Chapter 32 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

su"

ba koda zata tashi yaya ta gyara ko ina a shiyan tayiwa yaranta wanka ta kimtsasu girki kuma indai yaya na gida sai tayi harda nata.

Wananne yasa ta watsar da komai suke zaune lafiya a yanzu da yaya ko abu zasu saye tare suke sayen

abinsu saidai a gansu dashi gidan .

Sukuma sauran sai suke jin haushin hakan suka dauki laifin suka mannawa yaya wai itace take saka ai

hakan don a tura masu takaici.

Na tsani irin rayuwan nan wallahi a zauna aita jidali ana fitina irin rayuwan gwaggo Asiya ke nan kullum

da sabon fitinan da zata kawo a gidan mu.

You know what yaya wallahi abubuwan da akaiwa mama a lokacin koda nake yarinya har yanzu ina

tunosu a raina irin yadda baba ya dinga musgunawa mama a lokacin.

Ba abinda ya tsaya min a rai yaya sai irin kukan da mama keyi a cikin dare kuka mara sauti kukan dake

zamawa mutum lalura a rayuwa wanan ya kasa fita min rai har gobe ina jin sautin wanan kukan a cikin kunnuwana yaya .

Yanayinta naga ya sauya lokaci guda ta soma fadin bake kadai ba Salma mu duka ai wanan abin ba

zamu iya mamtawa dashi ba a rayuwan mu.

Duk dauriyan mama kada mu gane damuwanta a lokacin kinga koke karama kin fahinci halin bakin cikin

da take a ciki gashi ya kasa fita maki rai har yanzu balle mu dake da girman mu a lokacin.

"Wanan yasa kikaga har na girma baba bai cikin raina yaya idan na dubeshi abubuwa da dama,ne nake"

tunowa game da wanan rayuwan.

Shiyasa kikaga ina ji da kawu hassan bawan Allah nan yayi a rayuwansa sun fahinci idan basu dauketa

daga gidan nan ba a lokacin komai na iya faruwa da ita wata kila da mun rasata a lokacin.

Amma suka rufe ido don su cece yar uwarsu duk da an bar kowa a katsina amma haka ta daure ta

zauna a kaduna ita kadai.

Murmushin talaici nayi lokacin don jin abinda yaya din ke fadi wanda ni kadai nasan yadda nake ji a

raina kan mutanen nan da suka hana muna uwa zaman aurenta a dakin mijinta.

Suka sa rayuwan mu ya koma hannun dangin uwarmu a yanzu duk da ana cewa wai an shirya banga

wani shiri ba a nan da tsufansu ansakasu yawon hanya akoda yaushe ?

Muma bar zancen nan Salma din abin baida dadin tunawa wallahi kinga gwaggo hafsatu dai

sarakuwatace a yanzu ko ?

Wallahi salma na kasa sakin jiki da ita ko yaran nan idan muje katsina har muka shiga gidan muna wajen

gwaggo laraba gaba dayan mu wanda hakan bai mata dadi.

Niko na fake da itace uwar mijina ai shiya muke mata kara na fada inda sako zai kai mata kuma naga

alaman taji don takanyi irin hausa a fakaice din nan tace min ko naki ko naso dai itace ta haifi ubansu ban isa in rabata da jikokinta ba.

Abin ban haushi kuma salma ita bata iya masu irin yadda gwaggo laraba ke nuna ita kakane a garesu

tundai boy da bakin jinin dakin mama ya shafeshi takan ce duk mugun halin yan dakin mu ya kwasa na miskilamci da tsanan mutane .

Shiko baba cewa take wai duk kakan mu dan kwara ya kwaso bai dauko gida ta ko ina ba kinji wani

sabon sheri kuma sale salin tace ba dan yaya bane wata rana.

Ai bata isa ba wallahi na bada amsa tace aidata ga wuri data fadi hakan dan nata bai bada kafan da za

a fadin hakan bane ni idan ance zamu katsina kamar inyi ihu lokacin da bamu da muhalin kan mu.

