Chapter 18 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

gida yo dama ai gudu gado tayi wanda a cikin"

jininsu yake dan kwara har ya mutu wazaice yasan garin daya fito ?

Kinga kuwa itama kiris ya rage tarihi ya maimaita kanshi ashe tagudu yar iska har madi ako manta da

tarihinta a cikin dangi har abada.

"Haba hafsatu wanan kamar wace ta samu sa,an yita don Allah abu ya wuce a barshi daya wuce mana"

"abar tuna baya kaddarantane yazo a haka ai rubuttacen al,amarintane hakan ya faru."

Ai kaga kaji matsalan ko sai idan tazo tana tarawa mutane diyan shegu a gida sai kuma kice kaddarace

shima kaddara ko iskanci dai ?

Batin fada maki ya mariya wallahi sai naga bayan bakin auren nan da baba ya hada da yaran nan don

saina tayar da tsohon gaba a gidan nan idan yaran nan basu rabu min da yaya ba kuwa ?

Zata aika indai gwaggo hafsatune abinda ta fada a ranta ke nan lokacin matar da ba irin zagin da bata

shigo tayiwa mahaifiyarsu tun suna kanana har sun saba inba da tsotsayi ya gitta baba Alu yai masu iyaka da juna ba ?

Wanan yasa a ranan ko gigin fita gaida gwaggo hafsatu din batayi ba don tasan fitanma ba zai haifar

mata da da mai ido ba lokacin yasa tayi zamanta a daki bata fita ba.

A dakin ma data zauna ai bata tsira ba don karshe kira tasa mata a cikin murya mai kaushi ta fito da

alaman barci a fuskanta tun kan ta karaso ta tareta da fada da masifa da cin mutunci.

Tana fadan wa take kome ta taka da zataji muryanta ta shigo gidan taki fitowa ta gaida ita ko gadara da

isa irin nasu da suka gada zata kawo mata tunda ba kunya suka gada ba dama a wajen uwarsu ?

Kiyi hakkuri gwaggo barci nakeyi bansan kin shigo ba rufa min baki yar iska mara kunya banza kawai

mara mutunci don baki san kunya ba har kin san ki shige daki kibar yaya tana aiki a tsakar gidan nan ko ?

Ninace ta koma daki ta huta aina fada maki don Allah yaya rufa min baki idan ina magana da mara

mutuncin nan don Allah ?

Wai wanance zata gudu wai akan sulaiman shida ya kamata ace ya gudu shida aka hada da mugun abu

amma don basu san kunya ba wai itace zata gudu ?

To dama gudu ai angadoshi ta ina za aji kunyar hakan zakiga abu a gidan daga ke har yar uwarki can

mai ido fiki fiki kamar na bayin farko wallahi wallahi saita kasa fadan abinda zata fadi tana kutawa a karshe tace mu zuba daku a gidan nan yan iska kawai kusan kunshigo inda ba a maraba daku wallahi.

Ke jeki dauki abincinki a madafi yana can a rufe gwaggo mariya ke fadin hakan ta mike taja tsuki tana

fadin abinci kan aibatayi fushi dashi ba tunda an gaji cin ciya dama.

Karyan banza yaya Salisu aka raina wai kinji dije nacan kaduna sun kama mata haya sukai karya wai

gidantane na gado da aka zuba yan haya a ciki ?

Anface gidantane hafsatu karamin dukiya mahaifinsu ya bar masu a lokacin ba mamaki hakan gaskiya

don da sun mika mata tun lokacin kema kinsan da yanzu an kadar dashi ai.

Ke kin yarda ke nan gidantane kwarai kuwa Asmau kinsan yar uwar matar yayansune itace ke fada min

tace gidane babba sashe daya aka gyara mata daga ciki a nan take zaune yanzu.

Ohh ashe ita duniya tayi mata dadine da har ta dauki kafa tabar diyanta ta koma zaman kanta yanzu a

kaduna ?

To auren nata kuma fa yaya ke nan isalinsa kuma kowa ta aje da zai mata bautan diyanta kin dai san

koya sha giyan wake Asiya bata kula mashi da yaran nan halima kuma natama sun isheta ai ?

