Chapter 25 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

zaki diba wajenta yanzu sai wahala ?

Kinfi halimane ita data sake ana komai da ita ko ita ba mutum bace da bata kishin wani abin amma ta

danne tana nuna ba komai ta mike tana fadin ai shike nan tunda haka kace ni zanwa kaina gata a nan.

Safiyan sallah da safe kawai mukaji fitana inma ance da kokawa ba a mussu don bamuyi saurin fitowa

ba daga daki duk wanda ya yunkura zai fito mace ke hararasa ya koma ya kwanta sai salmace ta mike ta bude kofan gifan namu a ciki take da mutane dam a lokacin.

Ganin an bude kofan yasa suka juyo baba Alu ke fadin amma kunji kunya udan kunsan kunya kujita a

nan saidai tsiyan abin baku san kunya ba ku da alama ?

Har yaushe mutumin da kake adawa dashi haka zaka tsaya duban wani abinsa kaiya ance su kare ba a

san harara ba ta rufe ido ta mika maku kayan nan har gidajenku tasa kun aika wai kuma bayan haka ku wayi gari kuna rigima akan wanan abun.

Yanzu meya kawo tashin hankalin nan inna ta soma bayani tana fadin baba rainin hankali da wayaune

banso da aka kawo kayan nan danye yarinyat nan hindu ta mika min nace uwarta na barci ta bari ta fito ?

"Tace min a,a aina gifane mu gyara dai bari su tayamu na aikawa Asiya tace nuce makwadaiciya ni abun"

duniyansu ya dama a kawo mota da kaya gidan nan ba abinda ya shilleta naje na karata da kwadayina dama kuda wajen kwadayi yake mutuwa.

Mun gyara nakaiwa yaya Dije daki tace naje dashi wajena na aje can muke aiki ai ba ruwanta da zancen

"girkinmu nakaiwa malam na nuna mai yace gashi nan dai ta kwashe komai ta fada a bainan jama,a"

Takare da fadin wai da safen nan ina udar da sallah saiga roba Asiya ta aiko wai na raba na bata kason

ta nacewa yaron ya wuce ya ban waje .

Matan gidan da iyayyen mu maza suka amsa da kwarai tacigaba shine ina zaune ta fado min daki ta

soma bincike tana kokarin wai sai ta raba na mike na kwada mata mari biyu masu kyau a fuskanta fada ya kaure muna.

Kin mun daidai baba tsoho ya fada gobe ta koma kai takakka ga wani in takamatar jidali da rashin

mutunci ?

Gidan nan keda hafsatu da badon kowa ya iya bakinsa ba na tabbatar da babu kowa a cikinsa yanzu

saboda masifan ku kun bata muna sunan gida kuna kokarin raba kan kowa a gidan nan tir da rayuwa irin naku wallahi.

Dama tunda na gansu jiya suna kusku zan rufe gida nasan ba alheri suke shiryawa ba a lokacin baba ni

meye laifina yanzu magana takawo min na bata hakkuri fa ?

Hafsatu meye matsalanki da hadiza gidan nan yau dai ki fada min dalilin wanan abin kin sani sarai

hadiza kanwar abokinane koda aka kawota gidan nan kuma komai na mutunci hadiza nayiwa kowa gidan nan.

Da hadin bakinki hadiza da yaranta yau suka bargidan nan badon bata son mijinta ba don kawai sheri

irin naki da kuke kulawa a gidan nan na fada maki matukar sunanki ya fito akan zuwan nan nasu kukace

zakuyi wani sheri zan saba maki kin dauka hakan wasane ko to ga abinda kika kulawa sakaran nan Asiya sai kije ki hada kayanki yanzun nan ki bar gidan nan indai zamana kikeyi a wajena .

Salati aka saka yace tasani na fada mata na kirata a waya itace na farko danajawa kunne kan zuwan

bayin Allah nan gidan nan .

