Chapter 29 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

a rika kai zuciyana

nesa don Allah a gujewa shiga hakkin juna a kiyayye kuma .

Nasiha mai kashe jiki ta hadasu tayi masu kafin ta mike zuwa falon danta a nan sukai sallah magariba

inda aka gabatar masu da girkin amarya sukaci sun yaba don sauran sungani don bata taba yarda taci abincinsu saboda akasin da ake samu.

Wanan din ma tundaga ganin yadda aka karramasu daga kulan da aka sako masu abinci su hudu da

plate masu kyau da daukan ido hakan yasa tasa aka bude abincin don taga me aka girka ?

"Tuwon yayi gwanin ban sha,awa a kulan ga miyan egushi da yaji hadi yai kauri kassan miyan da akai"

amfani dashi ya karawa miyar armashi sai ruwan sha dana wanke hannu a sabon jug da roba komai a cikin karramawa akai masu shi.

Sai kusan karfe tara sukai sallama suka koma gida tun bayan fitansu gidan ya koma shiru don kowa

part dinshi ya nufa ita dai hindu wanka ta shiga ta fito ta zauna ta gyara jikinta a wajen maigidan ya shigo ya sameta .

Inda take ya nufo ta cikon mirro suka hada ido dashi tayi kasa da kanta tana dukar dakai ya karaso ya

tsaya bayanta yana fadin yau haka suka wahal me dake haka yau hjy tace min kinyi masu girki mai dadi sunci.

Shine nake sauri nadawo inci nima abinda ya fadane ya sakata murmushi tana fadin suda basu sanar

damu zuwansu ba aida girki na musanman zanyi masu yau.

To a taso a ban nawa nima inci inji in yaso sai inba da tukwuici gaba daya ta mike tana kokarin dauko

hijjab din ta don tayafa don sai sun gilma ta dan filin dake tsakaninsu dashi.

Ta bayanta taji ya rike wanda hakan yasata sauke ajiyan zuciya tana dan nokewa yana fadin amarya

komai baki gwanin burgewane don Allah kada ki yafa gyalen nan ki hanani ganin ajiyan da Allah yai min wanda rabona ya dawo gareni a yau.

Kanshi yakai saman wuyanta yana dan sunsuna tana nokewa take jin dama ace shi din natane ita kadai

"ba tare da kowa ba datafi kowa sa,a a duniyan nan idan haka ya kasance a gareta."

Kada wani yashigo ya samemu haka fa ta fada a cikin sanyin murya yace and so what ko wani ya shigo

ya samemu ai tare da matana aka sameni ko ?

Ya dan jaye yana fadin balle waya isa ya shigo nan yanzu bayan ansan ina ciki saidai idan na fita ko ?

Hakane fa da yake gidan mai iyaline dole da dokan daka sakawa hakan yaji maganan nata har kasan

zuciyarshi ya dai daure koma meye aishi yaja ta fada mai tunda bai fada mata gaskiya ba tunda farko don haka murmushi yayi mata a fili kawai.

Suna zaune a falonshi yana cin abinci ga hasken lantarki daya haska ko ina na falon hakama gidan

sukaji anshigo masu falon ba sallama a lokaci guda.

Kasa yake zaune saman kafet yayi irin zaman da addini yace ayi wanda malam bahaushe yafi

girmamawa yayin cin abinci din .

Ita kuma hindu tana gefenshi zaune tana duban wayanta ta mayar da hankali akan wayan sukaji an turo

kofan hakana anshigo din.

Binta yayi da kallo harta karaso inda suke din zaune yayin da hindu kallo daya tayi mata ta dukar dakai

tacigaba da abinda takeyi a wayan nata .

Ita kuma takaraso tacigaba da fadi a daile Alh an sayo min sakon nawa kuwa a daidai lokacin hindu ta

dago tana fafin ina wuni ?

Lafiya kawai ta amsa take duban mijin nasu dake faman sudin hannu shiko a dake ya dago kai yana

fadin bansayo ba.

Tace don me ta fada cikin mamaki ya dago kai saida ya dubeta yace don haka naga dama tunda bake

kadai bace ai ?

"Bani kadai bane akwai wace tace tana son a sayo matane bayan ni nike ra,ayi nace ina so kuma na"

"saba fada aika sayo min ko yanzu don ,,,,,,,,"

Sai kuma tayi shiru bata karasa ba yace karasa mana don naga na kara aure yanzu ko koba abinda kike

son fadaba ke nan ?

Kona fada karyane tunda haka dinne ai ban zaci hakan ba tun yanzu daga gareka saukin abindai duk

rawan kanka wani ya rigaka sanin wajen ?

A tunanen ki ko amma a zahiri ba haka zancen yake ba koma hakane hakan yafi min wani sabon

armashi a wajena don hankalina a kwance ba zargin komai ?

