Chapter 28 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

wasu dama abinda ya kaisu ke nan lokacin gulma.

Antaso kai tsaye gida muka nufo damu da yan gidan mu bamu biya inda su mama shari suka sauka ba

bansan meyasa suke son idan munzo muna sauka a gidan mu ba.

An dai yiwa mama kara a wanan bukin dama haka duniya yake idan akwai lasa anayi dakai ba kunya

"wanda a baya saidai inna halima da gwgg balarabane suke zuwa sha,aninta ."

"Sai gashi wana karon yan zuwan sunyi yawa an dawo bangaren mama din ana ta sha,ani da kowa"

"kamar ba,ayi zaman da bai faduwa ba a baya."

Washegarima ni a zatona ranan zamu koma kaduna sai gashi mama tayi sammako ta fita zuwa gidan

uncle tun muna saka rai da dawowanta har yamma don sai dare ta dawo aka kawota da kaya niki niki na buki wanda nasan aikin mama sharice.

Don har kano muka takata taje sayayya don komai na bukin itace tashirya sai mama Hussai da kan yo

waya ta bada nata shawaran a lokacin.

Gashi Allah da ikonshi anyi an gama lafiya sai zancen watsewa don yan kaduna wasu har sun juya da

sauran garuruwan nesa irin Abuja duk washegari suka koma gidajensu.

Koda mama ta dawo nayi barci don dama a daki na wuni kwance ina jagulan wayan da nake amfani

dashi lokacin idan caji ya kare in saka haka na wuni kwance cikin rashin sakin jiki da yan gidan namu da yanzu suka koma min baki a wajena.

Yawan shiru shiruna da zama kusa da mama ko wani lokaci yasa ina fahinta tare da nazarin kowa a

cikinsu iyakata dasu gaisuwa idan sun rutsa dani idan basu rutsa ba kuma ba ruwana da mutum.

Sungaji sunyi korafi a kaina mama tana fada masu ko a can haka nake ban damu da shiga mutane ba

haka yasama ban zama a wurinta ina gidan yar uwarta mama shari tun zuwan mu mu acan muke dama.

Yanzu daine da yaya tayi aure nake jin amce wasun mu zasu koma wajen mama din amma bansan ko

hardani ciki ba.

Nikan washegari na soma shirin kayana ina zaune ina hada jakata mama ke fadin wai me nakeyi

hakane na dago ina fadin mama bayau zamu tafi bane ?

Nasan haushi taji ta rasa me zatace min sai wani irin harara data jefo min a lokacin tana fadin dauki

kayan nan kikai min cikin gida ta lisafa min suwa zankaiwa na fita ina turo baki .

Dole naje sassan gidan har lungun baba ibrahim marigayi nakai masu manyan robobi da snack d8n buki

ina dawowa kuma karo na ukku ta izani part din yaya farida in kai mata nata.

Na dauka din dolena na hari part din dashi inda na samu su yaya a zaune suna karyawa shida yaya

"sulaiman nagai dasu suna kokarin jefo min ba,a fuskana a daure yayan muke fadin wanan ai bata da marmari daka ganta nan ."

Ban dai tsaya ba na fito abina na barsu suna zancen yan dakin mu suna lissafo halin kowan mu ban

tsaya jin sauran zancen nasu ba na fito.

Sai wajajen karfe biyu saiga yaya Nuratu tazo sallaman mama zasu tafi a ranan haka na kafe saida na

samu nabi hankalina ya kwanta muka bar garin katsina musalin karfe ukku na rana zuwa kaduna.

Inda mu kadaine a gida kowa ya shige dakin su nikan tunda nayi wanka nayi sallah ban ko nemi abinci

ba sai washe gari koshi yaya Nuratune tazo ta tayar dani da barci tana fadin ga mama a waya.

Na karba fada ta soma min meyasa na biyo su Anty Nuratu nasan bata gida sallon su barni da yunwa

wani ciwo yazo ya shigeni kuma ?

