Chapter 31 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

murmushi

naja plate din zuwa gaba saidai ba zan iyaci ba gaskiya a gabansu.

Shiko ya saki jiki sunaci suna hira da dan uwanshi wanda hakan ya nuna sabonsu yana nan har yanzu

yadda suka taso kanana a baya.

Yayane karona barkatai takoma fadin Salma fa ta kasa sakin jiki taci komai kunyar wa takeji wurin nan

wai nan fa duka yannaneki kada ki bari a shamceki ?

Gaba dayansu dukkansu suka maido hankalinsu gareni suna kallona yaya Ahmed ke fadin kunyan wa

zataji cikin mu niko sulaiman mai koranta ta saka dan kwali ?

Murmushi a sanyayye na kara sakewa a fuskana na dauki gutun bread din mai hadi na dan gutsura tare

da daukan ruwan shayin na dan kurba zafinsane bai mun ba hakana dai na daure na dan kurba na aje cup din.

Naji yaya Ahmed na fadin kokefa salma yar uwarki duk ta damu wai bakici komai ba tun jiya nace ta

barki zakici ai dole tunda yunwa baisan sarki ba balle bafade ba ai?

Wani irin lumshe ido yayi yana gyara zama a cikin kujeran da yake zaune a kai wayarshi yake latsa a

hankali can ba tare daya dago ba .

Cikin muryansa mai amon sautin a hankali yake fadin ba wai bata ci bane abincinne na nan yayi mata

nauyin ci a yanzu.

Saboda a can ta saba da shan coffe da dan snack a tsatsaye a can din so sai mutum ya duba idan yaci

mai nauyi haka cikinsa ba zai dauka ba ai .

Aiko akwai aiki gaskiya saukin abin indan kin sauka gidan mama shari dama can kike ai amma wajen

mama kam kinsan sauran tuwone abjn karyawanta a gidanta.

Yar autan mama zatabawa tuwo haba dai don Allah aiko da munci mama taran hakan yaya Ahmed ke

fadan hakan gareni nidai ina dan masu murmushi kawai bance komai ba.

Kai Ahmed muje kada in makara ya fada yana mikewa tsaye yaya Ahmed din shima ya mike yana fadin

kaga na manta da zaka fita fa mun kusa makara ai yana duban lokaci a jikin agogon dake manne a falon nasu .

Ita dai tayi masu a dawo lafiya nikan a hankali na sauke ajiyan zuciya don sai naji kamar an cire min

kaya a lokacin don a takure nake gabansu dama.

Saida ta dawo take fadin kinga yaya Sulaiman ko salma bari inawa hindu baki ciki sosai na rashin

hakkurin da batayi ba a lokacin ta zauna dashi.

Gashi yanzu duniya a hannunsu yake kinsan ya koma garinsu daga baya bayan rabuwansu da yayan mu

ina zan sani na fada ina share zancen.

Wallahi ya koma wajen dangin babansu ai yanzuma gaba daya bai damu da katsina ba ai can Jalingon

yafi bada karfi sosai .

Yayi ta karatune ai shi bai tsaya ba irin na yaya yana ta karatunshi yanzu haka ya zama professor a

karatu saidai kuma yana bussiness sosai a yanzu ga gwaunati kuma tana damawa dasu.

Amma yaya taki hakkuri ta zauna dashi yanzu gashi Allah ya buda mashi ya zama done suke fada aji .

Nan ne gidan zamanta tunda kikaga ta zauna a nan din na fada cikin damuwa naji tace ba laifi gaskiya

don shima da nasa kokarin sosai wallahi gashi ya barta tana aiki kuma yanzu.

Yaranta nawa na tambaya tace biyune ta haifa dashi mana duka maza da ukkune na farkon yazo ba rai

ai kinsan halin gidansu da kishin tsiya karma ace mutum biyun nan da Nabila da Azizza dasu take ta kwamawa har yanzu.

