin in tambayeta ba kasan dan yau ina iya

"mata tambaya ta kuma gudu daga nan din ba,a san inda zata nufa ba kuma ."

Sai gaku yau Allah ya kawo yau satinta biyu a hannuna da kwana biyu baba haruna yace kwarai kuwa

anyi haka tun ranan aurensu ke nan nima gaisuwa naje zan dawo shine fa muka hadu a nan garejin da ita.

Sukai mata godiya bisa kokarin rike masu ita da tayi na tsawon lokaci har Ahmad na mata fada idan

badon ta fada hannun iya mutumiyar arziki ba waya san hannun da zata fada kuma ?

Tunanen da nayi ke nan dan nan duniya yanzu ta baci balle suna ganinta haka ai shike nan sai a nemeta

a rasa kuwa cikin garin nan .

"Haka suka kamo hanyan gida dole da ita ana sallah la,asar suka shigo katsina tsoho suka kira suna fada"

mashi sun iso ya tambaya kun sameta tare muke da ita ya soma fadin Alhamdullahi Allah abin godiya tunda ta dawo lafiya.

Yana kashe wayan yace a kira mashi hjy laraba da uwani tare da matarshi daya suka zo yake fadin kuje

gidan mariya ku shiga da yarinyar nan dakinta angatane anganta tana zaria Amadu da haruna dazu sukaje daukota.

Kafinma su karasa labari ya karade gidan ga hundatu nan ta dawo ai ga hindu nan sukayo kofan gida

ruuu ake fada masu ai ba a zo nan da ita ba ?

Suna gidan mariya can baba yace a kaita saboda me yarinyar da tabar gida kwana da kwanaki za a

dauka akiwa yaya mugun abu tun ba a binciketa anga halin da take ciki ba ?

Kowa kallo ya bita dashi itako cikim halin ko in kula taci gaba da fadin fissabillahi fa maganar gaskiya

ayita idan yazo .

Yarinyar nan idan ta dauki ciki ko wani cuta aka mannawa yaron nan fa a bar mutane da wahala kome !

Kai haba don Allah ina da sulaiman da hindu duk nakine da har kike tunanen haka koma meye ai abin

baikai haka yadda kike tunane ba wata daga ciki ta katseta.

Inda bata saurarra ba tacigaba da fadin wanan karon saidai baya yayi komeye a kai amma ba zamu

yarda ba gaskiya haka kawai yarinya taje ta zubar dinta yanzu a kwaso a dunkula akaiwa yaro waya sani ko duk dadewan nan tana dakin wani boye ?

Amma ko gaskiya dai wanan magana bai dace ba a bakinki gaskiya inna halima ta tare da fadin hakan

gareta.

Ku bari a fadi gaskiya kowayema ba zai yarda ba ai itace tace bata sonshi yanzu a dauko ragowan wani

turawa yaro kuma kuce kar ai magana gwaggo Asiya ta karbe zancen tana fadin haka juyowan da zatayi sukai ido biyu da Fadila.

Kame kame ta somayi ta juya itama zuwa ciki tana mugun magana suka hade da hafsatu din daya yafo

hijjab zata ketara zuwa gidan yar uwar nata.

Saidai tana saka kafa kofan gida mijinta na fadin ina zaki gidan yaya mariya waya gaiyaceki wanda baba

ya gaiyata ai suna can sunje ke waya gaiyace ki ?

Dole ta koma bayan tayi ya barta rai bace yace maza ta koma gida inda suka shiga da hindu din cikin

gidan fada sosai suka taru sukai mata a nan dakin sarakuwarta kuma gwaggonta suka barta suka fito bayan sun kaita dakinta da yake gyare tun ranan da aka daura aure.

"Acan cikin gida part din baba Audu fada gwaggo hafsatu keyi tana fadin yanzu shi yaron nan tun ba,aje"

ko ina ba ya fara masu bauta ke nan ko ?

Shine mai zuwa dauko hindu don gantali har yaushe yaushe da har ya fara gantalewa ha akan mace ?

Shirmen banza shirmen wofi kina nan kina hauka to kinji hannun wata tsoho boyar Allah ta fada ashe

mota daya suka shiga daga nan katsina zuwa zaria .

Ya soma basu labari aka cika wajen kowa yana saurare ai dama munce hindatu nada wayau ba zata

taba aikata wani abin asha ba ta dai gudune kawai saboda wancan da take son aure.

Rasa bakin magana tayi don bayanin da baba Audu suka shigo da baba haruna sunayi kamar yadda

tsohuwar ta labarta masu komai.

Dole kowa yayi shiru aka koma fadin yanzu ba don ta fada hannun kwarai ba waya san abinda zai faru

da ita Allah dai ya kyauta abu kam baiyi dadi ba gaskiya.