Na tsani wanan hadin gidan da akeyi gidan mu idan bake ba yaya waya dace don Allah kaf cikin irin

hadin nan ki duba su yaya kulu yadda suke fama don Allah da mazajensu.

Bamuyi aune ba sai da mai aikinta ta shigo tana fadin hjy me za a girka da darene yasa muka san lokaci

yaja ta mike da sauri tana fadin subbahanallahi ta fita.

Ido na lumshe a hankali ina tariyo hiran mu akan matsalolin gidan mu wanda ya kasa gushewa har

yanzu wanda ba kowa bane ya ja hakan saisu matan gidan da kansu da suka kasa zaman lafiya a tsakaninsu.

Sukan mazajen gidan daga manya har yara ai kansu a hade yake tunda suna zumuncin su a tsakaninsu

gwargwado hali kuma babba yana jin dan uwa a jikinsa.

Da yamma tare da yaya muka fita zuwa dauko kayana inda tayi mamaki kwarai da shirgina da tagani

"muka dawo gida ana magariba sai dai mun tsaya mun sayo fruit dana nuna ina sha,awan sha."

"Wanka nashiga don nayi tsarki bayan na fitone nayi haraman sallah a ka,idance kamar yadda addini ya"

koyarwa mace tayi din.

"Ban sake fita ba don bayan na idar nagama addu,oi na na dan sha fruits din da mai aikinsu ta kawo min"

na samu waje na kwanta.

******* ******* *******

Tun bayan rabuwansu da yaya Ahmed gidansa ya nufo yana shiga ya zube saman kujeran dake falon

remote ya jawo ya kunna tv yana kallon wrestling saidai zuciyan sa ba wasan kokawan yake kallo ba a lokacin.

Tsuki yaja ya dauki remote din yana yawon tashoshi don ransa ya daina yi masa ciwo akan tsohon

fanin dake damun zuciyarsa.

Akan mace macen ma da yanzu tana gidan wani harta hayayyafa a can din shi yana nan ya kasa samun

sukini a kanta kullum yana fama da sonta a kasan zuciyarshi.

Tun yana saka rai da fitowanta ta dawo gareshi har yake samun labarin haihuwanta da wanan bakin

mutumin mara fasali data zaba sama dashi.

Saidai a yanzu ganin wanan yarinyar ya tayar mai da mikinsa sabo don duk motsinta hindune sak yake

gani tana masa yawo a rai.

Gizon da take mashi yafi komai daga mashi hankalinsa a falke ko a runtse ido itace yake gani a gabansa.

Zai iya cewa wanan din kamace ta jini kawai dake yawa a jininsu amma salma din tafi salma komai da

za a duba a jikin mace.

"Tabbas tun tana karama tafi duk yaran mama din sha,awa da kyau balle yanzu data girma idonta ya"

bude ta zama wata fresh gwanin burgewa a idon kowa.

Karya kake kaima kasan abune daba zai raba yuyuwa ba don akwai katanga mai nauyi a tsakaninku a

yanzu gargadin da zuciyarsa tayi masa ke nan lokaci guda kan tunanen da yayi.

Tsuki yaja yana ba zuciyar tasa amsa da zancen banza ke nan tunda Allah bai haramta ba ai koda kuwa

"ace ya haifu da salma tunda bata tare dashi shari,a ai bai haramta hakan ba ga musulunci."

Jamilace ta fado mashi a rai don itama zamanta dashi yana iya kawo mai cikas don furcin da akace

mama Dije tayi a lokacin baya daya kawo har hindu ta salwance mashi kan zai auri dije hindu ba zata koma gidanshi ba suyi kishi da jamila din.

Zancen banza ke nan ya ba kanshi amsa sulaiman yanzu ba da bane baka under control din kowa a

yanzu sai abinda ka zabawa kanka na jin dadin rayuwanka yanzu .

