Chapter 39 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

garin kamar da bakin kwarya haka na shiga bayi nayi wanka tare da dauro

alwala nafito duban time nayi naga magariba yayi na tayar da sallah .

"Ina idarwa antyna tana shigowa take fadin mama ke fadin ko kinyi barcine nace idona biyu isha,i nake"

jira nayi in kwanta.

"Abinci fa zanci kafin na kwanta na bata amsa ta juya ta fita ta barni a dakin addu,oi nakeyi kafin na"

tashi bayan dan lokaci na gabatar da sauran sallolin .

Nafito suna falo har lokacin ruwa ake zugawa a garin na nufi kitchen na debo ruwan zafi a flask nafito

kayan tea na dauko na hada na zauna nan wajensu ina korawa.

Bayan nagama daki na nufa na kwanta don ban dogo hira sosai dan gara lokacin dasu yaya ke nan ina

kai tara da wani abu a tare dasu.

Washegari ranan saboda gajiya ban fito hada breakfast barci nayi sosai da safeb don anty ta wahal

dani a cikin kasuwa da muka tafi.

Ina tsaka da barcine naji yusuf yana tayar dani wai ke sarkin barci ki tashi ga baki nan a falo hakan yasa

dole na tashi ban fito ba saida na kewaya na dan fito na gyara fuskata na nufo falon .

Dan turus nayi don ganinsa zaune kasa samab dadduma sallah mama a falon mama din tana gefe zaune

"saman kujera ita kuma sai fara,a take a fuskanta na ganinshi."

Na karasa fitowa nan mama din ke fadin ke ashe yayan ku na gari tun jiya baki fada min ba a hada mai

abin kari ?

Saida na dan dubeshi nace shiyace kada in fada kada yazo baizo ba inyi karya na dan dubeshi a lokacin.

Kamar kullum wanan yaudararen murmushin nasa ya sake don a gaban mutane saiki rantse ai bai

magana.

Ya watso min idanunsa nayi saurin kauda kaina gefe daya na dan raba mama na zauna a hannun kujera

yake fadin rowane ai don a bar mata abincin ta cinye ita kadai ?

Ni kaina amsan dana ba mama din sai naji wani iri amma yaya zanyi ban iya karya ba balle in koya

akanshi a yadda mama ke hira dashi sam bata daukeshi suruki ba don yadda naji ta zake tana tambayanshi akan iyalinshi.

A gogonsa ya duba yana fadin mama ni zan koma zanga wani kafin in wuce akwai wani da zamu hadu

yau can Abuja dashi.

Ya mike tsaye tare da takowa zuwa gaban mama ya aje mata daurin yan dari biyar yana fadin mama

ayi hakkuri da wanan don Allah ba kudi da yawa a hannuna wanan bakauyan nazo karbawa farida sako wajenta dama.

Muka fita tare dashi lokacin yaya ta fito daga daki suka gaisa faram faram dashi itama ya debo kudi ya

mika mata muka fita dukkan mu ukkun mama na mashi a gaida gida.

Saida ya bude mota ya duboni yana fadin ga abinciki nan na sayo maki nasan wancan ya kusa karewa

ko shiyasa na biyo in baki jin hakan ya dan sani dariya har fararen hakorana suka bayana a fili ina fadin.

An fadama ni sarki cine suna can ko tabawama banyi ba suna gidan mama na barsu yace sai ki aje

wanan a gidan mamana tunda kin zama maigida biyu.

Ya cire yusuf ya karba daga hannunshi ya shiga dashi cikin gida sai faman sheri da yake min yana fadin

wanan yar me kuke bata haka tayi kiba azizzah ?

Har ya wuce yana kan min sheri kudin dai ya ba yusuf ya fara godiya muna mashi dariya ya tafi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/20, 10:53 AM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,,,"



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Munshigo gida mun rabar dashi akan yace jibi zasuzo kadunan da ya Ahmed don aikin dake kawoshi an

kammala zasuzo su duba wajen da yaya.

Falo muka samu mama a zaune yusuf ke fadin kinga arziki mama aini wanan shigowan yayi min dadi

kudin nan har tufafi zan saye a cikinsu yana nunawa mama kudin dake hannunshi.

Zuwan salma dai yai muna dadi ai donta yazo gidan nan yaya Sulaiman ne zaka gani haka free yau gashi

har falon mama kuma aka fita yana dariya.

Mutumin da fuskanshi kullum a daure yake ga yara har da manya nayi mamakin jin yana wasa da salma

haka ai yau ?

Ai yaya Ahmed yace na daina kyaleshi kada ya kwareni shida yaya farida ai sukaja har yake ce min wai

bakauya Allah haushin kalman nan na bakauya da yake kira min nakeji da farko.

Abin ya hade biyone keko yana maki wasa ta gwaggon mune alakan dake tsakaninmu ke nan abokan

wasa muke dashi ai sai kuma yayan mu daya aura kinga nan akwai wasa a tsakani kuma ?

Ai yaya ta fada min nifa kinsan kaf gidan mu ba wanda nake tsoro kamarshi da yaya Ahmed ina karama

"da mun fitane nida Sa,id yanzune zai koromu gida yacewa Sa,id yaje yasaka wando ni kuma a saka min hula ko dan kwali."

Saida tayi dariya take fadin aiba ke kadai ba kowa bai bari ba a lokacin don bai wasa da kowa a gidan

mutumin da magana kamar yana mashi wuyane har yanzu.

Shi haka ya taso dama ai sai wanda ya yarda ya kuma soyewa yake jin muryan sulaiman ai yana daga

cikin abinda keba gwaggon hafsaru haushi saboda sabon da nayi dasu a lokacin.

Ko abinci tace wai sai nawa sulaiman keci wai nayi munafunci ina son in kwance mata yaranta saida

baba Alu yace meye bambancinta da babanku don sun dafewa matarshi ai fuska suka gani suke zuwa.

Don Allah ita tafaye tsegumi matan nan ko wancan satin dana shiga gida naje gurin gwaggo laraba fada

ta somayi dani wai mu yan raba daya biyune sai inshigo in shige dakin hjy laraba ko gaisheta banson yi.

Halintane haka mana ita kada kayi hurda da kowa sai ita kadai ta dinga juyaka yadda take so idan kaki

kuma kun saka kafan wando daya ke nan da ita a gidan .

Ai abinda ya hadamu ke nan fada har gobe don me nake shiri da gwaggon ku laraba abinda ta tsana ke

nan ayi hurda da hjy laraba ita ?

Wai meya kawo makine a cikin katon kwalin nan yusuf ya jawo kwalin yana tambaya ya soma budewa

don ganin abindake cikin kwalin .

Kayan abincine irin na turai ya sayo min nina rasa ina yake samunsu koda nake Abuja dasu yaya sukai

mai korafin bancin abinci in an girka sai gashi ya kawo minsu suna gidan mamana na barsu a can .

Ita yaya farida ta manta ba komai nake cibane don koda tazo din nan tana ta korafin hakan sai ki girka

abinci salma kikici kuma ?

Kayan da Yusuf ke fitarwane take kallo tace ashe ba karamin kaya bane nace ko a can tsadane dasu ni

ina naga kudin sayensu a can ?

Dan kari yanzu kudine sosai wajen nan ashe mama ta fada nace gaskiya kudine sune dai abincin can din

sai filawa da yan abin tsotso haka abincin ke nan dai a wajensu.

Gaskiya yayi kokari ba kadan ba wanan kayan haka autace fa yusuf kowa lalabata yakeyi yati farin jini a

wajen iyayyenta.

Wai mama baba ba zaizo bane kafin muje katsina yaya azizzah take tambayan maman mu ita kuma

takw bata amsa da zuwanshi ai haboneshi ko yaushe ana iya ganinshi yazo.

Nidai na mike nashige daki bayan nace kowa ya dauki abinda yake so a cikin kayan na barsu suna

dubawa har mama tace suyi yaya dashi idan sun dauka ?

Nace suci mana mama suji abinda turawa keji abincinsufa bai kai namu dadi ba amma kuma sai bakin

tsadar tsiya dasu.

Ke kwashi kayan ki zuwa daki idan ya kare a nan wazai saya maki ku bakuko tunanen sune abincinta

muma ai abincin mune yusuf ya fada ya dauki wani kwanko da yake zaton madarane a ciki ina mashi dariyan keta a wajen don abinda ya dauka din kamar custand yake ba madara bane.

Na idar da sallah antyna Azizzah ta shigo dakin take fadin salma har kin kwantane na mike nace zan

fito inci abinci ai ta zauna a gefena take fadin .

Nifa yau a cikin mamaki nake naso inyi magana dazun kuma mama tana wajen a lokacin jin hakan yasa

na dam dubota kadan hankalina yana ga waya.

Wai kinsan ban taba ganin wanda yaya Sulaiman ya sake dashi irinki ba sai tayi shiru nima ban dago

irin na farko ba saurarenta nakeyi a lokacin.

Tace Allah sai zuciyana ya ban akwai abinda ke shirin faruwa a tsakanin ku sai lokacin na dan dubo ta

nace kamar mefa ?

Time will tell amma wallahi yaya sulaiman yana sonkine salma don irin kallon da yake maki ya wuce na

yan uwantaka ko kuma don ya auri yaya yake hakan kallone da kulawa na daban yake maki a yanzu.

Anty na fada ina kallonta kafin nace saboda me kikace hakan don kawai yana kulani a yanzu ai wanan

don yaya Ahmed yake min haka ?

Saboda yaga yadda yaya Ahmed yake kula da yan dakin mu shima kuma ance ai a baya su din suna

shirine da mama sosai nina dauka don hakane kawai ?

Ta dan murmusa tace dani kwarai kuwa salma Allah yaya Sulaiman sonki yakeyi so kuma bana wasa ba

ni dai shawaran da zan baki shine ki taka a sannu don Allah ?

Don wanan abin har inda gaskene akwai babban yaki a gabanki ta cikin gida data waje don sai kin

shafawa idon ki barkono kin liki kunnuwanki da auduga.

"Don kinga ko a dakin mu nan bamgaren mama sai ra,ayi yasha bambam a cikin mu wasu zasu soki dashi"

wasu kuma zasuga haka ai bai dace ba tunda ya taba auren yar uwarki a baya.

Ni kan a wajena salma matukar kina son shi wanan ba matsala bane ace don ya auri yaya ba zaki

aureshi ba yanzu ai a wajen Allah hakan ba haramun bane ?

Ni abinda zan fada maki shine tsakani da Allah kada kiyi sakaci da daman ki salma ko anyi fushi dake

kan hakan aibake kikace ya saki yaya don ya aureki yanzu ba Allah ne ya kaddara hakan a kanku .

Don haka salma ina son ki saki jikinki kibar dan sharewan nan haka da yawa kodai baki aureshi ba ai kin

debe rabonki wajenshi idan kuma zaki iya toshe kunnuwanki ni dai shawaran da zan baki shine.

Kada kisakacin da zakiyi dana sani a nan gaba don idan aka tara maza dari a kasan nan yana da wuya ki

samu uku irin yaya sulaiman a wajen komai.

"Kinga kuwa ashe ko wani mahaluki yana sha,awan kasancewa a karkashin innuwan irinsu don ya lakato"

abubuwa da dama na rayuwan dan adam bawai ina nufin don dukiya ba salma komai ma zaki karu dashi da zama da sulaiman.

Kema haka kuma salma irinki a yanzu sai irinsu yaya sulaiman saboda nasan ba wani namijin da zai

ganki haka har ya dora idonsa akanki ya kawar saboda kema kin tara komai da ake bukatan mace dashi.

"Na dan girgiza kai ina fadin ra,ayinkine hakan anty amma ni sam banda ra,ayin irin haka ai bayan haka"

"mutumin nan shima bai nuna yana ra,ayin haka ba."

So ina ganin hakan kawai shawaran zuciyarkine yasa kike ganin kamar akwai wani abu a tsakanina

dashine ?

Zakice nace kiris ya rage a yadda naga take takenshi ya nuna maki abindake zuciyarshi nidai kinji

shawaran dana baki ki daure ki dake duk abinda zai faru ya faru din kada ki bari daman ki ya wuce a hannunki.

Nishim ciki nayi iya binta da kallo a tunane itace dai kila taga mun dace a idonta ta fita ta barni ina

tunanen maganganunta .

Wani jan yakine zai hau kaina idan yaya sulaiman yace yana sona naga ai yaya dai bata gidanshi yanzu

to meye na jan yakin ?

Ko matarshi da akave yar uwarmuce ita ina ruwana da ita tunda ba a kanta zan zauna ba kawai dai

babu wanan abin da take tunane don taga tsarin ido a kaina .

Ko don wanan mugun hali na yaya hindu da take ganin ba a isa da ita ba don abin nan da naji da

kunnena tayi da mama ya matukar tsaya min a rai.

Sam ban dauki zancenta da muhinmanci ba sai bayan kwanaki sun shude ne da yaya ta kirani tana

tambaya ina ina yaya Ahmed suna gari kuma yaya sulaiman na azumi in hada masu abin buda baki zasuzo nan gidan mu suyi buda baki.

Zan dan fitane a lokacin na fada amma ina dawo zanyi kokari in hada muna kashe wayan sai ga kiranshi

ya shigo min yake fadin bayan mun gaisa Yusuf yana gida nace yanzun nan ya shigo yazo ya karbo kaya ki hada min abin buda baki ya fada kai tsaye.

Cikin mamaki nace ganshi zamu fita zuwa kai dinki nida anty azizza ni take jira ok ba zan samu ba ke

nan no idan mun dawo da wuri zan dan hadama wani abu mai saukin dafawa ai.

Abinda nake so na nake so na saya zan aiko ki gyara min da hannunki kuma mama tana gida ai na sake

fada ba zaki tsaya ki gyara ba ke nan ?

Zanyi mana idan na dawo daga wajen dinkin azizza ta tafi ke ki tsaya idan ansha ruwa zan kaiki gun

mai dinkin.

Da sauri nace No ka barshi bari na turo ya yusuf din zan bashi nobaka ya kiraka nan na soma kiran yusuf

din ina fada mai abinda yace.

Shiko da sauri ya karbi number din ya fita daga gidan ina zaune saman hannun kujera na lankwashe

kafata sai lokacin mama ke magana tana tambayan waye nace yaya Ahmed da ya sulaima.

Suna garina nace ehh yaya farida ta fara bugo min waina hada masu abin buda baki suna azumi yanzu

shine wai a turo ya yusuf ya zo da abinda za a hada masu din.

Aida sun fada mana a duba in bamu dashi a nan sai a sayo a hada masu din basai sun sayo ba kuma

nace sunce sun sayo yaje ya dauko sai tayi shiru.

Ba zancen fita ke nan kuma Azizza ke fada daga inda take zaune nace babu gaskiya don wanan aikin

bansan lokacin da aikon zaici ba.

Baifi awa biyu ba yaya yusuf din ya soma shigowa da katon din kwai daya rungumo a jikinsa zasu kai

biyar duk ya girke a falo haka yayi ta shigowa da kaya mama na zaune tayi tagumi tana bin kayan da kallo.

Kai yuduf harsu nawane za aiwa girkin abinda take tambaya ke nan bayan tasa min kira daga falon na

amsa nida antyna muka fito turus naja na tsaya ina bin kayan da kallo kamar za a bude shago.

Wananfa na tambaya ina bin kayan da kallo a cikin mamaki lokacin yusuf ya shigo da buhu da aka saka

nama an gyara anyi komai iyaka dafawa a gyara kawai a lokacin.

Wai abincin su nawane za ayi haka Azizza ke tambaya tana kallona nima yusuf na duba don son jin

amsa yace nifa su biyu na gani kawai bau kuma min bayani ba yadai ce inzo da wanan driver a sauke kayan .

Shi kuma wanda ya dauki kayanma dan garine ai ku tambaya mana mama ta fada cikin wani yanayi

azizza tace yusuf ya kirashi yaji ?

Muryanshi tarr a wayan yana fadin mu biyune dagani sai Ahmed ai ya juyo yana fadin kinji nace ai su

biyu nagani a wajen.

Sauran duk mu zamu gyara abin mu yusuf ya fada ka samo kankara nan gida waya wani gida da suke

sayo kankara idan ana da bukata.

Mun hada masu wajen abinci kala ukku mairai da lafiya muka hada komai yusuf ya tafi kai masu inda

suka sauka wanka nayi tare da sallah na idar na dawo falo wurin su mama dakw hira.

Kula na bude na debe ferfesun ina dan shan ruwan a hankali tare da duba wayata dake ina charting da

kawata Lidia dake lokoja.

"Itace dai abokiyar hiran tawa don ko a can munyi sabo da ita sosai don al,adunta irin na hausawane"

addine ba daya ba amma saboda rashin yan gida yasa shakuwa ya shiga tsakaninmu da juna.

Tana yawan bugo min ko sa in bude data muyi hira sai hakan yake dauke min hankali da komai anan

aga nashige daki nayi shiru suke dangata hakan da rashin son magana da kowane banyi ?

Koda yusuf ya dawo har na shige daki sai gashi ya shigo yana fadin ga yaya nan waje wai kuzo ya kaiku

ku karbo dinki ?

Cikin mamaki nace da daren nan kawai a barshi dare yayi shima yayi azumi yana son hutu ai saiga

Azizza ta fado dakin take fadin bazaki tashi mu tafi ba ?

Haba anty a cikin daren nan kamar abin gudu azumi fa yayi yana son hutu tace don Allah taso muje kin

sani ko alheri ke kiran mu dole ta tasani a gaba na tashi ta samu mama tana fada za a kaimu mu karbo dinkin.

Itama mama abinda na fadane ta fada yaya ke fadin ai yafi sauki mama kinsan su teloli basu barci a

shago suke kwana wani lokaci.

Kardai a dade don Allah mama ta fada sai gani na fito muka fita yusuf dashine a gaba muna bayan

motan koda muka isa shagon ita da yusuf din suka fita suna fadin jiramu mugani ko andinka kada abar yaya shi kadai.

Haka yasa dole na zauna tare dashi a motan don na fara tsarguwa da zancen da mukayi da ita don

itama ke nan ta fadi hakan inaga wani na waje me za a fada kan kulanin da yakeyi yanzu.

Ina jin lokacin daya furzo iska daga bakinshi zakice wanda zuciyarsa tayi mashi taurine a lokacin akan

wani abu cikin wani karamar murya naji ya ambaci sunana da SALMA .

A hankali na dago kaina na dan dubeshi bai kallona yana zaune ya rike sitiyarin motan da hannu daya

yana