Nace Allah mama nagaji da garin ina jin kamar inyi ihu idan naje garin nan duk da banganinta zagi ta

sako min tana fadin ungo nan yar nema kawai kina da garin dayafi maki katsina ne a duniyan nan ?

Shiru nayi sai kuma ta koma fadin gara da kika koma kiyi karatu kafin mu dawo don jerabawan da kike

dashi sati biyu masu zuwa nima nacewa Dije ai gara da kika bisu yafi .

Sai mun kwana biyu don ba yanzu zamu dawo ba ki maida hankali kiyi karatu sosai kin dai san

alkawarin da kikai min ko inki cika maki nawa idan bakiyi karatu ba na amsa da to mama Allah ya dawo daku lafiya tace in bata anty din na kai mata wayan na dawo daki .

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/8, 10:02 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Sati biyu tsakanin auren hindu dana Sulaiman inda aka iza mai takaici tare da tsauyeshi don ko kusa ba

za a hada jamila da hindu ba.

Tsaye tsaye take ga kaudi ga surutu ga nuna iyayi ga tsugula don komai ita tasani ba bakunta ko shayin

wani irin rayuwansu din nan sak shine gareta.

Sati biyu da kawota ya kulle kayanshi yace zashi jalingo kowa yana mamakin hakan don gwaggi hafsatu

taso hanashi tafiya yace tayi hakkuri yayi niya auren nan ya tsayar dashi bai tafi ba.

Sulaiman mu kakeson yabawa kunya bayan gatan da mukai maka wancan hinduce ta gujeka yanzu

kuma kai ke shirin gudun Jamila ?

Meye a garin naku da akwai aida mahaifinku ya rigaka zuwa tsunta babu mama ina dai son inje inga

gidane shiru din nan yayi yawa haka ?

Lah lai sulaiman ka nuna min ba da kake ba ya dago kai ya dan dubeta cikin mamaki nan ta shiga fada

mai bakaken maganganu dake nuna bata yarda yaje ba.

Ta muzantashi tare da dangin ubansa wanda hakan yaiwa sulaiman sin zafi ya mike ya fita yana mata

sallama yaro ta aika aka kira mata gwaggo Asiya a lungunsu tana zuwa tashiga fada mata.

Asiya kinga yaron nan yana son yaba muna kasa a ido ko wai sai gashi yazo min da zancen tafiya

garinsu yanzu .

Tafiya garinsu wajen wa zai tafi tunda ga mahaifinsu nan da kowa nasa zaune suma basu je sulaiman

yana son kawo wani abu cikin zancen nan fa yaya ?

Indon wanan mara mutuncin yake abin nan garama ya daina don ita tana can gidan mijinta lafiya ko jiya

naji tana waya da ubanta wai zata fara karatu.

Shi kuma uban har dadi yake ji bai tsawata mata da hakan ba ina zai tsawata keko yana ci yana sha

hankali kwance ai yanzu sai yadda akayi dashi kuma ke nan ?

"Na fada mashi ai bamu ba zuri,an wanan matan marasa mutunci don haka gara ya san abinda yakeyi"

ya rike matarshi yafi mai alheri tunda sun nuna mashi matsiyaci yake .

Basu rabu ba saida suka hada bakin yadda zasuje su sameshi a gidan suyi mashi cin mutunci d9n ya

dawo cikin hankalinshi ya zauna lafiya da matanshi.

Saidai sun makara don washegari koda sukaje gidan ake fada masu ai yanzu kila ya wuce kaduna don

motan farko yabi asubanci yayi yabar gari saboda nisan inda zashi din.

Eeh tsunttaciyar mage bata zama mage dama lalai sulaiman ya nuna min ban haifeshi ba ban isa dashi

ba nace kada ya tafi yasa kai ya tafi idan yaje ubanwa zai tsunto a garin ?

Kema yaya mariya da kaifinki wallahi in gaskiyane ubansa yaje mana ko wani nasa amma ba laifi dan

da baka haifa ba bai taba zama danka ai yaje din yaga tsiyan da kakansa da iyayyensa suka guduwa a can din kila hankalinsa zai kwanta ai.

Ban fahinci zancen ki ba hafsatu yaron nan idan ni banje gida ba su yakamata suje ai san garin mu ko

don irin gorin nan da yanzu kika soma yi masa .

Muryan mijin mariya din mutumin da ko yatsa kasa mashi a baki sai yaga dama yayi magana shine ya

bata amsa yana fitowa daga dakinshi.

Kada ki dauka don kin ganmu nan a rakube ko bamu da gatane a can da gatan mu wallahi muna da yan

uwa kamar yadda kuke da yan uwanku a nan.

Muna da gata kakar kowa tunda ba shegu aka haifi iyayyen mu ba kawai dai matsala aka samu da

mahaifin mu yazo nan ya zauna bai nuna muna gida ba.

Da kike kiran sulaiman da tsunttaciyar mage a yau hafsatu me sulaiman yayi maki na butulci don kawai

"zai raya sunan ma,aiki Allah yaje zumunci shine kuma ya zamo laifi a gareshi ?"

Kuna abinku ba abinda baki fadawa yaran nan kan hakan tun suna kaka in akwai wanda yasa hankalin

sulaiman komawa gida kece hafsatu kece da yan uwanki da kuke masu gorin hakan kullum .

"Kuna nuna kune gatansu gaba da baya don dole subi ra,ayinku ko hakan bai masu dadi ba mu abin farin"

cikine tafiyan shi garin mu yau tunda mu ancire muna gida a rai shi gashi an samu zai tafi gidan ya dubo muna su.

To ashe haka zancen yake ban sani ba habu ai gara daka fada naji abinda nakewa danka yana maku

ciwo kai da matar ka da ku karbi danku ai a hannuna tun yana karaminshi zaifi.

Yanzu anga ya zama mutum da za a fara cin moriyanshi shine ake son fito min a mutum a nuna min

halin yan adam na butulci ko ?

Hafsatu kike rike sulaiman ko mijinki ya rikeshi Habu ni kake fadawa hakan ta tambaya don bata taba

tunanen haka ba garesu yace nagaji da halinkune yau ?

Nagaji da irin cin fuskan da kuke shigowa gidan nan kuna muna kai tsaye ba shayin komai don anga ina

da hakkuri da kauda kai yasa komai ya fito bakin ku baku jin nauyin idona kuke fada muna kai tsaye.

Nasan yar uwarku kukeciwa fuska shiyasa hakan bai faye damuna ba amma yau da kika fito haka a

mutum dinki kema kika fadi abindake zuciyarki game da yan uwana a gaba dole in baku amsa akan hakan .

Irin maganan nan yasa yaron nan hamisu yabar gidanki shi kuma daya zauna yana hakkuri hafsatu baki

barshi ba ya hutu bai bugun gaban kanshi ke nan sai abinda kika yarda yayi don kin ta dashi ?

Aiba haka kikewa Ahmed ba ko ina tare suke fisabillahi kinyiwa yaron nan adalci a rayuwansa mutum ya

"dinga tuna mutuwa mana a rayuwanshi idan mune yau ba mune gobe ba koda kuwa muna rayen wani abin za,ayishi bawa yana kallo baida lafiyan yin yadda ya saba."

Don haka mu dingawa juna uzuri don Allah kada muce zamu wuce gona da iri ni nabashi shawara ya

"wuce a yau tunda babashi Audu ya bashi kwarin giwiwan zuwa ke kuma kince a,a dake da Audu waye a gaba ?"

Abinda na dade da sanine habu dama kwanciyan mage kai min akan yaran nan idan lokaci yayi ku facal

dani gefe daya to wallahi baku isa ba ashe abin naku shiri kaida matar ka da danka ban sani ba ?

