Chapter 23 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

sulaiman din.

Amma gaskiya mariya baki kyauta min ba kin cuci yaron nan kinko san nauyi abinda aka aikata mashi

kuwa ?

Kina ganin zai yarda daku duk da yarone mai hakkuri sulaiman yana da fahintar duk shirine kukai mashi

haka don kucinwa wani manufan ku akanshi ?

Hakkuri take bashi kawai a lokacin yace ba komai ta tafi ya fahiinci inda zancen nasu ai ya dosa ita da

danta duk anyi amfani dasune a lokaci daya.

Haka kuma yasa ya zauna da sulaiman din shima bai boye mashi komai ba duk yadda sukayi da

mamansa hausatu ya fadawa tsohon shida Ahmed.

Yace yaje Allah yaiwa rayuwansu albarka inda ya juya wajen sulaiman din yana fada mai saura kai mai

sunan manya kaima nasan nan da kwana biyu za asa ka sako min jikata ai ?

Baka taba jin hakan insha Allahu tsoho Ahmad ba raggo bane da zaiyi raki ko yaji tsoron barazana ni

duk wani barazana kafin aiwa sulaiman ni aka farayiwa shi a gidan nan ai.

Ran tsohin ya baci sosai inda ya zauna da baba Audu da baban mu akai zancen ya nunawa gwaggo

hafsatu yasan shirinta duk abinda ta aikata yaji komai .

Borin kunya ta soma mashi tana fadin don kawai an kawoma gulma saboda anga zamu fashewa yaro

haushi da takaici za a fito da wani zance haka kuma ?

Gwaggo laraba ta dafewa wai itace taje ta tseguntawa tsohon zancen to ko baba Alu bai isa hana

wanan aure ba ai tunda jamila dai ba jikansa bane ai.

ZAINAB IDRIS MAKA

"[11/30, 8:14 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Zaman kaduna a yanzu har mun saba dashi tun muna dan abubuwa na yanayin mu na can yanzu mun

sake jiki mun soma mantawama da asalinmu.

Hakasu yaya hindu idan kin ganta ita da fadila da aziza anty Nuratu sun wayar dasu sosai anso yaya

hindu ta koma makaranta amma furcin baba Audu yasa dole mama sharifa ta kyaleta a gida.

"Wajen shekara daya ke nan yanzu hindu din tana gida har lokacin kuma ba,a bari yaya farida tazo gida"

ba a yadda muka jima wai cikine da ita a yanzu.

Hjy laraba tayowa maman mu waya akan tazo ta duba baba ibrahim dake fama da jiki don jikin nasa

yayi nisa sosai a yanzu wanan yasa aketa zancen zamu katsina amma bamu san rana ba.

Mama bata mayar da hankali muje katsinan nan ba sai da kawu ya bugo mata waya akan ta kwasomu

tazo damu katsina mu gaida dan uwan babanmu dake jinya.

Ankai ruwa rana sosai da sukace idan taje mu sauka a gidan a nan inda muka taso a nan zamu sauka sai

mama bata yarda ba hakan kuma plan din mama shariface da kawu.

Sunce tunda aurenta bai mutu ba salisu yaki sakinki dije bamu son ayi kotu dashi yaranku shidda dashi

yaran nan idan sun taso zasuga bamuyi masu adalcin ba nan gaba kiyi hakkuri kibi wanan shawaran tamu don Allah.

Mama shariface da maman mu a falo suke wanan zancen baki da makusa khadija kin waye yanzu ko

wani nada niyar kawo maki iya shege baiga wurin hakan ba a gareki.

Kije da shirinki kuyi bukin sallah ku a can da yaran nan suga gida a gansu su san har yanzu kina da

kirkinki da suka sanki dashi a baya kodon tsohon nan da farida .

Kinga masu cewa babu aure a tsakanin ku kuma yanzu zasu tabbatar zaman ki a nan kusan shekarun

nan da auren salisu a kanki kuma baki watsar ba.

