Chapter 20 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

mikata ga hukuma ba ka bari a taushesu a basu hakkuri yartace fa duk

yadda kake ganin kaine uba itama uwartace tana da hakkin hakan ai akan yarta ?

Hadizatu ki ba kanki hakkuri ina mai tausaki ki kara hakkuri ki dauki hakan a kaddaran yarinyar nan don

Allah zancen nan ba sai anje ga hukuma ba dije mu duba bayan mu aiwa juna ragowa don Allah ?

Shiru tayi kanta duke kafin ta dago tana fadin ina son diyana baba tunda har ankai ga soma samun

haka don ba a ganin idona a kusa.

To aban diyana gidan nan dai ba dawowa zanyi in kara zama ina kumsan bakin cikin safe da marance ba

har ciwon zuciya na neman kamani na sunnu don haka a ban diyana su koma kusa dani in duba abina a can ?

Karya kike wallahi baki isa ba dije baki isa ki daukar min diya zuwa wani waje da babu tarbiya ba babu

tsarona a cikinsa in ban isa ba aiga wace ta isa tayi yadda takukeso da yar kuma kana goyon bayanta don kana tsoronta ?

Anyi tsoro din in haka kike tunane nace ki tafi ki barsu a nan ne dama ya kara fada cikin jin haushi to

"shike nan tunda mu bamu isa ba kai Audu ku tafi shari,a saita bawa mai gaskiya gaskiyanshi ai yanzu idan sunje gabansu."

Baba adaiyi hakkuri baba ibrahim ya fada yace kai salisu kayi shiru muji abinda baba zaice har yayi

shirun ya sakw fasin don gani salisun mahaukata zan dauki yara in danka maki ?

To kaji ku bari suje gaban hukuma kada na yanke hukuncin da bai mashi dadi ba nan gaba ashe salisu

haka kake zuciyanka kuma na banzane tunda mace ta shige gabanka mama sharifa ta fada a hasale zaiyi magana baba Audu ya tareshi da hannu.

Tau yanzu dai duk gaku ga kuma yan uwan ita Dije a zaune har ita niba zancen daukan diyane a gabana

ba a yanzu donshi da duk inda yake ai Allah ke raya abinsa dama.

Wani wuya ko dadi bashi ke kashe daba amma irin wanan gardaman da kuke sonyi yanzu akan yaran

shine manya sukace ba a gardama kan diya kan fili kan gida don sai anyi hasaran rayuwa a tsakani .

Ni babban abinda ya dameni duk ba wanan shirme da kuka dauko bane a yanzu abinda nake sonji kai

Alh hassan matsayin auren Dije dashi salisu nake son sani a yanzu ?

Dan gyara zama kawu yayi kafin ya soma magana yana fadin to ai gata a gabanka baba nima abinda ke

raina ke nan muji meye matsayan aurensu yanzu don kowa yasan matsayinshi ?

Hakane ke dije na fahinci ba zancen dawowa dakinki kikeyi ba a yanzu zancen a baki yarankine a kusa

dake ?

"Hakane baba don gaskiya zamana a gidana da nake yanzu tare kuma da yan uwana da sana,ata yafi"

min kwanciyan hankali tunda zaman a nan yakiya a tsakanin mu yaban takardana in kama gabana shike nan.

"Assha Dije saki ba karamin abu bane kin sani mu a nan gidan kuma bamu da dabi,an sakin mata hakana"

gaskiya hakkuri za ayi a duba zancen nan aga meya dace ayi tunda akwai zuria haka kada kubar yaran nan a cikin maraici don Allah ?

Nasani kowa kuma duk mun sani kinyi hakkuri iya hakkuri abinda tun farko nake lurar dakai kenan ko

wani lokaci maraye kada akai wanan matakin kaji gashi har sanadin yarinyar nan yasa yau aurenka yana rawa akan sakacinka.