Matsala shine yarinyar ta soshi don gaskiya ya kamu ya kamu da son yar ficiciyar yarinya karama salma

a kalla zai iya bata shekara goma sha tara ko sha takwas ga haihuwa .

A cikin haka barci mai nauyi yayi gaba dashi ba tare daya san hakan ba shine har da mafalki akan

yarinyar saida kiran da wayarshi ketayi ya falko dashi.

Sai lokacin ya tuna a falon katafaren gidansa yake kwance shi kadai sai wanan yaron sada dake mashi

aiki a gidan yan share share da goge goge da dafa mashi ruwan shiyi.

Hannu yakai ya dauki wayan yana tsuki ya duba waye ya katse mashi farin cikinshi a wanan lokacin

kuma haka ko waye bai kyautawa rayuwansa ba don baikai karshen mafalkin daya soma ba aka tasheshi din.

JAMILA ya gani a rubuce kamar yadda yayi serving din sunanta a cikon wayanshi ya kara a kunnesa

cikin takaici ya soma fadin ya akayine ?

Ka tasone ta tambaya itama a bangarenta zuwa ina fa ya jefa mata tambaya shima a lokaci guda ?

Ba yau zakazo bane naga yau kwanan ka kusan ukku da dawowa ai and so what idan nayi kwana uku

ko goma nayi meye ruwanki da rashin zuwana ?

"Cikin mamaki ta furta a,a bata shirya fada ba a lokacin tace meye ruwana fa kace baban mammah"

muko keda ruwa watanka fa kusan hudu baka kasan nan kuma ka dawo ba zakazo gida mu gane ka ba ?

Tsuki ya kara ja cikin takaici da Allah waddai da rashin zuciya irin na jamila din mace kamar karya da

shegen son maza haka ita dai burinta gudane yazo su kasance a tare bata gajiya da yadda baya saman katifa kullum kamar harija ?

Ko muzo ne mu yaji ta fada yace wai meyasa baki da hakkurine ke idan kunzi nan din kuyi min me

sallon kizo ki jamin wani sabon bacin rai kuma tunda ba zaki sauya halinki ba ?

Baban mammah tunda aka gama ginan nan gidan nan bamu taba zuwa muka kwana a cikknsa ba burin

"ko wata mace kuma shine,,,,,,,,"

Dif ya kashe wayan don ba zai iya jimirin jin shirmenta ba kullum idan ba rashin zuciya ba harta manta

rabuwansu da ya tafi yana fushi da ita yanzu take neman kasancewa a tare dashi kuma ?

A bangaren jamila mamakine ya kamata haka na nufin har yanzu fushi yakeyi da ita ke nan kan wancan

zancen duk wanda yayi har ya tafi baisa ya huce ba hakana.

Haka kawai zata yarda aita zuwa mata gida kan dan wani dalili can don kawai suna takama sun hada

zumunta dashi saita bari duk wanda ya kwaso talaucinsa yace shi dan uwane sulaiman ya sani.

Dangin miji duk sun hade mata kai suna mata suna mara kirkine ita bata da damuwa akan duk abinda

zasu fada a kanta.

Ita burinta shine kada azo a damesu ana sake masu rani a hanata rawan gaban hantsi a gidanta komai a

saka maka ido a hanaka walawa.

Tasan maganinsa ai mama hafsatu zata kira ta fada mata komai ai dole ya baro abujan koda ransa

baiso yazo garesu.

Bata tsaya sanya ba tana wanan tunanen ta daga waya ta dannawa mama hafsatu din kira ya shiga ya

dan jima ta daga tana fadin jamila ce ?

Ko dazun munyi zancen ku da Lami ai nake fadin idan ba an kira ba baki damu da kikira kiji lafiyan gida

ba ko kin zata rokon da kikace mun dameki dashine zumuyi ?

"A,a mama wayan tawa ce keda dan matsala kwana biyu nake jiran baban mammah ya dawo ya sake"

min wata suka gaisa ta soma fadin

Mama karan baban mammah na kawo maki ya dawo kasan nan yau kwana ukku ke nan baizo gida ba

na kirashi ina zaton yau zai taso shine wai yazo yai muna me idan yazo ?

