Chapter 21 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

da farko.

Sai bayan da tsoho ya tara kowa daya dace maza da mata na gidan yayi masu bayani abindake gudana

a nan gwaggo Asiya cikinta ya duri ruwa don baba Audu dai bai gari a lokacin amma a wajen taron anyi magana dashi a waya inda kowa yayi shiru ana sauraren bayaninshi da yake fadin.

Zan dawo baba dolene mu mika Asiya ga hukuma da kan mu don kaga case din nan ba zancen da zamu

rufe bane tun da abu yakai haka girma ?

Zan kamo hanya a yau don wanan kudin dole sai munkai ga gwaunati an taimakemu gashi naji ance

ashe zancen yakai ga hukuma an samu wanda ya basu labari an fitar da zancen ance ba fadawa tayi ba kamar yadda muka fada matar babantane ta turata cikin wutan.

Wa zai fada kuwa banda dangin uwarta suka fada mana gwaggo Hafsatu ta fada cikin zafin rai aikuwa

ya hauta da fada yana fadin ke hafsatu ki iya bakinki duk kika jefa kanki a cikin case din nan banda kudin da zanja da gwaunati akanki ?

Kuka kawai akaji gwaggo Asiya dake gefe zaune tunda tsoho ya fara bayanin ance sai an fita da Fadila

kila asibiti waje zuwa india ta tsure dan ba karamin magana bane ashe ta daukowa kanta.

Da kuma baba Audu ya soma magana a waya ya kara tayar mata da hankali tasan za ai haka irin yadda

ta rufe ido taciwa baba Audu din da kowa na gidan mutunci a nan ta soma fadin.

Wallahi baba Alu banyi da wani niya a zuciyata ba sherin shadanne kawai ya kawo haka idona ya rufe

dukanta kawai naso nayi ashe tana kusa da wuta a lokacin.

Zance ya dau zafi kowa bai goyi bayan abinda tayi ba suka nuna a mikata ga hukuma shine daidai a

gaban kowa ta kira Iya mai zogala tazo gashi za a kaita wajen yansanda.

Da kikayi me za a daureki kan zancen yarinyar nan ne mama aina fada maki zancen ba karami bane

Asiya koda nake abina nasan irin iya shegen da nakeyi ba irin naki na haukan nan ba ?

Salisun da kikeyi donshi me auren salisu din ya karaki dashi yanzu banda hasara sai diya da kike haufo

mashi cikin talauci ni banga abinda wanan bakin auren ya karaki dashi ba wallahi.

Ga mazan arziki sunzo nemanki kika nace keda hafsatu sai salisu don kawai ku bakantawa matarshi ita

ta tsalake ta rabu da wahala ta barki a ciki yanzu ai ba ita kukaiwa takaici ba kanku kukayiwa yanzu ?

Wayan na hannun baba daya wafce a hannunta tana don ya bata amsa sai zuba tsohowan keyi kowa ya

"kasa kunne yana saurarenta a lokacin sherin waya ke nan jama,a."

Inda ta kare da zancen tana fadin saidana fada maki cewa ki rabu da yarinyar nan da yayanta tunda

bata tare maki komai ba amma kikaki gani zuwa gidan ai yanzu.

Baba ya amsa da Allah ya kawoki inna muna jiran zuwanki ai ya kashe wayan a hasale ya juya gareta

yace Allah ya isar min Asiya da kika sakani cikin wanan ukuban ina zaune lafiya da iyalina daga ke harsu hafsatu da suka matsa min a lokacin ?

Wuri ya rikice da surutu zance dai bayi dadi ba baba Alu ya tsawata akai shiru ya soma fada sosai dasu

yace a jira baba Audu ya iso a lokacin maizogala tazo da kuka tana ina Alu din yake ?

Aka nuna mata suna ciki da yayanshi maza shine tashigo ta zube kasa tana fadin haba Alu ku dauki abin

nan da kaddara don Allah ?