Ba wani shiri sai gaskiya idan zance gaskiya yazo a tsaya a iya ni banje gurin yan uwa ba shi bai tafi ba

kuma baku daina goranta muna hakan ba da wani zamujine don Allah ?

Sunyi dai ba dadi suka fito suna zage zage zuwa gida daga inda baba Alu yake ya hango fitowansu

hakan yasa ya fahinci ba lafiya ya kaisu gidan ba a lokacin .

******* ******* *******

Ba zance zaman kadaici ba don inda sabo wanda ya fito gidan gandu irin namu ya saba da zaman yawa

haka kuma wanda ke rayuwa a irin gidajen da rayuwa ya mayar damu a kaduna dole ya saba da zama cikin rashin hayaniya.

"Wanan shine irin zaman da hindu ke ciki a yanzu a gidan sabon mijinta kowa na sha,anin gabanshi gida"

ba mai shiga harkan wani saukin abin dai shine a tsarin ginan gidan mutum biyu zasuyi amfani da kitchen daya biyu kuma a dayan bangaren zasuyi amfani da nasu.

Don hakane ya tsara ba wai gaba daya za a hade a waje daya bane ayita amfani da kitchen guda yayi

"hakane kuma don gujewa fitina daka iya faruwa a tsakani da kuma kaucewa sanin halin kazantarsu inda ya raba Azziza da Nabila Na,ima da hindu a bangare guda su biyu."

"Na,ima tun farko ta soma fahintan saukin kan yarinyar tunda ta shigo gaida ita da kwana da yaranta ta"

dan zauna tana tambayan sunan yaran tare da rikesu suna dan hira kafin ta mike tana fadin anty baby ta rakani na gaida yan uwa ko ?

Wai banajin sun bude get din wajensu yanzu don banji motsin kowansu ba gaskiya haka yasa ta mike ta

koma part dinta tare da yara biyu daga cikin yaranta kuma basu dawo wajenta ba saida wanka da kwalliya a fuskansu.

"Wanda hakan yaiwa Na,ima din dadi a zuciyarta ance wanda yaso zaman lafiya dakai a waje da gaisuwa"

da diyanka yake farawa ita hindu hakan ya nuna alaman tazo da lafiya gidan.

Wanan yasa da rana ta tsaya tayi girki hardana bakin amaryan da yamma kuma tashiga ta kirata suzo

su dora girki hindun ta amsa da to Anty ta yafo gyalenta suka nufi kitchen din don dora abincin dare wanda a ranan wajensu mai gidan zaici abinci ke nan.

"A zaton Na,ima a yadda taga hindun ba zata iya komai ba sai gashi ta samu ba haka bane don yarinyar"

"ashe da kwazonta itama ta iya aiyuka a cikin tsabta wanda Na,ima din ke dauka a lokacin sallone da bakunta duk bari zatayi tazo a koma daidai."

Tuwon ma hinduce ta kwashe a cikin leda yadda sukeyi gidan mama shari lokacin yayin saka tuwo a

leda bai bi ko ina sosai ba a lokacin sai take ganin wanan bata lokacine ai gun mace.

Sun gama tuwo moyane datake kamawa yayan nata su hjy da tawaganta suka shigo gidan basu

"dakunansu inji yaran suna kitchen har kitchen din suka leka suna gaisawa hakan yasa suka fito daga kitchen din zuwa falon ita Na,ima din wanda hjy sam bata damu da shigowa ba koshi wanan don zasu shiga dakin amaryane iyakarta falon danta."

Takaicine ya kume hjyn ana fadin ta zauna take fadin a ina zan zauna ko sallon in zauna zanina ya baci

da datti wanan kazantar har ina don Allah ?

Mu a baya akace an kawoma amarya kokari kake ka gyara dan abindake gareka baka zauna cusuuuu

haka ba cikin ko in kula dakin amarya da haske naka a wullakace haka ?

