Chapter 36 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

taga dama in gani hakkuri

ya shiga bashi akan yaje don Allah a wuce wajen tana da gaskiya watan ka ukku fa baka kasan nan yanzu.

Ya dai samu ya ciwo kansa yace zai tafi din idan ya rarage abinda yakeyi a nan din amma bata isa

tasashi zuwa dole ba Ahmed dai baibarshi ba saida ya ciwo kanshi zai tafi.

Kwana biyu tsakani ya shiga jirgi zuwa gida bai fadawa kowa zuwanshi ba sai ganinsa tayi ya shigo gida

da magariba suna falo da yaranta da maizogale an baje abinci ana ci.

Yaran suka taso suna mashi Oyo yo daddy ya rungumesu yana shafa masu kai mai zogale ta soma fadin

miskili yau kaga daman zuwa garin ?

Ance ka dawo tun satin can ga matarka nan tana batun haukace muna ya akayi batayi haukan ba ya

tambaya fuska daure sun gaisa ya shige part dinshi cikin zumudi ta tashi ta bishi.

Ta shiga yana tsaye yana rage kayan jikinshi ta fada mai ta rungumeshi ta baya tana fadin baban mama

shine koka sanar da zuwan ka ?

Idan na sanar wata uwar zaki min abinci zan samu ko kwaliya ko zance mai dadi a wajenki dubanshi

tayi cikin mamaki tana fadin .

Haba dai wai fushin dashi ka dawo bai iya magana ba ya dan jaye jikinshi yacigaba da cire tufafinshi

yana fadin me tsohuwar nan tazoyi garin nan ?

Cikin mamakin da bata karasa ba take dubanshi tace mai zogalene fa ita din nake nufi metazoyi nace ?

Wurin mu tazo mana ta fada cikin takaici wurin ku wani abu akeyi data zo nake nufi tace sai wani abu

ya faru maizogale zatazo gidan nan ?

Ok amma kinsan agender din mu dake ko don haka ki shiryata ta koma gobe nan idan Allah ya kai mu.

"Kasan meka fada kuwa in shirya tafa kace goben nan ba,a dai yaya zanyi in kori mai zogale daga gurina"

kokai ai kadai fadane tunda kakankane kaima ?

"Haba dai ya fada yana murmushi yace to nace ta tafi tunda ba,a fada min zuwanta ba idan kuma ba"

zata tafi ba ni zan tafi in bar maku gidan ki zauna da ita ?

Yana fadin haka ya fada bayi ya kulle kanshi a ciki yana jin tana maganganu daga ciki tana fasin don

nace diyan yaya hauwa ba zasu zauna min gida ba ?

Shine yanzu zaka rama akan kakata to wallahi babu inda zata tunda bata tashi yau ko bakai nake aure

ba maizogale nada ikon zuwa inda nake ta zauna balle kaine mijina yanzu ?

Saida ya gama wankanshi ya fito ya shirya yayi sallah ya dauki key din motarshi ya fito har lokacin suna

falo zaune ya fito zai fita zaije wajen wani babansu a lokacin.

Sai ina haka ka dawo kana shan kamshi kamar bakaga mutane ba maizogale ke fadin haka gareshi da

yafito ya gitta zai wucesu ba tare da yayi magana ba .

Bai juyo ba sai fuska daya kara daurewa saida mammah yarshi tace dashi daddy ina zaka baka bamu

tsaraba ba ?

Jin hakan yasa ya tsaya ya juyo ga yarinyar yana fasin tunda kin roka nafasa baki ba zan bayar ba kuma

aina hanaki roko ko ?

Tace iam sorry daddy mum tace zaka dawo muna da tsaraba daga can ya juya har wayau din tsohuwar

bata daddara ba take fadin zaka bata ai yarintane tunda ka saba basu idan ka dawo ?

Nan ma din baiyi magana ba ya fita lokacin jamila din ke fasin kyaleshi don Allah maizogale idan bashi

yayi maki magana ba kisa mai ido don Allah ?

Wani abin akai mai tayi shiru kafin tace barshi kawai nace tsiya yake ji dashi kawai da jidali ya dawo

gidan nan yau .

Aiko ga alama nagani ina magana yasa kai kamar mutum mutumi ya fice bai ko kulani ba ina yayi

yanzu ban sani ba ta fada cikin fushi ta mike tana fadin yaran suzo suje daki suyi shirin kwanciya.

Ke ko tun yanzu zaki turasu daki dududu karfe nawa yanzu da zasu kwanta ?

Barshi ya dawo dai ai zai gamu danine ina nan zaune amma ki tura yara daki haka kawai basu sukai

maki laifi ba ?

Bata kula tsohuwan ba ta kaisu daki tace mai aiki ta shiryasu ta fice zuwa daki inda ta dauki waya ta

dannawa mahaifiyarta kira .

Jamila kuna lafiya ta fada lafiya mama dan rainin wayyon nan ya dawo yanzu wai sai me zogala ta

koma gida gobe ?

Ta koma gida akan wani dalili zata dawo gida dudu yaushe taje garin ko inna din tayi wani abune dashi ?

Nan dai ta fada mata komai tace oho rashin mutunci zai shuka muna ya turo inna ta kamo hanya ba

shiri komai ?

Bari na samu hafsat muyi magana yanzun nan itama din munafukace ai yanzu ina zuwa sai kowa yaji

labarin nan tunda hake take damu dama ina dai zuwa tukunna ?

Ta kashe wayan ta yafa gyale gidan gwaggo Asiya taje da zancen abindake faruwa ta soma fada

maizogala din mugun abune ko yaji tana maitane da zaice tabar mashi gida inda iyace data haifi uwarshi aiba zaice tabar mashi gida ba ?

Babu inda zata yayi abinda zaiyi nida nazone a fadawa hafsatu ta kirashi tun zancen baiyi nisa ba azo

ana canza magana kinsan halin gidan nan da tsegumi.

Saidai kash abinda basu sani ba shine sunyi shuka a idon makwarwa don kuwa inna na jinsu tana bayi

duk taji zancensu tun shigowan gwgg din gidan.

Haka sukai ta muku mukun zancen tsakanin su kada wani yaji yayi masu dariya a samu na tsegumi a

cikin gida don wanan abin tsegumi da kuma kunya ace wai Sulaiman tace maizogale tabar mai gidansa.

A can jalingo kuma tunda ya dawo ya shige dakinshi ya rufo kofan bai fito ba sai washegari da yafito

yana neman mai aikin gidan ta kirama ai yankinshi duka yana son yai masu alheri.

Suna kallo a gabansu yayi masu alheri baiko tsaya ya karya ba yasa kai ya fita har dare bai dawo gidan

ba tana ta bacin kiran waya sai can ya dauka ta soma fadin naga baka dawo gida bane na kira.

Na fada maki ai in baki sallami nai zogala ba zan bar gidan na juya nakoma inda nafito mana ina Abuja

yanzu haka .

Saida ya huta ya kira baba Audu yana fada mashi abindake faruwa akan ayiwa maizogala magana ta

dawo katsina tunda bata zauna da diyan yan uwanshi ba tayi mashi rashin mutunci shina bai zama da kowa nata .

Fadawa baba Audu da akayine ya fasa kwai a gidan don shi kuma yana sokoto yasa aka bugowa baba

daya fadawa su gwgg Asiya dacewa suyiwa maizogala magana ta dawo gida.

Wanan abu yaso kawo rikici inda sukaso har suyiwa baba Alu rashin mutunci shi kuma ya fito tsakar

gida yai masu tas akan don me zataje mashi gida ta zauna tasan yadda akayi wancan karon.

Ai goyawa yarsu baya sukayi shi sulaiman din shegene da ba zai dauki mataki ba gashi ya dauki mataki

ta hanyar da basuyi tsamani ba yanzu.