Baiyi ba kam yanzu ai sai yaya ta dawo dakinta kuma tunda gaskiya ya baiyana kowa yanzu yasan ba

itace ta boye hindutu ba da ake mata zargi inna Halima ke fadin hakan ga matan gidan.

Dama wace ita ana dai ganin kamar da sanin uwar ta tafi shine kawai amma ba wanda ke zarginta ai ?

Kudai abar zancen tunda hindatun ta dawo gida yanzu ita kuma uwar sai tayi hakkuri ta dawo dakinta

ta fake diyanta kuma ?

Kema aikin sani kwanan nan kina ganin ta dawo dama nauyin abinda yarta tayine yasa ta komawa gida

yanzu kuma tunda tadawo ai shike nan kuma.

Ta dawo mana aiga kangon dakin nata nan yana jiranta me za a fasa kota dawo abun kunyane dai yarta

tayi ba a hanamu fada kuma a gidan nan gwaggo Asiya ta fada ta juya ta tafi.

Lokacin da baba ya samu labarin dawowan hindatu din a sukwane ya dawo gida a zatonshi tana cikin

gidane ya shiga dakinshi sai gashi ya fito da zundumemen bulalan fata yana fadin ina yar abu kazan uban take yau sai an kwaceta a hannuna gidan nan

Hindatu kan ai tana dakinta don ko gidan nan baba bai bari anshigo da ita ba inna halima ta bashi amsa.

Aikin hankali dai yana ga maishi kai yanzu in tana gidan nan dukanta zakayi da bulalan nan daka dauko ?

Ta kuru yau bata gidan nan dakun sheda ai in wasa nake fada yarinyar banza kawai mara tunane tajawa

mutane zagi da zunde a cikin gari.

Ita kuma wanan sakaran ta biyewa yan uwanta suna zaune dakunansu lafiya ta hau zancensu ta zauna

ita game yan uwa taje ta zauna din ita tasani ai yanzu kuma.

Baba ibrahim tsoho ya tura ya fadawa su mama anga hindatu tana dakin mijinta yanzu haka donshine

washegari kawu da mama Gambo sukazo gidan .

Sun fara zama da tsoho aka gaisa yake mayar masu da zancen yadda aka sameta sun dan jima suna

magana a kai kafin ya fito da zancen mama yana fadin.

Ita kuma Dije saita dawo dakinta haka tunda yarinya ta dawo zargi ya kare kuma kawu ya danyi

murmushi yana fadin.

Dije batama garin nan tare suka wuce da sharifa kaduna naso lokacin in hanata tafiya amma ta nuna

kona barta ba dawowa zatayi gidan salisu ba yasa dole na barta ta tafi.

Shirmen banza ke nan ba zata dawo ba ina zata zauna tunda ga dakinta ai sai ayi hakkuri ta dawo ?

Gaskiyane malam nima naso hakan saidai a gaskiya yanzu ba zan iyawa Dije dole ba idan tace zata

dawo zaku ganmu da ita idan taki kuma sai in gyara mata gidanta na kaduna ta zauna a can din.

Shirmen banza kenan dakinta ai shine gidanta baka bata wuri ta zauna da auren wani ba kawu yace ina

ganin Alh baka fahinceni ha .

Niba gidana zata zauna ba ai baba gidantane data gada yana kaduna can din nake son in gyara mata ta

koma ciki ta zauna tunda zaman ya kiya a tsakaninsu.

"Ba zan yarda in zauna salisu ya kashe min yar uwata ba dama don tana ra,ayin zama dashine ai mukayi"

hakkuri yanzu ko tace ta gaji.

"Ba,a gajiya da bautan Allah zaman aure ai zaman bautan ubangijine hassan a daiyi hakkuri ta dawo"

dakinta ta fake dinyata don Allah ?

Sun dan jima da tsohon kafin su tashi zuwa gidan hindatu inda sukai mata fada kan bata kyauta ba

abinda tayi kuka kawai takeyi a lokacin sukai mata sallama suka fito.

Shi kuma baba da tsoho ke fada mashi zuwansu da irin zancen da sukayi game da maidakinshi din sai

cewa yayi.

Dijece keda gida kaduna wanan zancen karyane tana da gida duk dadewan nan ace ban sani ba sai

yanzu komai da suka gada aishi yayan nasu ya hamdame duka shi kadai yabar yan uwan.

Yanzu dai ka bari ta kara dan kwana biyu sai kubi sawunta ta dawo dakinta hakana kuma tsohon ya

fada ya tashi rai bace yana jin haushin yan uwan na mama.

Don me zasuso raina mashi wayau su nuna zasu ja mashi rai akan dawowanta dakinta shima zai nuna

masu bai damu ba ai.