Ita Azizza din saita fita kuma ta dawo kamar auren jaraba tsakaninsu wanan fitan na karshema da

uwarsa tayi fada tace sai ta fita gidan danta kuwa.

Mikewa nayi ina fadin ina zuwa yaya bari na duba sim dina idan ban barshi ba a can wajen sauri take

fadin Allah yasa kinzo dashi dai na amsa da Amin na haye sama.

Kwanciya nayi bayan na duba sim din ina son in dan runtsa a lokacin saidai kuma barcin ya gagareni a

yanzu don nakai gejin kwanciyan har yakai banjin dadi nasan don wahalan dana shane kafin na dawo.

Suna fita yake fadin yaya akayi yarinyar nan karama haka ta samu fita karatu waje yake tambaya cikin

basarwa ga Ahmed din.

Kasan abin Allah idan Allah ya nufa zakai abu babu mahalunkin duniyan nan daya isa ya hana hakan

gareka.

Anso a hanata fita din uncle hussaini ya samo mata karatun ai ita da danshi sukaje lokacin yana cikin

ganiyar kudinsa din nan .

Wai kasan ina da burin taimakawa bawan Allah nan a rayuwa abubuwane sukai min yawa a yanzu nake

mamtawa dashi wallahi.

Uncle mutum ne mutumin kirki mai son yan uwa da zumunci kuma ka duba fa irin dawainiyan da yayi

tayi a lokacin.

Daga gefe inda yaya Ahmed yake zaune yayi dan murmushi mai sauti mai nuna maganan ciki kafin ya

dora da Allah yabada ikon hakan komai sai Allah ya nufa ga bawa ai.

Nikan ai dole ina dan hinta mashi sosaima kuwa don ban manta mafari ka kyauta gaskiya dashi da

mama dije suna da matukar kirki wallahi koma ince dukkansu don ban taba ganin yan uwanda suke da kaunar juna irinsu ba a duniya.

Da karfi da yaji dai sun dauke mama daga katsina har yanzu saidai tazo ko har gobe kuwa hakan ai yafi

mata kwanciyan hankali don Allah.

Yanzu baba dai ke zuwa can din yayi kwanaki ya dawo kasan halin mama Asiya koshi saida ya nuna

mata namijin gaske yake aka zauna lafiya.

Subbahanallahi wai meya damuwansu da boyar Allah nan ne don Allah na rasa meya kawo wanan abin

basu kaunarta haka ita da diyanta.

Hslin matane kawai bandashi meye kuwa kayi kokari sosai Ahmed da baka saki farida ba a lokacin

yadda mama ta matsa akan sai ka rabu da ita a lokacin.

Nasan waye mama fa Sulaiman kaima kuma ka sani akan me zan yarda in shiga zancen mata dani da

farida din inga kara ai duk diyanta muke ta dalilin ba.

Lokacin sunso su bugawa mutumin nan zuciya wallahi kwanansa ke gaba don daya wulla tuni da yanzu

an manta dashi ko .

Mama mama uwata ta kaina sulaiman din ya fada yana murmushi tare da girgiza kai don tuno wani

abin da yayi lokacin sai dai bai furta a fili ba .

Don furtawa baida amfani a yanzu duk da har yanzu ana sarke da juna don ba a taba rabu tunda an fito

waje daya amma wanan matar da badon mahaifiyar Ahmed bane da tuni ya rufe babin xumunta da ita ko a yanzu.

Duk da yarsu dake gidansa sunyi abubuwa da dama nacin fuska da ba zai iya mantawa dasu ba sai

gashi a yanzu da Allah ya maidashi wani abu sune suke nuna an wahala dashi din.

Jamila tana jalingone har yanzu Ahmed ya jefo mashi tambayan daya katse mashi tunane a lokacin ya

dan ja tsuki yana fadin tana can har yanzu banjin zan dawo da ita garin nan nan maza sai ta koyi hankali da natsuwa tukun .