Haka kuma a sanadiyar auren farida da Ahmed keyi yayan ita hadiza yanzu haka ya samowa Ahmed din

"aiki a Abuja da gama karatunshi sulaiman ne nasa bai fito ba don jerabawanshi da aka rike a jami,a shima kuma ina da tabbas idan an sake zai sama mashi din kamar yadda ya samawa dan uwanshi ."

Amma duk hakan baiyi ba hafsatu sai kinbi ta karkashin kasa kinsa anyiwa matar nan rashin mutunci

don kawai a tozartata ita da yaranta me kike nema wanda yafi wanan mutanen da suka taimakawa danki hadiza da yayanta sun gama maki komai don ki sani.

Idan ba don hassan dayake taimako naba a yanzu da muna kai hakane inba wani ikon Allah tasan komai

baba iya shegene kawai na mugun hali irin nasu dasuka gado kawai sukewa mutane tasss yai mata bai

raga mata ba a gaban kowa kuma ya kafe akan sai tabar mashi gida a ranan sallah ko ya bata mamaki

ranan.

Kowa wurin bai bata gaskiya ba daga can baba ya fito daki yana fadin saidai su tafi su biyun duka amma

hafsatu bata fita tabar Asiya a gidan nan yau ?

Ita Asiyan ce tatsaya yiwa mutane rashin mutunci gwgg hafsatu bin bayan mijinta tayi don su koma

part dinsu suyi a can .

Haka zancen ya tabbata don kuwa baba ya nunawa gwagg Asiya halin maza ranan har saki ya shiga

tsakani da kowa yayi mamakin hakan.

Banda baba Alu donshi tsohon a gaban kowa ya nuna dama haka yake so in suna ganin gida ya zama

nasune yasa suke muzantawa matan yan uwansu bare to gara a nuna masu sun din ma ba kowa bane duk abu daya sukewa bauta a gidan aure.

A haka aka dora girki rayuka ba dadi sai maganganu gwggo Asiya ke sakewa wai tasan dama mama ta

shiryo matane tazo da gadara cikin gidan .

Itama tasan hanyar ai zata nunawa mama nasu wasane don saita rabata da gidan gaba daya ko diyanta

ba zasu kara waigen gidan ba balle ita .

Ba wanda ya tsaya kulata da aka dawo sallah tsaye baba yayi saida ta fita don har lokacin bata bar

jidalin ba har aka gama abinci aka kwashe inda aka raba aka a aikawa mutane yadda aka saba ana zaune ana cin abincin maizogala ta iso gidan da jidali.

Tana fadan maganganu marasa dadi akan mama kamar zata doki baba takuma juyo ta dawo kan

mama da jidalin har daki ta shigo nan mama ta kasa daurewa ta tanka mata da iya ina jin nauyinkine kan abu biyu zuwa ukku.

Na farko kin haifeni na biyu kuma ke uwace a gidan nan na ukku kina uwar abokiyar zamana.

Amma duk baki dubi wanan ba iya na taba maki wani mugun kallo ko mugun abu mara kyau duk abinda

kukeyi ina hakkuri to kada ki dauka ban iya daukarwa kaina matakine kece dai kika shigo har dakina da cin mutunci yanzu ko mama na fadin hakan ta mike tsaye tana fadin.

Hindu rufo min kofan nan yau inkai iyakan mutanen nan karshe don sai tsohuwar nan ta kwana asibiti

tunda bata da mutunci.

Hindun ta mike itama mai zogala ta juya tana fadin kakarai ki rufe kofa dani ki maisheni zaune naji ance

kashi guda gareki inkin taba mutum sai kinwa jilinsa lahani tayi waje kamar zata kife .

Nan ma kuma din bata tsira ba inna halima ta hauta da sabani sukai kanta ta fita baba Alu ta hadu

dashi ya soma tsinanta da Allah waddai akan wanan haukan da sukeyi akan kishi.

Yana fadin yarinyar nan ta dawo ke nan ba inda zata zama daram a cikin yayanta makiya Allah kawai

kunso ta wullakanta ku nakasata ita da yayanta Allah bai yarda ba ya koma kanku.

Don baki da kunya kin taso wai kinzo fada akan yarki to ita Allah ke kata yaki idan zakija da ikon Allah

ne kuma sai mugani yau ?

An yanka dabbobi sai suya aketayi a cikin gidan dole mama ta fito suna aikin da wasu na gidan sunayi

ana shan abubuwan sanyi da aka tanada har yara ba wani hayaniya ko tashin hankali .

Sallaman su Ahmed ne da sukai shigowan dare garin shida sulaiman don har yamma suna sokoto saida

suka gama abinda sukeyi suka kamo hanyar gida .

Sun shigo gaida mama inda sukai kicibis da hindu dake zaune tana shan minerals tana ganinsu ta shiga

dan kame kame tana gyara dankwalin gyalen data daura akanta lokacin take gaidasu.

Wai har dake akazo ashe Ahmed ya fada yana kallonta take fada mai tare suka tagaida sulaiman din

daya wani dan maraice a gefe daya.

Mutanen mamane na asali suka soma gaida ita da zuwa ana ya bayan rabo nan suka jima suna dan hira

suke fadin basu san gidanta ba a kaduna sun shiga sau biyu amma basu san waje ba.

Kwatance tayi masu sukace zasu nema insha Allah Ahmed ya juya wajen fadila yana mata ya jikin tare

da tambayanta karatu take fada mai poly suke ita da aziza yanzu yace good naji dadin hakan sosai wallahi na yusuf ya tambaya akace ya fita.

Daga kofa salma ta tsaya tana gaidasu ya juyo yana fadin kai badai salma bace haka mama filawa kike

ba yaran nan ne haka ta fito tana gaidashi ya amsa bata tsaya ba ta juya zuwa ciki sun jima suna hira da mama din kafinsu tafi.

Gidan ya koma normal da part din mu dana baba Audu anyi sallah lafiya kalauu duk da ana tsegumi

"gefe daya na yan bamgarensu wasu na ganin waida shiri maman,mu tazo gidan akan su gwaggo din."

Don akanta mata biyu sun fice lokaci guda matan dake adawanta a fili kowa ya sani amma a fili suna

nuna suma basu goyi bayan hakan ba.

******* ******* *******

Hannusa har rawa yake daya hango hindu din tare da Aziza da zasukai abinci gidan mama Gambo da

gidan uncle hassan .

Kai wai wancan ba hindu bace yake tambayan na zaune a bakin shagon yaron ya bashi amsa da itace

mana tun shekaran jiya suke garin nan ai.

Kai amma kuwa na kwabsa ya fada yana ciro wayanshi daga aljihunsa sai rawa hannunsa keyi wajen

duba number da yake nema lokacin.

Wayan tayi ringing harta katse ba a daga ba kira uku gana ukkun zai katse yaji an dauka murya da

alaman barci ya soma fadin.

Alh Allah barka da sallah aka mayar mai da barka dai waye don Allah nan ya gane baima da lagin nasa a

yanzu ke nan hakan na nufin ya goge layinsa a wayan.

Alh Allah isah ne maishago nan yan dawakai unguwar su hindatu mana ka manta dani ke nan yaji Alh

"na fadin isah isah kafin ya tuno yace a,a mutumina kaine yau a layin ya kwana biyu kuma ?"

Wallahi lafiya lau Alh nace barin kira in maka albishir mutumiyar fa na gari yanzu haka tazo daga

kaduna a nan sukai sallah wa ke nan kuma ?

Hindu mana hindu dai taka ba kasan ta kashe wacan tsinanen auren ba da iyayyen sukai mata ta koma

kaduna wajen mahaifiyarta ?

Eeh kamar ka taba fada min hakan kuwa ai Alh yanzune hindu take taka tsab kaga yadda ta koma wata

yar birni kuwa yanzun nan suka wuce gaban shagona ita da yar uwarta ina ganin unguwa zasu don na gansu da abinci.

Har yanzu bata da auren ke nan gaskiya mutumi banga alaman aure a gareta ba gaskiya amma zan

bincika dai na kara ji baima gusa ba yaji yana fadin kai inusa hindu aure takeyine yanzu ?

Yaji wanda yake tambaya yana fadin ina tunda ta rabu da sulaiman ai batayi aure ba har yanzu hakan

"yasa ya juya yana fadin kaji Alh bata da aure yanzu shine nace ko za a waiwayone kuma a gwada sa,a ?"

Watau matsalan iyayyen nan natane malam isah yasa kaga koda kaban labarin mutuwan aurenta

kwanaki ban maida hankali ba don harka ya hada da gargajiya abin dubawane.

Amma tunda tazo na bullo mu gaisa ban sani ba ko tana amfani da tsohon layinta har yanzu ina batayi

Alh aisai a samo maka wanan ba wahala bane a wajena .

Baida matsala zakaji insha Allahu ya kashe wayan kafin isah din yai wani magana kuma don barci yakeyi

wayanshi ya tayar dashi.

Suna gidan mama gambo suna falo ana hira da yaran mama gambo da ke gida dukkansu a lokacin

wayanta ya dauki kara cikin mamaki ta duba tana kallon number don ta jima da goge layinsa a wayanta tun aurenta da sulaiman ta goge duk wani layi da zaija mata barnan suna a lokacin.

Bawai ta manta dashi bane a ranta abune data sani tunda ta zama bazawara a yanzu yana da wuya ya

dawo gareta kuma yanzu.

Don haka ta dauka cikin tashin sanin waye a lokacin takai wayan kunnenta tana karawa nan yake

sallama yana fadin Allah ya taimaki gimbiya hindu ya kwana biyu da fatan anyi sallah lafiya kuma ?

Shiru tayi tana tunanen muryan kafin zuciyarta ya tabbatar mata da shine a layin a basarwa ta amsa da

"a,a yau din nan kuma ina wuni ina gajiya ?"

Lafiya kalau kece da gajiya ai ashe kina gari hindu koki nemeni alkawari ai baice haka ba gimbiyata .

Shiru tayi cike da mamakin dawowanshi gareta yanzu don maza da yawa haka suke su dawo don su

yaudari mace kosu bata mata lokaci ?

Bayan haka kuma gidansu zasu dauka don shine ta kashe aurenta ta fito don ta aureshi ba a gane

wayonta bai kai irin haka ba.

Haka kuma tana da labarin ba mace daya bace gareshi kamar yadda ta zata saidai bata zargeshi da

hakan ba don magana irin wanan kan iyalinsa bai taba hadasu ba dashi.

A sanyayye ta amsa mashi da fadin alkwari kuma akan me aiba nice ya kamata na nemeka ba don nazo

daka damu aika ya kamata ace ka san hakan kafin kowa.

Ya Salam hindu ki fahinceni don Allah kada kiga laifina kan hakan karki manta da yadda mukayi da

iyayyen ki lokacin ?

Wanan nake tsoro ba son tsohon nan nada fahinta ba hindu da sunyi karana a lokacin kan batarki suna

zargin nine na boyeki a wani wajen.

Ka boyeni don me kamar mara hankali ni ina zaria wajen yar uwar mamata na tafi yace haba nikan nayi

mamakin hakan sosai wallahi kin gudu bada masaniyata ba kuma baki nemeni ba lokacin tunda ance a kaina kika gudu ?

Wanda ya fadama yayi karya ni kawai auren zumuncin da za a hadane banso bawai akan namiji bane

da a kankane aida na nemaka tun lokacin ta bashi amsa da hakan.

Murmushi yayi don yagane gatsen tayi mai itama yace afuwan ran gimbiya ya huce yanzu dai kina ina

don ina son mu hadu don Allah idan ba damuwa ga hakan ?

Sorry don Allah kayi hakkuri hakan ba zai samu ba tana fadin hakan ta kashe waya tana dago kai suka

dubeta azizace ke tambayan waye kuma yayan mu ?

Wanine ta bata amsa ganin mama gambo data shigo falon da sakon da zasukaiwa mama haka kuma ta

debo kankara mai yawa cike da kula tana fadin kulan nan rikon sanyine dashi wanan zai kai kwana ukku idan dai ba budeshi kukeyi kuna barinshi bude ba kulan dane na farkom nima na tsohon mune na gada a wajenshi.

Sun dan jima kafin su taso dan wajen hjy gambo dinne yace zai kaisu gida don haka suka mike ya

saukesu idan sun fito gidan kawunsu hassan .

Har kofan gida ya kawosu a daidai lokacin kuma mazan gidan suna zaune a kofa suka fito cikin na

zaune din har da sulaiman da yan uwanshi ba yadda suka iya dole suka fito daga motan aka fara sauke

kayan wanda abinshane da mama zata rabawa mutane da nama kuma danye mai yawa kawu ya aiko masu dashi.

Aka kama aka shiga dashi ciki sukabi bayan wanda suka dauka din zuwa cikin gidan da kaya niki niki

nan kuma aka hau aiki mutanen gidan wanan sallah sun sheda alherin mama ya sauka a gidan don kuwa haka tabi ko wani lungu da wanan naman danye aka aika sadaka ana daga gidan kawu hassan aka kawo

sadaka.

Abin yayi matukar dadi ga wasu inda wasu kuma suke ganin ana masu karyan arzikine kawai yasa ake

abubuwa haka a cikin riya don akidar gidan kowa ya samu kansa ya sani kadai.

Nama dai gaskiya Alhamdullahi don gaskiya Allah ya horewa mama damu a wanan sallah ba tare dako

kwanbonta ba kuma sai alherin yan uwa da take cikinsa dumu dumu a wanan lokacin ba zakace ka mama bace da suke kallo fakiriya a baya cikinsu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/5, 10:05 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

"A takaice dai Alh Rufa,i yankan baya yayiwa yaya hindu ida yazo gun baba Audu wanan karon neman"

izzinin aurenta wanda hakan kuma ba shirin kowa bane sai isah mai shago da suka bada shawaran ga yadda ya dace yayi.

Ya kuma bi shawaran don ya samu baba Audu da zancen neman izzini abashi dama ya shiga cikin

masoyan dake neman auren hindu din.

"Baba baiyi kasa a gwiwa ba ya samu tsoho da baban mu akan zancen Alh Rufa,i din da abinda yazo mai"

dashi shiru zauren yayi na dan lokaci kafin baba Alu ya soma fadin.

Wancan mutumin daine ya sake dawowa gareta ko bai hakkura da itaba ke nan har yanzu ba za a

bashi ba yaje gaba ya nemi wata tunda akanshi taki zama dakin mijinta.

"A,a Salisu ba a haka akan me ba zamu bashi ba na fahinci mutumin kirkine shidin don kaga wancan"

karon aisaida ya nemi izini a wajeka ya fara nemanta haka kuma wanan karon ya sake neman izzine a wajen mukuma karo na biyu.

Amma Saidai ni a tawa naso a sake bata zabi akan sulaiman don dama naso in sameku da wanan

zancen saiga wanan maganan kuma ya fito.

Haka din daidaine baba don nasan sulaiman baida matsala a bangarenshi in yanzu akace zata koma

dakinta a shirye yake da ya karbi matarshi to matsalam yanzu shine ita yarinyar ?

"Tafi yar uwartane data zauna nata dakin lafiya da za a tsaya tambayan wani ra,ayinta can baban mu ke"

fadan hakan a hasale .

Salisu