Chapter 43 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

wasu na fadin munfita shiga a wajen yan bani na iya sukace wanemu ai ba a taba kaita don ko zinaren wuyanta ai abin kallone.

Wanan kus kus din sunayishine a tsakaninsu iya su don suna gudun baba Audu yaji labari yaci masu

mutunci yasa aka soma tausa murya.

A motansu yaya farida muka muka tafi wajen saka lalai din duk daba nisa da gidan mu mun samu

ansoma event din don haka kowa na zaune haka yaya farida da yayan mu suka ratso tsakiyan taron damu .

Aiko munsha kallo da nunawa nida antyna mune yan mata a ciki don haka mune adon gari ido a kan mu

kowa na gulma akan mu din .

Nina kasamce banda hayaniya wanan yasa banda rawan kai amma akwai miskilaci da izza a tare dani

"akai sa,a wasu yan gidan mu yan mata sukecewa yaya farida ga kujera suka mike suka bar muna inda suke zaune gaba din nan muka samu wajen zama ta gabansu."

Sam ina ganin dukkan taron ba zasuce sun sanni ba a cikin yan uwa don haka ko banza dole insha nuni

saboda hakan haka kuma ga inda akace nayi rayuwa sai kuma akan wanan matsalan dake shirin kunno kai a yanzu saida taje tayi manni da mutanenta kafin yaya farida tace mu fita muje muma muyi don ta

tambaya akace akwai kudin manni din antyna ta fada.

Munyi mun koma mu zauna a wajen muka samu wasu daga ciki sun zauna a inda muke kada kuyi

magana ku barni dasu yaya farida ta fada.

Hakan yasa muka tsaya a bayanta ta karaso tana fadin sai ku bamu kujerun mu mun dawo wayanda ke

zaune a sama sukayi kamar basu jita ba lokacin.

Nace ku bamu wuri mun dawo sai wata yar gidansu jamila ke fadin ai kujerun ba son mutum daya aka

kawo ba kun tashi mun zauna a kai ko kalas ?

Zance kike so ke nan nan yaya farida din ta soma kiran wasu daga cikin kannensu suna zuwa take fada

masu cewa mun tashi daga zuwa muyi nanni sun zauna muna a waje.

Dolema su tashi wallahi ko suwaye kuwa wata ke fadin yan gidan gwaggo habbice fa ko gwaggone fa

"inji suwaiba ita da bukinta idan badon itaba zai ai wanan sha,anin hakane balle wasu suzo da duwawunsu su zauna masu a waje ?"

A ranan na tabbatar daka kyautatawa dan uwanka ko na miji yana da dadi a duniya don tsaye yan

"matan sukayi abawa matan yayansu kuma ai aba yan uwan mu wajensu wallahi ko ayi bala,i aiba nan kuke zaune ba."

Shine jamila din ta taso tana fada wai zasu nuna masu bambancine kome koma an nuna ai ta isane a

nuna indai yaya faridace tunda abinta namune ta zube kudi ta hada muna wasa ace za ai mata wullakanci wallahi bai yuyuwa hakan saiko fitina ya kaure a wajen.

Kusan yan gidan mu suna goton bayan yaya farida har suna kokarin dambe a wajen sai kuma gori da

take fadin Farida tafinine ?

Tako fiki don ko bakaje ba kana ganin sakonta fada sosai akayi da kowa a wajen ranan yan gidan

dawakai suka fito karara suka nuna mata suna da cikinta dama ashe.

Tana fadi ana fadi ana janta ajasu manya na tsawatawa tana nuna bata bari sai balle ballen magana da

takeyi wai ana adawa da ita tafi karfin mutum wallahi.

Haka yasa su yaya zuwa wajen taron suna kwatar da tanzo ma ji kawai nayi an riko min hannu na juyo

a hasale inga ko waye ya kama min hannu haka ?

Yaya Sulaiman na gani a wajen yana murmushi yake fasin zo ki fita filin nan kada su illanta minke nasan

don kece ake wanan abin ba zan hakkura da wani ya kai maki duka ko zagi ba wajen nan sai kawai yaja min hannun na soma binshi kamar zonbi.

Sai kallon ya dawo garemu kuma har mun kusa kai mota antyna ta samemu tana fadin yau yaya zaka

haukata jamilafa a gaein nan .

Gasu can sun koma fada da yaya farida sosai wa anaci mata miji bayan fage tagane munafuncin da ake

kokarin hadawa kira min farida kubar wajen nan tun kan ta isa ta hango faridan tafe har lokacin ana masifa.

Ta karaso tana fasin kai kuma yaya dai ka kara haukata muna jamila yau abin nan da kayi gasu can sun

"dora sabon bala,i kuma ana riketa aida su saketa tazo wajen nan tagani."

Suka dai sakamu mota muka dawo gida tun cikin mota ake cacaca ina jin kaina kamar zai fashe a

lokacin saboda wanan abin..

Muna shiga gidan labari yazo masu baba Audu yana tsaye yana masifa irinta katsinawa yana fadin

dama nasani yarinyar nan sai takai ga jawo babban rigima a taron nan irin yadda naga sun fita gidan nan.

"Muka rabashi bata isa tazo gidan nan don wani shirme nata ba tace zata bata min taron jama,a shi"

sulaiman hauka yayi da zaiyi haka ?

Sun tsaya gaidashi na sulale jiki nashige cikin gida kai tsaye dakin mu na nufa ban samu mama kofa

rufe yasa na nufi dakin inna halima na kwanta saman gadonta.

Yaushe rabona da leka dakunamsu tun ina karama ficiciya muna gidan duk zuwan da nakeyi bani shiga

dakunan dayansu a lokacin.

Allah sarki inna halima a haka ake rayuwan dai har yanzu ke nan abubuwa basu dawo daidai ba dai a

gidan kenan ko ince wajenta sai naji taban mugun tausayinta a raina.

Ban taba tunane ko mafalkin inna halima a cikin tsarina ba haka ban taba kawo ai bata dashi

matsayinta na wance tayi rayuwa da iyayyen mu cikin amana ai tana da bukata ba.

"Sai gata a dakin kamar ta karanto abinda nake nasawa a zuciya tana fadin a,a salma haka kika kwanta"

saman gadagadan nan mai su daddaden katifa haka .

Ba komai inna ai an kusa hutawa insha Allahu tace Allah yasa autan yaya haka take kirana dashi tun

farko ni da nazo in huta saiga inna ta hanani hutun tana ban labarin dayaja hankalina akan zamansu da inna Asiya harda kwalanta.

Wani irin abu naji ya tsaya min a zuciyana na takaici har ina tambayan kaina wai wasu irin mutane da

taurin zuciya haka wai sam ba tsoron Allah a cikin zancen bayin Allah nan.

"Sudai idan ba ka nuna kana kasa dasu ba ka tsaya ka kaskantar da kanka garesu watau ba,a zaman"

lafiya dasu ke nan yanzu ina ranan haka don Allah ?

Mace da iyali kamar inna halima amma tana wahala haka ba a duba mata ko kadan kirana da antyna

keyi don basu ganni ba yasa inna dake kofan daki zaune fadin gata nan a dakina kwance.

Don hakan ban karamin dadi ina taji shigowa dakinta da nayi ba a lokacin nan antyna ta shigo ta sameni

muna bawa inna labarin abinda ya faru.

Saida inna halima ta dan juya baya taga idan babu mai zuwa ta kashe murya tana fadin keyi abinki idan

kina so kinji ai kowa nason hutu anga wajen hutune ba a sin kowa ya shiga ?

Waya fara shiga gidan tun farko ba yayan ku bane ta wankeshi ya wanke ta aka matsa mata lanba a

gidan nan harda aiken zagi dana cin mutynci karshe tagudu ta barshi ni sam banso huluncin da akayi nakashe auren ba ai.

Wallahi idan kinga kina sonshi kiyi abinki tunda Allah bai hana ba wurine da kowa yake so ko ita yaya

hafsatun yace yana son yar ta halan ba bashi zatayi ba a yanzu ?

Tunda sun juya mata baya kullum cikin korafi take anayi bada ita ba itako matar shiyan nan har wani

barazana take muna za a gidan daula suje suna sace sace a can akace ban gani ba dai.

Sai kuma ta kwashe da dariya tana fadin da wallahi haka zan nade kayana inje cin arziki in rama abinda

take min antyna tace sosai kuwa inna .

"A,a,a yau dakin inna halima zugar ya kawoku kuma yaya farida ta leko tana fadan haka gasu nan fa"

muna shan hiran mu auta tazo ta samu yaya na cikin gida shine tayo nan.

Nan yaya ta soma fadin akwai zama yau ance gasu can a zaure tare da tsoho nasan zai kirani ni kuwa

yau saina kulla masu sheri a wajensa wallahi.

"A,a hjy karama basai kinyi haka ba ai gaskiya zatayi halinta shi sulaiman dun aiba kurma bane nan kuma"

aka dasa sabon zancen dake sakani ina jin wani irin tsuma a kasan zuciyana.

Komai ta fajama famjauuu a yanzu kan matukar aka kirani zasu sha mamaki a wajena kuwa don amsan

da zan basu sai yasa da sun sani basuyi muna hakan ba ?

Idan ma suyine da niyar tozarta mu to Allah yafisu yafi sherinsu ance ko matan gidan ko yara bata

kaunar raga wani ya tsaya da mijinta yanzune zata daure damai shi kuwa.