Wani hankali kuma ga mace kamar Jamila ake nema a yanzu ka dai kara hakkuri kawai don abin kamar

haline haka rayuwansu yake da tainawa mutanen dake kusa dasu wayau.

Aiko su mama din da sukai hadin a yanzu ba kyalesu tayi ba don wancan zuwan mama tana min korafin

wai tazo katsina har ta koma bata shigo gida tagaida ita ba.

Kaji rashin hankalin ko katsinan ma da taje ai ban sani ba sai daga baya ita inna ke fada min ta dauka ba

zan sani bane kawai dai na bartane sai ranan dana gama tara mata.

Wayan Ahmed din aka kira yasa suka katse zancen shi kadai yacigana a zuciyarsa ba karamin tsuyesa

akayi ba a rayuwa hadashi aure da wanan yarinyar da yayi nadama yafi a kirga a rayuwanshi.

Daga kwancen da nake abinda nake tunane shine ta ina zan soma a yanzu gashi ban fadawa kowa irin

rayuwan dana gani ba a can na wahala.

Karatun kan nayisa Alhamdullahi amma an wahala fiye da tsamanin mutum don saidana hada da aikin

part time na samu na karasa na dawo din nan .

Saboda kawun mu daya samu matsalan rayuwa dama kuma haka rayuwa take game imani yau a

jerabeka da samu gobe a hana maka wanda hakan yana faruwa da mutane da dama a cewan manya baiwane irin hakan .

Don Allah na kaunar bawansane yasa wata rana ya tashi da samu wata rana kuma ya rasa irin haka

bawa mai imani sai ya kara tuna Allah dayane ya dinga istigifar da neman yafiya gun ubangijin talikai.

Nasan idan mun zauna da yaya Farida zata ban labarin halin rayuwan da uncle hassan din ya shiga a

yanzu wanda nake fatan in samu in rama irin abubuwan da yai muna na rayuwa.

Yaya faridace ta turo kofan dake rufe ganina ba barci nakeyi ba take fadin ashe ba barci kikeyi ba na

zata ai kin koma barcine kuma ai ?

"A,a na dai kwantane take fadin ina kika bar Boy ne wai ko shima ya dawone tunda ya gama karatu aiko"

ayanzu ?

Banda labarin shi yaya kinsan ba kasa gufa muke ba ai na bata amsa a takaice don kada ta zure a cikkn

hiran da muka somane na yan uwa ta dauko min labarin irin halin da ake ciki yanzu a kasan.

Ai yaya yana tambaya ko gaba daya kin zo da takardun ki a fara nema maki aiki dasu nazo dasu yaya ai

ban bar komai nawa mai muhinmanci ba a can.

Itama Aziza banan nan nan zata kare karatunta ai nayi murna sosai ina fatan alheri zan so ganin mama

kafin na zartan da hukuncin da nake son in dauka din a kaina.

Farko zabin iyayyena dole zanbi idan sun amince min da zama a Abuja nacigaba da aikina a yanzu

hakan zai min dadi sosai a tayuwana idan kuma sun hana saidai in zauna gida kaduna a gabansu na samu abin yi kuma.

Kusan a yanzu kasan nan ba karatune da wahala ba aikim da zakiayi shine abin wahala koda kasamu

din sai kuma ya kasance ba a bangaren dakafi kwaraiwa bane aikim zai fito maka .

Komai damace a yamzu matukar kana da long lef kana da wanda zai tsaya maka samuwan aikin baida

wuya da zaran an zube kudi masu yawa aiki sai ya samu gareka.

A yanzu ba zance ina da wani tsayayye da zai tsaya min har aikin ya samu gareni hakaba wanan yana

cikin abinda yasa na tsaya garin Abuja din a yanzu kafin na karasa gida wajen iyayyena.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/12, 9:52 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Tunanen yanayin rayuwa a yanzu ya hana rayuwana hutu saidai lokaci daya na tattara wanan abinda

shedan ke son kawata min na rudin duniya na barwa Allah zabin shi a kaina.