Nan dangi suka samu abin tsegumi kafin ai haka kowa yaji abinda ke faruwa wasu suga laifinshi wasu

kuma suga rashin kyautawanshi.

Zagi kam yasha shi wajen su gwaggo da tonon asiri don yaga yayi arzikine yakewa mutane diban

albarka yanzu.

******* ******* *******

Kawu hassan da matanshi duka biyu ya taso gaba yace suzo su tareni danshi hakim ne ya jawosu a mota

ya kawosu gidan mama shari.

Itama mahaifiyarmu a lokacin tazo ina daki aka turo Asmau tazo ta kirani gasu kawo da mama sunzo na

"tashi da sauri na fito falon a cikin murna,na ina gaidasu cikin farin ciki."

Muka shiga farin cikin ganin juna nan muka zauna hira inawa kawu bayanin komai yana fadin dakyau

my daughter iam pround with you haka ake son mutum ya kasance jarumi ko yaushe ai.

Abdul Hakeem yace zai dan fita nan kawu ya soma fada dashi yana fadin kaima kasan ba mai a motan ai

iya wanda zai kawomu nan ne nasa idan ka fita da wani zamu koma gida ?

Kawu bari ya fita mana na fada daga inda nake da sauri hakeem din ke fadin kaji hajjaju daddy kasani

ka zata bada kudin mai ne mu kara ?

Bari nazo to nace da sauri kawu yace haba haba keda kika dawo ba aiki kika fara ba balle ace asaki

dawainiya ai yakai waje cikin sauri.

Ban boyewa kawu ba nace ina aiki a can ai nayi har goge goge da aikon company don in kula da kaina

yace good mena fada maku hjy tunda akace yarinyar nan ta dawo ?

Wani iri mummy Binta matarshi tayi tana kawar dakai gefe daya cikin yatsune kafin can kamar an

tsimata ta soma fadin ba a hada rayuwan mace dana miji fa Alh ?

Ita mace tana da hanyoyin samu da yawa shiko namijifa aikin karfi zashi yayi a kasan mutane don Allah ?

"Lokaci daya duk suka kallota, cikin mamaki sai mijin ke fadin hjy Binta me kike nufi da wanan magana"

"don tana mace ,a,a yaya mama shari ta katseshi lokaci guda tana fadin."

Dama ai mace ba daya suke da namiji ba ai tundai in an samu namijin mashiriricine shi wanda baida

kishin zuciya ba ?

To nidai kada ki fassara min zancena da wani kalma sharifa ai yanzu take fadin tayi aiyuka da dama a

can din shi jna zaiyi dabaran yin haka a can ?

Wai meyasa ke baki son a zauna lafiyane Binta da Salma da shi yusuf ina daya suke gareki ko akwai

banbanci a tsakaninsu ?

Shiya banso zuwa ba wallahi naso in barku kuzo ku kadai daga baya sai inzo in mata sannu da zuwa don

gudun irin haka ?

Tunda baki so a zauna lafiya ba sunso yin abinda bai kamata ba don ni tuni na mike nashige daki cike da

mamaki a raina ?

A can ma dakin ina jin muryoyinsu sama sama dai kafin maman mu tashigo da kanta dakin tana fadin

ga kawunki zasu wuce nace tun yanzu take fadin ba dole ba hjy binta ta bata tafiyan.

Na fito inacewa kawu din ina nan zuwa gidan zuwa jibi yace ba komai ai ki huta abinki kinji salma kina

da gajiya ai tare dake.

Nidai nayi murmushi nabi bayanshi ina jin mamana na fadin hjy Basira sai anjima kinji ki gayar min da

yaran nasan ta baci ke nan tsakanin su da mummy binta saboda wanan maganan da tayi.

Wanda kamar maganan ya fito matane a hasale lokacin don tunda suka zauna dama take ta shakan iska

ta daina magana da kowa a wajen saida mijinsu yasakota a cikon zancen ta basu amsa mai zafi haka.

Suna fita mama shari ta soma fadin kaji min mata da maganan banza itama tasan wallahi ba zan kyaleta

ba dama ai naga take takenta tun shigowansu gidan nan.

Wani ya hana taiwa diyanta tarbiya da ake masu ai cewa tayi an matsawa diyanta ba a kaunarsu don

ba a sonta ita kowa ya barta da dabaranta yanzu laifin wa zata gani.

Ji shegen askin da yaron nan yayi a kanshi ai abin ke nan shima yaya da laifinshi ai ya bari diya sun

sagarce masu haka babu kwabo ?

Ai kinsan yaya shi ba damuwa yayi da duk abinda yaro zaiyi ba na juya na koma daki na zauna ina

tunane wanan hali na mama binta gaskiya da gyara a cikinsa.

Wayana ya dauki kara yayan mu hinduce a layin saida na dauka take fada min itace hakan yasani sakin

murmushi tana ta murna da dawowana take fada min idan an shiga weekend zasu zo gaidani.

Nace yaya dakun huta ai nima zanzo katsina din in ganku tace ina ai dole sai tazo kafin nazo din su

gaidani ta kare zancen da cewa ga Alh yace yana maki murnan dawowa gida lafiya.

Nagode na fada kusan shine zurfin maganata indai zakai waya dani kayi kawai amma ba wani dogon

hira na iya ba nake tambayanta yara tace sunje islamiya.

Mukai sallama ta kashe wayanta na koma na kwanta ina jin dadin yadda yan uwa suke nuna min

kauna a zahiri haka kowa ba farin ciki da wanan karatun da naje.

Kamar hadin baki saiga yaya Azizza ta bugo min itama daga zaria inda taje karatu suke fada min

weekend duk zasu shigo dubani.

Naji dadi sosai da nayi waya da yan uwana sai yaya fadilace kadai bamuyi waya ba a ranan da yusuf shi

mama tace ko lokacin muna iya ganinsa ai don kuum yana gidashi

Na kira yaya farida ina tambayanta daddy da jiki tace yaji sauki har ya fara wasanshi ai haka yake idan

abin ya taso mai sai kice baikai safe.

Muka dan taba hira ita kan ko banson magana sai nayi don hira take jana dashi sosai idan muna tare ko

a waya.

Wanan yasa muka dan shaku kuma lokacin muna yara sosai itace kamar uwar goyona ce ita a cikin

dakin mu don haka ita na saki jiki da ita sosai a lokacin.

Hakama yanzu dana girma still da ita nafi sabo a cikin dakin mu din nake tambayanta yaya lokacin take

ban labarin.

Yaje jalingo ya sasanta Sulaiman da matarshi tace kisan yar iskace ita shine ya nuna mata ya fita iskanci

kakanta ya kora daga gidanshi ba kinsan mai zogale ba ?

Nace ban santa ba take fadin haba salma tsohuwar nan maman gwaggo Asiya ta gidan mu nan take

fada min dalilin fadan tun daga farko har karshe.

Nake fadin shima ashe ya iya shine ya rama a wajen kakanta tace ai dama yace dasu sai ya rama sun

gashi shiru shiru su zata bai iya daukan mataki a kansu.

Yanzu dai shine yaya yaje yazo da tsohuwan ta dawo gida tunda bata iya dawowa ita daya hanya da

nisa .

Mama shari data shigo tana jin wayan da mukeyi ta karbi wayan nan na barsu suna ta zunduma zagi

akansu kinsan mu mata da daukarwa kanmu nauyi da alhaki banga abinda sukewa munna bani ?.

"Tsab na shirya ranan jumma,a da niyar zuwa gidan mama kamar yadda mamana ta umurceni dayi an"

hada masu tsarabansu da komai da zanje masu dashi.

Tsab na shirya don mama din ita zata kaini da kanta gidan mu mun fito inda muka sama wanan

saurayin yana gogewa mama motanta dayasha kura don ya jima ajiye shine da zata fita tasa ya goge matashi ranan.

Mun isa gidan mama din don tasan zuwan mu muka samu har sun gama girki yusuf yana zaune falo

yana cin nasa tunda yaga mama ya soma inda inda yana fadin yanzu yake fadin yagama yaje ya dubomu ai.

Dafani tayi tana fadin kaga diyata ai nan don ita bata gujeni ba tasan uwarta koda ta dawo turai sai

yanzu ta tako gidan nan.

Dariya yakeyi yana fadin ayi hakkuri maman mu tana ta zuga zancen na zauna kusa dashi lokacin ya

samu kanshi da mama ya dago yana how far salma wai sakace bake ba wallahi ?

Mukai dariya muka taba na yaushe rabo ya soma fadin mama kinga yarki har yanzu tana daukan kanku

"daya na fada mata Sa,id ne sa,anta bani ba."

"Waye sa,id mama shari ta tambaya mama tace dan kurman nan na wajen Asiya mana ai shine abokinta"

baicin abu saida salma itama haka suna kanana.

Diya tafi karfin uwarshi yanzu balleshi ai ki tuna min kinji sherin da yaron nan Sulaiman yayi kuwa

farida bata fada maki ba ?

Nan ta kwashe komai take fadawa mama din mama tace ashe yayi bakine haka yanzu har ya iya tsula

wanan tsiya haka maizogala ta gamu da daidai da ita ashe ?

Naso ina garin ince aman kine ya soma fita a kansu sun jima suna hiran muna gefe muna hira da dan

uwana daya sani gaba da tambaya.

"Saida akai sallah la,asar mama ta shirya ta tafi gida bayan ta dibi abinda sulaiman din ya sayo mata mai"

yawa mama ta ware mata a gefe daya yusuf ya loda a cikin mota.

Ni dai ina kallon ikon Allah sai bayan tafiyantane muka samu sakewa da mama dake nuna mata kara

"akaina gabata bata wani dogon mu,amula dani idan mama shari tana waje."

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/17, 9:46 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Na sake munyi hira da mahaifiyata na bata labarin rayuwan da nayi a turai da irin wahalan da nasha a

can din sakamakon rashin tallafi daga iyayye da bansamu ba daga baya.

Nisawa mama tayi cikin damuwa ta soma fadin Allah ya kara kyauta ubangiji yasa ki morewa wahalanki

salma rayuwa dama haka yake sai ka wahala kafin ka samu min godewa Allah da yabaki dubaran wanan aikin har kika samu kika kammala karatun nan lafiya.

"Kamar yadda ya zama dabi,ata ina idar da sallah dare ban fito ba ina jin muryansu a falo ita da Yusuf"

"suna hira amma banyi sha,awan fitowa ba lokacin na mike ina shirin kwamciya lokacin naji mama na waya."

Tana fadin gaba dayan ku duk gobe zakuzo ke nan to Allah ya kaimu gobe lafiya Allah ya kawo ku lafiya

kuma duk wanan zancen sam banji a raina wai infito in tambaya waye zaizo ba a lokacin ?

Haka na shirya na kwanta koda mama tashigo dakin ta samu har barci ya soma daukana lokacin nan

take fadin kwanciya kikayi kuma bakici abinci ba ?

Saida safe in Allah ya kaimu mama haka zaki kwana da yunwa naxce banjin yunwa ai mama shiyasa ban

nemi abincin ba.

Ganin barcin nake son yi a lokacin yasa ta fita ta barni a kwance din nacigaba da barcina hankali

kwance ta koma ta samu yusuf a falo yana cin abincin.

Washegari banyi wanan barcin safen ba din tunda na idar da sallah na soma gyaran dakin mama ina

kawar da komatsen dakin na fitarwa ina fitarwa waje har falo saida na gyara na koma kitchen din ta.

Ruwam zafi na soma azawa