Dabara kanin kafa mana hafsatu dama ai zaman hakkuri dije keyi a gidan yaya salisu kowa yasan da

wanan ai kedai kawai tunda ankai haka ayi hakkuri da juna kawai.

Hindu najin irin tozarcin da akewa mahaifiyarsu babu daman magana daki ta nufa da dan kulan abincin

a hannunta tana shiga ta nemi waje ta aje ta zauna ta rabbaka tagumi tana tunane.

Wanda ba komai take tunane ba sai zancen gwaggo hafsatu din a kansu yaya kuma yar uwarta zata

zauna da wanan matar matsayin sarakuwarta ?

Ita dai harga Allah a yan kwanakin da tayi a gidan bataga wani abun ki daga gwaggo mariya ba yadda

suka saba haka take da ita .

In bada yau dai shigowan ita hafsatun data koma dari dari da sarakuwar nata kan babatun da yar

uwarta ta shigo tayi akanta da mahaifiyarsu hardama yar uwarta farida da take matsayin sarakuwa a gareta.

WAYE GWAGGO MARIYA DA SULAIMAN ?

Anihim mahaifin gwaggo mariya da gwaggo hafsatu mahaifinsu daya haka kuma mahaifisu da daya

haifesu da kuma wanda ya mahaifi namu mahaifin baba salisu wa da kanine zumuncine mai karfi a tsakaninsu.

Kuma ance akwai fahinta sosai a tsakaninsu kafinsu kaura Allah ya karbi ransu don a yadda akace

bayan rasuwan kakan mu rikon baba a hannun babansu gwaggo din ya taso.

Ita gwaggo mariya na fada maki a baya ta kasance a cikinsu ita kadace uwarta ta haifa a lokacin ina

maki bayanine mai karatu don gaba ki fahinci yadda alakar tamu take .

Don gidane irin gidan hausawa family house din nan nagado mai dabaibaiyi kowa dan uwane wanima

sai ki dauka au barene amma in an zauna akai maki bayani akwai zumunta sosai a tsakani.

Itama gwaggo Asiya matar baban mu ance ta uwa suka hada zumunci mai karfi dasu gwaggo hafsatu

din uwayensu daya a nan gidan.

Itama nasu zauren kaka guda suke da mahaifin mu dai zumuntan gashi nan masu a sarke kowa gwaggo

kowa baba a gidan namu kamar yadda muke da kowa yaya a yanzu.

Mijin gwaggo mariya shine bare a cikin mu shine baba Alu yai mata gata din tana da gado ya tsankwara

mata dan waje a cikin fili yace su gina su zauna a nan da iyalinta su huta yawon haya tunda tana da gado a ciki wanan ke nan.

Diyansu biyar da mijinta da akace ainihin mutumin jalingoneshi shima zaman mutunci akayi dasu na

unguwa daya aka zama kamar yan uwa dasu haka.

Mijin nata ya kasance irin mutanen nan da basu magana shiru shirune su to sulaiman zance shiya gado

da tsayi da komai na mahaifinsu ya dauko har da hasken fatansa irin na fulanine sak garesu.

Sam sam bai dai hayaniya sai ince gado yayi ta uwa da uba irin haka a wajen iyayyebshi shine kuma

dansu na farko da suka haifa amma rikonshi yana hannun gwaggo hafsatune don ace tun yana karami take daukansa da sunan itama ta samu da mai kyau irinsa acewan manya.

Sulaiman mutum ne mai hakkuri sam baida kwaramniya bashi da rigima kuma ga sanyin hali da sanin

mutuncin mutane duk da iyakarshi da kai gaisuwa sai ya zauna wuri har ya tashi bai wuce ya fadi kalma daya zuwa ukku ba.

Allah yayiwa diyan gwaggo mariya baiwan ilimi na boko dana arabiya yayi secondary a FGC cikin

katsina shida yaya Ahmed wanda baba Audune ya dauki nauyin hakan garesu.

"Bayab sun gama kuma ya samo masu gurbin karatu a jami,an sokoto inda yake zaune a sokoto din"

yana aiki harkalla a sokoto cements.

Wanda yana samu sosai yasa yake damawa a cikin yan uwa wanan yasa baiyi kyashin rike diyan ita

gwaggo mariya ba din a wajenshi.

Sulaiman din ya kasance dogo dan siriri lauka lauka mara jiki kina ganinshi kinsan shi din jinin fulanine

na asali.

Hakakuma baida rigama ko kadan ko sin a sani don da wanine keda kokarinsa da yanzu kowa ya gama

"sani don irinsu ake kira da dan baiwa a cikin al,umma."

Saidai sam rashin rigimansa yasa ba kowa yasan da hakan gareshi ba gaba dayansu sun taso suna shiri

sosai da mama dije don a lokacin.

Don mutanen tane shida yaya Amadu indai suna gida suna lungunta suna wasa a lokacin don shine ma

basu kaunar irin yadda gwaggo Hafsatu takewa mama din .

Wanda kuma hakan ya dauko asaline da saboda yaran sukayi da ita tun tana amaryantaa gidan suna

yara sukuma a gidan.

A cewan gwaggo hafsatu munafuncine don zata kwace mata yara ita kuma bata son irin hakan da takeyi

da yaran.

Ba saboda komai don kan mama dake hade da gwaggi laraba datajata a jiki tun shigowanta gida yaran

kuma sai suka saba da ita ba don komsi ba kuwa.

Don kawai idan ta gama abinci a lokacin tana sakawa yaran tunda suna hira a wurinta ita kuma don

tana tare da kishiyarta gwaggo laraba shine dai asalin kiyayyansu da juna har wanan lokacin.

"Gwaggo laraba a baya takayi ba,a tace takamawa yayanta yaran idan an masu wanka da kwaliya sun"

"shigo cikin gida wajenta ta dinga ba,a tana zolayansu."

Inda gwaggo Hafsatu kanyi fada ta nuna bata kaunan haka din har taso ta mayar da abin fada da har

wata rana case yakaisu gaban baba Alu.

Yake fadin tana fada kan hakan ta san kaddara ko akwai matan wani daga cikinsu ta nunawa tsohon ita

dai bata son hakan tunda uwar yaran itama bata kaunarta ?

Shine fa tsohon yaga abin ba iyaka an dauko hanyan raba zumunci tun yanzu ya yanke wanan

shawaran a ransa kan in yana raye zai hada wanan abin yaga iya gudun gwaggo hafsatu din da take son gurbata masu gida da akidar tana banza.

A ranan bayan ta koma gida da yamma yayan suka kirata suna gaisheta da wuni ta amsa tare da

tambayan ya suke Ahmad din yace lafiya ga sulaiman ya fada inda sulaiman din ya karbi wayan suna gaisawa.

Yau ai naje gidan yaya mariya nayiwa marakunyan nan tasa a gidan ita harta sanu wajen mike kafa tana

barcin rana ya katseta da tambayan wa ke nan yaya ?

Mara kunyar nan mana hindatu kaji min ya harta manta da abin kunyar data aikata watau ita ga yar

iska yayana aiki tana kwance nayi mata tas na fito.

Muryan Ahmad taji a wayab yana fadin da tayi maki me don Allah nudai ki rabu da yaran nan inma

haushine kiji haushin babanki din suma dole akai masu a kan mu ai.

To ubana sannu ubana don yanzu kaine ubana ai fada zakai min don nayi abinda ya dace ko kai naga

kanka na rawa akan yarannan waikai ga mai mata ko to bari kuji dukkanku wanan abin badani ba wallahi .

Kit ya kashe layin yana wurga wayan saman gadon da suke kwance ya dubo dan uwan basa don ya

karanci yanayinsa duk da yasan ba zai taba gano komai game dashi ba.

Koda kuwa abin ya zazzafeshi ba zai taba nuna hakan ba zai daure ya nuna baiji komai ga maganan ba a

lokacin.

Ban san meyasa mama takeyin haka ba wallahi abin nan dai anyishi ya wuce don me zata dinga tayar da

zancen nan kuma ?

Sulaiman din baiyi magana ba nunawa yayi tankar badashi yake bama a lokacin shima yasan amsanshi

ke nan dama gareshi kyaluwa don hakane bai damu ba ya cigaba da nuna rashin jin dadinsa ga abinda uwar ta fada.

***** ***** *****

Tun bayan tarewanta gidan da aka gyara da sunnanta wanda yasha gyara da kayan zamani don gaskita

kawu hassan dasu mama Gambo ba karamin kokari sukayi mata ba duk da ba karyan arziki amma da zata samu haka a dakinta na aure ai tafi kowa gata a gidan ke nan lokacin.

Ciki da falone guda biyu sai falinsu a tsakiya da kitchen da store dinta ta waje sai dan fili da zata iya

aiyukanta wanjen .

Haka sauran part din da yan hayanta ke ciki yake kamar yadda tsarin nata yake wanda duk shekara

"kawu hassan yake karban kudin yana mata hidiman rayuwa dashi saura kuma a,dana mata kudin."

Wanda a ciki sukai mata hidimar yayanta don sunbi Farida itama da abin arziki kayan dakine kawai

wanda akaiwa ita hindu aka barshi zaman na farida din a yanzu.

Don ita hindu nadune a dakinta da suka kai mata aka saka mata ance ko a wurin jerasu an samu

muhawara da yan uwan baba da suka nuna an raina abinda sukaiwa yarsu ke nan.

Mama gambo da mama sharifa da sauran yan uwa suma suka hau bakinsu don sunriga da sunba tsoho

hakkuri akan basu sanda za ai kayan ba sukayo mata ya kuma gamsu dasu ya yarda a jera mata din.

Sai gashi su yan uwa yan bani na iya suna son kawo tsegumi ga hakan suka dakatar dasu da fadin ko

wani da arzikinshi yake zuwa duniya ai.

Yanzu kan duk da ana ganin kamar hankalinta ya kwanta ganin inda take zaune an wadatata dakomai

na rayuwa amma a wurinta babu jin dadin da suke tunanen ta samu saboda abu daya shine kuma diyanta.

Tunanen diyanta a yanzu dashi take kwana dashi take tashi duk da bata rasa komai a rayuwanta nan

yan uwa suna tsaye kullum a kanta.

Amma wanan abin shine damuwanta a yanzu dan ba karamin kokari tayi ba wajen shanye hakan ta

nunawa kowa diya basu dameta ba .

Musanman idan ta tuno da kananan salma da babanta da suke kananu a cikin yan uwa don sanin halin

rayuwana gidan data sani kuma tasan halin kowa.

A yadda taji yaran suna nan dakinta har yanzu bai bari kowa ya daukesu ba tasan duk wanan yana cikin

"plan dinshi nason jawo ra,ayinta ta koma gareshi."

Amma ta shanye ta daure ta nuna yayan basu gabanta sai a yanzu da zaman kadaici yasa ta soma gane

kowa nasane nashi ashe ?

"Don dan dan,uwa bai share maka hawayenka sai naka takanji tausayin matan dama basu taba"

haihuwan ba balle su san zafin hakan da take ji.

Wanan yasa a ranan bayan ta idar da sallah magariba ta kira wayan hjy laraba wanda ba kasafai take

kiranta ba haka sai lokaci lokaci takan nemeta su gaisa haka itama hjyn takan dan samu lokaci ta kira din su gaisa.

Saidai ba sosai ba don gudun abinda zaije ya dawo ace tace kota aikata yasa suke kiyayyewa juna

hakan don sanin halin gidan yawa.

Koda ta kira suka gaisa take tambaya a karo na farko tun bayan barin gidan da yaya su salma hjy ?

"Su salma na lafiya dazun nan suka shigo shiyan nan ita da Sa,id kinsan shine abokin wasanta ai ina jin"

hjy hafsatu tana korasu suje gida.

Katseta tayi da fadin nikan Dije meye gaskiyan zancen nan ance kina gidan kanki a yanzu zaune dama

ashe kina da gida kaduna ba a sani ba ?

Wallahi Allah kinsan a baya muna cewa an muna sherine ba iyakan dukiyan baba ke nan daya bari ashe

hadin bakin su yayane tun lokacin an raba komai tsakanin mu shine ya hana aimun bayani ashe ?

Sai daga baya yake sanar dani yadda abin ya kaya yake fada min gidana na nan a nan kaduna mai part

hudu shina samu rabona a lokacin ya hana a fada min ne don sanin halin malam da sukayi.

