Chapter 34 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

sai dan kwalinshi da nayi rolling din kaina kafana plat harf cover ce a saye

sai hand bag dina karama dana dan rika a hannuna.

Na fito da rakiyan yaran da mai aikinsu boy yana cewa zai bini nace ba dadewa zanyi ba ai indawo

wanan yasa ya lake min wai inje dashi.

Tunda na fito na hangoshi zaune a mota nagane dagani sai shine tafiyan ashe na karaso ina gaidashi ya

amsa hankalinsa na kan motan kome yake duba ciki oho ?

Ganin ya bude gidan gaba yasa na nufi can din har lokacin hannun yaron yana a cikin nawa muka karasa

bakin motan na shiga na zauna ina fadin boy ai zan dawo insha Allah.

Na dan bude handbag dina ina duba ko zan samu abunda zan bashi ban samu ba ji nayi an miki min

kudi kamar wanda ya karanci zuciyana lokacin yana fadin karbi ki bashi.

Saida na dan dubeshi naga har lokacin hankalimshi baya kan mu namika hannu na amsa ina godiya na

mikawa yaran da murna suka karba tare da ja baya don motar daya tayar din a lokacin.

Tunda na shiga na zaune ya lumshe idanunshi yana shakan kamshin turaren dana shafa a jiki wanda

komai nawa kamshin wanan turare takeyi saboda yawan amfani dashi da nakeyi a jikina komai na company Dorve nake amfani dashi lokacin.

Are you set ya fada har lokacin bai kallona kamar yadda nima ba kallonshi din nakeyi ba na amsa a

sanyayye da yes yake fadin ok boy ku koma gida kunji kada ku fita ko ina fa yaron ya amsa da kai a lokacin ya rufe glass din motan yai masu horn muka soma barin haraban gidan.

Garin ya burgeni sosai kullum akwai cigaban zamani da ake samu na sauye sauye a zamanance wanda

"ke kawowa al,umma cigaba a rayuwa ba sai mun gani a kasashen waje ba ko muji labari."

Saida muka hau titi da kyau ya dan kalloni gami da cewa Auta yaya dai you seens worried meya faru ko

kadunan ne baki son zuwa mu koma gida ko in kai katsina kuma kai tsaye ?

Dan guntun murmushin iya gefen baki nayi lokaci tare da furta babu kawai nace a cikin wani rauniniyar

murya kamar an min dole a fitan maganan.

Tsayin lokaci muna ta gudu a motan ni har mamakin yadda yake wanan gudun nakeyi a kasan zuciyata

inda nasa a raina cewa sauri yake kada ya rasa abinda zai kashi kaduna din.

Can yake fadin i wander yadda kika iya kwaso kaya haka masu yawa daga can da alaman kinsan kan

garin sosai naso mu saiwa su mama tsaraba aje masu dashi ga kuma motar tacika da kayanki.

Nan ma dai murmuahinne nayi still ko kina tsamanin ba zaki sake komawa bane kika debo kayanki

haka inma akwai wanan tunane ki cire don komawa insha Allahu ya zama wajibi a gareki sai kin kara kari ilimi.

A samu mace a gidan baba Alu da za ai alfahari da ita a kasa ana kwantacen gidan ku wanan babban

nasarane a gareki kinyi kokari sosai wallahi .

Wanan ko yasan dawan gari nima banki hakan ba ai a rayuwata saidai wanan din da yaya na samu har

na karasashi yanzu balle ya dauko zancen in koma kuma uban wa zai dauki nauyina a yanzu kuma ?

Bayan bangon namu yanzu yayi rauni tunda akai mashi makarkashi aka mai sauyin wurin aiki abubu

suka dinga tsayawa tsab a wurin mu.

Sannan yanzu yana min zancen komawa wanda haline ke hakan kaf gidan mu waye zai min wanan

gatan idan ba kawu din da Allah ya tsaga da rabona ba ya kaini karatun a lokacin.

Naji kinyi shiru ko ba zaki koma karatun bane jin meya fada yasa na dan juyo ina fadin wanan ma

opportunity ne kasani yanzu kuma kawu baida karfin kaini karo karatu ko banza yana da wuya su baba su yarda.

Haba dai an an wuce wurin akan me ba zasu yarda ba tunda kowa yanzu zaiga amfanin karatun naki ai

a gidan Allah yasa nace a sanyayye ina gyara zama.

Kawu ai so nake ya rubuta ritaya ya dawo nan abuja ya kama aikin company akwai wani wajen da

abokina ya gina mutum akeso mai shekaru da rukon gaskiya kamar su kawu da suka gwane da aiki insha Allahu fatan da nakeyi ke nan a yanzu don ba a kammala wajen bane yasa ban fadawa kowa ba sai ke

yanzu.