Iyasu kadaine suke wandakansudin ko hjy inna don tana mahaifiyarshice take gane wani abu a zancen .

Duk inda kika bi a gidan kus kus akeyi ranan kan wai ai soyayya mukeyi da yaya sulaiman har matarshi

ta gane haka ?

"Wasu su goyi baya wasu su karyata zancen wasu kuma suce abune da ba zai yuyu,ba masu Allah gwai"

sunfi yawa dai kam.

Muna nan zaune saiga yayan mu tafito a nan kofan dakin innan ta tsaya tana fadin toni zani gida yaya

farida ta dago tana fadin tun yanzu ?

Take fadin to me zan tsaya inyi kuma nakira Alh yazo ya daukeni yace ya kusa karasowa yanzu jin

hakan yasa muka mike duklan mu don mu rakata ga yara ga kayan a hannunta kuma.

Mun taka zuwa waje can dan nesa da gida mku tsaya duhun magariba ya soma a lokacin muka yana

tsayawa dabe na kaurewa kuma a kofan gidan namu wai ashe fadan ne kuma aka kara tayarwa a lokacin

su dai suka sheka zuwa rabo nikan ina tsaye banje ba har saida ta saka yaran a mota zata zauna ta juyo tana fadin.

Ke ki fita zancen mutanen nan fa keme zakiyi mata da mijinta kuma tunda ita bata son kowa ya rabi

mata miji kowa ya sani a gidan nan kuma .

Nagode na fada mijinta namin shirin baiga tsaraban turai ba nace ba a kawo ma turare ba ?

Yace bata ban ba kinsam halin hundu ai sai yayi mata dadi idan ta tuna tabani sai cewa tayi ban bashi

don zuwa zaiyi ya aje yar iskan matarshi ta feshe .

Sam banji dadin hakan ba don turare na musanman na sayo masu tun daga can don maza kuma da

nazo na cite mashi nace tabashi sai cewa nayi bari zan baka wani kafin mu wuce.

Yana godiya yaja mota suka tafi nikan na raba wajen na shige cikin gida abina don ban iya tsayawa

kallon wanan shirme ga lokacin magariba yayi.

Mama na samu ita kadai a dakin tana sallah uwar daka nashiga na soma cire tufafin jikina kafin na

shiga bayi na waysa ruwa tare da doro alwala na fito na soma sallah.

Can naji muryoyinsu sun shigo ana mayar da magana wanan karon kan muryan gwaggo Asiyane kamar

"zai fasa gidan don bala,i."

Ke Salma naji mama ta fada da kakausar murya nayi mata alama da ina sallah hakan yasa tayi shiru

ina idarwa na mike na samesu a falon ina fadin mama gani sallah nakeyi koda kike kirana.

Salma ba nayi maki magana ki fita harkan sulaiman ba ashe ?

Mama ina ruwana dashi kamar ya ina ruwanki dashi salma ki rabu mata da miji mana tunda bata son

hakan ko so kike ki dauko wani maganan da bashi ba ?

Ance ana tsaka da fada yazo yaja hannunki kada a bugeki kowaye akaiwa haka a gaban mutane dole

ran meshi ya baci balle ita da dama take bidan irin haka tayiwa mutanen iskanci.

Koda ta samu hindu a gidan sulaiman lokacin iya abinda zata nuna min ke nan a matsayina na uwar

hindu balle yanzu taji hakan ?

Mama laifinane koni na kirashi shi dai zakiwa magana ya rabu sani tunda matarshi bata son hakan

muryan gwaggon mu Asiya dake mugun zaki akan mu wai yaya mata ana neman inda za a cunasu da karfi da yaji ba dole ido ya rufe ba yanzu tunda anga wajen ci yanzu.

Aida sulaiman din da aka aurawa hindu shi don baida komai gudunshi akayi karyan turai yakare ke nan

an dawo ayi kwace a gida .

But na fice ina jin mama na kirana na karasa fita saboda idona ya rufe na tsaya ina cewa by d way an

"fada maki kowa irin zuri,an kune da kuke cunawa da karfi da yaji."

Ki tambayi sulaiman din idan na taba kula shirmensa ku baku da kai baku da lissafi sulaiman ba nemana

yakeyi kawai zumunci mukeyi a tsakanin mu amma duk kun ruda gida da hauka haka ?

Kam uban nan ba don antyna kila ta turani daki mu ba a lokacin kila da gwaggo Asiya takai hannu a

jikina lokacin don kuwa cikina tayo da zafi antyna ta tareni tana turani daki.

Ita uwar naku data izaki in ta isa ta fito mana bakar akuya mai kai yara ga barna ta san komai tana abu

kamar bada saninta ba.

Maizogale ba maizogale bakar munafukam ba mahaifiyar mu ba yusuf ya fada daga bayan ta kuma

saita koma fadin .

Au dama ashe kun shiryo min ne ban sani ba ashe da shirin ku kuka zo garin nan to a zuba shege ka fasa

mu duku gidan nan.

Yadda gidan nan yaiwa uwarku kamshin dan goma saidai zagaye kuma mu zuba daku mugani a cikin

gidan nan ta dai son don walwala amma ba din keba Asiya.

Wai kina dauka ana tsoronkine dama bafa tsoro bane kawaicine na zumunta ake maki dama don baba

amma ai ba zamunta damu daku kaf din ku kuwa ?

Antyna take fadan hakan saigashi daga cikin gida da kofan gida anyo ruuuu zuwa part din mu kuma.

Antyna ke fadin ku har kuna da bakin magana a kan hakan ashe farau nada dadi ramuwa da ciwo ko da

karfi da yaji kuka cire yayan mu gidan gwaggo mariya saboda kun shirya aurawa danta waccan mara lissafin .

Dama ta barkune kudin da zakuje gidanta tana fasin yan aiki su kawar da kaya ga barayin iyayyenta

sunzo kada kuyi mata sata.

Kota fada ai bamuji ba yaushe kuma abinda kowa ya sani gari kaf sulaiman shike son salma a yanzu ba

salma bace ke son shi.

Wai sai ga maman mu tazo ta zata mari Antyna sai ji nayi yaya na fadin kada ki duketa mama jin hakan

yasa na fito nima da sauri daga daki ina fadin.

Mama akan wa yan nan mutanen da basu da mutunci zaki mari yar ki yau ko wuka kika sokawa antyna

baki fari wajen matan nan imatukar ba kanki taga kin sokswa yuka ba.

Cin fuskan da tozarcin ya isa haka bafa tsoro ake ji ba zaman lafiyane kawai da kawaici tunda baki sani

ba kuma a zuba.

Inna tazo tana jana tana ya isa haka hausan nakima yana kokarin kwacewa sai kin hada turanci ku

barshi haka don Allah ?

Tura uwar turai ko uwarta mai karyan boko a gidansu meta tsinana an dai turata karuwanci gashi ko ta

dawo tana muna a nan yanzu za a soma bin mazan mutane.

Nasam a ranan da gwaggo Asiya tana da diya mata a gidanmu fadan zai zama na family din mu to sai ya

kasance mazane kuma wasu mashiririta haka dai shi babban ma da aka fada mai cewa yayi ina ruwana ai ita tajasu ni ba ruwana wallahi.

Tau tau abinda baba ya shigo gidan yana fada ke nan tun daga nisa tau garesu ba masu abin kunya

ban tambayeki ba ce yana dakatar da ita tun daga nisa.

Haba don Allah ace gida duk akai taron arziki sai an kare minshi da fitina don Allah Asiya banja maki

kunne ba tunda mutanen nan suka shigo garin nan.

Basu din ki ba basu aza maki nauyinsu a kanki ba kin kama bakinki ko gaisuwa kin yanke dasu yanzu

kuma meya kawo hakan ?

Sai Ka tambayesu mana yan cin amana kawai macutan bakinka da sukazowa mutane da tsiyan da suka

saba a gida.

Tir da harshen ki Asiya zakace hakan mana tunda an kitsa azo aci muna fuska ga yan kauya wai akan

me kike ta wanan kumfar baki hakane ni ban gane kan zancen ki ba don Allah .

Waifa malam Sulaiman ne yake neman salma shine ya jawo wanan fitina haka cikon mamaki baba din

yace wani sulaiman wai ?

Sulaiman dai dan gidan mariyan ka na gidan nan daka sani to sai akace me idan yace yana son salamatu

hakan haramun ne ?

Ko haka an rubuta haramunne a cikin hadisi naga hakan aiba kkmai bane ko da hundu taki zama ko

ince aka fitar da ita ai an dauki jamila an bashi ko ?

Ko kuma ba a san ita hindu ta aureshi bane da aka bashi jamila ya aura yanzune dayazo da kanshi yace

yana son salma kuma yazama laifi a wajen ku ?

Au shike nan aahe dama hadin bakine hakan gareku ita kuma mama na fadin ko maza sun kare a

duniyan nan salma ba zata taba auren sulaiman ba .

Aikin banza ke nan matukar suna son junansu ai banga wanda zai hana ba Alllah dai yai maka albarka

salisu ban taba jin dadin kalamin ka ba irin yau ?

Kayi min daidai wallahi ka kuma biyani asha baba kaiko yaya ai ana barin halas don kunya ko ba irin

wanan ba hafsatu ya juya ga gwaggo hafsaru din.

Dake magana yana kallonta yace ai naga hakan ba haramun bane ko amma ana duba ai abar wani abu

kobar maganan nan hafsatu don bamu taba haka dake ba a zahiri ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/23, 9:37 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH*