Chapter 22 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

hau dije haka

gaskiyane kuma kowa yasan Dije ga hjy laraba kaida ta tsaya a gidan bata irin na sauran matan gidan aganta da wanan yau gobe a ganta tare da can waje daya tatsaya a cikin gidan zamansu kuma na rufawa juna asirine don ita gwaggo larba asali kawar su yaya gambontace tare suka taso dasu haka mijinsu baba

Audu abokin kawun mune hassan wan su mama.

Gwaggo hari a part din mahaifinta take zaune mijinta rasuwa yayi haka bata taba haihuwa ba yasa

bayan rasuwanshi ta dawo gida cikin yan uwa ta zauna dole tana kallon draman da ake zubawa a gidan.

***** ***** *****

Sosai sulaiman ya shiga damuwa bayan kashe wayansu dasu baba din abinda zai iyayi kenan a lokacin

amma bai zata yaji baba na furtawa a fili abinda sukayi a wayan ba ya dauka su iyayyene zasu gyara zancen sai yaga abin ya tabbata a haka saki ?

Ya matukar son hindu a ransa shiyasa duk fada da zagi da cin mutuncin da mamanshi hafsatu take

kiran wayansa tayi mai akan ta bashi umurni yaki bi yana biyewa Ahmed ko ta fahinci shiya zugashi akan kada ya saketa a lokacin .

Yakanyi kokarin kare dan uwanshi akan ba haka bane su baba yake duba yadda zasu dauki abin amma

ta bashi lokaci ai zai sallameta very soon a cewarshi.

A ranan data kirashi tana saka mai albarka kan jin ya saki hindu har take fadin saura shi wanan mara

kunyan guda Ahmed dashi kadai na haifa dana mutu da bakin cikin dan banzan yaron nan a gidan nan.

Tayi ta babatu Ahmed din yana kwance yana jinsu a kusa dashi don dakinsu daya donshine komai a

tare sukeyi a sokoto din da karatu ya kaisu bawai sunje zama da baban nasu bane haka kawai.

Ya fahinci mamanshi hafsatu a cikin zancenta kamar shi din makamine yanzu a gareta zataita juyashi

yadda taso don ita tayi mai komai a baya duk da sai iyayyensa sun saka mashi hannu a cikin wasu lamuransa dole kusan ma in badon baba Audu ba saidai yace iyayyen da suka haifeshine suke kula dashi

kawai sunan dai yana hannun mama hafsatu dine kawai bata iya mai abin naira daya daga jikinta wanda

zaman itace maicin riba dashi kawai ke nan.

Yana jin lokaci yayi da yana gama karatunshi zai lalubi yan uwan mahaifansu a jalingo ya ganosu su

sansu shida yan uwansu donshine sauran yan watanin yake son dasun zana jerabawansu ta karshe jalingo din zai nufa ya gano gida tunda iyayyensu sunki kaisu amma sunsan wajen.

Baijim zai iya tsayawa ya daure irin abubuwan nan da yan uwan mahaifiyar nasu ke masu shida yan

"uwansa kullum gara ya fita ya gani ko sa,anshi yana wajen katsina ?"

Ko yace ya zauna a nan ba zai juri rashin hindu din ba a yanzu a zuciyarshi yana fatan ace hindu din

nada cikinsa wananne kadai yasan iyayyen nasu zasu yarda ta dawo dakinta sucigaba da zamansu koda kuwa zaman zai dore ga haka zaici gaba da hakkuri da abinsa hakana tunda yana sonta din.

Da wanan tunanen Ahmed ya dafashi yana fadin aina fada maka tun farko kada ka aikata hakan yanzu

ka fahinci komai ko ?

Mama tana son amfanine damu akan matanmu don ta musgunawa mama Dije ta kan yayanta na rasa

me matar nan tayiwa mama da bata kaunarta yanzu dai kaji abinda ta fada ai game da ita ko ?

Bata damu da damuwan mu ba san kanta kawai tasani ita ta biyawa kanta bukata koda kuwa hakan ba

zai muna dadi ba don haka duk abinda zatayi ba zan taba furta sakin farida daga bakina ba don yarinyar batayi min komai ba sai zalla gimamani da takeyi a matsayina na wanta mijinta kuma.

Kayi babban kuskure a kawai kace su barta harta huce tadawo dakinta kaga dole su fahinci kana son

matarka dai anan .

Amma Ahmed kaji irin warning din da mama takirani tayi min idan nayi haka sai taga ina son in mata

butulcine kuma a yanzu dana girma ?

Ko da kayi din indai mamace hakane zai biyo baya tsakanin ku kadai san halinta ba saina fada ma ba shi

habu ai yanzu ya kama kanshi da ita tunda yayi nisa a karatunshi tayi korafi kuma ta barshi iyakansa ya shigo ya gaida ita shike nan tsakaninsu a yanzu.

Bamu daya da habu kasani habu yarone haka kuma ita innan mu ba zata yarda in ce zan dauke kafana a

wajen mama ba bama zan iya hakan gareta ba gaskiya.

Sun kai wani lokaci suna tatataunawa kan abu daya karshe suka mike don su fita bawani shirin arziki

sukeyi da mama karima ba matar babansu kuma duk saboda gwaggo hafsatune haka yake kasancewa a tsakaninsu.

***** ***** *****

"Ginan gidan ya matukar bata sha,awa anihin gidan an ginashi da sunan iyalin marigayi dan kwarane da"

niyar sune zasu dawo nan su zauna daga katsina suyo kaura zuwa kaduna sai Allah bai nufi hakan garesu ba kuma a lokacin suka dai kare rayuwan a katsina.

Wanan kuma dalilin da ita auta dije tagajeshi shine basu bata tarkace ba sai yaya hassan dinsu ya saye

tarkacen data samu a lokacin akaiwa gidan kudi ya biya mata aka hada da kason kudinta a ciki shine dalilinda har mutane basu sanda zaman wanan gidan a gareta ba a kaduna din sai wanda ta samu a katsina aka sanda zamanshi kuma daga baya ta matsa zata sayar suja jari da mijinta dole dai aka yarda ta sayar da gidan daga ciki kawu hassan din ya ware wasu gudin aka sai mata fili babba saurab kudin ya mika masu taba baba sun dai dauki lokaci gaskiya yana juyasu kafin bakin mutane yaiwa kudin yawa suka

lalace dama gasu abin gadone filin dai yaya nan har yanzu shikan an hanata sayarwa.

Hindu tayi mamakin ganin wanan babban gida haka mallakin mahaifiyarsune wai lalai kakansu ba

karamin dukiya yayi a lokacin ba ke nan ?

Shiyasa yanayin mahaifiyar tasu ya fita daban dana kowa a gidan duk da ana cewa ita din aurene

mukkadari ya hadasu da baban mu din a lokacin .

"Amma ba sa,an aurensa bace ita wanda ance sun dama gaskiya tun soyayyan makarantace ta hadasu"

har yakaisu ga aure don anso aki yarda da farko amma data dage saishi a lokacin mahaifiyarsu dake raye tace a barta tayi abinta tunda tace saishi.

Ni dai sai ince haka muka taso bamu san dadin kakanin ba a rayuwan mu don babu ko daya da muka

samu a raye cikinsu .

Banda zalla tsagwama da kyashi da hassada yan uwan uba da muka taso a cikonsa babu komai na jin

dadin yan uwa inba dawowan mu kaduna ba din nan a yanzu da yan uwan mahaifiyan mu ke nuna muna kauna sosai.

Sun shiga gidan suka samu fadila tare da makwaciyar mama data bari ta kula mata da ita a zaune suna

cin abinci a kwano daya suna hira sukai sallama suka shigo.

Fadila na daga kai ta hango hindu sai kawai ta fashe da kuka tana fadin yayan mu ashe zan ganku

kuma da sauri hindu din ta karasa wajen yar uwar nata ta rugumeta tana kukan itama.

Mama shariface ta katsesu da fadin yau ga tsiya zaku sakamu kuka haka don jin dadi bayan sauki yazo

muna maza a share hawayen nan karna ji kukan nan kuma.

Kafin hindu din ta dago tana goge fuska da gefeb gyalenta tana fadin sannu fadila mun shiga damuwa

"ainun ko farida ba a bari muga juna da ita gwaggo hafsatu tayi muna iyakan ganawa a tsakanin mu sai sa,a muke haduwa wani lokaci idan mun shiga cikin gida gaida baba ko wani abu ya faru."

Kallon bana fada maki ki natsu ki fahinci meke gudana ga diyanki ba mama sharifa tayiwa mamanmu a

lokacin inda ta dora da fadin ban fahinci tayi maku iyaka ba da junan ku ?

Wallahi mama matar nan bata da imani idan naji muryanta sai naji kamar kasa ya bude inshaga don

nasan ba alheri bane ke kawota gidan.

Kinga mike ki shiga da kayanki wancan dakin idan kin huta sai ku gyara ku koma ciki keda fadila kome

tayi tayiwa kanta ai Allah ya raba dai yanzu faridace ta saura a ciki kuma itama Allah ya fisheta kaidinta mama sharifa ke fada.

Ta mike ta dauki dan jakar kayan da mama shari dinta hada mata tashiga dashi dakin a lokacin shari din

ke fadawa dije kingani ko mena fada maki dama ?

Bari anty aina fahinceki sosai wallahi Allah ya bar zumunci amin ta amsa tare da fadin zancen cikin nan

zanzo ranan monday inkaita asibiti ayi test don kinsan halin mutanen ku da sheri kada daga baya ciki yazo ya bullo wani magana kuma ya shigo ciki tunda ba fada muna gaskiya yanzu zatayi ba.

Ta dan jima suna hira da yar uwarta kafin ta mike bayan sunyi sallah magariba ta tafi saboda dare da

yayi tace zata koma wajen yaran ai yisuf yaban mamaki mama ta fada tana mikewa tsaye.

Ke na rabaki da danamiji ai shi ko dafashi akeyi a can gidan ubansa yafi mai ko ina haka diya maza suke

ai karkiyi mamaki wallahi.

Dan nema da an barshi ya tafi ai da kafansa zai dawo gidan nan tunda Asiya ba fasa halinta zatayi ba ai

tana kyala ido taganshi sabon fitina zata fito dashi kuma mama dije ke fadin hakan ga danta yusuf da yaga mahaifinshi ya lake wai zai bishi zuwa katsina ya koma gida.

Kinsan lokacin da yace zai tafi irin kallon da salisu yayi maki muka hada ido dashi yayi saurin kawar da

kai dariya sosai taba mama wanda dama hakan suke son gani gareta ba irin yadda a kullun take takure gwanin ban tausayi ba a cikinsu .

Wanda dama hakan suke bukatan suganta ta dawo hadizanta na baya da suka santa ba irun yadda

takoma daga bayan nan ba bakin cikin namiji na neman ya kashe masu yar uwa.

Allah nasan zai so hakan da yaron yayi khadija yasa na kai idona a kanshi ta sake kwasan dariya tana

fadin ai shima yasan irin haushinsa da kikeji a yanzu.

Wallahi banson butulcine khadija ki duba fa yadda nake da Salisu a baya amma akan wanan bakar

matar nasa yar iska ya juye yana son kawowa mutane rashin mutunci waishi ga dan iska ?

Mutuminkine fa anty taja tsuki tana fadin a baya ba yanzu dayace bai san mutunci ba ai mun raba gari

dashi shima ya sani yaushe rabonsa da kawo kafansa gidana ?

Baida kunyane yasa yazo yau ai don shifa na canza layin waya nake amfani da wanan dana dawo

saudiya dashi dole don ya soma kirana yana min dadin baki tunda baida kunya.

Kika yarda dashi dai ke kika jiyo ai don matukar ba rabuwa yayi da Asiya ba tsiya bai karewa gidanshi

tunda ba daina halin tsiyarta zatayi ba donkr tashigo gidan dama saboda a rabaku.

Saida suka gaji da magana kafin ta bude mota tashiga zuwa gida don dare nayi sosai koda taje ta samu

yaran sunyi barci sun kwanta a falo suna jiranta.

Itama mama tashiga ta samu hindu da Fadila suna hira sosai ta leko tana fadin ba zakici abinci bane ke

hindun ta dago tana fadin nakoshine mama .

"Ke har yanzu kina nan da zama da yunwa ke nan ko a,a mama ina cin abinci ai gwaggo mariya idan"

banci ba fada take min sosai fadin haka da tayi yasa ta dan kallo yar nata kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya zuwa nata dakin a lokacin.

"Kinyi sa,a mama ta sauko da yawa yaya ranan da mama ta bugo mata waya kinzo tayi fada sosai tana"

cewa da nan kika fara zuwa dakin koma a ranan baki kwana a kaduna.

Amma sai naga kun dawo nan tare da ita kuma dasu baba sukazo daxun har nace shike nan bamu

ganin juna zaki tafi na zata zaki bisune ai yau din ya akayi suka barki yaya ?

Mun rabune dashi ya sakeni ta waya ya fadawasu baba dazun da saurin kanwar tace saki kuma yaya

garin ya haka ya faru kuma ?

Zai wuce mamanshi tace ya sakeni da an kirashi ita gwaggo Mariya din yaya wace gwaggo mariya

gwaggo hafsatu dai ba ita bace mamanshi ?

Duk hiran da sukeyi a kunnen mahaifiyarsune inda hindu din ta soma ba fadila labari a takaice irin

yadda hafsatu ta sakata gaba da zaran ance baba Audu baya gari fadila har Allah Allah nakeyi ya dawo don in huta da ukubanta.

Haka zata debo wanki harda na wasu ina ganin har kayan gwaggo Asiya tace na wanke nagoge masu in

aika mata dasu idan nagama.

Kuma mahaifinku yasan da hakan muryan mamace ta jefo masu tambaya daga falo inda take zaune din

tace ina zai sani koya sani kuma me zaice tunda gwaggoce ?

Maganan anty shari ya tabbata ta fada a fili ta kara fadin ita farida fa tace farida bata da matsala ance

ko cikin gida tsoho baya bari ta shiga idonsa na kanta duk ya dawo sai ya tambayeta idan bai ganta ba kinga ba dama tayi mata wani abu ke nan.

A ranan mama ta kara gaskanta basu kaunarta da gaskiya tunda har hafsatu ta iya yiwa yarta haka ta

bita har nasu lungun tayi mata cin mutunci saboda ita ?

Haka yasa ta mayar da hankalinta kan yar nata tana kara gyarata don gaba tunda a cikinsu dama itace

bata shaku dasu ba sosai.

******* ******* ******

Bamgaren farida kuwa tayi kuka har tagaji da jin labarin sakin auren yar uwarta tayi tunane gaba

dayansu ita kadai ta rage a katsina yanzu gaba dayansu sun koma hannun mahaifiyarsu.

Kamar basuyi rayuwan katsina ba a baya tana bakin cikin ganin yadda kofan mahaifiyarsu a yanzu ya

koma wani iri har tarkace ake tarawa a kofan nasu yanzu.

Wanda kamar gwaggo Asiya din ta mayar da wurin store dinta wajen aje kaya don ma dan dogon dakin

nasu yana rufene gam da kwado da kila har ciki zata dinga aje kayan nata .?

"Amma baba yasa kwado ya rufe dakin takan shiga wani lokaci da safe kafin ya fita wajen sana,anshi ko"

kuma da dare idan ya dawo ko kuma idan cikin matan nasa basu da lafiya ko yara idan inna halima ta aika mata saita shigo bayan haka bata yawan shigowa wajensu din don ba ama bari ta fito kaida kai .

Tsohon kan bata hakkuri yace Farida kisa a ranki watana saidai labari idan Allah ya budawa mijinki zaku

tashi daga gidan nan ku koma muhalin kanku.

Wanan zamane na dan lokaci kukeyi a nan ki kara hakkuri kinji farida naso auren yar uwarki ya dore da

sulaiman don sulaiman yarone mai halin dattako kingashi to irinsu ake kira da dan baiwa .

Amma ina hakan bai yuyu ba don sulaiman ba mijin rabuwa bane shi yarone mai hakkuri da sanin ya

kamata ga komai .

Idan yana wanan maganan takan fahinci irin bakin ciki da takaicin da tsohon kanji kasan ranshi game

da mutuwar auren yar uwata din.

Takan shige daki tayi kuka saboda zaman kadaicin daya kamata a yanzu inda shiko tsohon ya shiga

sawo mata abu ke nan yana tambayan metake so yaya akayine meya faru sai yaga ta dan sake zai barta .

Dawowan gwaggo harira gidane takan dan samu abokiyar hira suka dan zauna suyi hira taji labarin

abindake wakana cikin gida wani lokacin a bakinta don ita tana shiga tayi hira da matan gida.

Rabuwan aurenshi da hindu baifi wata daya ba yazo ganin gida tare da baba Audu donsu duba jikinshi

nanne maman ta sameshi da wani zance na daban akan tana son ya neme jamila diyar gwaggo Asabe.

Bama shawara ta bashi ba kamar umurnine a lokacin tayi mai da ya nemi ita Jamila din dake zaman

diyarsu dukansu diyan mata zallah ke nan a cikin jikokin gida Usman mai rasuwa kakansu ke nan.

Gwaggo Asabe itace babban diyar maizogala da ta haifa a gidansu gwaggo hafsatu mijinta daya rasune

"tayi wanka ta auri kaninsa kuma baban su gwaggo Asiya ke nan anan maizogala ta shigo da sabon nau,i duk ta watsa masu gida don wanan mijin baikai wancan na farkon zafi ba a wanan lokacin ta dito da true"

colour dinta a gidan.

Da mamaki gwaggo harira ta dawo tana tseguntawa iyayyenta abin dake faruwa inda iyayyen sukace

tabar fadi kada farida taji hankinta ya tashi.

Abinda bata sani ba Faridan idonta biyu a lokacin kuma taji komai da suke magana a kai a lokacin .

Inda da farko hankalinta ya tashi sosai dajin zancen abinda akw shirin yiwa yar uwarta din saidai a

lokaci kurciya bai bari taji haushi sosai ba ta dauka ai yar uaartace tace bata son shi ai ?

Don haka ko sunyi hadin ma ba laifi bane ai suje suyi tayi hakan ba laifi bane don sunyi itace tama

fitowa gwaggo da zance tana tambaya ashe yaya sulaiman Jamilan gwaggo Asabe zai aura kuma ?

Cikin mamaki gwaggo hari take fadin har zancen ya fito fili ashe zancen gidan nan dai ba a boye yake

ba hakane ke dai ance ita zai aura kuma yanzu wai don a izawa hindu da mahaifiyarku haushi bama za a bari ta cika idanta ba za ai mai auren debe takaici wai ?

Allah yasa matarsace ita din Faridan ta fada tace to amin zasu dai kasawa yaro hankalinsa kuma gida

biyu tunda bai gama tararin rabuwansa da matarsa ba suce kuma aure zasuyi mashi yanzu din.

Ita dai da ake wani abu a gidan don taji takaici ko taji din hakan bai damunta tunda har lokacin haushin

yar uwarta take ji a ranta.

Shiko tsoho koda zancen yazo mashi baiyi wani mamaki ba illa iyaka fatan alheri yayi masu yana

murmushi sai yanzune yake fahintar wani abu kan fitan hindu din gidan.

Dole akwai wani abu a kasa da su manya tun farko suka kasa fahinta game da yarinyar duk da zargine

don yasan hakan zai iya faruwa shiyasa yasa masu dokan yabaci a lokaci ita da yar uwarta.

Saidai a yanzu ya jefa ayyan tambayansa da anya fitan yarinyar nan gidan sulaiman kuwa ba hadin

bakin yayansa bane kuwa anya yayi abindaya dace yayi a lokacin kuwa kan tsaron auren da shine sanadin hadashi ?

Da gwaggo mariya ya fara zama ya yaketa Allah ta fada mashi meye matsalan tashin hankalin yarinyar

nan tunda alama ya nuna sun fara fahintar juna da mijinta ai ?

Tunda da bakinsa ya furta akwai iddanshi akanta haka na nufin yana kebewa da ita wani lokaci ke nan ?

Gwaggo din da farko bata so fada mai gaskiya ba amma kuma ya hadata da Allah dole ta zauna ta dan

fada mai irin matsin lamban da Hafsatu keyiwa yarab daga hindu din har shi