Chapter 41 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

yaya sulaiman da yazo ya saya

muna kaya masu yawa ranan.

"To yaya sulaiman fa kikace nace umm,hmmm tace dankari to wai,ke salma wani irin shakuwane kukayi"

haka da yayane wai ?

Nace nothing kawai dai muna gaisawane dashi bayan haka ba wani abu irin haka ai to Allah ya sauwaka

amma haka kawai koda yake ance rabon mutum ai baya wuceshi dama sai mun hadu a katsina sai naga kayan nace to shike nan yaya nagode da kulawa itama tace No ba komai baturiya .

"Duk dabi,unki salma ya koma na turawa yanzu abu kadan godiyane ga mutum nayi dariya muka dan"

taba hira akan yara ta kashe wayanta.

Haka yaya Azizzah ta matsa min sai muje kitso duk da nace kaina yana min ciwo wani saloon muka ba

nisa da gidan mama matar ta iya aiki sosai manyan kalaba nasa tayi min sai gyaran goshi da tayi min na bata kudi mai yawa tana tagodiya muka fito zuwa gida.

Da dare nake jin cewa za ayi tafiyan da motar kawun mune zaiba da mota a kaimu har katsina dashi

inda naji dadin hakan sosai dama banson shiga motar haya da akace wai ita zamu bi.

Ba tafiyan safe mukayi ba zuwa katsina din don haka karfe hudun yan ma da wasu mintuna muka iso

garin mota bai tsaya ko ina ba sai kofan gidan namu.

Wanda tun a waje nake ganin wajen kamar ya canza min kuma hali zanen dutse don kuwa dai gwaggo

"Asiya ta tuna min da baya zakice bata san da munshigo ba tun bayan sannuku da zuwa da tayi muna a cikin jam,i bata kara kula kowan mu ba."

Duk da zuwan da akeyi ganina ana salma barka da dawowa gwaggo hafsatu ma nayi mamakin zuwa

taron mu da tayi a ranan balle gwaggo laraba da a take ta aiko muna da abinci har da drinks masu sanyi.

Abin haushi da takaici mun samu yaya batazo gyaran dakin da mama tace tazo ta bude ta gyara ba dole

muka hau gyaran wajen da gajiyan mu har da yusuf da yake namiji bai fita ba saida yaga mun gyara wajen tas ya fita.

Mama ko sai mita takeyi kan yaya tana fadin ai zatazo ta sameta a nan tun yaushe tayi mata magana

da taki zuwa ta gyara mata part har mukazo muka sameshi haka ?

Nikan muna gama gyaran na shiga bayi nayi wanka na tsabtace jikina na fitone na saka kayan barcina

na kwanta abina a daki.

Suke ta faman kai koma mama da antyna ina daki sai anzo ganina nake fitowa mu gaisa i koma daki

kuma.

"Bayan magaribane ina daki naji mama tana kirana wai in fito ga Sa,id yazo yana nemana hakan yasa na"

fito da sauri nagashi shima ya zama mutum sosai gashi tsakaninshi da yusuf na rasa wanda yafi kama da mahaifin mu sosai.

Don su biyun su suka dauko mahaifinmu sak a kamanni baki ya rike wai yana mamakin girmana nace

shima ai yayi girma sosai har ya fini.

"Zama yayi ya kura min ido zakice tv yake kallo saiga baban mu da fara,anshi ya shigo yana muna sannu"

da zuwa tare da fadin ina salman take wai ?

"Baba gani na fada daga inda nake zaune rike da hannun sa,id yace to to ashe mutumin nata yana nan"

tunda na fada mai a kasuwa kunzo har da ita ya matsu mu dawo wai ya ganta .

Yarinya ta kawo muna abinci ta aje tana fadin wai gwaggo Asiya tace ta kawo mama ta karba tana

fadin angode ta aje na sauko na durkiusa ina gaida mahaofin namu da wuni.

Da alaman yaji dadin ganina sai washe baki yakeyi yana fadin Allah mai iko Allah ya nufa andawo ke

nan salma barka da dawowa gida lafiya nace bagode baba.

"Saiga Sa,id yana kwaikwayona aka kwashe da dariya yana misali wai gaba daya na canza kamar bani"

bace yar karamar yarinya dana tafi.

Shima dai yayi fushi tunda ban damu dashi ba tunda na tafi nace ba wanda zan ba sakone ai inda naje

yana da nisa sosai.

Antynane tashigo take fadin ance su yayan mu faridama sun iso da daren nan masha Allahu baba yace

yana mikewa har yakai kofa ya juyo yana fadin Dije baku bukatan komai ko ?

"A,a ban bukatan komai yanzu gaskiya to ko za a sayo maku ruwan shayi don ita wanan bakuwar turai"

"din a,a tazo da abincinta ai."

Balle salma ba wani abincin kirki takeci ba ita haka naga na koma kamar kwai a cikin dangi kowa yana

tarairayana daga daki mune yaya ta leko tana fadin kicewa kurma mamanshi na kiranshi don Allah .

Gata can tana ta fada wai tunda ya dawo yazo ya shige daki kamar wanda yaga wanìúi abu yaki fitowa

na tabashi nace yaje mamanshi na kiranshi waje.

Yace wai mu kyaleta ita ta faye damuwa don Allah shifa ba yaro bane yanzu Allah sarki sai naji yaban

tausayi da yake fadin hakan gashi duk ya isheni da irin warin maza din nan amma haka na daure na zauna dashi muna hira.

Yake fadin bari yaje ya dawo muyi hira a raina nace kaji a salansa indai nice koda zaka dawo nikan nayi

barci ai sai ga baba Alu ya dogaro yazo ya zube a dan dakalin gefen dakin mama yana fadin ina bakuwar turai din in ganta.

Allah ya nufa sai kin dawo ban mutu ba yar nan na fito muka gaisa dashi akai yaya bayan rabo da juna

nan kuma suka hau hira da mama yana bata labarin ciwonshi nikan na sullace jiki na shige daki na kwanta.

Sai barci don na gaji sosai ga hanyar sai a hankali barci mai nauyi ya daukeni ban falka ba sai cikin dare

kishi fitsarine ya tayar dani amma duk da darene ina jin hayaniya a wasu sassan gidan.

Da safema na makata don tunda nayi sallah na koma kuma na kwanta ban fito ba sai wajajen sha daya

da rabi na fito mama ke fada min kurma yayi mayawa da mayanni yazo wajena .

Tashi nayi na shiga wanka na fito na samu antyna take fada min wai in shirya mu shiga wajen yaya

farida ta aiko muje nace nagaji ban iya fita yau gaskiya.

Ina zaune ina karyawa da cornflakes yayan mu ta shigo gidan da yaranta ina jin tana gaisawa dasu inna

kafin ta shigo dakin mu tana fadin mama sai kika samu banzo na gyara daki ba kuma ?

Da bakizo ba ai mun zo mun gyara ko ta bata amsa fuska a daure tace ayi hakkuri mama na zata sai yau

ai zaku shigo sai gashi ana ce min kunshi jiya ai.

Ta daga kai ta dubi labulen da muka saka masu kyau dasu tace mama ashe kinzo da labule din har ina

batun in kawo maki wasu nawa ku saka idan kun tashi in debe abina.

Kamar mama ba zata bata amsa ba can kamar an kwantota tace hindu rashin mutuncin naki har yakai

haka aga kin aro min abu daga gidanki bayan na wuce aga kina kwanta kuma ?

To lalacewan nawa baikai haka ba himdu aiba ke kadai bace da baki saya min ba autana ta sayo min

itace ta sayo min har da ragowa gasu nan kuwa har biyu.

Ai salmace ta saya maki wa yan nan amma suna da kyau gaskiya halan nawa yadinsu suke salma ?

Na dan juyo ina fadin bani nayi ciniki ba antynace ta yi dom kayan da yawa ban ganewa gaskiya ina

fadin haka na tashi but na fita don in dauraye kofin hannuna.

Mukai arba da gwaggo Asiya data kafa kujera daga kofanta ta zubowa kofan mu idanu kaina kawar naki

gaida ita har na gama na juyo zuwa dakin mu din .

Nayi hakane don taji zafi itama tasan gaisuwa yana da muhinmaci ga dan adam yasa naki gayar da ita

da kwana .

Nashiga daki na fito ina tambayan mama ko za ayi abincine take fadin tunda akwai miyan kai da

mukazo dashi a bari sai yamma a tuka tuwo kadan na amsa da to tare da juyawa zuwa daki.

Ina dakin ina jinta tana tambayan mama ina miyan naku indan diba inci bread dashi ba zan iya cin

wanan masam ba yayi sanyi gaskiya.

Wai meye matsalan matar nan ne kodon tana yar farine wauta yayi mata yawa haka wai itace babba

kaf a gidanmu ko ince a wurin iyayyena kila shiyasa take kamar bata da wayau haka.

Ni dai ina daki ban fito ba har take fadin ina zata koma gida sai lokacin take fadin ina salmane ke inkiga

"mutane sai ki shige daki kamar kina jin warin mutum,"

"Nazo tun dazun kin shige daki kinyi zaman ki kamar kurma a,a kada ki damar min yarinya don Allah"

kema kinsam halin salma ai da rashin shiga mutane ko ?

To nidai nayi gida sai dai gobe idan za ayi kamun amare zan shigo mama tayi masu sai anjima suka tafi

naja ajiyan zuciya ni kadai a dakin .

Antyna ta dawo da kaya yara na biye da ita tace yaya farida tace ta kawo nan gida nan mama ke fadin a

kira inna halima .

Bayan tazone mama din ke fadin ta kwashi kayan nan farida ta aiko musu dashi wai ayi amfani dashi har

ta duka zata dauka sai kuma ta dakata tana fadin .

Tau yaya yau kuma bani keda girki ba in dauka ya zama abin fada ga matar gidan nan kinsan halinta ai

da fitina ba fasawa tayi ba har yanzu.

Idam sunyi magana fada masu ninace ki gyara min ina shike nan jin hakan ta dauka ta fita dagani sai

yaya muka kallo juna nake fada mata yadda mukayi dazun tace ashe irin nawa akayi don wallahi ban yarda da irin abinda tayiwa su yaya a baya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA.

"[12/21, 10:09 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

"Ina daki akwance naji mama na kiran sunana tare da fadin kizo ga mutuminki nan Sa,id yana nemanki jin"

"ance sa,idne yasa na fito daga dakin ina saye da wani dogon riga skin ties tundaga England nazo da abina tare da dan hulan da nake hadashi da sukai matcher da juna zakice tare aka dingasu da kayan don launinsu daya."

Yadda ya sake min min murmushi haka nima na sake mai murmushi tun daga nisa na zauna yake fadin

ni inata jin dadina ko yaushe ina daki kwance ?

Nace kaima ai yace ina ni bangashi ba wahala yayi kai yawa yana neman kudin da zai dinga tufafine ya

shiga mutane nace ina naka ka saka mana bakaga mutane sunyi yawa bane yace nasa din aiba masu kyau bane sun tsufa.

Duk a cikin maganan kurmanci hira dashi hae yake fada min ya tara kudi mai yawa amma gwaggo da

baba sun amshe mashi kudin yanzu da kyat ya samu kudi zaije ya sayo kala guda a dinka mai ya fitar da kudin yana nuna min.

Nace dashi ya ban in sayi gyale mana shiru ya danyi ya bata rai kafin kuma ya miko min yana fadin inje

insaye din shiya huta ai.

Karban kudin nayi na mike zuwa daki yana zaune ya bini da kallo da nashiga dakin suka maida hira da

mama na fito da kudi yan dari biyar biyar a hannuna tare da nashi din.

Na hada na mika mai baisan lokacin daya kamo kudin da hannuna ba ya hada da goshinsa wuri daya

yai shiru nima banyi kokarin fisge hannun nawa ba na kyale inga gudunshi idan yayi haka yayi matukar jin dadin abinda dan uwa yai mashi ke nan yake hakan a lokacin.

Wai kuka yakeyi ko me nace gashi nan dai wai farin cikine nake gani kinsan haka yakeyi idan yaji dadin

abu ai haka yakeyi.

Ya dago kudin ya dagawa mama waita gani bai mai ba ya mike ya kamo hannunta ta rika kudin tasa mai

albarka.

"Mama tace tagani tayi addu,a yace duk gidan nan ba,a tausayinsa akwai masu kudi da yawa da yawa"

amma ina basu son shi sam.

Ya fara kwantance mutanen gidan dake da hali ya soma da yaya Ahmed mai gemu baki bai son shi mai

hanci dogo dan gayu mai mota mai kyau mama tace sulaiman ke nan yace kai baida kirki ko kadan yace a saya mashi mashin ko keke sunki saya mashi.

Dariya nakeyi sosai da yake kwantancesu din har su baba karami bai bari ba saida ya kwanta muna

halin kowa shike fada muna ai sulaiman yazo da iyalinshi mu bari mu gani komai bai basu sai su baba zai ba kudi.

Kai ai yarone na fada yace shine yaro muna zaune muna shirmen mu boy ya fado dakin kai tsaye

"wajena ya nufo nake fadin a,a boy kaida kazo yace mamansu da baban ."

Nan kurma yake tambayana wai na gansu kuwa suna jin dadinsu muna tsaka da dariya suka fado dakin

mu da sallamansu ashe yaron da iyayyensa yake.

"Ya Ahmed ya shigo yana fadin a,a kurma nan kake wajen mama mama da sukaiwa shigowan bazata sai"

kane kame takeyi tace ya dai zo wajen mutumiyarshine salma.

"Allah sarki ashe bai manta da ita ba ina zasu manta juna kaiko an taso tare irin shakuwan salma da sa,id"

ai bata wasa bace don dai Allah ya raba abinne haka .

"A,a sulaiman duk tare kukene ta fada ya amsa da eeh mama ance kinzo nace mushigo mu gaidake da"

zuwa ai take fadin wallahi munzo babanku ya matsa sai in taso tun shekaran jiya ayi komai damu haka nada kyau kwarai mama ya fada.

"Ina wunin ku yaya nayi a jam,i ban zabe kowa ba yaya Ahmed yace salma ance kince baki zuwa katsina"

"nace a,a saboda me kuma keda garin ku ?"

Murmushi nayi kawai bance komai bayan sin zauna ya dubi kurma yace sarkin jininin nan kuma ya tare

maku lokacin mama ke fasin har da karanku ya kawowa salma kuwa yace ba a sonshi ita kadai ke son shi a gidan nan.

Nasu dai yazo dayane yaya Ahmed yayi mai hannu yana tambayanshi abinda yace min sai yayi

murmushi yana kada kai hakan ya fada din.

Yanzu wai nan ya zauna ta saya mashi mashin ne ko keken dinki tunda kowa yaki ya saya mai nan yaya

sulaiman din yace ai gara dai keken dinki din yafi.

Idan Allah ya hore min duka zan saya mai lokaci guda insha Allahu wanan kadai za a mai yasan ana

kaunarshi a yanzu lamarinsu suna son a dinga gwada masu kaunane a cikin yan uwa komai aka fada ko yaushe a cikin tsarguwa suke su bayanin da nakeyi ke nan a falon sukai shiru suna saurarena .

Kinsan bokan turaine ita har hanjin mu tana gani a wajen nan nace haba dai hakan ya kamata ya

kasance tunda Allah ya jerabeshi da lalura haka.

Nikan na mike tsaye ina fadin ya taso muje suna dubana ina zani dashi nace zan fitane muje ya sayo

yaddin dayace a bada dinki.

Duk dariya suka kwashe muna dashi lokacinne yaya fadila ta fado dakin itama tana fadin wallahi

salma kin kyauta nace kuzo kikaki zuwa kina nan manne da mama ke ko yaushe ?

Haba dai yaya bakin zuwa nayi ba naga mu fita mubar mama ita dayane bai dace ba ai hira akeyi sosai

"a dakin kurma kuma ya dameni muje din muje inda zamu yasa na mike nace muje sa,id ."

Ke kibari nazo na fita daku ina zaki haka dashi yaje can ya baki wahala abinda ya fito daga bakin yaya

sulaiman ke nan a gaban kowa da dakin yayi shiru.

"Ba kunya kuma ya mike muka fita yabar yana Ahmed muka tafi da Sa,id din dani da yusuf mun jima"

"muka dawo da sa,id dake ta washe baki don alherin daya samu din."

Mamace kadai a dakin mu zaune na shigo da ledan kayan fruit na aje a gaban mama ba yabo ba fallasa

a yadda ta amsa min din a lokacin sallah naje nayi bayan na idar naji shigowan antyna tana tambayan su salma basu dawo ba har yanzu.

Ta dawo tana ciki wanan yasa na fito ina fadin mun dawo anty nagajine wallahi kinsam fita da yaya

"akwai wahala har keken dinki ya sayowa Sa,id fa yau suna can wai ana hada mashi shine ya dawo dani gida."

Ke meke tsakanin ki da Sulaiman ne mamace ke fadan hakan gareni duk muka kallota nice nace mefa

mama wani abune ?

Tambayanki nayi don ku ba hankaline da tunane gareku ba wani lokaci sai kuyi abu da gangan akan

rashin hankali .

To ki kama kanka kada ki wuce gona da iri a wajen nan kuma ki tuna nan katsina muke kina fita dashi

yanzu za a fassara maki zance da wani abinda ba shiba a nan .

To a fada mana meye don an fada mama indai gidan nan ne ai sun saba da kullawa mutane sheri dama

"don kawai,,,,"

Azizzah zanci abu kazan ubanki ina zance da yata zaki tare kada in mata fada alhalin kowa yanzu yasan

shakuwarsu da sulaiman yayi yawa me hakan ke nufi wai kin dai san abinda ba zai yuyu bane kina kula sulaiman tunda kinsan irin abinda ke nan tun farko.

Meye a ciki mama idan na kulashi ni ina ruwana da wani ko abinda wani zai fada can hakan bai dameni

ba ai indai nasan kaina badai zan aikata wani abin asha da za a zargeni akai ba.

Kuyi min shiru don Allah ta fada a cikin bacin rai sai mukai tsit lokaci guda fuuuu na mike zan nufi daki

tace dakata kiji salma haka yasa nayi tsaye a waje daya cak man gara daga kafata ba balle in motsa .

Inda mama tacigaba da fadin kin dai san yadda kuke da shigen dake tsakaninki dashi dan uwan kune

"don dan gwaggokine haka kuma ya auri yarki hindatu kin dai sani don haka kisan yadda zakiyi mu,amula dashi