Wallahi wanan karyane kuma kamar yadda kike karya ko abin ai sirine baki taba gane hakan amma

alama kan nuna kanshi a zahiri.

Fada dai kawai ta juya zata fita sai kuma ta juyo tana fadin dadin bakin maza ko tun yaushe muka wuce

wurin cikin wani tsawa yake fadin .

Aziza kifice muna daga nan tunnkan ranki ya baci dani da daren nan yadda ya fada tasan komai zai iya

faruwa a lokacin kamar yadda ya fadi.

Yasa ta juya ta tafi ya dan bita da kallo yana fadin stupid mara hankali kawai wawiya da bata san ciwon

kanta ba kawai ?

A dake hindu din da gabanta sai faman faduwa yakeyi tun fara wanan rikicin nasu ta dago tana

kallonshi fuska a dake tana fadin ka gama a kwashe kayan ?

Ina zuwa bari nabi wanan mara hankalin in mata worning ya fada a fusace tace akan me aibadakai tazo

fada ba danine nida nashigo masu rayuwa ?

Bin hindu din yayi da kallo ya dauka bata iya irin wanan ba sai gashi yaji tana fadan magana haka daga

bakinta.

Tana hakan tashiga tattara kayan dayaci abinci din wanda a baya sai dai da safe a kwashesu daga inda

yaci din wani lokacin har rana suna wurin sai idan an tashi wanke wanke ko yayi bako zaisa a kwashe.

Sai gashi hindu din tun a daren ta kwashe ta tsabatace wurin tana kara fesa kamshin datazo dashi a

hannunta kafin ta koma dakinta don tayi shirin kwamciya a lokacin.

Ba abinda ya dagawa Aziza hankali sai yarinyar data gani a zaune irin zaman nan na ni dakai kawai ga

uban kwaliyan da tayi na daga hankali dole yau ya sake mata layi a gaban yarinyar nan har yana fada mata wai ba ita kadai bane ai to dawa ke nan da wanan yarinyat ke nan yake nufi ko me ?

A kwana daya har tana neman kife mata gwaunatinta wajenshi bayan uban kudin data kashe wajen

gyara da mallakan shi ita kadai wanan ma ai ba zai yuyu ba da sake wallahi.

Wai harda munafukin gaisuwanta ita ga mai ladabi ita za a nunawa ladabin shegu a gabata makirci

zallah wasa take bata san ko waye Aziza ba ke nan ?

Ranta a mutukar bace haka ta rufo kofa ta zauna falo ta raba dare a zaune a falon kafin ta samu ta

mike zuwa ciki ba abinda ke mata yawo sai cin mutuncin hjynshi da nasa a yau ita Azizza zaiwa hakan a gaban kishiya ?

Dolema ta nunawa yarinyar nan bata kai ba wallahi sune katsina ta dikko badai tsoro ba zasu buga

agani wa zai bar wani a gidan nan ita da itane shege kafasa a cikin ruwan sanyi zatayi waje road da yar banza cikin kankanin lokaci.

Irin huduban da shedan ke mata ke nan a lokacin ta raba dare sai kusan asuba ta samu barci ya dauketa

saboda kishi daya rufe mata zuciya.

Washegarima ta jima bata fito daga part dinta ba har lokacin da ya tashi daga barcin safe ya karya ya

fito fuska na annuri irin na wanda yake cikin farin ciki a lokacin.

"Da part din Na,ima ya soma inda ya shiga ya samesu tare da yaran suna karyawa suka gaisa da ita yake"

tambayan kwanansu ta amsa da lafiya sukai dan hira da yaran sama sama.

"Ya fito rike da yarinyar Na,ima din karama zuwa dayan part din wajensu ya gaisa dasu ya shiga yadda"

yaga Nabila tana mashi kallon banza yasa ya maida hankalinshi ga yaran.

Kafin ya fito ya shiga wajen azizza din wace ya sama a kwance saman dogon kujeran dake gefe daya a

falon itama din kallon banza ta watso mai sai dan murmushi yayi kawai bai tsaya ba ya juya ya fita.

Sai hakan da yayi kuma ya kara bankata mata rai watau ba zai tsaya ya san tayi fushi ko tana cikin

yanayi na bacin raiba haka?

Daga dakinta sai kitchen ke fito da ita waje bata kara kula ta fito cikinsu ba duk da tana jin motsinsu a

tsakar gidan harda muryoyin uwayen gidan daga kitchen.

Tana sane taki kulasu don yawan zama irin hiran nan daga nan ake samun daman fahintar ta inda za a

shanmace ka ba dai zatayi zaman gaba dasu ba amma zata kiyayye tsakaninsu yadda ba za a samu matsala daga bangarenta ba.

Abunda ta yarda a zaman irin wanan kada kayi zalunci ko sheri ga abokin zama don karshe sai lamarin

ya kwabe ya baka ruwa ka koma daka sani don haka ta daukarwa ranta cewa ba zata yarda ta bada kafa da wani matsala zai fito a wajenta ba.

Sai kuma aka koma gulman hakan ana fadin ita wacan metake ji da bata fitowa ko jira take mu sameta

a wajenta ne ?

Nabilace ta soma magana irin hakan tsuki Azizza taja tana fadin wani dan iska zai bita sau wanda ya

mayar da kanahi banza ko niko kallo bata isheni ba balle banda farin fatan meye a cikinta banda takaici.

"Na,ima dake jinsu ta danyi murmushi tana fadin bata da matsala don ban ga matsala gareta ba gaskiya"

kawai bakuntane bata saba damu ba tukun.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/9, 9:21 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Shekara goma sha hudu tsakani da wanan labarin abubuwa sun faru da dama rayuwa ta gangara a yanzu

wasu girma ya soma kamawa wasu kuma sun cigaba inda wasu ana nan jiya wa yau dai a rayuwan.

Tana sanye da dogon riga mai ruwan ja mai zanen filawa farare ba sol ba daga kasan rigan sai gyalen

daya rufo kanta amma bai wani rufe gashinta mai santsi da shekin baki ba daga gaban kan.

Kayan sun matukar karban jikinta sosai don sun mata kyau a jiki ga zobuna guda ukku data saka a

yaysun hannunta wanda ba sai ka tambaya ba kasan gold ne haka duk da rigan mai dogon hannune idan ta daga hannu zaka iya hango awarwaron dake saye a hannunta suma dai gold din ne.

Tana sahun first class a cikin jirgin yayin da ake sanarwa jirgin zai tashi daga Dubai zuwa Nageia na ciki

su shirya don haka kowa ya shiga daura dammara a jikinshi.

Salma dake zaune tun shigowanta rike da wayanta a hannu ta dago don daura nata belt din tana

kokarin daurawa ta samu ya dauru ta sake nufashi tana kashe waya tare da ajiyan zuciya ta dago kai kenan don ta gyara zama suka hada ido da sauri ta kawar da kanta gefe daya.

Duk da ta kawar dakai daga kallon gefen jikinta ya bata ita yake kallo ta a daidai lokacin kuma jirgin ya

"daga a hankali take addu,an sai dan bakinta dayasha janbaki kawai ke motsi ta a lokacin."

Saida jirgin ya koma normal ya zauna a sararin sama da kyau a lokacin ta bude dara daran idanuwanta

masu tsananin haske tsakiyan kamar an diga ruwan zaiba a cikinsu tana sauke ajiyan zuciya lokaci guda tare da gyara zama tana sauke ajiyan zuciya.

Sai lokacin ta dan waiga shima ita din yake kallo a lokacin dai tambayan kanta tayi da ina tasan wanan

guy din da shima murmushi yake mata na sani ko kuma kama da wata.

A hankali ta dauko airphone dinta ta manna a kunnuwanta wanda zai hana mata jin yanayin komai a

lokacin ta lumshe idanuwanta sai barci.

Jirgin dai Allah ya kawoshi Nigeria lafiya inda ya sauka a garin Abuja yan uwa da abokan arziki sukazo

tariyan yan uwansu sai dai bata ciki dan ita din ba kowane a yanzu yasan da zuwanta ba kasan.

Kusan tana daga na karshen fita daga jirgin haka tazo ta gitta ta gabanshi yana zaune yana waya

wani kamshine ya daki hancinshi a lokacin dayasa saida ya lumshe idanunshi bai shirya ba saboda dadin kamshi da yaji har cikin kasan ransa.

Kafin yace zai yunkura ya tashi ta bace mashi daga gani haka ya tako matakalan benen jirgin ya sauko

ransa a bace duk sannu da zuwan da yaransa keyi mai bai iya amsawa ba lokacin don takaici don gani yake kamar sune sukasa bai samu daman tsayar da yarinyar ba a lokacin.

"Tana bayan motan a zaune a bayan motan da ma,aikata ta turo daukanta sai bin garin take da kallo"

gaba daya kasan ya juye mata a sanin da tayi a baya don yanzu gaskiya akwai cigaba sosai da aka samu.

Wayanta ta dauko tana bin address din gidan yayan nata kamar yadda ta kwatanta mata a waya har

Allah yasa suka shigo unguwar na maitama inda take bin gidajen layin da kallo har tagano number gidan da aka kwatanta mata din tace mai mota ya dakata a wajen.

Dan murmushi ta saki a fuskanta don zataga na gida a yau zataga yar uwarta da suka dade basu hadu

ba tsawon shekaru goma sha.

Layin da ta saya a hanya ta saka dashi tayi amfani ta kira layin yar uwar nata dashi ya shiga ta dauka

suka gaisa ta soma fadin kina cikin gidane in sbigo ?

Wacece ke magana aka tambaya kima gidane nace ta sake fada ina nan jin hakan yasa ta soma kokarin

sauka daga motan.

Ina ciki wai dawa nake magana ta fada ta karasa fitowa daga motan ta nufi get din gidan tana

kwankwasa aka amsa daga ciki maigadi ya leko yana tambaya.

Don Allah nan ne gidan engineer Ahmed kt ya amsa da nan ne ta juya gun driver ta sanar dashi ya

soma sauke mata kayan daga cikin motan zuwa bakin get din gidan.

Tabashi kudinsa ta juyo tana takun kasaita tankar wace ke tsoron taka kasa a lokacin gashi kamar iska

yana kadata don yadda take takon.

Maigadin ya bude get din da sauri don yasan bakuwar gidance duk da baiji hausa a bakinta ba a

lokacin amma taso zubi da yanayin hjyn gidan zaice.

Tsaye take tana tunanen to waye wai ta kirata haka koma waye bari tayiwa maigadi magana idan ta

karaso ya sanar mata a daidai lokacin taji karan budan get din yasa ta tsaya daga baya tana duban maishigowa din.

Cikin mamaki take bin yar uwar da kallo tana fadin wai wanake ganine kamar Salma daga saman bene

kafin ta juya da sauri don ta sauko kasa.

Sun hade suka rugume juna a cikin murna da jin dadin ganin juna a lokacin aka soma murna da ganin

juna tace yayan mu nayi kewanku da yawa ?

Tace Salma baki kai mu ba ai muda kullum sai munyi zance a kanki da inda kike tayi murmushi tana

fadin yaya fa ?

Ya tafi office sai dare zai dawo gidan nan idan sun taso jan hannun yar uwar tayi da mamaki zuwa ciki

inda ta zube a kujera tana lumshe ido.

Wai Salma yau kece a gabana don Allah yaya Farida ta sake fada salman tayi murmushi tana walwale

dan gyalen dake daure a wuyanta tace nice yaya ai ban fadawa kowa zuwana ba don in baku mamaki.

Ban son ace sai anje tarona kafin ka iso kowa yagama sani duk a dameka da waya din nan haka dariya

"faridan tayi tana fadin halin dai yana nan na gudun jama,a ko ?"

Idon ta dayi har dashi har garza garzan giran idonta mai kama da tayi kari sukai harr lokaci guda take

fadin surutune banso yaya hayani yana damuna da yawa wani lokaci.

Nidai bari na kawo maki abinci nasan wanan safiyan haka tafiyan dare kukayi ke nan ta amsa da ehh

mun taso can da darene ai amma kada ki kawo min komai yanzu wanka kawai nake son inyi indan huta.

Kai ta girgiza tana fadin wallahi salma kin koma irin mutanen can wa zaice ke din yar kt ce idan ya ganki

haka inba hausa kikayi ba hausan takima a yanzu kokarin kwancewa naji yanayi ai.

Mama fa dasu yaya hindu ta fada tana kara lumewa a jikin kujera mama na nan lafiyansu kalau wallahi.

Baki tambayi baba ba sai ta dan bata fuska kadan take fadin yaya yake wajensu yana lafiya kalau

kwanan nan mukaje katsina baba Alu badai lafiya muka dubosu har kaduna muke wajen mama ai saidai bamu kwana ba muka juyo.

Har yanzu wanan tsohon yana nan faridan ta amsa da baba Alu yana nan saidai ya kara tsofa yanzu

tsoho mai ran karfe yana nan kuwa tsaye dinshi.

Mai aikinta ta kira tazo ta dauke kayan yar uwar nata zuwa dakinta tare da kawo mata ruwan sanyi

tazo ta dauka ta koma ta kawo ruwan kamar yadda aka umurceta dayi.

Bata jima a falon ba ta mike zuwa ciki don ta watsa ruwa din ta huta itama farida mikewa tayi ta

biyota da hand bang dinta da sauran kayanta data bari a falon.

Gidan nasu ba laifi sama da kasane irin ginan zamani din nan komai akwai a ciki na more rayuwan dan

Adam sai hakan ya tuno mata baya lokacin da gwaggo hafsatu take masifan bata yarda Ahmed ya dauko farida zuwa nan Abuja ba.

"Saidai ya barta can katsina yana zuwa idan ya samu lokaci sallon ta biyoshi nan din a samu sa,an kwace"

mata da saida baba Audu ya tsaya ya nuna mata shine ubansu shine mijin kuma ita mata ta hakkura da zuwan nata.

Me kike tunane haka zaune farida data shigo tana aje kayan take tambaya ta bata amsa a takaice da

gwaggo hafsatu right lokacin da take masifan bata yarda azo Abujan nan dake ba