Chapter 26 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

ina son ka gane kowa da irin rayuwanshi munyi abin nan da farko ba aji dadinshi ba bansom a

maimaita abinda ya faru a baya kuma .

A bata zaba idan tace zata koma sai a mayar da ita dakinta din shi kuma wanan a bashi hakkuri ba

rabonsa bane don ban bashi baki ba nace saina zauna daku munyi shawara akai.

Ai zancen Audu gaskiyane a binciketa kada ai mata dole baba baiso haka din ba da sukace yaso kawai

ace za a maida ita dakinta a lokacin.

Don shine da dare aka kira hindu din tana jin ance ana nemanta wajen tsoho su baba duk ta tsure dajin

kiran haka taje ta samu tsohon da baba Audu inda baba Audu din yake tambayanta ina zancensu ya kwana don ya fada mata tun farko baison dogon zawarci din nan kada tace koya mantane ?

Koda basu zoba shi yana da niyar zuwa kaduna yaji inda don haka tsakanin Sulaiman dashi wancan Alh

dake nemanta ta fada masu waye ta zaba acikinsu yanzu.

Kai ta dukar kasa hawaye ya soma zuba mata baba Alu yace tokai Audu kagani bata da niyar fitar da

kowansu ke nan yanzu kuma tunda har hawaye take min a nan ?

Tama isa yanzun nan ba sai gobe ba ta fada min ko in yake mata abinda nake gani daidai a gareta don

haka ina saurarenki me kikace ?

Baba banson kowa a cikinsu aimin hakkuri na kara dubawa zan turo insha Allahu hindu din ta fada a

dan maraice.

Banda abinki hindu ai hakan gatane gareki babanki yai maki ina wancan mutymin akansane kika gudu

wancan lokacin to yanzu Allah baiyi ku zauna da sulaiman ba sai shi ya fito a daura dashi din.

"Kuka takeyi ta kasa magana Allah ya sheda taso Alh Rufa,i amma a baya a yanzu bata jin zata iya"

aurensa da mata biyu tana ganin yadda a kullum ake kwasa da mahaifiyarsu ita kuma tace zata fadawa mai mata haba ina haka zai yuyu.

Jin shirun yasa baba fadin tashi kije zamuyi maganan da Audu idan kin kasa fada muna zaki fadawa

gwaggoki laraba ai wanan yasa ta mike da sauri tana sharan hawaye ta fita daga dakin.

Sin jima suna tattaunawa a kai washegari saiga gwaggo laraba ta samemu a dakin take fadin wajen

"mama tazo da hindu nan ta soma fadin abinda ya kawota akan hindu tayi zabi cikin biyun ko Alh Rufa,i ko sulaiman."

Zancen sulaiman ai bai taso ba a yanzu don hindu bata zuwa tayi zaman kishi da Jamila nima yaya na

kare balle nace nakai hindu gidan mariya yanzu su zauna da jamila ?

Nima dai nayi wanan tunanen gaskiya mutanen nan basu da mutunci ki duba yanzu ba wani dalili

sukaso tayarwa mutane da hankali badon Allah ya doraki ba akansu ba karamin wullakanci sukaso suyi maki ba da yaran nan wanan zuwan naku.

Son angishesu anyi masu bazata ba shiri ai baba ya fada masu badake suke adawa ba da yaya Salisu

suke adawa tunda har da diyansa suke ki aiba diyanki bane diyan gidan nan ne su.

A karshe dai mama ta aikawa baba Audu da adan bata lokaci idan mun koma zata kirashi a sanar dashi

abinda ake ciki bai samu magana ba koda gwaggo laraba ta koma don jikin baba ibrahim daya tashi a lokacin.

Hakan ya hana suyi wanan zancen da ita a ranan saidai kafin ma tazo din ya soma magana shima bai

son ta koma gidan sulaiman saboda su tunda sun kirkirowa sulaiman auren jamila a yanzu fitina kawai hakan zai haifar a tsakani kuma ?

"Anyi haka saiga Alh Rufa,i ya soma zuwa lokacin ana saura kwana biyu mukoma kaduna don masu"

karatu a cikin mu saboda za a soma shiga makaranta.