Haka yasa da zamuyi tafiyan ba karamin kaya mama ta labta a bayan hilux din mijin mama shari ba

yadda in mun je ba zamu wahala ba ba zamu nema a wajen wani ba kuma a gidan.

Shigan dare mukaiwa katsina ana sallah saura kwana guda a lokacin za ai bukin babban sallah sai ji

kawai mutanen gida sukayi ance ga Dije nan da yara sunzo .

Hinduce a gaba tashigo rugume da wasu kaya fadila na bayanta sukai sallama su inna halima dake aikin

sanwa na dare sukaji sallamansu sun shigo hindu din take mika masu gaisuwa tana nufar dakin mu da inna ina wunin ku.

Wacece ganin ta nufi dakin mu kai tsaye ta bude baki tace hinduce tana ba gwaggo amsa data leko

daga dakinta don jin murya da tayi .

Hindu a yau gidan nan eeh gwaggo ina wuni ta fada tana kokarin budan dakin dakey din dake hannunta

lokacin inna halima ta karaso wajen tana haska mata toci duk da akwai hasken wayanta da take amfani dashi a lokacin.

Sukajiyo hayaniyan za a shigo gidan suwaye kuma tafe tare dasu maman mu muke ai gaba dayan

mune mukazo hindun ta bata amsa a lokacin a takaice.

Allah sarki inna halima halinta dai yana nan yadda yake har yanzu ko tana da kishi ko damuwa zata mai

da abu wasa ita ta juya kuma zuwa wajen mama dake shigowa dasu gwaggo hari tana fadin yau hajajuce gidan nan ?

Tafiya haka babu sanarwa wallahi haka tafiyan ya kama halima mun sameku lafiya ta fada tana maida

hankalinta wajenta sai kamshi kawai ke tashi daga jikin mama din jiya ba yau ba ke nan inji tsohuwa.

Tamike kai tsaye zuwa dakinta da yaran suka bude har lokacin gwaggo Asiya bata leko ba zakice bata

gidan a lokacin .

Mama ku tsaya mu share dakin muryan hinduce take fadan hakan a daidai lokacin farida ta karaso da

gudunta jin ance gamu gaba dayan mu munzo a bazata nan ta fada jikin mama ta rugumeta sai kuka kukan murnane kona bakin ciki a lokacin oho ?

Hinduce take fadin ya da kuka haka kuma ta sake mama ta juya wajen yar uwar ta rugumeta aka hadu

ana gaisawa da juna.

Batasi wai yaya kece haka nake gani ta fada cikin mamaki tana karewa yar uwar kallon a cikin mamaki

don ganin yadda gaba daya ta sauya ta kara jiki kafin ta koma kan fadila da sauran.

Tare suka gyarawa mama dakinta namune na yara dake manne dana mamanmu suka bari sai

washegari a gyaro don dare da yayi a lokacin.

Mahaifin mu ya shigo da mamakin ganin mu don da alama dawowanshi ke nan a lokacin yashigo yana

fadin bakin kadunane yau a gidan gaba dayan mu mu shidda muka fito zuwa gaidashi inda yake tsaye kofan dakin mu mukai kasa muna gaidashi lokaci daya.

Duk daban shiga ransa ba amma yanayisa ya nuna ya shiga wani hali a lokacin yadda yarasa yadda zaiyi

"sai wasan baki yake yana kiran sunayen,mu daya daya bayan daya muna amsawa."

Ya leka dakin yana fadin ina ita maman taku tana sallah aka fada mai lokacin tsoho ya shigo shima

yana fadin hjy dije ashe kuna hanya tafe ?

Ta idar ta shafa ta taso don samun tsohon ta soma gaidashi da sannu baba mun sameku lafiya nan tayi

kasa cikin bada girma tana gaidashi ya amsa a cikin jin dadi yana fadin kin kyauta hadiza kin kyauta da kika kawo muna yaran nan a wanan lokacin ?