Hannunka baya rubewa kayar Asiya dai yarkace kamar yadda shi salisu yake danka ayi hakkuri a duba

lamarin nan a san abinda za ayi don Allah ?

Haka dai aka aje zancen sai baba ya iso gwaggo balarabace ta kira mama tana sheda mata duk yadda

akayi da irin tonon asirin da sukayi don baba har maizogala ya kalla a gaban kowa yayi mata cin mutunci akace .

Da taimakon Allah aka samu ba sai anfita waje da ita ba aka samu akai mata aiki sun dade mama tana

jinyar yarta a zaria inda matan gidan namu ake rabawa tsakanin gwaggo laraba da gwaggo fati da matar baba ibrahim suke musayan zuwa taya mama zama da yar nata asibitin ta bangaren mahaifin mu ke nan.

Shima mahaifin mu din wanan abinda sukayi dasu maizogale na tonon asiri yasa ya fahinci kuskuren

daya aikatawa iyalinshi kan sonkai daya biyewa ita gwaggo asiya sukai ta musgunawa mama a zamansu.

Haka yasa yake neman wanke kanshi a yanzu wajen kowa don ya kula ba karamin kuskure ya aikata din

ba sona tsakani da Allah mama ta nuna mashi.

A lokacin ta sadaukar da rayuwanta akan aurenshi ta mikamai ragamar komai har daduk abinda ta

gada a hannun iyayyensu akan a rufawa juna asiri a zauna lafiya tare.

Wanda bai duba hakan ba daga baya da ita gwaggo Asiya din ta shigo rayuwanshi saiya rufe ido yana

cusgunawa mama da sunan ai bashi yace ta bashi dukiyanta ba ganin damanta yasa ta bashi don kanta ai ?

Yanzu kuma da yake son wani rayuwa haka ba dalili bane da zata hanashi jin dadin rayuwanshi a yahaka

don kudinta yana hannunshi.

Ita gwaggo Asiya kancewa mama anci kudinta anci banza kuma ba abinda zatayi kan hakan aiba rokoki

yaya yayi ki bashi ba kece dadin aure yasa kika damka mashi kudin gashi kuma bai hana ya dankaro maki kishiyoyi har biyu ba dole kuma ki zauna damu din.

Izgili dai irin haka takan fadawa mama din idan fada ya hadasu a gidan abu kamar an kafeta a lokacin

sai dai tayi kuka ta share hawayenta tayi hakkuri ta zauna hakana don yara wai ?

Sai gashi yanzu data soma shakan iskan yanci ta kula baba yana son ya soma shishige mata irin a koma

irin da din nan ita kuma a yanzu tana ganin ta wuce ajinsu dagashi har matar nasa bata iya rayuwan da akayi a baya yasa take kawar dakai gareshi a lokacin.

Yayin da muke zaune a gidan mama Shari dan maman mu da bata gida a lokacin saboda wanan abin

saida suka share wata shidda kafin aka sallamosu suka dawo gida.

Duk da sun dawo gida a lokacin muna zaune a hannun mama din har tsawon wani lokaci don kula da

mara lafiyan da mamakeyi.

Haka kuma zaman mu a hannun mama sharifa mu kanmu yana muna dadi don tankar mama muke

daukanta gatan dama mama batayi muna ba shi muke samu a wajen mama shari yanzu.

Ana cikin haka kwatsam yaya hindu ta dawo gida akan ba zata koma gidan mijinta ba wai ashe tun

bayan kaita cikin rikici suke shidai badashi ba saidai gwaggo hafsatu dake mata cin mutunci ta uwa ta uba akan ba zasu zauna da yayan mama harsu biyu saboda an raina su.

Ko wanan dawowan gudowa tayi inda ba a san data gudu ba a can katsina an dai nemeta an rasata

akace shine tayo kaduna wajen iyayyenta mata.

Tayi kuka muna tayata tana ikirarin a taimaka mata ita dai ta bar gidan ba zata zauna da Sulaiman ba

bata dai son shi bata kaunarshi gaskiya.

Take fadawa mama shari don a nan ta sauka bata nufi wajen mama ba zuwanta da kwana ukku su baba

harda tsoho suka biyo bayanta suka sameta a gidan mama shari don bata jema gidan maman mu ba dake unguwar kawo nan ta nufo wajen mama shari din.

Tana fitowa ta samesu a falon alfarma na gidan an cika masu gaba da kayan abinci amma sun kasa

tabawa da kuka mama shari ta fito masu da ita a lokacin.

Hindatu ashe ba zan sallamaki daga cikin yarana ba kuwa wanan abin bakin cikin da kike jawo min

cikin yan uwa dame yai kama don Allah ?

Ka sallamata saboda me da kake fadin bakin ciki metayi na assha yanzu kuma kai don Allah salisu ku

dinga bin komai a sannu tun gida na fada maku idan yarinyar nan tace batayin auren nab a hakkura hakana don Allah kada akaiga bata goma daya bai gyaru ba shi baba na fada mai kuma ya fahinceni.

"Ke zaki komawa sulaiman koko a,a ki fada kowa yaji don ba zamuyi maki dole akan abinda rayuwanki"

bai so ba kinji ko ?

Haba yaya ta nata za a bi ko hankali batafi farida ba haka taga yar uwarta tayi ko ta taba jin wani abin

asha da farida tayi tunda aka kaita gidanta ?

Mamanmu Dije ke fadan hakan ga hindu din a hasale ita kuma mama sharifa ta karbe da fadin wayasa

bakinki a zancen nan yanzu ko in tashi tunda ke kika haifeta ?

Baikai hakaba yaya matsalan hindune yake daure min kai wallahi don Allah ku dakata haka don a hanya

muke tafiyan nan na karfin hali mukayi mukazo don munbar ibrahim babu lafiya a gida .

"Zaki koma ko a,a ki fada muna jinki amsanki muke jira tayi kasa da kai tana gimjin kuka ya daka mata"

tsawa yana fadin ko badake nake magana bane kin kyale sai kuka keki cika kunnuwan mu dashi.

A daidai lokacin muka shigo gidan mun dawo daga school saida muka shigo falon sosai muka shedasu

yusuf yai wajen baba da gudu yana fadawa jikinshi.

Gaidasu mukayi da zuwa muka shige ciki nikan dai tsoron mahaifina nakeji banga fuska tun farko a

gareshi ba haka kuma abin na taso dashi nima ban kaunarshi har rain.

Dan nema mahaifinka kagani kawai anan baba Alu yake fadan hakan ga yusuf din bayan an natsa

sukaci gaba ba zaki koma ba ko muna son kai karshen zancen nan a wajen nan din hankali ya zamo waje daya.

Ta girgiza kai alaman ba zata koma ba sai waya akaji baba Audu yanayi da sulaiman din yace kai

sulaiman gamu a kaduna mun biyo matarka data bar gida ta kuma ce ba zata koma gidanka ba don haka sai ka furta mata saki Allah yasa hakan yafi zama alheri gareku baki daya.

Ya amsa da amin baba na saketa saki daya idan ta gama ida tayi aurenta Allah ya bamu alheri ya fada

cikin tausayi shike nan ai komai ya kare baba Audu ya fada bayan ya gama sakawa dan nasa albarka ya dago yana fadin.

Wallahi baba ban taba ganin yaro mai saukin kai da biyayya irin wanan dan ba da anyi magana biyaya

zai nuna a take koda abin bai mashi dadi ba kuwa.

Kuka babanmu yasa ya mike ya fita inda hankalinsu ya koma kanshi kaiko Salisu addua ya kamata kayi

bakasa kuka ba kamar karamin yaro kuma ?

Itama hindu din kuka takeyi sosai a lokacin nasan ganin baba yana hawayene saboda ita yasa ta soma

kukan itama hakana.

Baba Audu yaje ya dawo da baba falon yana fada dashi sosai inda yake fadin haka ba yana nufin

munbar hindu bane komai mukkadar ne daga ubangiji saidai abinda nake son ki sani shine ?

Ba zamu kamunci dogon zawarci ba a gareki dakin gama ida tunda mijinki yace akwai idansa a gareki to

ki gagauta kawo muna miji mu daura maki aure dashi.

Da fatan kinji mena fada kada in nuna maki halina don ina ganin sunan nawa kawai kike ji baki san

halina ba tunda bamu taba haduwa dake ba ?

Haka dai sukai yan jawa bansu suka mike aka bar wajen bayan tsoho yasa mama ta tambayaeta bata

"da ciki a jikinta tace a,a daga haka sukai sallama suka tafi ."

Tun lokacin da mama shari ta tsawatawa maman mu tana zaune falonne kawai tankar bata ciki ranta a

bace cikin takaici da bakin ciki da tashin hankalin abinda yar nata taja masu.

Tasan wani faifai za a bude nata idan sun koma da wanan mumunan labarin mara dadi dolema a zageta

duk da ba ruwanta a ciki amma laifin ba zai wuce kanta ba dai ?

Wai khadija meye matsalanki da hindu yarinyar nan tunda na buga maki waya tazo garin nan Khadija

baki leko gidan nan mun taru munji matsalan yarinyar nan ba ?

Yau khadija yaran nan ina kike son su dafa suji sanyi haka kikaga inayi da yaran nan don Allah a yau fa

khadija yaranka sune abokanka sune aminan ka bayansu duk duniyan nan ko uwa daya kuke da mutum watarana sai yayi hassadanka .

Dago kai tayi ta dubi yar uwar tace kwarai ina fada maki a wanan zaman ko da muke ciki sai kiga uwa

daya uba daya amma ana hassadan juna da bakin ciki abin zabban munya kuma dole dai ana tare.

Idan kinga dama gata nan sai ki nuna baki sonta a cikin yan uwa in kuma kinga dama kina iya jawo

yarki a jiki ki nunawa duniya yarkice fa ita har gobe kuma kaddara yana kan kowa a duniyan nan.

Don haka yanzu zabi ya daura gareki kuma kina dai ganin yadda nake dasu Nuratu har wa yan nan

kananun naki dake gidan nan yanzu.

Sai kaja yaro a jiki zai sake dakai yarinyar nan tunda tazo gidan nan na fahinci tana cikin damuwa amma

bata da wanda zata fadawa taji sanyi a duniyan nan.

Kece ya kamata ki zauna da ita kiji meya damuwanta data kasa kwantar da hankali ta zauna dakinta da

yaron nan da iyayye suka hadasu amma khadija kin kasa hakan why kike son zama bagidajiyace wai ?

Anty ya wuce akan wanan mutumin mai mata ta kwallafa ranta ta kasa tsayar da hankalinta a waje

daya ta zauna da dan uwanta ?

Fine idan shi takeso tagama iddan ta in an bincika baida matsala sai ta turoshi wajen magabatanta a

daura masu aure ko ?

Anyi auren so an samu matsala balle na kiyayya is hard fa ka iya zaman rayuwa da wanda baka so ka

zauna hakana a cikin dauri tunda ba jahiliya period muke ba yanzu ko wani bawa da kaddaransa a duniyan nan.

Naso ace ta zauna tayi karatu ta kara ilimi amma kuma kinji abinda wanan babban nata ya fada dokan

da yasa mata na tana gama idda ta kawo mijin aure ta aura.

So yanzu is left for you nadai fada maki gaskiya naso in rike ta a gidan nan wajena amma zata biki

saboda ta kama maki kula da yarinyar nan mara lafiya dan kwana biyu ba kuma hakan na nufin ba zata zo nan ba idan taga dama zata iya zuwa nan ta kwana biyu zanyi magana da yaya yasan abinda ake ciki.

Shiru mama tayi don jikinta yayi sanyi da maganganun yar uwar nata wanan zama da sukayine ya

samawa yayan namu sauki akan matakin mama din a lokacin dole da zata tafine mama shari ta hada mata kayan yaranta su Nuratu don ta samu na sawa takaisu gida da kanta a ranan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/28, 10:24 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

A bangaren iyayyen mu maza sun koma gida da bayani mara dadi don an tabatarwa mutanen gidan

cewa baba Audu ya raba auren yasa Sulaiman ya saki hindatu din.

"Hakan yayiwa mutane da yawa na gidan zafi don ba,aso hakan ba akwai kuma yan bamgaren su gwaggo"

masu cewa haka yafi don ba a boye ba gwaggo hafsatu tace saura ita wanan ke nan shima ya dawo ya saki tashin ai suje su samu uwarsu su kama bariki tare .

Subbahanallahi gwaggo Hari dake zaune ta fada ta juyo tana cewa hafsatu din asha hafsatu na dauka

yayan salisu ai yayankine ?

Wanan ba uwarsu kikewa fatan sheriba ai mu duka wanan abin ya shafa tunda dai yar dan uwanmune

ita hindatu kina magana kamar dama kinsan da zancen za ai sakin ?

Kinji nace ba diyanshi bane abindake raina na fada tunda ba fin wani sukayi ba a gidan nan in kyau suke

takama dashi akwai mata kyawawa a gidan nan da za aura mashi wanda suka fisu.

To ba dai a gidan nan ba kaf kuwa indai zance kyau ko wani abu ake nufi kedai a bar zancen Allah yayi

ba matarsa bace ita din da zasuyi rayuwa a tare.

Ooho dai na fada saura wanan mai surar kamar yar tsana na tsani in bude ido inga yar nan mai shishigin

tsiya a gabana shima zai dawo ai ya sameni yazo tura mata diyanta can su sameta .

Nifa bawai wani abuba wallahi na tsani yaran matan nan gaba dayansu sai gashi baba yayi wanan hadin

ganbiza din wai yayan mu baba ya dauka yabawa yaran nan a matsayin matan aure a gareshi.

Ina ruwan yara da fadanku wai hafsatu abinda nake son ki gane yaran nan yayan yaya salisune fa

hafsatu ko yayan yayane fa ina ruwana da wasu yayanshi can wai Hari ?

Shiru gwaggo harira tayi bata kara magana ba a lokacin saidai a kasan zuciyanta tana tunanen

abubuwa da dama game da zancen da hjy hafsatu din keyi a lokacin tun kafin takai karshe taji tana fadin

Nifa Hari tun lokacin da yaya salisu ya so nuna muna wai shi din wanine a gidan nan na tsaneshi kuma

akan ita Dijene ai lokacin ya samu gadonta suna ci tayi kyau tayi ja duk kyan mutum ya tsaya kusa da Dije a lokacin saiya raina kanshi.

Itama wanan jakan na zata ai intashiga zata iya da Dije dinne ashe duk cika bakine na bazan bata iya

komai da ita nida naso tayi fitan wullakanci a cikin gidan nan sai gashi ta kasa duk irin shawaran da muke

bata amma wai Asiya ta kasa fitar da matan nan saida nata ya hadata da mijinta fita salin alim a gidan nan.

Imani ya cikawa gwaggo hari zuciya lokaci guda taki yarda ta nuna bata goyon bayansu don taji komai

da take shiryawa kan iyalin dam uwan nata don irin su gwaggo hafsatu balaine a waje sosai.

Akarshe ta fahinci don kawai suna shiri tsakaninsu da gwaggo larabane wanan abin ya