Don haka na sawa raina zancen zuwa gida kawai alokacin ba sai na tsaya nan din nayi wani planning ba

duk abinda Allah ya nufa ga bawansa daidaine a wajen Allah matukar ka rugumi rayuwa a yadda yazo maka.

Da niyar washegari zan fadawa yaya farida zancen wucewana kaduna na kwanta barci sai dai washegari

din kuma ina kwance a dakin da safe misalin goma na safe

Tashigo tana fadin Autan mama wai barcine haka salma ki tashi kici abinci mana har abin kari yayi sanyi

fa kina kwance.

Motsawa nayi ina mika na yayye rufin jikina ina fadin rana yayine ashe sai tayi murmushi tana bude

min windon dakin tace kigani da idon ki.

Na sake hamma gami da mika ina fadin gashi ina son in fita idan kayana sun shigo yau din nan na dauko

gobe in wuce zuwa gida kaduna ?

Takai zaune bakin gado tana dubana tare da fadin na zata zaki kwana muna biyune ai a nan don har

ina kokarin nasa a gyara maki daki da zaki zauna a ciki ?

Don zakifi jin dadin zaman Abuja da zaman kaduna a yanzu don ba kowa gidan kamar da da muke da

yawa inba azizza bace ta dawo ?.

"A,a ko zan zauna ai dole inje inga iyayyena ko shekara nawa nayi rabona dasu, bansa su a idona naba"

yaya?

Tace kina nan zagi gansu indai su mamane shigowa Abuja yazu a wajensu kamar habone .

Don mama shari tana shigowa kan matsalan idonta mamace kuma ke rakota duk zata zo din nasan

zuwansu yasa ban yi maganan kije ba ai don nasan zasu zo din kwanan nan.

Kinsan yaya Nuratu tana garin nan itama da maigidanta saidai ba a unguwa daya muke ba sai kin huta

nasa a kaiki suna can a gwarinpa.

I No i cant wait sai sunzo gara naje din na samesu a can dai zaifi na fada ina mikewa tsaye.

Yar Auta ke nan kekam kiji dadi an barki kina fantamawa a gida haka keda Azizza tunma ke din nan

mama shari da mama sun tsaya maki ba a ko zancen aure gareki yanzu .

Mukan ko bari mugama huce karatun jerabawan karshe ba ai muna ba ai tsoho yasa aka yaba muna

ruwan lale zuwa gidan maza.

Dariya nayi ina fadin amma kuma auren ai yai maku dadi ko ba gaku zaune da mazajenku lafiya ba ?

Tace ai da a barmu ko karatun mu dan soma yanzu dai Allah ya taimaka ita yaya tayi karatu ta samu

yanzu tana aikinta nice dai yaya ya hana aiki a yanzu kuma .

Ai nima tunda na dawo nasan zancen aurene yanzu gabana shiyasa nake son indanyi nisa dasu tun kan

a bata min plan dina da zancen wani aure can.

Wa zai naki zancen aure yanzu keda ko saurayi kila baki dashi yanzu kinsan dai basu farawa suce zasuyi

maki irin abinda sukai muna ai ?

Kin sani ko don haka wanan tsohon mai taurin rai ya tsaya duniya bai mutu ba dariya sosai na bata a

lokacin na wuce ina fadin da saidai yaje ya zauna a matsayina gidan.

Wanka nayi bayan nafito na gyara jikina na saka wani dogon riga daga cikin kayana falon na nufa don

in karya nan naga yaransu a zaune falon don ranan ba school basu fita ba suna gida lokacin.

Yaran suna ganina suka nufoni da gudunsu zuwa jikina na hadesu duka ukku na rungume a jikina ina

fadin hello my dear kun tashi lafiya ?

