Chapter 37 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

kafin in fara gyaran kitchen din don ita mama bata da kowa a gabanta

yaya fadilace kuma tana porthercourt wajen mama hussaina ance takai wata takwas a can wurinta suna zaune tare.

Ruwan shayi na juye a flask na fere dankali don in soya lokacin na fita falo na nake tayar da yaya yusuf

ya fita ya sayo kwai da zan soya.

Mama ta idar da lazuminta ta fito daga dakin yaya Fadila inda ta kebe tana ibada saboda takura nan

take fadin keko baki hutaba salma tun asuba nake jin motsinki gidan nan.

Gurin yayi tarkace da yawane mama na gyara sai abinci dana dora muna na juya fadin ina kwana mama

ta amsa da lafiya kalau salma Allah yai maku albarka naji dadin hakan dana ganki baki dakawa kanki girman kai kin tafi turai ba ?

A raina nace girman kai ni awa a can ma aiba jin dadi nayi ba balle inzo nan ina hura hanci garine da

idan baka so kanka ba kuma ka tsarkake zuciyarka zaka samu alheri sosai a cikinsa.

Amma a fili amsawa kawai nayi da amin inda tacigaba da fadin ubangiji Allah ya baki miji nagari da zaki

huta har yan uwa su huta a karkashin innuwanki salma.

"Naji dadin wanan addu,an da mahaifiyata tayi min tunda farar safiya haka azuciyana nake amsawa da"

Amin ya Allah ko wace mace nason hakan taje inda zata huta har yan uwa su huta a karkashin innuwanta suma.

Wanka na shiga bayan nagama gyara gidan mama tsab nafito na gyara jikina tare da sako kamshi na

samu wuri na kwanta indan huta daga falo naji mama tasa mun kira na amsa na fito.

A falon na samesu zaune da yaya yusuf wanda ni kadai kece mai yaya a cikin mu don kadai ya girma a

dakin mu sauran duk yayyun mune.

Zauna ki karya ta fada da alaman umurni take ban ba wai tambayana ba yadda na iya nakai zaune na

dan zuba iya ruwan shayi tare da dan saka sugur kadan na soma juyawa duk suna kallona kafin tace meye haka salma ?

Iya wanan ya isheni mama na bata amsa gaskiya mamaki ta damu tayi min korafin bakyason jin

abincinsu koda andafa tunda kika dawo.

Ina ci mana saidai ba sosai ba ai gata nan kamar a karyata jiki ba kwari yusuf ya fada yana jawo kwan

da mama ta aje a gabana takai hannu tana buge mashi hannushi din dayaje diban kwan.

Don Allah mama ki bari na cinye kawai tunda bataci kinsan halin salma fa tunda ba komai take ci ba ita

sai lokaci lokaci.

Hararanshi mama tayi tana fadin ai sai kayi taci kace dama kai aka sayowa don kaci nan nace ko yaci

meye mama ya dauka yaci kawai.

Sai cewa yayi gaskiya mijinki zaiji dadi salma idan anyi abin kwadai sai ki bar mashi ya kwashe duka shi

kadai .

To ka sani ko wanda zan aura shima haka yake kamata dariya ya kwashe dashi yana fadin jam wallahi

indai kika auri miji haka bakunta gidanku zaiyi wuya ke nan salma.

Wuyan me ba sai in tashi in dafa maka ba kaci saika koshi aiba zanki dafa maka ba idan kazo nasan dai

abinda kakewa ke nan ko ?

Ya dan karkato gareni yana fadin fada min yan mata inane zaki kinsan in karamin garine nikan badani

ba gaskiya komai dadin da kukeci kuwa gidan ku.

Kaima kasan ai ban zuwa kauye sai wani ilkon Allah dani da kauye ai tunda na guda daga gidan mu ai

nake tsoron kauye a raina.

Dadine ya kama mama a lokacin sai murmushi takeyi tana kora ruwan shayin dake hannunta don bata

taba kawo zanyi zancen aure a kusa ba a yanzu.

Amma yau gashi yusuf yasa a gabanta muna zancen aure dashi haka da alaman ubangiji ya amsa

"addu,anta ke nan a kaina."

Zancen kauye da muka daukone yasa ta saka muna baki tana fadin katsina dinne kauye ko ina baku da

inda yafi maku katsina a rayuwa ai ko ina kukaje kuwa a duniyan nan.

Kunya ya kamani din sam na manta da mama na gaban mu lokacin na biye mashi muke zancen nan

haka yasa na wayance zancen da fadin Allah ya yusuf akwai ka da tambayan kwam ?

Na mike ina fadin bari nidai naje na dora girkin rana kada kuma inzo ban gama da wuri ba kayiwa

mutane korafi don kai lahira ce baka cika ?

"A,a barshi kuyi hiranku ni zan tashi inje in dora kinyi wankaki ga gajiyan gyaran gidan nan da kikayi baki"

ko huta ba ?

Mikewa nayi na wuce ina dariya don ya yusuf da yake ce min baki kalan matan kauye ba ai balle ace za

a badake katsina mama ki bari yau tayi muna dahuwan turawa muci don Allah shine ya ban dariya na fice zuwa kitchen din.

Na dora ruwan dafa shinkafa na debo kayan miya ina wankewa motar su yaya hindu ya tsaya kofan

mu naji matan gidan dake can waje sunayi masu sannu da zuwa.

Ban dauka su bane don haka ban damu ba saida naji hayaniya a falon mu nasan bakin na mamane

"lokacin ta nufo kitchen din tana fadin a,a mama kikasa yar London kitchen kuma tun bata huta ba ?"

Hannu na daure na nufosu muka hade muka rungume juna cikin jin dadi da ganin junan mu tana fadin

wai Salma kece kika koma haka ?

Dariya nayi nace yaya hindu kema kinyi kiba sosai kamar bake ba yusuf ne daga kofa tsaye yace ba dole

ba karamin ci sukeyiwa Alh ?

Yaya ina Alh ki na fada cikin katseta da juyawan da tayi zataba Yusuf amsa duk da hakan saida ta bashi

amsa da fadin ba dole ba tunda shiya taramu muci.

Kafin ta juyo gareni tana fadin ke dai yana lafiya tace a gaidake da tare zamu zo dashi ai sai matarshi

bata jin dadi suka tafi asibiti.

Allah sarki Allah ya bata lafiya nace a lokacin yaranta suka shigo su ukku sunyi daidai ga haihuwa ita da

farida ke nan kowa yaya ukku ukku suka haifa.

Saidai ita yaya hindu bata da mace duk mazane su ukku sabanin ita yaya farida ta surka da diya mace

cikin haihuwan nata.

Kamo yaran nayi zuwa jikina ins fadin hello my dear ya kuku ina rugumesu nace ya sunan ku suka shiga

fada min sunan su daya bayan daya ina maimaita sunan nima.

Falo muka fito gaba dayan mu inda muka samu mama a cikin jin dadin da ganin iyalanta haka ni kaina

naji dadin ganin yaya hindu don ba alaman damuwan rayuwa a tare da ita.

Tayi kiba abinta tayi kyau haskenta yana nan kuma duk da ta dan dushe kadan a yanzu amma hakan da

take yayi mata daidai gaskiya.

Saida take fadin farida tace sun kusa shigowa suma nan na tuno munyi waya tace zata zo ai hakan

yasa na koma kitchen na canza tukunyar abincin don an kara yawa a yanzu .

"Ba,a jima ba kuwa mukaji shigowan nasu suma nan gida ya kaure da ihun murna da ganin juna azzzih"

ma ta karaso ita kan munyi ihu da murna sosai don tare muke hannun mama Shari koda aka turani karatu waje.

Tare muka koma kitchen dasu boy dan yaya farida yana biye dani don yaron ya lake min sosai tun

zamana a gidansu.

Mun gama aka zuzubo zuwa falo nan muka baje a falon ana hiran yauahe rabo da tuna baya sai a

lokacin nake jin za ai buki a katsina yayan baba Audu dana baba haruna mata za aiwa aure daga ciki har da kanwar yaya Ahmed ciki da suke daki guda.