Don kece bera sarkin haihuwa yasa ba zaki iya gyara waje ba na zata ai zakiyi koyi da abinda amaryan

tazo dashi ki gyara ki duba yar nan a tsaye haka tana kitchen amma kamar zata office sallon kwana biyu ku juyata ta koma irinku ke nan kamar yadda ita wanan sakaran tazo ta koma yanzu akace .

Gaba dayansu a daidai lokacin suna falon tabisu da kallo a wullakance tana fadin kun daiyi hasara

"wallahi ku duba don Allah yaushe akai kayan nan daya koma haka Na,ima ?"

Keda Nabila na rasa meye damuwanku auren wanan yarinyar da zaku dawo gidan nan ya gyara maku

dakunan ku fa amma duba don Allah kaya kamar sunyi shekara goma da sakawa don kazanta ?

Ga mijinku dan zamani dan kwalisa bai iya zama a cikin wanan kazanta haka ku takaicin yadda yaketa

kara maku abokan zama baisa kuyi zuciya ku gyara ba sai yaushe zakuyi zuciya don Allah ?

Ta juya fuu ta fita daga dakin cikin takaici da bacin rai wa yanda suke tare suka juyo suna fadin ku gyara

mana Nabila aiko don masu zuwa ganin amarya kwa gyara wajenku ?

Basu da akewa fadan a gabanmu ba har mu da zancen bai shafa ba mun shiga hankalinmu ance kukan

kurciya jawabine mai hankali ka ganewa.

Zancen hjy makamine a wajen hundu don kaf abindata fada anyi mata darasi akan hakan haka kuma ta

taso ta samu hakan a gidansu.

Duk da dakunan uwanyensu simitine zallah a lokacin amma duk gari ya waye sai anmasa guga biyuba

lokacin kuma ko ledan kasa babu balle tiyes din nan na zamani.

Idan an gama a saka kajiji ko turaren wuta daki ya dauki kamshi a sake labule safe da yamma hakane

mama kuwa ko yaro yazo ya wuce fiye da biyu part dinta sai tasa an share mata lungu ana shara zuwa biyar idan gari ya waye.

Haka da kaci abu ko kasha abu da roban mama ko kwano takene zaka wankeshi don dan roba na nan

aje da ruwan wanke wanke ko yaushe a gefen dakinta .

Hjy ta fito ta barmu a ciki yayin da cikin hindu ya duri ruwa da alaman wanan hjyn babu mutunci ko

"sanaya a idonta balle ragowa don ko Na,ima kuka kawai takeyi irin da hawayene kawai ke zubowa a lokacin don takaici."

Ganin sauran sunbi bayanta yasa da sauri hindu din bin bayansu itama Amina ke fadin ga dakin

amaryan fa hjy baki shiga ba kuma zaki wuce.

Tsuki taja ta juyo tana fadin inane dakin ai koya mata wanan halin bamzan zasuyi itama Amina tayi

gaba tana fadin ina me dakinne tazo da sauri tabi bayanta aka shiga.

Kamshine mai sanyayya rai daya hade da sanyin AC yabi dakin zaune takai sauran ma suka zauna yayin

"da hindu tayi kasa cikin dan murya tare da fargaba ta soma gaidasu da wuni bayan wancan da akayi tana sababi dakin Na,ima."

Ido ta dan kurawa hindu din nadan lokaci kamar tana nazarin yarinyar kafin can tace da ita tau me

"sunan yan ketare su hema,malin da Amita dariya yayan nata suka kwashe dashi sukace suna mai dadine fa hjy."

Allah yasa yadda kuka yaba sunanta da dadi kuzo ku yaba min halaiyanta na kwarai nan gaba mu sheda

"wanan auren sanadin alherine garemu baki daya aka amsa da amin ta sake fadin aita hakkuri don Allah, gaba dayan ku banson jin wani abin asha daga gareku."

Ayi zama na hakkuri da amana ko wayace zomu zauna yace azo a saba don haka