Kinga bamu gabanshi kenan ma a yanzu ni mama na gaji da wanan halin da yake min wallahi harda

fada min bakar magana yanzu yayi kafin ya kashe min waya.

Gobe zan shirya yaran nan mu sameshi a can Abuja din da sauri mama hafsatu din ta tareta da fadin

karki soma wallahi kindai san yadda akayi wancan karon kika samu kika koma dakinki kan taurin kai ?

To mama idan baizo ba mu sai mu sameshi ai amma Jamila na fada maki kada ki soma in kuma kince

zaki bada miyau bakina ba .

Kin dai san yadda yayi muna wacan karon ke meyasa baki da hakkurine wai akan namiji ?

Duk kikai ganganci takawa tunda kunyi haka dashi kema kinsan matakin da zai dauka a kanki bakyau

kinfi kowa hasara idan hakan ya kasance tsakanin ku dake da uwarki kuke da hasara yanzu ai.

Sam bataji dadin zancen maman nata ba da yanzu take ganin itama kamar shakkun sulaiman din

takeyi ba irin farko ba da suke juyashi yadda suke so din nan ?

Gaskiya dolene ta taka katsina wanan karon ayi wadda za ayi a tsakaninsu kudi ko nawane zata kashe

ba zata yarda ya dinga juyata yadda yaga dama ba haka ?

Ita da kanta zata shiga ta fita ta sameshi a hannunta itama ta dama kamar ko wace mace da mijinta ke

jin kansa a zamance haba abin ya isa haka suna kashin kudi kamar basuyi ita da mahaifiyarta ?

"Da tare dasu mama hafsatun sukeyi sai suka fahinci cewa itama kanta take nemarwa sa,a wajenshi"

donshine suka basu baya suke abinsu yanzu su kadai ita da mamannin nata su biyu.

Ke nan tana nufin da mama Asiya wace suka hada uwa daya da mahaifiyarta ke nan don mama Asiya

din tana da kokarin shiga mata malamai gaskiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/14, 12:06 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Yau shigan kanan kaya yayi shigan tayi matukar karban jikinsa launin baki da jan riga sai agogon hannu

daya daura ya saka takalma bakake kasancewan wandon bakine.

"Sai dan glass daya faye mannawa a idonsa har hakan ya zama masa dabi,a ya fito ya dauki key dinsa"

gami da shafo sumar kansa daya kwanta kub a kansa yasha man gyara ya fito mai da zanen kai kar an tsaya a zana masashi lokacin saboda kwanciyar suman.

Lemo kawai ya tsaya ya kurba yasa kai ya fito daga gidan kai tsaye fita yayi daga unguwar zuwa cikin

gari yaso ya wuce kai tsaye gidan Ahmed a lokacin.

Don tun tafiyan matarshi Jamila jalingo farida ta soma saka mai abincin safe dana dare duk yadda ya

dakatar dasu ita da mijinta suki hakan komai ruwa ko iska sai Ahmed din ya kawo mai abincin gida ganin wahalan tayi yawane yasa ya dakatar da hakan.

Inda yayi alkwaein shi zai dinga zuwa nan gidan yaci tare dashi Ahmed inda ya fake da idan sunci a tare

"zaifi samun cin abincim sosai sukai na,am da hakan."

Tun wanan lokaci matukar yana gari zai kokarta yazo gidan ya samu dan uwansa suci abincin in kuma

baizo ba Ahmed din ba zaici ba sai yakira waya yaji dalilin rashin zuwansa din ?

"Dan ka,idane shi kamar bakin bature al,adunsa da akidarsa idan ka sanshi masu tsaurine shi bai ragi"

bai kari akan lokaci idan ya baka time.