Tabas nasan zuwa katsina dolene gareni don ya zama wajibi koda kuwa nace zan zauna wajen mama

"shari har su dawo ba za,a yarda ba."

Haka yasa naja bakina nayi shiru ina saurarensu karshema can na haye saman kujera na kwanta ina

duban wayata .

Daga inda yaya farida take zaune take fadin amma dai wanan wayan da kika dawone kika sayeshi ko

naga bashine kika zo dashi ba wanan sabone fil ai ?

"Duk suka juyo gareni don duban wayan da take zance a kai nace a,a ranan dana dawone yaya ya saya"

min wanan din yace wancan yayi min karami.

Ya sulaiman ko ai yafi da nan indai shine rabonka idan ya ratsa sai dai kaji dumus kawai shiyasa da suke

fadin rowa gareshi ni ban yarda ba gaskiya .

Ina ta hadu dashi yaya hindu ta tambaya cikin basarwa tace shiya kawota gida mana daga Abuja da

tare zasuzo ai da babban boy sai daddy ya tashi ba lafiya ranan yace ya wuto da ita.

Kamar bata sauraren karshen zancen ta juya gun yaranta tana magana dasu kafin mama tace suna dai

"fadine kawai sulaiman za,ace baida alheri ?"

Baiyi masu yadda suka zata bane mama in kinji yadda gwaggo hafsatu ke zaginshi wallahi sai abin ya

baki mamaki mama ko bukin nan fa kaf yan matan nan shiya saya masu gadaje ashe jiya baban boy ke fada min.

Ki duba don Allah shine wai za ace baida alheri dama ba haka suka zata ba dashi ba sun aura mashi

Jamila don su juyashi yadda suke so ba.

Indai yaya Suleiman ne kar yake kallonsu wallahi yanzu ya bushe fitilanshi bai raga masu koda wasa yy

Farida ke fadan hakan tana basu labarin mutan katsina.

Wai da gaskene yace mai zogala sai ta dawo katsina bai yarda ta zauna mashi gida ba jalingo da

gaskene mana mama.

Lokacin da suka samu sabanin can ai tsayawa sukayi sukace Jamila tafishi gaskiya sai yaran su koma

gida ba zata zauna dasu ba .

Shi kuma yace atafi a haka sun dauka wasane sai gashi ashe da gaske yakeyi yanzu haka babban boy zai

dawo da ita nan gida dole don ya kafe wallahi saita dawo kosu rabu.

Ashe haka sulaiman yake mama ta fada tace wa sanin da kikai mashi mama ai yanzu wallahi duk ya

manna masu tsoronshi a zuciya ba mai mashi gaba gadi irin da kuma .

Har ita hafastu din wa tayi ta ganima idan bai gyara mata zama ba na yarda kudi yana canza mutun

wani lokaci haka kuma mace.

Auren nasu gashi nan dai ga kamarshi gata kamar kaska yayi mata tsiya a cikon mutane tana lake bata

iya komai sai cin mutunci da wullakanci.

Sai kace matar gidanmu Azizza matan nan ta zamowa Alh jaraba kuma yaki rabuwa da ita shiyasa da

zamu zo yana fadin wai zaiko samu zuwa ga Azizza tace bata da lafiya nace kaita asibiti bari mu taho.

Yanzu ko nawa ya kashe kwana biyu tsakani zakiga Nabila ta kwanta itama sai ya kaso mata kudib

dayafi na Azizza yawa .

Ga yan iska su kishinsu mana haukane ashe ba su zasuci kudin ba saidai ya fitar yakaiwa masu kemis

suci shiya daukarwa kanshi hakan mana.

Sai ranan da sukai fada kuma zakiji tonon asiri a wajensu kowa na gorantawa dan uwa hakan mu kan ai

mun saba ganin haka a gidan mu.

Karki soma wanan haukan ina fada maki idan zaka zauna da mutum zauna dashi tsakani da Allah duk

me yayi maka kanshi zai koma .