Duk zuwa zaiyi sai ya girgiza kowa don zaizo da alherin da sai anyi mamakin hakan ana washegari

zamu bar katsina da safene muka tashi da mumunsn labarin rasuwan baba ibrahim din mu.

Baba ibrahim dan baba Alu ne tana daga cikin diyansa maza hudu da suke rayuwa a cikin family house

din mu.

Baba ibrahim mutum neshi da bai faye rogima ba haka kamar shine idon baba da kafanshi a gidan saiga

shi mutuwa yazo ya daukeshi cikin dangi a daidai lokacin da ake bikatanshi a cikon mu.

Wanan ya jawo muka kara kwanaki a kaduna don mama tace sai anyi sadakan ukku ko sati zamu tafi

haka yan uwa da abokan arziki suketa shigo gaisuwa don mama bata zama a part din mu tana can suna karban gaisuwa a lungun baba Alu tsohon gidan.

Inda mu kuma muke a namu part din sai jefi jefi muke shiga cikin gida wanan mutuwan da akayi kuma

yasa su gwaggo dawowa dakunansu don baba tsoho yace su dawo dakinsu hakana.

Zuwan mama shari da mama gambo muka dahe mata akan zamu koma kaduna mun gaji da zaman

katsina hakkuri ta bamu akan mu bari zamu dawo ai muma.

Saida akai satine muka dawo kaduna din a cikon moyan gidan kawun mu daya bayar akawo mu dashi

muna zuwa gaba daya a gidan mama muka sauka.

"Mun dawo da sati biyu aka daurawa yaya wani auren da Alh Rufa,i wanda bawai ta tsayar dashi bane"

baba Audune ya daura wanan auren dashi.

Don kawar da tsegumin da aka fara bayan mu cewa wai yaya din zata koma gidan sulaiman suka fara

halinsu suna zage zage shine baba Audu yaiwa abin tufka ya daura airen a bazata kafin su koma sokoto shida inna karima amaryanshi.

Da labari yazo muna yaya taso tayar da hankalinta kan zancen amma dasu mama suka zaunan da ita

suka bata magana sai kuma ta hakkura tunda sunce zasusa ya mayar da ita karatu.

Tarewane baba din daya bugo waya yanawa mama bayani yace sai idan ya dawo daga sokoto zancen

tarewan don haka a dakanceshi har ya dawo.

******* ******* *******

Yadda abin ya faru kuwa yana zaune a falonshi da dare yana cin abinci kiran baba ya shigo a wayanshi

ya dauka suka gaisa nan baba din ke fadin yana son da safe yazo da magabatanshi ayi zancen aure donshi zai koma sokoto wajen nemansa.

Yaji dadin hakan ba don komai ba sai abinda ya yarda dashi akan yarinyar nan hindu matukar ya

sameta ita din alherince a gareshi don ya kara noticing din cewa hanyoyi arzikinsa na budewa duk sanda yake tare da ita.

Ya samu yazo da iyayyensane wanda sananune a gurin baba Audu din anyi magana bisa ga tsarin aure

"nan baba Audu yace ai tunda sunzo sai a daura kawai a wuce wurin shine dalilin daurin aure tsakanin hindu da Alh Rufa,i."

Saida bayan angama komaine ya kira mama yake sheda mata harda dalilin gagawan daura auren a

lokacin ya fada mata komai kuma ta gamsu.

"Don kota nuna bata yarda ba ba yadda ta iya shiko Alh Rufa,i yasanda bawai ya samu kan hindu din"

bane sosai donshi kanshi yana mamakin sauyawanta a yanzu.

Wanda ba abin mamaki bane duba da yadda a yanzu idonta ya bude .

Don zama dasu anty Nuratu yayan mama shari tayi matukar wayewa da abubuwa da dama game da

zaman duniya a yanzu sabanin can baya da take kamar yar kauye.

An daura aure ko hjynsu bata sani ba sai bayan an daura din mijinta ya dawo yana bata labari don tare

dashi akaje yana zaune da safe ya kirashi a waya don yasan idan bai sakashi ba mahaifiyar nasu zata iya

nuna bacin ranta akanshi kan bai daukeshi da muhinmanci ba yasa ya bugo mai waya yazo zai turasu wani wajene .

Sai gashi ya dawo yana bata labari shi yau yaga mamaki mutane masu mutunci daga zuwa neman aure

an dauro auren a lokaci guda ?