"Allah yayi maki albarka hadiza Allah ya shirya maki zuri,an ki yasa masu albarka kinji hadiza kin kyauta"

"min kwarai da wanan abin da kukayi wallahi a,a zuwa haka a bazata munji dadi kwarai wallahi."

Salisu gashi can nace a dora girki su dan dafa abu mai sauki na tambaya ai akace baka dawo ba take

fadin ai baba ka barshi suyo girki da zasuci dashi suka zo mungode.

Kuma ayi haka hadiza bako yazo baici abincin yan gida ba sai nasa eeh baba ba komai kada a wahala

don Allah a shirye mukazo son karmu dorawa mutane wahala.

Ina Asiyane baba ke fada don baiga gilmawanta ba a lokacin ai tana gidan nan ne tunda muka shigo ai

bamu ganta ba na zata taje unguwane ai ?

Gani mana ina nan zaune zama kamar garin maye ina dakine ina sallah ta juya wajen mama tana fadin

sannun ku da zuwa dije saida kowa ya dubeta lokaci guda mama din tace mun sameku lafiya dai yaya yara kuma suna lafiya kalau ta fada tana juyawa wajen baba tace gani naji kana nemana ?

Yanayin yadda tayine kila yasa baba din fadin barshi kawai kai usman zo kaje gun isah ka amso masu

lemun kwalba ka kawo masu tunda ba zasuci abinci ba ?.

Shine dama kiran ai sun gani da suka shigo suka nuna basu ganni ba koni suke son in fara gaidasu oho ?

Ta juya tana fadan hakan baba din ya bita da kallo cikin mamaki badaice komai ba ya juya gun yaron

dake fadin baba gani yana fadin yawa usman don Allah karbi je gurin isah ka karbo masu kayan sanyi kaji.

Da sauri yaron ya karba ya juya da guda kai usman ka hado muna da maganin sauro a cikin kudin ta

fada daga kofanta cikin jin zafi .

To hadizatu Allah ya hutar da gajiya kinji saida safe in Allah ya kaimu kuma aita hakkuri don Allah akai

zuciya nesa munji dadi kwarai da zuwan ku wallahi.

"A,a abin arziki haka gida ya cika gwanin sha,awa Allah dai yai maki albarka hadijatu Allah ya raya maki"

yaran nan su gama lafiya ta amsa da Amin baba jeka huta idan na idar da sallah zan shigo in duba ibrahim ai donshi muka zo mu dubashi ku kuma ga yara baba ?

Kin kyauta kwarai yar albarka ko haka kawai kin mu komai wallahi Allah ya kara rufa maku asiri keda

yan uwanki kunyi komai wallahi hadiza.

Amin baba azizace tazo da sauri tana haska mai waya tare da fadin baba tsoho barina haskama kada

ka fadi ya tsaya yana fadin wacece yar nema nafiki gani garau wurin nan ai.

Ya fita mama ta koma daki tana kiran hindu ta amsa ta shiga take fadin bawa yaran nan abincin sauran

ki mikawa maman ku a rabawa yan uwanki.

Ok mama ta don cigabane zallah a rayuwansu yanzu babu zancen muku muku a garesu irin na da can

baya don ba zancen ki gansu ki kawo masu rainin wayau kuma cikin lamarinsu don komai a waye sukeyisa so cool dasu duka.

Sai lokacin uwar ta juyo ta dube salma da tun gaisawa da tsohon da mahaufisu ta juya ta shigo daki

take kwance saman katifansu da aka kayar wanda sabone fil sukazo da abinsu.

Kaita gyada tana fadin ke kuma baki tsaya kun gaisa da baba kika shigo daki kika kwanta salma meyasa

kike hakane don Allah ?

Me kuma nayi mama ta fada tana kallon uwar ta koma ta sake kifewa yadda take har uwar ta idar da

sallah ta kara feshe jiki da turare kafin tace da yaran suzo suje part din baba ibrahim su duba shi.

Sun rufo kofansu sun tafi gaba dayansu duboshi inda suka samu yana jin jiki sosai gaskiya Allah da

ikonsa ya gane sunzo din suka gaisa da mama da yaran sun dan jima a gurinshi zaune shiru yana ya gode mama na haba kai don Allah daina wanan godiyan mana ai yiwa kaine suka fito suka shiga part din baba

Audu wajensu hjy Laraba suka gaisa.

Aka danyi yaushe rabo sai bin yaran suke da kallo kafin su fito zuwa wajen baba tsoho sun dan jima a

can don yaran har sun dawo sun barta tare da baba Alu dake ja mata kunne akan gwaggo Asiya

Inda yake fadin abinda nake sonki dashi yata yadda kikazo har ku koma kada ki yarda ki biyewa

shedancin Asiya ko irinsu hafsatu a cikin gidan nan.

Kuyi abinda ya kawoku ku gama ku koma lafiya keda yaranki tsiya na nan suna hadawa game da yaron

nan Sulaiman don Allah duk yadda zasuyi kokarin iza maki takaici akan hakan kada ki biyewa haukansu a haka zasu kare yan banza marasa mutunci da kima .

Insha Allahu mama ta fada tayi mai saida safe suka fito ita da salma dake lake da hannun uwar zuwa

nasu shiyan tana zuwa ta samu hindu ta gyara wajen kwanciya tayi shirin kwanciya suka kwanta.

A sakarcin gwaggo Asiya dai tana zaune ta kasa ta tsare duk ba itace da girki ba a ranan amma ta zauna

ta fake tagani ko baba zaice mama ta karbi girki a ranan.

Saboda tasan sakacin halima sarai dan magana zai mata ta hau ta yarda da abinda zai fadi din ta bar

mama din da baba saidai taji rufo kofan mama tanayiwa inna halima dake aiki a waje sai da safe.

Kafinta sauke ajiyan zuciya ta mike ta hada abinda zata hada ta rifo kofanta itama cikin bakim ciki da

takaici bata san abinda wanan matar tazo nema duk da yayanta.

Don zuwan nasu an shamceta an mata girshi anyi mata bazata don komai bata shirya wanan bazatan

ba a yanzu.

Dijece wai ta kama haka zakice matar wani gwaunace ita ko minister don sai ki rantse ba dijen da suka

zauna aka buga kishi bane cikin wanan gidan.

Wa zata duba tsakanin ita da yaran duk da ganin darene tayi masu amma kaf dinsu tankar basuyi

rayuwa a wanan gidan ba a baya.

Ta ina zata soma da wanan matar mai naci mace kamar manya duk wani sallo da tugun kisan kishi

kisisina da kutungwila tayishi akan wanan matar amma har yanzu ba cin galaba a gareta saima abinda zai firgitata da ita kawai take gani .

Ashe koda suke haukansu suke yawo suna fadin an raba auren ta don yan uwanta sun dauketa ashe

baba munafuntarta yayi yana da aure da dije har yanzu tsakaninsu.

Yau wai malam ne ke rawan kafa akan dije gaban kowa wai asayo mata lemon kwalba ita da yaranta

suko ko oho yaushe rabonshi da basu ko sisi a gidan ?

Yaushe rabon da wani abin arziki ya shiga tsakaninsu haka ta manta gaskiya don saita kwamace a yanzu

da zaman Dije din gidan da zamansu a yanzu.

Ta ina zata fara ita ta ina zata soma da wanan fitinan a yanzu tasan akwai aiki ja a gabanta kan yaki da

wanan matar a yanzu.

Taso data fita ace ta fita ke nan ko kekowa gidan har abada sai gashi yau kwatsam dije ta dawo masu

gidan har da yayansu a matsayin kishiya kuma kishiyar da basai an fadaba tasan tayi masu nisa sai hange a tsakaninsu yanzu kuma ?

Amma ba zata yarda duniya su sakata gaba da dariya ba haka zata turza ta daure ta nuna mata har

gobe tana nan a Asiyanta data barta itace dai lamba taran gidan baba Salisu har yanzu.

Don ba wata mace da zata shige mata gaba ta hana rayuwanta shakat kamar yadda yan uwanta suke a

sauran gidajen aurensu suna damawa a cikon gida koda a wahalcene wanan akidarsuce hakan.

Tun a cikin daren labari yakai ko ina Dije tazo da yayanta kaf kuma sun sauka a gidan wanda hakan ya

daurewa da dama kai masu zato kojin cewa sun jima basu da aure a tsakaninsu sunfi mamakin hakan.

Don ba yadda za a saki mace ta zo gari kuma ta sauka dakinta a gidan mijin koda ya kasance bata da

kowa a garin ai tana neman gidan abokan arziki ta sauka har ta kare laluran daya kawota ta koma.

Amma hakan yana nufin an maida auren ke nan ko kuma dama basu rabuba yadda ake fada aurensu

yana nan da mijinta ashe inko hakane ai yan uwansa mata ke shelan hakan a gari cewa sun rabu da dadewa.

Sanin tana da gidan sauka ga yan uwanta cikin gari yasa abin ya kule masu kai harda wasu da yawa a

cikin gidan wanan labarin zuwan matan ya daure masu kai sosai a yanzu.

Washegari da safe tunda mama ta tayar damu mukai sallah muka koma muka kwanta zance mama

kamar ko a gidan ta bata barci don idan ka kwana a kusa da ita koda yaushe ka falka fitsari zaka ganta a tsaye ko zaune tana ganawa da ubangiji sarki Allahne

Ko anan ma kusan hakane ta faru a lokaci don duk falkowa nayi zanganta a tsayene tana sallah wanda

nasan akan mune yayanta sai neman nasara na duniya da lahira datake nema wajen ubangiji Allah .

Wanan halin na mama yana matukar burgeni ba ita kadai ba kuma kinga mama Shari da zaki gani kallo

daya ki dauka wayewane zallah a rayuwan to ba haka take ba don kuwa itama kusan hakane ibadane tsagwaronsa a wajenta.

"Don ko tarbiyan da zata doraki akai nlcikin nau,in addini zata koya maki komai yadda rayuwanki ba zai"

shagala akan duniya ba.

Muryan gwaggo Asiyace ya falko damu a ranan daga barcin safen da muka koma a lokacin tana fada

da inna wai ai inna bata ganta ko yaranta da yunwa ba da zata aiko mata da abincin da bata san dame aka dafoshi ba ?

Ita da yaranta dake dauke da yunwa suje suci suke da kanyan yunwa da har za a kawo masu rainin

wayau ita kan ba ita ba wanan rainin hankalin bamai kawo matashi wallahi.

Motsin da mama taji a gefenta yasa ta juya tana kallon yaya hindu tana fadin kin falka tashi mana ki

dora muna abin karyawa kafin a fara shigowa duk kunyi wanka .

Idan zaki dora iya bakin mu dana dakin halima kadai zaki dinga dafawa tace to mama tana mikewa

saida ta mike tayi mika ta soma tambaya me zata dafa ?

Dan kallonta mama tayi ta kawar da kai kafinta soma fadin idan dakin kike har yanzu wa zaki tambaya

abinda zaki dafa mariya ke nan zaki dama a kullum ?

Murmushi tayi don tasan gatsen mama cikin gyarane a garemu hakan yasa ta juya tana saka dogon

riganta na zaman gida mai dan free style ta bude kofan ta fita zuwa lokacin babama ya fito don jin sababinsu tunda farar safiya haka ya fito yana magana.

Yana fadin wai meye hakane meya faru kuma kudai baku raina zancen fada a gidan nan sallon tunda

"safen nan kuma acikawa mutum gida