Abindana saba fada maka dagani saikai ko wani dan uwaka a wajen tare damu zan maimaita makama

a yau idan ka bari yarinyar nan ta suboce maka ba karamin hasara zakayi ba ?

Aiya sani don ko yanzu yaga zahiri banga abin tsayawa jayayya ba a nan wallahi tace dai ta gaji da zama

a nan cikin iyalinka kana tozarta ta da diyanta wanda kowa yasan hakane fa salisu abinda ta fada gaskiyane ?

To sai ka zaba a yanzu idan kaga baka iya sakinta sai ka barta can ko kuma kai Alh hussaini a duba

zancen nan agani a sama mata wani gidan nan kusa cikin gari inda zata zauna da iyalinta shike nan a wuce wajen inya ranan girkinta kaje ka samesu a can a huta wanan zancen haka baba Audu ke fadan hakan kai tsaye.

Amma dai yaya kasan banda zarahin gida biyu a yanzu gaskiya in tana hakkuri tayi ta dawo dakinta ta

zauna da yan uwanta in kuma batayi to nikan banda halin gida biyu kowa ya sani ?

To bata takardanta da yayanta ta kama gabanta tunda ta barmaka din amma ka kasa rikewa sai yayyun

yaran nan ke dawainiya da kannensu.

Ina yaro zai iya rika yaron dan uwansa din Allah gashi a karshe ankai ga abinda ba ason akai har

yarinyar nan tana batun rasa rayuwanta ?

Shiru falon yayi na dan lokaci kafin tsohon ya dauki zancen yana fadin watau Audu zancen saki abune

mai nauyi fa ba a sanin nauyi da girmansa sai bayan an aikata hakan.

Auren soyayya yaran nan sukayi na nagani ina so yanzu kuma abin ya koma haka sanadin yarinyar nan

Asiya data shigo masu rayuwansu daga baya.

Wanda dama abinda nakewa maraya gudu kenan ga auren a lokacin bai gane hakan ba yanzu in sakin

yaga yafi mai sai ya saketa din gata dai a gabanmu ta kwashi yayanta tatafi Allah ya raya yara dai sunsan gida ba sai an nuna masu ba.

Amma ni gaskiya banson zancen sakin nan wanda naga ku yan uwan ita Dije shi kuke bukata a yanzu ga

yar uwarku wanda a karshe hakan zaita haifar da matsala don haka a dai duba don Allah akwai abinda yasa kuka ina hana a aikata hakan a yanzu.

Baba zan ari bakin shi salisu a nan in ci masa albasa dashi kan hakan ita dije yanzu zata tafi da yaran

wajenta.

Da ita wanan da akace za a karbi sauyin asibiti zuwa zaria kaga hakanma zaifi masu kusa sosai inyaso

daga baya sai a zauna a kara sulhuntawa aga yadda za a tsara abin tunda zancen yazo da sabani haka ina ganin hakan zaifi amma zancen zuwa hukama don Allah ajeye ayi hakkuri hakan.

Badon baba yaso ba dole zancen manyanshi akabi akan mama zata tafi da diyanta gaba daya wajenta

tunda gwaggo Asiya ta iya aikata hakan ga yarta a bayanta basai hukuma sun shigo ciki ba iya wanan zasuyi kadai su huce mata zuciya a lokacin.

Amma wallahi Alh Audu banso ka yanke zancen nan haka ba aidaka bari aje ga hukuman yasan abinda

suka aikata da matarshi babbane ?

Mama sharifa ke fadin haka tana mikewa tsaye shiko ya taso mata aka taushi ransa na tafasa yana

hadiyan zuciya suka shiga cikin gida yaran futu futu dasu Aziza na girki waina gida saiga iyayyen nasu sun shigo.

Mama sharifa ta dubeta tana fadin ke dauko hijjabinki ki hado kan yan uwanki kuzo mu tafi don Allah

babu ko gaisuwa ga mutanen gidan .

Da sauri yarinyar ta fada daki tana tayar da yaran dake barci itama ta fada dakin saida hawaye ya zubo

mata don tausayin yaran ita salma a kwance wai bata da lafiya tana fama da zazzabine kwana biyu.

Haka tasasu gaba zata fita gwaggo Asiya dake zaune ta tsare Aziza din ta kala batace mata ba sai inna

halimane ta leko tana fadin hjy kece ashe kika shigo eeh tare da yan uwa muke nazo tafita da yaran nan ne.

Tafiya kuma ta tambaua cikin mamaki tace eeh halima zasu koma hannun uwarsu kafin a karasa kashe

muna su a nan sunbar maku gidan naku sai a zuba ruwa kasa ashe ina shike nan kuma ?

Aikuwa dai za a zuba din asha son ko yanzu sunan Asiya yakai inda Asiya bata sani ba aiko nayi kokarin

raba icce da kasa har sanyen shi.

Kaico bakikoyi abin kwarai ba don dabaki fada ba in alheri kikayi ki saurari yadda Allah zaiyi dake kuma

bamu da boka bamu da malam ga Allah dai muka dogara shine kuma zai share muna hawaye insha Allahu.

Inkun zalunci dije a gidan nan Allah ya gani idan itace ta zalunceku haka yana kallo saukin abin hisabi

yana hannun ubangiji dai bari ganin kinci albarkacin tsohon nan dasu Alh Audu a yau to ga Allah muka barki saiya fitarwa yarinyar nan da hakkinta.

Jin hayaniya yasa baba Audu shigowa yana tambayan ya akayi Allah yasa inna halima na nan har Asiyan

ta soma fadin haka kawai ta shigowa mutane da gadara tana zagi.

"A,a Asiya ba zagi ga zancenta muna magana kika tsoma baki kina fadin kin fisge ice da sayensa kin kai"

kin isa har inda baki sani ba to kaji ko kaji kin samu matsala babba Asiya kin dafa kanki da kanki a gidan nan don zagi girbe abinki komai dadewa kuwa.

Aka dai lalaba suka kwashi yaran suka fita dole baba yana kallo wanan ne mafarin tasowan mu a wajen

mahaifiyarmu aka rabamu da gidan ubanmu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/27, 9:19 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Haka suka nemi transfer zuwa asibitin zaria don a duba Fadila wanda a wanan zuwan da mama tayi

tsoho yasa yayanta suje su ganta a gidan kawunsu.

"Ba zatace bataji dadin ganinsu a lokacin ba don a gaskiya babu wace za a duba a ce tayi sa,an daki"

cikinsu don jikinsu bai nuna hakan ba a yadda yake nuna amarci jikin amaryam.

Tare da gwaggo Harira suka zo don ita tsoho yace ta rakosu su gaida uwarsu akuma kaisu su duba yar

uwarsu kafin a tafi da ita .

Ba wani sakin fuska ga hindu da mama tayi saidai ga farida da take dan zolaya su kansu sunga canji

sosai tare da mahaifiyar nasu ayanzu.

Don canji irin na rayuwan walwala da sake dayin abu cikin natsuwa a gareta yanzu don ba irin lokacin

da sukai zaman gida ba.

Alokacin dako yaushe yanayinta ke nuna damuwa a tare da ita dama yayan nata saboda rashin walwalan

da babu a zuciyarta lokacin.

Koba komai sunji dadin ganin hakan a tare da ita yanzu don har mama din ke fadin farida tsarabanki na

nan tafe idan mun koma zan aiko don kayan sunzone bayan wutowana nan katsina.

Saina koma zan aiko maki dashi yan uwanki dai gamu nan a tare zamu tafi dasu yanzu ayi ta hakkuri

don Allah a zauna lafiya da maigida kuma .

Ban fahinta ba hajjaju mama Shari tadago tana fada a yar uwar nata naji kina fadan wani zance mara

dadi ita hindu nata tsaraban fa ?

Wace yar uwarta ta tambaya cikin wani yanayi na ko in kula itama No no no look khadija karki soma inji

ko in gani wallahi ?

Ko a bayana naji kin nunawa yarinyar nan hindatu wani hali khadija zamu samu matsala babban dake

wallahi.

Matsala kuma wanda da baki tsamani ba a rayuwanki wanan wani kidadancine haka kike kokarinyi ga

yarki ?.

Idan kin mata haka ina kike son ta dafa taji sanyi ko dadi a rayuwanta bayan gunki ?

Su wayan can kike son ta koma bi ana mata wullakanci kamar bare ko kome ?

Shiru tayi a lokacin don fahintar zancen da mama shari din keyi ba wasa a cikinsa a lokacin iya

gaskiyarta take fada mata har cikin zuciyarta .

Ta karasa da fadin noses act har yanzu kina da sauran gidadancin da salisu ya shayar dake daya ajeki a

ciki ashe ?

Kada ki ja yarki a jiki yanzu ki fahinci damuwarsu shi yana can yana jan yayan kishiyarki kekina watsar

da naki ?

Da mamanmu tana raye shi salisu har ya isa ya mayar dake haka nasan ko aurensa ba zakiyi ba balle

har hakan ya faru dake ?

Kama kanki wallahi tun hakan baidawo ya dameki ba nan gaba ina zan yarda da wanan akidar banzan

kaddarace tana kan kowa balle yanzu meya rage kuma ba abinda ya saura tunda tana dakinta zaune.

Wanan yasa koda zasu tafi a lokacin take tambayansu zancen kudi da sarka data gani a daki farida tayi

"kasa da kai tana fadin nina ajesu mama kudin da Alh Rufa,i yaba yayace da zasuyi sallama dashi da sarka da wanda ya ban na daure na jefa bayan gado."

Dama ina tunanem koda zaki tafi kin gani kada wani ya shiga dakin yin bincike bakya nan ya gani ya

dauka ashema kin gansu kin dauka ?

Suna wajena tabasu amsa faridan tace tun lokacin daya bata yaya ta miko min ina tsoron kada kiyi

muna fada.

Shiyasa na boye ban fada maki ba ta danbdubeta kamar zatayi magana sai kuma take fadin zata yi

"tunane a kansu koda za a sayo masu wani abu su fara sana,a dashi"

Har kofa suka rakasu suka tafi bayan sun kara masu nasiha akan zamantakewan aure da zama da

mutane suka bar gidan zuwa asibiti duba yar uwarsu.

Shiko baba bayan tafiyansu yan uwa suka zauna dashi inda baba Audu ya lurar dashi manufar hakan

don matukar bai bata diyan nan a yanzu ba za a iya samun gagarumin matsala don gun hukuma zasu tafi kuma sai hukuma ta daureshi shida Asiya wallahi.

Baidai so hakan ba amma ba yadda ya iya ya mike ya shigo ciki da Asiya din ya fara cin karo tana karasa

"girki tana korafi dakin nasu da aka bari wagale ba,ako rufo ba ya jawo kofa yana daurewa da niyar inya fita ya samu key yasawa kofan."

Ai daka bisu zaifi hakan sauki muryan Asiyace ke fadin hakan tana duke ya juyo ya dan dubeta baidai yi

magana ba don ransa dake matukar bace a lokacin.

Bayan ya rufe zai tafine inna halima ta fito tana fadin shike nan sun koma wajenta ko zasu dawone

malam ?

Su dawo ku karasa mata diya da ukuban ku tunda kun kasa rike minsu cikin amana ai gara ta dauki

abinta taje dasu kusa da ita.

Angama dashi mana keko ai ba azo ba saida aka shiryowa hakan ina zai samu sukuni yanzu tunda yayi

tozali da rabin ransa yau aiba zakiji amsan kwarai a bakinsa ba kuma ?

Asiya ki iya bakinki kada kiga na kyale kicigaba da dankara min magana wayaja hakan inba ke ba ?

Data tafi tabar diyanta tabar maku gidan ai batace tana son yaran ba da farko saida taga kina batun

kashe mata su daya bayan daya tazo da zancen a bata diyanta.

Tunda nema nake in kashesu sai a kashe min nawa mana ai tana da kudi tasa a kama nawa a kona a

rama mata bansan ranka ya baci ba dani saida ka fada yanzu da bakinka kaima ?

Abinda aketa fada ke nan cikin gidan nan da gari kasheta nasoyi dama to a kashe din aina isa mutuwa

nima bashi ke nan ba kodai an kasheni diyana basu taba zama wurin Dije ?

Eeh gaskiyane aka fada ashe Asiya yau burinki ya cika Dije da kowa nata sin bar gidan saiki zuba ruwa

kasa kisha ko kiyiwa Allah sujadan godiya ga hakan daya faru tunda burinki ya cika.

Kin nakasa mata ya kin kuma fitar da ita gidan har yayanta sai ki zuba ruwa a kasa kisha ga gidan nan

sun bar maki saiki wala yadda ranki keso yanzu a ciki.

Saiko inyi tunda naga bayanta ita da gidan kuma saidai ta kalla don sai gani sai hange yanzu a gareta

daba kuna kurin kun itace uwar gida mai garke ta baza maka diya mata a gida ai gashi yanzu diyan suna neman haukataku ?

Kai Salisu fito gidan nan muryan baba Audu daya tsaya daga kofa yana bawa dan uwanshi umurni kan

ya fita ya kyaleta ya kara fadin ba kasuwa zaka bane ?

Can nayi yaya fito ka fice gidan nan ya fada yana nuna mashi hanyar fita dole ya fasa shiga dakin ya

nufo fita din ta sake fadin ai da a kaini kotu din a kulle insan kaji dadi ?

Asiya ko kina ganin kinfi karfin hukamane wai da ba a iya kaiki kotu din to yaya zai shigo yana son

hawana da fada don diyanshi sun tafi tare da matarshi zai dora laifin a kaina ?

Na dai fada maki kika kara maganan a kaiki kotu zan nuna maki karyan iya shege wallahi don yar dan

uwana yatace wallahi wallahi ko ji nayi kin furta hakan a bayana Asiya saina shigo mota nazo garin nan nakaiki ga hukuma an daureki na shekaru masu tsayi kuwa.

Shiru tayi don tasan zai iya hakan gareta tunda ya fada ganin tayi shiru ya sake fadin zancen banza da

wofi kawai zaki zo kinawa mutane iya shege shi salisun ai ya daukan maki hakan har kike ganin kamar ba a iya komai dakene a gidan nan.

Moi tayi bata kara tankawa ba ya juya yabi bayan baba yana fada saida suka fitane ta soma kuka tana

fada wai zata bargida tunda tagane ba a sonta da mijin nata ita gara tabar gidan yafi tunda akanshi yan uwa nason hade mata kai sun zabi bare da ita.

"Suna isa kaduna asibiti akakai Fadila nan ma gado aka basu suna masu fadan meyasa ba,a kawota"

asibiti da wuri ba har ta fara kangarewa haka.

Sabon jingan kudin aiki akayi dasu don zasuyi mata aiki a mikar da jijiyoyinta da suka samu matsala a

cewan likitoncin.

Kawu yaje gidanmu da kanshi yayi masu bayani halin da ake ciki kan abindake faruwa da yarinyarsu

hankalin kowa ya tashi dajin hakan da irin kudin da za a kashe ga matsalan yarinyar.

Saidai kinsan matsalan gidan yawa irin namu na hausawa dole hankali yana rabuwa biyune irin haka

dan a take munafukan gidan ke fadin ba sunce zasu iya kula da yaran ba ?

Don me da suka san bazasu iyawa tun farko basu barsu katsina ba suka kwashesu zuwa kaduna don

karya nan tsegumi ya dan fara yawo sun dauka abin wasane