Irinsune saidai su jiraka don alkawari badai kajirasu ba idan kunyi alkwari dasu wanan yasa suke mai

lakani da bakin bature wasu kuma suce dan bature saboda akidan boko dake rayuwanshi.

Yanzun ma gidan nasu yake son zuwa don alkawarin da sukayi da Ahmed din akan zaizo su je wani fili

da Ahmed din ke sin ya saya aminci da amana yasa bai saya ba din kai tsaye sai ya shawarci dan uwan nasa shine zasuje gani a lokacin.

Duban time yayi yaga akwai sauran lokaci bida ga alkwarinsu hakan yasa ya nufi shago ya sayo

abubuwan amfani na gida don yakaiwa farida ayi amfani dashi.

Wanan koda matarshi ke gari yana hakan ga yan uwan nasa wanda halin yana cikin abinda ya kawo

radhin jituwa sosai tsakanin yaya farida da matarshi.

Don ko abu tace a sayo masu ko yara yakan hada ita da farida ya saya masu ko yaran Ahmed da nasa

wanda saidai tayi aune dasu ko farida din ta fada mata cikin jin dadi dacewa yaya Sulaiman ne ya sayo muna ai.

Sai hakan ya fara kawo matsala inda ta soma zarginsa akan me idan ya tashi masu abu zai dinga hadawa

da farida ko yayanta ?

Yakan bata amsa yace saboda ni ba butulu bane jamila bani manta mafari iya abinda yake fada mata ke

nan ya kyale .

Wasa wasa maganan ya fara calculating a cikin dangi inda aka dangata abin da cewa saboda hindu

yakewa farida haka sai suka boye zancen ai saboda Ahmed ne da iyayyensa yasan ya kamata.

Har zancen ya dawo kunnen gwgg hafsatu ita kuma ta dauki zancen da zafi ta fassarashi gida biyu akan

don Ahmed ya kasane zai tsaya sai sulaiman yayi mashi abu ?

Koko mutuwan zuciya takaishi ga ya bari farida tanawa Sulaiman hilla don ya taba auren yar uwarta zai

dinga mata alheri irin haka ?

Ran yaya Ahmed ya baci sosai da zancen mahaifiyar nasa bai boyewa sulaiman din komai ba haka yasa

ya canza sallon akidar nasa yake raba kayan saidai duk kudinsu daya amma bai fasa masu alheri ba din ya gayawa Ahmed shine babba a garesa don yayiwa iyalinsa koshi alheri baiyiwa banza ba ai zumunci yaiwa.

Wani shayi yaje dubawa inda idonsa ya sauka ga kayan cima irin na yan gayu haka zancen su akan

salmane ya fado mashi a rai ya tsaya ya jido su coffe shayin waje iri iri da kyan gwangani irin na waje masu yawa ba tare daya damu da tsadan kayan ba lokacin.

Akai masa packages dinsu ya biya aka loda mai a mota ya nufi gidan dan uwan nasa da kayan niki niki

yana hanya kiran wayan mama hafsatu ya shigo mai a wayan.

Inda ya rage dan gudu ya dauki wayan yana fadin mama zan kira ina hanya yanzu saura kadan in karasa.

Kai Sulaiman kana hanya zuwa wajen matarka ko kana hanyar ina yanzu ta tambayeshi cilin kakausar

murya da zai fahinci ransa a bace yake lokacin.

Ina hanya zanje gidan Ahmed zamu fita ya bata amsa da hakan shima take fadin shi yana lake da

matarsa mai kama da chingun kai kuma kana kokarin wofintar da naka Sulaiman.

Baiyi mamakin jin furcin mama din ba a lokacin don inda sabo ya saba zata nuna a gabanshi tafi

kaunarshi da Ahmed amma sanin hali yasan akwai hassada da bakin ciki da take mashi bayan fage.

Kasan halin jamila ta bugo waya tana min korafi akan kazo yau kwana hudu bakaje gida ba kuma baka

da niyar zuwa saboda me wai kake hakane don Allah ?

Yanzu mama so take saboda ita in tsayar da