So idan naji zancen nan ya fada yana kada yatsan hannunsa sai abin ya ban dariya yasa har na dan dara

kadan ina fadin wa zan fadawa yaya ?

Dama abinda yake so ke nan yaga na sake don shiru shiruna yayi yawa yasashi jana da hira haka har

"yaci sa,a na sake din ga zancen kawu da yasan in yayi min zanji dadi yasa ya fito da zancen gabana ."

Don a gaskiya lokacin niyarshi ke nan saida ba fada ba din don yana son ya taimakawa kawu din don

haka ko shakikin nasa Ahmed baisan da zancen ba.

Mun kawo wani gari da bansan sunansa ba naga yaja mota ya tsaya ya fita yana fadin sorry dan bani

two mins yana fita daga motan sannu a hankali na sauke ajiyan zuciya.

Tare da tunanen ashe yana magana hakane idan yaga dama don ni sam banyi mai daukan haka ba

gaskiya nafi zaton ma dai ko yanzu daurowa yayi mai din muna biyu kawai a motan.

Mun dan bata lokaci a dan wajen mai kama da kasuwa ana saidai komai su doya irrish tomatos da

sauran abubuwa .

Can ya dawo yana fadin sorry na barki a zaune ko ya shigo mun dan taba tafiya kadanne wayanshi ya

dauki ringing ya lalubo ba tare daya duba a lokacin saida ya dauka ya duba mai kiran nasa yaja tsuki naga ya kashe wayan gaba daya lokaci guda.

Can muna gab da ahiga kaduna wani wayan yai kara ya dauka yana fadin Ahmed ya akayi naso in mun

sauka in kiraka inji ya jikin daddy din yace da sauki don ina dan jiyoshiba lokacin har yana tambayan ashe

bamu isa ba sai naji yace insha Allahu mun kusa karasawa na dan tsaya na sai abune a hanya kada muje masu hakana.

Ban daiji me yaya din yace ba naji yana fadin bata da hankali don Allah kyaleta kawai ya kuma tsaya

sauraron yaya din can yace narasa irin damuwan nan wallahi mace kamar manya niko cikin mata ban taba ganin mara hankali ba irin jamila Ahmed.

Har muka shiga gari yana lake da waya suna wani zancen nikan nasha jinin jikina zakice ban cikin motan

a lokacin.

Sam ban shedama mun shigo gari sosai ba saida naji yana fadin gidan mama za a kaiki direct ko gidan

mummy sharifat ?

Gidan mummy kasan ai a can nakeni dama ok kayan nan yaya za ayi dasu na zata kayana yake nufi na

bashi amsa dasu zan tafi gurinta nake tunda muka bar katsina ai .

Ok ina nufin tsaraban dana saya koda yake no problem barin fara saukewa mama din kada driver yaga

na tsayar dashi sai lokacin na fahinci ashe akwai motan dake bin mu a baya ke nan da wani kayan.

Bai tsaya dogon magana ba dai ya dauki hanyar gidan mama wanda inba da muka shiga unguwar

nagane tsohon tankin ruwan dakw kafe yayi tsaya shekara da shekaru a wajen yasa na fahinci unguwarsu mama muka zo .

Dan nisa dasu ya tsaya inda ya fita naga driver din yana gangarawa zuwa bakin get din gidan da yanzu

ya tsufa don irin na da dinnnan ne dama.

Nan ya fito da wani mutum dake kallon gidan yana sayar da kayan miya naga suna magana yana gyada

kai kafin ya juya wajen driver sukai magana ya ciro kudi ya mika mashi kana ya juyo zuwa motanshi inda nake zaune.

Ya bude ya shigo yana fadin kada nayi laifi kuma wajen mama sharifat yasa ban kaiki ko kusa da get din

gidan mama ba kada hakan ya zamo laifi kuma a gareni daga baya ki dawo su ganki.

An gode da kokari yaya na fada a hankali ya tayar da mota muka bar unguwar mun danyi nisa yake

fadin saukin abin akwai mota a gidan mummy din ko don na duba nisan dake tsakaninsu da mama gaskiya akwai dan jayawa a tsakani.

An daina taxi ne a garin yanzu nake tambaya a cikin mamaki akan me zaki shiga taxi kuma haba dai

hakan aiba girman ki bane yanzu.

Ni wani girma ke gari yaya abinda kega mutum aishine nasa komai a hankali ake yinsa ai muka sha

kwanan gidan muka shiga layinsu yawancin gidajem an sauyasu an canza masu fasalin ginan su.

Nayi mamaki kwarai yadda bai manta gidan ba haka yasa nasan yasan gidan ke nan a kofan gidan yaja

ya tsaya yana danna horn kusan sau hudu kafin wani saurayi ya leko yana duban motan damu.

Saida ya tambaya da nanbne kafin ya juya ciki yana bude get din gida muka kutsa da kan motan zuwa

cikin gidan ya samu waje ya faka motan gefe daya yayin da nake tunanen duniya yau gidan mamane

haka sai mota daya dake tsaye daga gefe sai wani tsohon motansu kuma da gani ya jima wajen bai aiki don har tsyunsa sun nutse a kasa.

Balle murfin motan nayi na fita daga ciki lokaci saurayin ya karaso yana gaidamu da zuwa yake fadin

hjy tana ciki ko yaron ya bashi amsa da tana nan ok zo don Allah ka shiga mata da kayan nan ciki ya fada.

Suka juya na nufi kofan shiga na dosa cikon kaguwan inga uwata mai kaunata da shagwabani wace nayi

shekaru ban gani ba ko muryansu baifi a kirga ba danaji tun zuwana can din.

Hannu na sanya na murda kofan tare da sallama zuwa ciki don komai yana nan yadda yake ba a canza

ba balle gidan ya bace min.

Ina karasa shiga Mama din na hango a zaune ta kafa glass a idonta tana duban wayanta taji sallama ta

dago tun daga nisa nace mummy iam back ?

Wa nake gani haka kamar salma ta fada tana dagowa sai kuma ta saka murya cikin dagawa tana fadin

eeh diyata ta dawo kuna ina ku fito ga Salma .

Karasawa nayi cikon sarsarfa na fada jikinta na makaleta muka zube a saman kujera take fadin uwar

taki ai bata da karfi irin da yanzu salma.

Duk wanda ya fito ya ganmu sai yaja yayi turus suna mamaki don basuji ana zancen dawowan nawa ba

a lokacin.

Nan aka shiga murnan ganina a lokacin keda waye waya kawoki gida mama ke fada cikin mamaki nace

Abuja muka sauka mama daga gurin yaya farida nake .

Shigowan saurayin nan ne da kayana ta soma fadin waiko da gaske ta dawo dinne fa yashigo yana

fadin ina za a kai kayan mummy ?

Aje a nan tukunna aiko dakina ba a gyara ba yau saurayin ya aje muka shiga gaisawa da juna a cikkn

murna yaya badariya yar wajen mummy ta fito da goyonta daga daki tana fadin.

Wa nake gani yau auta kece kika girma haka mamanki na nan tana tausayunki kullum kinyi karama a

cikkn duniya ?

Nayi dan murmushi kawai har lokacin kuma hannuna yana sarke a cikin na mummy din ya sake

shigowa da kayan yana fadin mummy yace zai wuce yana saurine .

Waye ya kawoki ta tambaya nace yaya Sulaiman ne na gidan mu da da yaya Ahmed zamu zo sai daddy

ya tashi ba lafiya suka kaishi asibiti yasa bamu zo ba .

Wai sulaiman dai sulaiman yaushe rabona dashi koba shine akace ya zama wani done ba yanzu mijin

hindu nada ko dan gwaggon ku ?

Nace eh shine dai haba jeka kace ya shigo mana sai kace bako kuma a gidan nan ai a da can suna zuwa

gidan nan da mijin farida din.

Yaron ya juya zuwa masa iso a tare suka shigo dashi ya shigo da sallama inda mummy ta kasa boye

"mamakinta tana fadin a,a,a sulaiman ai in a hanya na ganka ba zan shedaka ba wallahi."

Ya tsaya sun gaisa din lafin yace zai wuce don yana da meeting kada ya makara kudi masu yawa ya

ajewa mummy din da zai fita nan ta kallonsu tana fadin ko ruwa baku kawo mashi ba ?

No nagode ina azumine mummy ya fada ta mike rike da hannuna muka fita tare har kofa yana ta zauna

ya gode amma saida muka kaishi kofa ya tafi muka dawo ciki aka dora sabon murnan yaushe rabo.

"Nan dai mama ta umurci da akawo min abinci naci ban iya cewa a,a ba na bari aka kawo din na dan"

cakula sai hira suke jana dashi niko duk nagaji saida zan dauki magani a jakata na tuna na barshi ashe a motan kuma wajen murnan ganin gida da uwata .

Ko can gidan mama ba karamin daurewa nayi ba daya tsaya din nan kamar nayi tsuntsuwa na shiga ciki

naji amma na daure na dake ban nuna hakan ba a lokacin.

Dan salatin da nayine yasa suke tambaya nake fadin na manta da jakata a motar yaya din saboda doki

yau zakiga uwarki ko yaya badariya ta fada.

Zai dawo dashi ai idan ya gani Allah dai yasa ya gani din ba sai ya kama hanya ba kuma abashi wahala

mama ke fada.

Mun dai jima a wajen zaune kafin na mike zuwa dakin mu wanda muke zama a cikknsa kafin mu tafi

inda zuciyana yake cike da tunanen halin rayuwa don sabon sauyi masu dama da nayi notice shigowata gidan duniya ke nan na fada a raina.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/15, 10:01 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Wayan anty Badariya na amsa nake kiran layina sai lokacin ya farga da jakar a motanshi har yakai inda

zai tafi yana gab da shiga wajen na kira har wayan ya katse bai daga ba .

Na kara kira karo na biyu can naji andaga saidai ba magana na soma fadin yaya nice Salma na manta

da jakata a cikin motarka da zan fito.

Babu kudi cikine yasa kika manta dashi ko nace ai inba kudi akwai abin amfani donga wayata nan

shima kudine wanan aiba waya bace don da baki manta dashi ba ai ?

Murmushin nishin ciki nayi lokacin guda don abinda ya fadi din game da wayata kafin naji yana fasin

sorry kiyi hakkuri don Allah.

Na karaso inda zamuyi meeting din kada in makara idan na fito zan kawo maki wayar har gida hope ba

matsala nace ba komai nagode yaya nerve mind ya fada ya kashe wayar.

Ajiyan zuciya na sauke ina fadawa saman gadon rigingine tare da soma duban dierking din dakin na

soma tunane akanshi.

Guy din ya hadu iya haduwa ga tsayi ga dan jiki dan sajen daya bari kuma a fuska ya kara fitar mai da

suranshi hancinsa kamar shiya zanawa kanshi .

Soman kanshi bakinr wulk yana sheki har zaka iya hango fatan kanshi don gyara tsayinsa yasa baida

alaman tubi irin da wasu mazan keyi idan sun soma girma din nan.

"Uwa uba ga ilimi kuma ga masu gidan ranan sun zauna a wajensa ya Allahu Ar,rahaman me yasa yayan"

mu ta rabu dashi ?

Duk da yaya farida tace ba haka yake a da ai koda baida muni da mace zata kishi na hali dana zahiri

saidai ace kamar a kamashi ya kare irin sirintan fulani din nan da suke tasowa dashi.

Ainun yana da kirki sosai ko dan abinan na danaga yayi cikin yan kwanakin nan hakan na nufin shi din

mutumin kirkine sosai .

Sannu a hankali na lumshe idona yanayin a lokacin iya na zumuntane naji bawai so ko wani kwadayi ba

sai dai don zumuncin dake tsakanin mu kawai ?

Salma yanzun nake jin wai ashe tsohon mijin hindune nan ya kawoki dama wanan ne hindu taki da

farko ashe ?

Anty Badariyace ke magana dani tana tsaye sabe da danta a kafada wanda da gani basu dade da

haihuwanshi ba nace yaya sulaiman ba shine ai.

Kinsan abokin yaya Ahmed ne da tare dashi zamuzo ai sai danshi baida lafiya suka tafi asibiti dashi.

Wai amma hindu tayi missing din miji wallahi yanzu ance wata yar uwarku kuma yake aure ko bayan sun

rabu da hindu din ?

Haka akace na fada cikin irin halina na basarwa tace wallahi yanzu mummy ke fada muna ai shine

wanda hindu ta aura da farko dama dan uwankuneshi ashe sosai ?

Kamar cousin muke dashi duk gidan mu daya dasu iya abinda na fada ke nan lokacin tace kai amma

hindu tayi mistake gaskiya data rabu da wanan champions din wanan ai mijin nunawa tsaraneshi ?

Gashi mama tace ya zama last done yanzu ga ilimi ga kudi ai duniya tasune ko ita hindu taganshi haka

yanzu sai taji ba dadi a ranta gaskiya.

Ga wayanki yaya na kira ya dauka yace yana wurin meeeting yanzu sai ya fito zai kawo min kin dai

bashi wahala salma zai kara dawowa gidan nan kuma ?

Jin nayi shiru ta koma fadin hau far to yaya can din ya karatu kuma mama nace ta rude yarta ta dawo

suna kitchen yau harda ita ana hada abinci.

Haba dai dasun barshi ai ke kada ki kwafsa muna don Allah ki barmu muci dadi yau gidan albarkacinki

mummy ce yanzu zata yarda ayi mata fakaca da abu irin da yanzu tunda kinzo ai dole aci dadi kwana biyu har hudu ma insha Allahu.

Abindata fada din yasa na sake jin wani iri a raina quit sure nazo da dan kudi saboda iyayyena wanda

"nake tarawa na scholarship dina dana part time work da nakeyi a wani ma,aikata da dai dan abinda nake samu a can din ."

Don banyi almubazaranci da barna da dukiya ba irin na yayan masu kudi da sukeyi aita sharholiya ana

abubuwan lalacewa da sunan more rayuwa