"Nafada ina shafan kansu tare da jin kaunarsu yana shiga min a raina yaran daban sha,awansu ga kuma"

tarbiya da suka samu tsagwaru irin na bahaushe don ko bayi ka fito idan suna kusa sai sun gaida kai da fitowa.

Hannunsu naje muka nufi dinning dinsu da gaskiyan yaya don abincin yayi min sanyi a lokacin na kasa

ci sai sune ma suka karasa cin abincin lokacin.

Amma kai boy banjin kayan danazo dasu akwai mai maka a ciki ina fada na kamo hannun babban dan

yaya farida da muke kira da boy na rike muka nufi kujera.

Ke har tsaraba kika tsaya yowa keda ke karatu aina fada maki tunda kawu ya samu matsala nake wani

aiki a can din ina hadawa da karatu ban zauna zaman jira ba dana wahala.

Sallaman da akayine ya katse muna hiran mu da yar uwata wanda ba kowa bane mijintane tare da

yaya Sulaiman suka shigo .

Yaya din na fadin maman boy kin gashi nan baiko da niyar zuwa yau din fa saida naje na dauko maki shi

nace to ya taso ba zamuyi hasaran abinci ba don an dafa donshi.

Ai daka barshi yaya itama salma bandaiyi magana bane ta kasa cim abincin data diba din ga yaran can

suna ci yanzu haka.

To ta samu dan uwa din shima kinsan haka yake zama cikin turawa ya bata ku a can din banda shitme

ba abinda mutum ke samu na kwarai da zai rayuwa.

Zakice bashi yayi magana ba don ko daga kai baiyi ba balle motsawa daga yadda yake zaune tunda ya

shigo muka gaidashi suka soma magana shine yake fadin .

Akwai abincin sosai ai nan irin wanda ake dashi a can ta samu tana hadawa da na nan kafin bakinta ya

saba da abincin gargajiya.

Nidai ina zaune kurum sai wasa da nakeyi da hannun boy suna ta hiransu inda jefi jefi yake saka masu

baki sukan kamar an hadane dama don kowansu akwai zuba a ganina.

Nan take fadin yaya gaji Autan mama yau kuma da zancen gida ta tashi wai da zaran kayanta ya sauka

zata bar garin nan gobe !

Mama tayi kira ke nan banga laifinta ba shekara nawa bata kusa da mama yanzu kuma tazo kasan ai

"dole taje ta dubasu kingama in tafiyan mu yazo guda zuwa jibi sai mu wuce dake ke,nan ko ?"

Yafi sauki wallahi nan dai zuwa jibi ai kayan zasu iso insha Allahu bari na dauko wayata na fada daga

nan ban dawo falon ba kuma nayi zamana a dakin tare da yaran dake debe min kewa.

An dauki lokaci sai ga yaya din a dakin take fadin yaran su tashi suyi shirin islamiya driver su zaizo

daukansu suka nufi wajen mai aikinsu ita kuma ta zauna muna hira.

Take fafin yanzu muka gama waya da yaya hindu naso fada mata cewa kin dawo sai kuma nayi shiru

nace aida kin fada ko kiban wayan mu gaisa da ita.

Indai itace ko anjima zakiji ta kira ai kinsan gidansu gidan drama ce nace har yanzu tome za a fasa

"tunda ana tare indai kinji rikici ita da Nabilace ko azizza baki taba jinta da wanan Na,iman uwargidansu."

Wai shi me zaiyi da mata haka ya cika gida kamar zai kaisu kurmi ya sayar suko sai faman kishi sukeyi a

kanshi ba ko wace tana nuna itace tauraruwan gidan.

Kinsan ita uwargidan nasu ai yana da wuyane ajisu don yaya ta riketa tankar yar uwa itama tun tana

sanyi yanzu kansu daya .

"Kinsan lokacin da aka kai yaya gidan ai sunso hade mata kaine har ita Na,iman sai yaya din bata kula