Haka ya koma part dinshi yana fada burgan banza burgan wofi kawai shi za aso rainawa wayau suce

wai zasu gyara mata gida a kaduna wai kuma gidantane ai data gada ?

Ita Yaya din take da gida aida ka sani su dai suce kawai zasu kama mata haya ta zauna a ciki amma

banda zancen karya kuma ?

Yayi barazanan da kwana biyu fadila ta tambaya zasuje suga mamansu yace suje kada su dade sai dai

da sukaje basu jima ba suka dawo.

Don ance ai Dije din ta koma kaduna kawunsuma yana can yaje gyaran gidanta dama yan haya aka

zuba mata a ciki ab tayar da yan hayan ana gyaran gidan donta koma ciki.

Waiko dagaskene zancen gidan nan wai kadafa maganan nan ya zamo gaskiya malam kila dama sun

boye maka hakane sin gaskiya da yanzu gidan ya salwanta.

Gidafa ya kara fada kafin ya juya ya fita ai kuwa anyi abu gaban yan baki nam danan labarin hakan ya

bazu a ko ina na gidan

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/25, 10:11 AM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Zaman tsakanin hindatu da sulaiman yaki dadi don ranan da yazo kin shiga dakin tayi a tsaye ta kwana

waje saida safene tashiga dakin .

Bai kula da hakan ba bai kuma damu da ita bamecewa kowa komai a cikinsu duk abinda sukeyi idon

mahaifiyarshi yana kansu saidai ta nuna bata gani ba.

Don ita daban take da yar uwarta tana da hakkuri ga sanin ya kamata ga biyyan zumunci donshine ba

ajin muryanta da yan uwa.

Kusan abu dayane ya kwasosu da mahaifinmu saidai dan banbamci don ta kasance ita daya tilo a cikin

yan uba shi kuma mahaifinmu su hudune sauran Allah baiyi su rayu bane yanzu ya zamo shi kadai a cikinsu.

Amma da yake baba Alu yana tsaye da kula da zumunci sai ba a gane hakan saboda duk dan dan uwa

yana bashi hakkinsa yadda ya dace a gidan.

Wanan yasa tafiyan yazo da sauki mutane basuma ganewa don gaba daya kan iyayyen namu a hade

yake duk ko da dan barakan da aka samu a baya na rabon gadon waje da baba Audu ya tayar da bori akayi wanan bai kawo baraka mai tsawo ba tsakaninsu ba.

Saida hindatu tayi sati biyu cif a gidan sulaiman gwaggo hafsatu ta samu fita zuwa gidan yar uwarta

gwaggo mariya don baba Audu ya kasa ya tsare yana zaune gari yaki tafiya su Ahmad ne suka koma saboda karatunsu.

Ranan daya tafi da safe baiko bar jahar katsina ba ta wanke kafa sai gidan gwaggon mu mariya inda ta

samu yar uwar na aiki a tsakar gida suka gaisa da ita take tambaya kai tsaye ya naganki kina aiki ina wanan dagar tsiyan da aka daukowa mutane ?

Wa ke nan kuma hafsatu yarinyar nan mana Hindatu yar rainin wayau kawai da wullakanci tagama

yawon ta zubar dinta ta gama sayar da mutunci a bariki an dauko an kawowa dan mu don shine baisan ciwon kanshi ba ko ?

Haba hafsatu hannunka baya rubewa kayarda yau ko bariki ta shiga ai hindatu tamuce dole mu karbeta

a gidan nan balle wallahi yaya haruna yazo har nan yayi bayani ba yawon banza ta tafi ba.

Kawai dai kaddarantace yazo a hajan tayi shara tayi wanke wanke shine kawai dama nace ta dingayi

ina jin tana ciki ta kwanta.

Kaji ai kaji matsalanki yaya wani kwanciya zatayi a yanzun nan ita data zo aure ai kawai duk wani aikin

gidan nan ki mika mata ki koma ki nade kafa kina kallon yar iska tunda bata da mutunci.

A cikin barci take jin muryan gwaggo hafsatu din ta dauka mafarki takeyi a lokacin sai daga baya ta

"fahinci inda take kuma wanan muryan ba,a mafalki take jinsa ba zahiri a fili yake shigowa kunnuwanta a lokacin."

Zubur ta mike zaune daga inda take kwamce kasa a takure a gefen kujera a cikin dakin tana mai cigaba

da sauraren muryan gwaggo din dake fada a lokacin.

"Inda take fadin hada zuria da Dije ko tsiya zuri,an fatalwu da basu da asali kwashe kwashen mazane da"

kwadayi ai yakai yaya Salisu dauko wanan bakin irin ya kawo muna gida.

"Yanzu gashi suna neman zamawa mutane bala,i cikin