Bari kedai hjy abin nan yai min dadi a yanzu sosai ga kwanaki naso in sayar ai don lokacin bansan gidan

ba da auren hindu ya taso amma ya hanani yanzu ga abin yai min dadi sosai.

Ina ganin indai Allah ya nufa insha Allahu bana ina cikin masu sauke farali da yardan ubangiji don an

biya min makka zan tafi bana din.

Makka dije tace insha Allahu hjy in muna da rai da rayuwan ganin hakan zan tafi sauke farali yaya ya

cika min da sauran kudina zan tafi .

Ai shine nace ko wanan mutumin zai yarda in dauko salma dashi yusuf in dawo dasu wajena nan suyi

karatun kwarai don akwai makaranta nan kusa damu mai kyau ?

Karki soma kema kinsan ba zai yarda ba don dama wani dama yake nema da zai mayar maki da

martanin hakan a yanzu don haka kada ki soma zancen yaran nan.

Sunyi haka kamar da kwana biyu yaran suka shigo part dinsu kamar yadda suka saba shigowa jefi jefi

komai dan uwan yayiwa yarinyar na mugunta hjy Laraba ta fito tana masu fada.

Anan take lalashin yarinyar tana fadin salna nakoyi waya da mamanki ashe zataje makka bana bari kuka

ta sayo maki riga kinji ko bakison rigar makka ?

Dariya inna mairo ta kwashe dashi tana fadin makka banzane hjy laraba a daiyi sunan kudin amma

wani abin ai yafi karfin mutum dai ?

Allah makka zata bana insha Allahu indai ubangiji ya nufa muna cikin masu rai da Dije za ai makkan

bana din nan tace an biya mata zata tafi.

Wai da gaske kike ko wasa haba dai zan mata karyane din bata kusa kome zakiko soma don makka ai

ba gidan wasa bane in suna karyan arzikin su wanan karon kan sunyi karya kan.

To Allah ya kaimu aga mai karyan cikin mu tabawa hjy hafsatu amsa ta juya zuwa part dinta ta barsu a

wajen ana cecekuce a haka inna halima ta iso wajen ta samu labarin itama.

Da yamma da maigidan ya shigo take fadin ashe mijin hjyne malam bana zaka dogayen riguna har ka

kyautar kamar zai tafi ya tsaya yana tambaya wa zaije makka ?

Tace yaya mama yaya dai matarka mana ance an biya mata makka zata tafi bana shiru yayi na maimaita

kalman makka a bakinsa kafin yace to Allah ya kai mu mugani din !

Ta amsa da amin tana fadin wani fitan ka kaucewa waje ashe alherine wani lokaci don ita kan yaya

wanan abin alheri ya zamo mata yanzu don sai alheri keta bin rayuwanta ko yaushe .

Har yakai kofan daki zai shiga ya dakata tare da juyowa yana fadin Ko zaki gwada ki ganine ko kema zai

"zamo maki alherin ,?"

Tace ni a suwa masu shi ai sun gwada gashi muna ji muna gani yaja tsoki yana fadin zancen banza

zancen wofi kawai ?

Halima ki kiyayyeni a gidan nan akan zancen Dije jallabiyance ban taba sakawa ba kome da zaki kawo

min maganan banza a yanzu inta iya ta tare a can har abada mana ?

Ya shige dakinshi a lokacin gwaggo Asiya ta soma magana kasa kasa tana zage zage tana fadin waya san

abinda akeyi a kadunan har da tara kudin makka haka amma bata bari mijin yaji meta fada ba don kar nata ya sameta itama .

Haka rayuwa yayi ta gangarawa har tafiyan ya soma sun kasa kunne suji ance mama din ta tafi ko tazo

"don tafiya sai aka ji shiru kwatsam kanwar mama mairo tayo mata waya tana fadin ashe matar gidanku tazo saudiyane itama gamu nan madina tare dasu ai ashe ta kaduna tazo ita ,?"

Aiko gida ya dauki zance kwaaaaaa baifi kwana biyu ba da sukaita dariyan zolaya sunawa masoyan

mama sheri wai har da jakkai an gama jida amma ba mama a cikin tafiya ?

Kunji wai ashe Dije na maka gashi can sun hadu dasu Safiya a madina makkan ma sai