Auren wa kukaje nema hkyn din take tambayanshi yake fada mata komai daya faru nan uwar ta soma

"fadin nikan Rufa,i wanan aure da yakeyi haka mai zaiyi da mata hakane ?"

Hjy ce Allah kin tuba don Allah yaro a lokacinsa Allah bai hana mashi ba saiya tsaya ya tauye kanshi kan

"abinda yake ra,ayi ?"

"Yana ra,ayin kara auren nan yasa kikaga hakan su kuma don sunga kudi daga zuwa nema sai kawai su"

saka a daura auren saboda kwadayi ko ?

Ai kaji zancen mata ba kaji kuma wani sabon magana yanzu Allah yasa saida ya fada muna dalili ina

"ganin wacan yarinyar ce daya nema ba a bashi ba kwanaki ta fito itace ya aura din yanzu kuma wan mahaifinta da yai hakan ya fada muna dalili don ya yaba da hankalin Rufa,i zaisa su bashi ita yayi mata"

bayani kamar yadda baba Audu din ya fada masu a can.

Ai ba zaka ga laifinshi ba kai tunda halinku daya dama maza haka kuke yanzu ai shike nan meya rage

tunda ya cika hudu yana dariya yace sai fatan zaman lafiya a yanzu kuma.

"Zaizo aiya sameni da sauri mijin ya juyo gareta yana fadin hjy kice mashi me aurene fa sunnan ma,aikin"

Allah me zakice idan yazo zakiyi jayayyane da ikon Allah ?

"Naki yanzu shine addu,a akan yaran nan kiyi masu fatan alheri da samun cigaba a rayuwa ki zama"

tsayayya a tsakani bamai ware gefe daya tagoyi bayan bangare daya ba.

"Ai dolena tunda ya riga ya aikata hakan ba dole in tsaya kaida fata insa mashi ido ba kamar Rufa,i zai"

zauna da mata hudu har yaushe ya auro wanan gashi ba a zauna lafiya ba zai dauko wata.

Allah yasa hakan ya zamo alheri yasa wanan auren ya zamo sillan canzawan komai a gidan ta amsa da

amin tunda kace hakan ai hakan muke fata dama.

Zaizo ai nasan zaizo yayi maki bayani zuwa anjima ya fada ya mike yana fadin zaije wancan gidan nasa

ya dubasu tayi mai a dawo lafiya ya fita.

Ita kuma ta dauko waya da niyar kiran kanwarta sai kuma ta fasa don dan tunanen da tayi nata bari

"saishi Rufa,i din yazo taji meke faruwa aure haka daga sama ba sanarwa ?"

Yadda ta zata zaizo hakane ya faru sai gashi da kannesa mata biyu sun shigo suna gaba yana bayansu

suna mai sheri karamar ke fadin ina mama fito danki yau angone fa ?

Zaune suka sameta cikin falo kallo daya tayi mai sai ya bata tausayi din har fadawa taga yayi mata

lokaci guda take fadin angon me kuma can ?

Allah mama yau babanki angone fa kuma kai ubana nikan wani ismin aurene kasha haka lokaci guda ka

cika gida da mata nayi musu dazun da Alh ke fada min ?

Wallahi hjy haka Allah ya nufa sam ban dauka abin zaizo haka ba sai gashi sun dawo suna fada min an

dauro auren daga can din nima sai naji wani iri don komai ban shirya ba gaskiya.

Da wani iri kan aure haka kamar wa yanda suka matsu da yar tasu daga zuwa tambaya sai daura aure

kawai ?

"Mama mutanene masu wuyan sha,ani wallahi idan sun fadi magana basu tayarwa dattijan kwarai ke"

nan zakace hakane mama niko wani magana kwakwara bamuyi da yarinyar ba izzinin nemanta na tambaya shine aka kirani na turo manyana yau suyi magana dasu.

"Yasa nakira Alh nan naki da baba ma,azu suka tafi tare da wasu makwabtan baba din sai gasu sun dawo"

suna sheda min an daura auren ma ai a lokacin.

Sadaki fa hjy ta tambaya cikin mamaki yace dama na basu dan kudi su rike suka dawo min da rabi wai

sun bada rabi a sadaki aka daura auren dashi .

Zance kamar almara yace wallahi hjy ai mama irin auren nan yafi albarka fa kanwarsa habiba ta fada

Allah yasa uwar ta fada cikin wani irin yanayi na damuwa a lokacin.

Nifa hakan nyayi mi; dadi don yar iskan nan mara mutunci aziza tana zaton itace tafi kowa yanzu gashi

ai an dauko mata wata sai muga tsiya kuma ?

Bazawarace kenan ko hjy din ta tambaya yace bazawarace hjy saidai ai bata zauna gidan mijin ba

lokacin tagudu karshema suka koma kaduna da zama ita da mahaifiyarta wanan yasa har na auro aziza ai.

Da yake kara auren yana ranka ba lokacin kadaiyi adalci a tsakaninsu kaga wanan badon kana tsaye ba

da tazo ta jagula maka rayuwa da iyalinka saita samu kaima ka iya yasa ta dan lafa.

Yanzu ina zaka aje ita wanan din ajiyan zuciya ya sauke yana fadin wanan baida matsala mama filin can

"na bayan dakin ita Na,ima zansa a mayar dashi irin nasu kinga sai su zauna bibiyu ko wani part ?"

"Kana nufin tarewan bama yanzu ba ke nan a,a mama zan dan basu lokaci su shirya tunda suma girshi"

akai masu da auren kinga suna bukatan time ke nan a yanzu.

Sun dai tayin tsare tsarensu yadda ya dace da yan uwanshi kafin yayi masu sallama inda aka aje

maganan zaizo da matan nasa a fada masu zancen auren washegari da haka sukai sallama da juna ya tafi.

******* ******* *******

Hankalin sulaiman ya tashi matuka da labarin daura auren hindu da wani ya sameshi saidai ya daure bai

nuna komai ba kamar yadda gwggo hafsatu take fada mai.

Anyi hakane don kada ya riga hindun aure ai yanzu ta gane adawa akeyi dasu yan gidansu yasa ake

"masu abubuwa ba bisa ka,idaba a gidan ana nuna masu wariya a cikin dangi."

Idan gaakiyane ai kamata yayi a goya masu baya ga auren jamila amma baba Audu yazo sin hada kai da

baba tsoho an daura mata aure kafin nasa alhalin sunsan nasa shirin auren da akeyi yanzu.

Ba komai mama haka Allah ya nufa bawai basu son mu bane ita ai macece kinga bamu daya da ita

yanzu da sauri tace dashi rufa min baki don Allah kai yarone meka sani son Allah ?

Ka dauka sonka sukeyi a hakan da suke nuna muna ba zasu taba son mu ba ai tunda sunsan munsan ba

kaunar mu sukeyi tsakani da Allah ba kabar mutanen nan kawai dama shi baba Alu da baba yusuf mahaifin baba Audu ke nan aibasu kaunar mahaifinmu akace .

Mama ayi hakkuri don Allah zan kiraki anjima mu karasa maganan yanzu ina kan hanyane ya fadi

hakane don katse dogon zancen da zata dauko mashi a lokacin.

Koda suka gama wayan yayi tunanen akan zancenta baiga illan mutanen nan a garesu ba asalima sune

dai masu tausaya masu har mahaifansu har suka taso haka ?

Amma zancen mama a kullum shine sudai ba a kaunarsu mutanen dake bada dukiyansu da komai nasu

akansu sune ake nufin wai kuma basu kaunarsu ?

Yasha tambayan mahaifiyarsu meyasa mama din suke hakane basu kaunar a zauna lafiya ko yaushe

takan bashi amsa da hakan ya samo asaline daga iyayyensu mata da basuyi zaman lafiya dasu baba Alu din ba a lokacin.

Yasan abinda mahaifiyarsu ta fada shine gaskiyan maganan duk zancen su mama hafsatu din fadane

kawai don kar a zauna lafiya baijin saboda ita zaki zaman lafiya da yan uwar mahaifiyarshi tunda basu nuna mashi komai ba.

Haka kuma wanan auren alkakai din da zasu kara mashi a yanzu shine abu mafi kuskure da muni da

zasu aikata don wancan karon hinduce ta kishi amma wanan karon yasan shine wanda zai bijerewa bukatansu idan ba Allah ya gyara ba .

Don gaskiya baijin ko burbushin son Jamila a zuciyarshi saboda sak halaiyan iyayyen nata mata takwaso

gaba daya rashin mutunci da yankar kauna duk ta iya nasu ko ba zaizo daya ba gaskiya.

Yana ganin daya koma zai nufi jalingo kafin bukin nasu din yanzu dai kokari yakeyi ya samu takardunshi

su shiga hannunshi don shine muradinsa kawai a yanzu.

"Gaban manyan jami,an aka kaishi aka zaunar dashi ana watso mashi tambayoyi akan jerabawan da"

suke ganin kamar bashi yayisa da kanshi ba amma a take yake basu amsa wanan ya ceceshi aka saka hannu a bashi takardunshi kawai.

"Tare kuma da bashi zabi idan yana bukatan aiki dasu a nan jami,an shirya suke su daukeshi aiki don"

suna bukatan irinsu jajatattu masu kwazo a wanan fannin ?

Tun kafin ya iso gida labari mai dadi ya isa inda gwaggo hafsatu ta hau cika baki tana nuna isa da sun iya

haihuwa da sauran zance dai haka a cikin gida tana saka sunan hindu da tayiwa kanta ita danta yayi gaba a yanzu itako ta kare a cikin kishiyoyi ?

Kamar yadda ko wani dan uwa yaji wanan labarin hakama mama da labari yazo mata tayi murna ba

tare da nuna komai ba na hassada a zuciyarta har fili duk da taji irin maganganun da mama din keyi game da yarta hindu.

"Tana mata fatan Allah yasa auren Alh Rufa,in ya zamo mata alheri itama a rayuwanta ita da dukkan"

"sauran yayanta addu,anta ke nan a kullum tare da sauran musulmam duniya."

"Ranan da Alh Rufa,i zai zo kaduna baizo shi kadai ba sai tare da yan uwanshi mata su biyu da kuma"

wani abokinsa hamza da suka taso tare wanda bai boye mashi komai nasa.

Basuyi tsamanin haka zasu samu gidan nasu ba don sun dauka karamin gidane aka saya masu don su

zauna sai sukaga babban gida kuma wai mallakin uwartane dakw zaune a wancan gidan nasu nagado a da ?

Sun yaba kwarai da irin tarbon da suka samu a wajen mama din da yan uwan hindu din da suka sama

sunzo harda mama shari a lokacin don zuwan nasu.

Suma sun yaba sosai dasu anyi magana ta fahinta da juna inda mama shari take rokansa da yabari

hindu din tacigaba da karatunta a nan ko kuma ya mayar da ita can katsina ta samu tacigaba da karatun.

Yayi alkawarin hakan inda yace zai karbi takardunta ya nema mata gurbin karatu a katsina din don zafi

mashi sauki da itama mama tayi murna da hakan .

Kamar yadda sukazo da tsaraba garemu haka itama mama tayi mai bazatan tsaraba din don tasan

halinsa da bajinta taga suma ya kamata su nuna mai hakan.

Yan uwanshi kan sun yaba sosai da hindun sunyi photuna a cewansu zasu kaiwa hjynsu taga sabuwar

sarakuwar nata akai sallama suka tafi cikin dafin rai.

A hanya yar uwarsa habiba ke fadin wanan yar akwai kunya da ladabi yaya zasu zauna lafiya nake gani

da matanka indai haka take da gaske gaskiya ba matsala.

Ba wanan ba ai habiba kinga Aziza yanzu itace matsalan gidana ina cewa wa yan can kazanta da rashin

sani ciwom kai to ita kuma azazi ba haka take ba.

Yawon ta shike daga min hankali habiba ga kwaso abokai a shige daki ana ihu ga girki bata iya ba shiya

na soma neman ita wanan din ?

Duk da bansan ko ita din kuma wace iri bace don ko wani dan adam da nasa kalan matsalan a rayuwa

zama da aziza yasa na koma tsoron mata a yanzu wallahi.

Aure ace wata tara amma har an fara kai ruwa rana haka abin ya fara isana habiba aziza na neman

daga min hankali a gidana ?

Saika kara jajircewa ka nuna mata kai tsayayyen namijine a gidanka inba haka ba ta zubarma