Mama ina ruwana tunda basu tare min komai ba nima ai akwai inda zan kwaci abinda yafi nasu suma

sun sani bakin cikina guda shine rashin zuwan nan da bamuyi ba yau tare amma ba mamaki kuma ki ganshi garin nan ko kuma ya turo muna kudin sayayya .

To me zaisa ka damu kanka akan shirmen banza su tasu kalan kishin ke nan ai su zauna aita cin kai har

da diya sai an hada a cikin fada.

Bari kiga idan an hadu yadda matan nan zata dinga budawa suko yan gidan mu suna binta kamar

basarakiya tana iya shege a cikin mutane.

Waiwa kike zance yaya hindu ke tambayan Azizza tace matar yaya sulaiman mana Allah haushin matan

nan nake ji ranan wai tana gulman mu kuma gani tsaye wai yan dakin mu mun faye daukan kai kamar munfi mutane.

Wanan tajine ana fada ai ba sabon abu bane a gidan tunkan tasan saka wando ake fadan haka gareku

don yanzu ta fada ai tushi tayi don an fada kafin ita .

"Na rasa me muka tarewa mutanen gidan mu koda yake ba kowa ba gaskiya kada inyi jam,i nace duka"

don gaskiya yawanci duk sun dawo daga rakiyan gwaggo hafsatu yanzu.

Ita wanan wata bari kowa aibata bari ba sun dai gajine sun gane ba riba ga abinda sukeyi sun kama

kansu yanzu mama ta fada.

Amma yaya hindu ke zakiyi muna anko ko ta wani dubota tana fadin ina naga kudi koni ban saya ba

balle inyi maki Azizza din tace dani da Salmafa bani kadai ba ?

Banyi maku alkwarin hakan ba gaakiya haba matar Alh ankon da baifi dubu goma ba zakice baki masu

yaya farida ta fada cikin zolaya.

Nima nema nakeyi balle inje dinka masu suna yan mata ga hjyn Abuja nan ta dinka maku mana sai ko in

dinka masu amma yanzu aike tace kiyi masu anko din.

Anya kuwa hindu kokece a gidan daula ba irin halin nan na matar sulaiman zakiyi ba dan anko din da

zakiyiwa kannenki zakice ina kika ga kudi to Allah ya baki kiyi masu din.

No badani ba gaskiya ina ganin niko bukin ban zuwa sai daga baya idan an kare bukin ko kuma inje

kafin buki in gaidasu.

Buki Batullah nefa salma aiko don mu kije katsina ke har yanzu halinki yana nan na rashin son tafi

katsina ?

Nan kuma aka shiga hiran kurciya aka bar zancen anko don yaya hindu tayi fushi da abinda mama ta

fada game da ita yasa ta fuske taki magana a lokacin.

Sun shiga sallah na tsaya nayi dubaran gyaran falom kafin naje nayi sallah a dakin mama nashige don

in huta .

Mama din tashigo tana fadin salma ina kika tura manjan miya wajen gyaran store nace yana ciki mama

bayan kofa na saka maki har ta juya nake fadin mama badai girki zaki dora ba yanzu nake zancen in fito in dora ai.

Salma ki huta kinyi aiki da yawa bari kawai har nayi talge saura tukawa kawai tuwone nake muna da

daren nan bance komai ba don zan fita din in kamawa mama aikin.

Sai kuma ga Azizza ta shigo tana fadin ina can na matsawa yaya hindu tayi muna anko kinsan halinsu ba

daya da yaya farida ba .

Yanzu dai yaya farida tace mu bari ai zata dinka muna dama nace akwai kudi a wajena da an bata tace

na barshi tunda tace zatayi muna saidai banso hakan ba gaskiya.

"Kodana shiga kitchen suna sama a ciki suna aiki na karba suna a,a nace su bari na karasa suna tsaye"

harna karasa komai kafin suka fito daga kitchen din na gyara wajen don safe.

Da dare da yaya yusuf ya shigone nace barin baka kudi don Allah a sayo kayan tea da kwai da za ai

breakfast dashi da safe.

Haba akwai kayan tea dana zowa mama dashi ai yaya farida ta fada nace bari ya sayo a kara kada a

shanye mata yaya hindu tana shiru batai magana ba .

Da wanan tunanen na kwana ashe da can banda hankalin da zan iya gane halintane na kan daiji mama

na yawan fada da ita akan lalaci da rowa kuma a sanina ance ta daina yanzu.

Meyasa banga ta rikowa mahaifiyar mu komai ba kamar yadda yaya farida tazo da katon kwali da kuma

ghana most go da kayawa mama din ?

Amma sam mama bata nuna komai akan hakan ba son washegarima da aka tashi ana breakfast itace

ke fadin yaranta basu breakfast da madara search daya sai biyu.

Ku dauko mana ku kara mama ta fada tace ai zan dauko masune ta mike ta kara cikin wanda yaya

"farida din tazo dashi suka sha sukai hani,in."

Nan yaya ke tambaya mama ina kika fito da doya haka da irish mai yawa tace wallahi dana ya kawo min

shi kaya guda haka.

Na dibawa maman ku na dibarwa matan gidan nan amma ya saura haka da yawa tace wallahi kamar na

sayo fa saidai munyo sammako basu fito ba nace sai nazo nan a saya maki.

Ki huta ga Sulaiman nan ya kawo muna ai wai yaya Sulaiman kike nufi ranan da ya kawo salma ko ?

Muna Asibiti baban boy ya kirashi yace basu iso ba ya tsaya kada yazo hannu sake hakafa yake

kyautanshi idan ya tashi kamar bai san zafin kudi ba.

Nan take basu labarin kyashin da matarshi keyi a kansu wai yana hada qualities dinta damu yana sayo

muna abu iri daya idan mijina ya tashi saya min halan tare yake sayo muna ?

Bata da kunya ai kin sani jamila ai kila ta rage wani abu yanzu da tayi aure aike farida kinsan halinta tun

muna school yaya hindu ke fadin hakan cikin hade rai.

Ta kara da fadin ni shiyasa kikaga ko gaisuwa ban tsayawa yi da ita don ba zan yarda tace zatayi min

rainin wayau ba takwalan baza kawai kazama.

Muna school fa sune kazaman aji aita dukansu saboda kazanta da rashin kokari haba ku barta haka yar

uwarkuce .

Kuma wanan ai dane yanzu ya wuce don ko ita ta manta da hakan yanzu tunda tana gidan daula duk

wanan ya tafi ai.

Yauahe baba zaizo garin nan mama tambayan data koma yiwa mama ke nan kuma a lokacin tunda

mama tace abar zancen a lokacin.

Ina gefe daya ina jinsu zakice hankalina bai garesu amma duk hiransu ina nazarin komai bandai da abin

fadane a fili sai a zuciya.

Ina kuma auna yadda ake labarin wanan matar nayi nayi in tunota a cikin dangi na kasa a lokacin don

an jima ba a tare sunyi wanka sun shirya zasuje gidan mama shari da gidan kawu su gaidshi yaya.

Yaya farida taso a fita dani nace ba zanje ba hutu nazo yiwa mama idan naje gida a yau mama bata bari

indawo gidan nan nima din gaskiya ba zan dawo ba.

Zasu fitane ake zancen abinda za a kai masu idan anje ita yaya farida data dauko zancen take fadin

kayan tsarabansu yana cikin motansu ta bari take fadin saidai yaya ko?

Nifa ban riko kkmai ba haba yaya har kawu da mama ban riko ba saidai in basu dubu biyar kadin takai

karshe mama ta hauta da fada.

Wai meyasa kike wanan rayuwane haka a cikin yan uwa ko kinyiwa kowa bansa harda su ba ai haka

kwanaki yaya gambo ta kawo min karaki nan na dai kyalene bamyi magana ba lokacin.

Mama ni bam riko wasu kudi bane masu yawa ko baki riko ba ai kinsan ya kamata tunda gida zakizo

ganin mu meye amfanin samun diya a duniya ?

Iyayyensu su huta yayin da karfin su ya soma karewa ko sai diya su tallafi iyayye kuma ki daina wanan

halin tunda kema kin haifa ai ?

"ZAINAB IDRIS MAKAWA[12/18, 10:05 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,,,"



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH