Chapter 42 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

ba mai zurfi ba."

Jin tayi shiru yasa na nufi daki ta juya wajen azizza itama ta hauta da fada tana fadin kin daiji abinda

Asiya ta soma fada a gabanki ko ?

Kina zaune take fadin gan gaji asiri am asirceshi har yanzo gidan nan saidai yagaida ita a tsakar gida ya

fita baije dakinta ba komai abinshi dai bai dawowa da hindatu ta zama matarshi .

Me take nufi da wanan zancen tun dazun nake zaune a dakin nan ina faman tunane akan magananta

sai naga ai kamar fitan da yayi da hindune ya bata mata rai.

A mama ranta ya baci mana batace ba yadda zai mayar da hindu gidanshi ba amma yana iya kawo

makwafin hindu din gidanshi ko yayan kan tayi mai nisa a yanzu amma ai yana iya auro wata ?

Wai meyasa ke baki da fahintane haka azizzah ina fada maki abinda zata juya zancen kina kawo min

wani shirme can shiru naji yaya tayi bata kula da lamarin ba ta kare fadan ta tamike ta fita cikin gida wajen gwaggo balaraba.

Lokacin antyna ta samu shigowa wajena a dakin na kwanta rub da ciki take fadin mena fada maki

salma kinga mama ma ta soma harbo jirgin ku ko ?

Barci na soma inda nake jin magananta sama sama na dago nace and so what antyna wanan abin da

gwaggo tayi ta haskamin wani hanyane da ban taba tunanen haka ba in yau yaya sulaiman ya gabatar min da kansa his highly welcome to me ba wani jayayyan da zanyi suje su mutu din .

Amma kinji mama ta soma kawo zancen yayan mu a cikin maganan tana nufin hakan ba mai yuyuwa

bane ke nan saboda yayan mu ?

So what ina ruwana da zancen yaya tunda ba ita zata zauna min dashi ba yaya ta haifeni ko mama da

baba matukar dayan su ya goya min baya zanyi saboda su gwaggo Asiya wallahi.

Me za ayi saboda gwaggo Asiya yaya farida ta budo labule tana fadan hakan sai antyna tace rashin

kunya ta dan bimu da kallo tana fadin ku bisu dai a sannu don Allah watse lafiya don Allah ?

Na fahinci mama da yaya farida suna masifan shakkun mutanen gidan mu ai yaya tana da dalili don

akwai iyayyen mijinta da nata to amma ita mama shakkan me takeyi haka a kansu ?

Azizza fito falo ga abinci nan na shigo dashi ku raba take fadi ki dibawa yaran nan don Allah suda yusuf

kar yazo bai samu abinci ba .

Dama kinbawa salma don yanzu kwaliya zanyiwa amarya ta fada tare da fita dakon dole na fito na

dibarwa yaran abincin na adana saura tunda naga tuwone a lokacin.

Mama ta dawo na dibar mata har ruwan sha nakawo mata dana wanke hannu na juya zuwa cikin daki

don inyi sallah.

******* ******* *******

Wacece akace anganka dazun da ita gaban mota abinda ta fada ke nan daya shigo daki yana cire safan

kafarshi.

"Tsit yayi kaman yana dan tunane kafin ya karasa cire safan dukka kafa biyu daga kafa,fuwanshi ya"

wurga gefe guda.

Ance an ganka da wata kamar bakuwa kunshiga mota dazun da ita cikin fushi ya juyo ya soma fadin

wanda ya fada maki bai gaya maki ko wacece ya ganni da ita ba ?

Ai tambaya nakeyi ko wacece yace nayi maki kama da mai aika alfashane ko wani abu makamancin

haka da zaki tsureni ki tambayeni.

Tambaya aiba laifi bane ni yazama laifi a wajena tunda ba wani ya aikeni ba in kuma akwai wanda ta

aikeni yazo gani ta juya a fusace ta soma magana acikin gunguni tana fadin aida ka fada min ko wacece din.

Abinci takawo mai dakin ta samu ya shiga wanka ta zauna jira har ya fito take fadin ga abincin nan dan

kallonta yayi kafin yace a koshe nake .

Amma kasan dai ke don Allah ki ban wuri ina son in huta haba wanan wani urin rayuwane wai mutum

baida tunane ko lissafi nagaji don Allah.

Shiru tayi tana binshi da kallo kafin takai dubanta kan abincin yau idan baici ba duk uban kudin da aka

kashe ya tashi a banza ke nan ?

An wahala sosai wajen karbo maganin data hada abincin nan dashi data sani kada ta bata kudinta saita

bari insun koma gida ta hada amma kuma ance kada ya wuce kwana ukku ba ai amfani dashi bane ai .

Cikin daurewa tace dashi abincin da kake sone na hada fa da kaina kuci dake da yara kuma zan huta

nace maki pleaae .

Dole ta dauka da niyar taje ta dawo saidai kafin ta dawo din yayiwa kofanshi key ya kashe wutan daki

alaman dai a gajiye din yake lokacin.

Me wanan ke nufine da ita haka wai duk wani shiri nata kamar yana zaune kovwani nashi aka shirya a

karo na biyu ba zata yarda ya bata mata shiri ba wanan karon.

A yadda ta sanshi ba zaki taba a yau tunda ba wani fitina a tsakaninsu don haka koshi zaiso ya kasance

da ita a wanan ranan balle ita zancen ta zauna ta lissafa irin kudin data turo gida akan wa yan nan aiyukan har ta manta yawansu a yanzu.

Don haka bata san lokacin data kai hannu saman kofan nasa ta fara duka ba a cikin haushi yana ji daga

ciki ya kyale bai bude ba don takaici.

Tunane ya somayi wani munafukine ya fada mata cewa ya ganshi da Salma sun fita a mota dasin shi da

gida ke nan duk abinda mutum yakeyi idon mutane yana kanshi.

Yanzu cikin zancen nan meye abin gulma don Allah a ciki yaja tsuki yana gyara kwanciya sai sake sake

zuci yakeyi a lokacinbya rasa gano mafita a kanshi.

Washe gari tunda ya fita sallah ana idarwa suka shiga wajen baba Alu tare da Ahmed ana hiran yaushe

rabo don basu samu zama da tsohon ba dama.

Sunkai kusan tara tare dashi suna tatainawa akan matsalolin rayuwa suna tashi kuma cikin gida suka

nufa wajensu gwaggo hafsatu aka gaisa su hudu dama suka taso a tare munir kaninshi cikon na biyar

"dinsu munir din din kuma yanzu yayiwa katsina tawaye buki ko wani sha,ani bai kawoshi katsina wasan dadi."

Sai an dauki lokaci mai tsawo bai tako katsina ba don yanzu ance yakai shekara ukku bai tako katsina ba

duk da mahaifansu har yanzu suna katsina zaune su.

Dama mahaifiyarsu takan je jalingon ta danyi watani a can tunda yanzu ba ita kadai bane a wajen

mijinta ya kara aure lokacin da dama ya samu garesu.

Fitowan mu ke nan zamu gidan yaya hindu don ta bugo waya muzo zamu tayata daukan kaya banso

zuwa ba amma antyna ta matsa min sai in tashi mu tafi.

Mukai kicibis dasu zasu fito daga cikon lungun baba Audu muke gaidasu ya Ahmed ke tambaya sai ina

haka yan mata da wanab kwaliyan ?

Kai tsaye antyna tace gidan yaya hindu zamu mu dawo yanzu to ina mota da zaku dashi mai Nape

zamu samu mu hau idan nunje sai mu dawo da nata kila .

"No kada ku hau Nape ya fada daga inda yake tsaye yana jiran ya Ahmed din ina sama,ila yazo ya kai ku"

"ya bada amsa har lokacin wayanshi yake dakila ya kira sama,il din da yazo ya dauko mota yakai mu unguwa idan kaje ka jirasu su dawo ya fada."

Ku koma idan yazo sai ya shiga ya kiraku ya sake nanatawa ga antyna din don ni kai na kawar garesu

tsayin da mukayi kamar yama isheni a yadda yanayina ya nuna a wajen.

"Dole muka juya muka koma ciki saidai kafin mu isa part din mu sa,ima ta taremu tana fadawa antyna"

zancen sun tafi karbo kudi anyi masu wullakanci wajen mijin Lawisa yar gidan gwaggo hafsatu.

Dan tsayawan da mukayi da itane har wanda aka turo ya kaimu yazo ya dauke mu zuwa gidan.

Mun bi kishiyoyin nata mun gaidasu kamar yadda ta umurce dayi muka dawo part dinta muka zauna ba

laifi gaskiya komai nata neat acan can da wajen sai kamshi ke tashi dama tana da tsabta .

Don yaron mama idan baiyi tsabta ba sai Allah ya tambayeshi abincin muka dauko muka fara dawowa

tare da yaranta muna tsayawa motar matar Sulaiman na tsayawa a wajen inda ta bimu da wani irin kallo na tsarguwa da ita da yan uwanta da suke tare.

Ko kallon gefensu banyi ba antynace ma ta tsaya gaidasu ni ban ko kulasu ba sai yaran da nake faman

tattarawa mu shige cikin gida take tambayan antyna ina muka fito hakane ?

"Tace daga gidan ya hindu muke muje dauko abune sai naji tana fadin kai sama,ila dama su zaka kai"

unguwa daka fita da mota dazun ?

Yace eeh bamu dai tsaya mun karasa jin me take fada ba nayi gaba ban tsaya ko kallon inda suke ba

muka shige cikin gidan.

Wai ashe hakan ya bata mata rai sosai har ta kasa kannewa saida ta kirashi a waya tana fadin wasu

yan iskane kabada mota akai unguwa.

Yace yan iskan gidan kune ko tace komai tsiyan mutum bai dawowa da hindatu gidansa dai yanzu don

na tare gaba na tare baya inma wani abu kakewa ka bari.

Yace wanan tsohon magana kika dauko ai yanzu an wuce wajen ki sake wani kuma wa yan nan dai da

kika gani sun fi karfin ki Jamila gara ki kama kanki dasu wallahi.

Aiko mu muna part din mu bamu san zance yana circulating a cikin gidanmu ba saida inna halima ta

jiyo meke faruwa tazo tana kwarmatawa inna abinda ta jiyo.

Abinci nake ba dan yaya hindu karamin naji mama tasa salati tana fasin abinda nakewa gudu ke nan

yanzu gashi ko ya fito tasawa Antyna kira tazo take fadin.

Kun fita da motan Sulaiman ne dazun tace eeh yaya Ahmed dai yace a kai mu bansan ko motarshi bane

kona yaya sulaiman .

Azizza meyasa baku gudun tada zaune tsayene wai tace me mukayi mama kafin tayi magana inna

halima tace ga matarshi can tana fisge fisge da yan uwanshi wai ana son a shigewa mijinta motar dako ita bata shiga yabada akaiku unguwa dashiq ?

Mun fita aji ke nan da class ko tunda mun ya bamu min fita da ita aiba laifin ku ake gani ba laifin

mamanku da hindu ake gani kuma yanzu ?

Zanwa sulaiman magana don Allah ya daina kula yaran nan bani son abin magana halima yadda

mukazo mu koma lafiya shi nake fata.

Saboda me yaya ai insun isa su zo gabanku mana su fadi zasu raba zumuncine kome ance ai ya bata

amsa mai zafi shine take wanan haukan a cikin mutane.

Yaya farida da bata san hawa ba bata san sauka ba zuwanta ke nan gidan aka hauta da habaici da har

tasha jinin jikinta ta taso zuwa part din mu taji kome ya faru ?

Nan ta samu yaya hindu ma ta iso bayan sun gaisa take fadin anyi wani abune yau a gidan nam naga

dakin gwaggo hafsatu da yan uwanta ana ta habaice habaice mana ?

Gasu nan suke son su jawo min magana salmace dai da sulaiman suke dasawa tunda ta dawo din nan

tace kwarai kuwa tun a gidana abuja kuwa .

To kingani dama haka nake gudu kada a mayar da zancen wani abin tsegumi kuma nayi mata iyaka

dashi jiya fa ashe akwai magana kuma tafe yau kan haka.

Saboda su zataki kulashi meye a ciki idan ta kulashi ta dai rabu dashi don Allah ina ruwanshi ma da ita

inba wani abu yake so ba kuma yayan mu ke fadan hakan a lokacin.

Meko yake so shike nan za a hana yayi zumunci da mune aini ban sani ba wallahi dana bawa mace

amsa don iskancin nan ba zan dauka ba yanzu ?

Zan mai magana da kaina ya daina tunda abin ya zama haka ban iya jidalin nan din Allah mama ta sake

fadan hakan rai bace.

Haba mama kice dashi me kuma kawai ki kyalesu din Allah duk abinda zasu fada suje su fada anyi din

bashike nan ba mutane dai basu son zaman lafiya ko yaushe da irun fitinan da zasu kawo muna.

Ki barta tayi mashi magana ai mai iyaka dasu tunda matarshi bata son hurda damu don Allah yaya ta

sake fada a cikin fushi ba za a bari ba din barin kira yaya Ahmed in fada mai tana kokarin daga wayan ta dake hannunta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/22, 9:24 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

"Waya ya kara a kunnensa sai Ummmh ko a,a,a,aa ke fita daga bakinshi yace ki kashe wayan zanzo in"

bincika meke faruwa yanzu.

Yaya Ahmed ne da yake sauraren matarshi dake mai bayanin abindake faruwa a cikin gidan da irin

matakin da haka zaisa ta dauka din.

Iska ya furzo daga bakinsa yana fadin kaji ko wai Jamilace ke cin mutunci a cikon gida don taga su

Azizza a motar ka ?

Barta tayi idan ta isa tazo ta sameni mana wanan wasan hauka takeyi sai ranan da taga motar gaba

daya a hannunsu kila zata shide ranan ke nan ?

"Wai babba in tambaye ka mana don Allah meye tsakanin ka da Salma nifa naga kamar ,,,,,,,,"

Umm humm fadi mana kaga kamar me ban isa bane ko ita bata isa bane zumuncin da aka yanke da

karfi da yaji nake son na sake kullawa a yanzu.

Kabar maganan nan don Allah yaya Ahmed ya fada kamar a razane yana mai kallon ido da ido shi kuma

yace dashi iam telling you insha Allahu niyata ke nan a yanzu.

Mutumina ka debo mai zafi fa anya abune kuwa da zai yuyu karka manta da salma ba mutuwa tayi ba

haka kuma iyayyen mu da sukaki wancan kaeon suna raye har yanzufa ?

Amma kasan hjy Inna bata taba cewa kada in auri salma ko da cewa mahaifiyarsu inna mairo ita suke

kira da hjy inna a family din.

Kai Ahmed ya girgiza don ya gane me yake nufi a nan idan har hjy inna bata hanashi baiga dalilin da zai

tsaya jin zancen wasu iyayyensu mata ba kuma.

Yaso yayi magana amma kuma ba bakin hakan a yanzu gareshi lokaci yakai da idan sulaiman yace abu

kaf family ba mai iya mussu dashi wasan dadi haka .

Saidai ya daure yace gaskiya sulaiman ina ganin wanan abin zai kawo bacin rayuka a bangare da dama

don haka don Allah ka hakkura ka nemo wata yarinyar ka aura koni na baka support din aure ayanzu gaskiya.

Ba daga ni bane ai daga garetane ya nuna zuciyarshi kai tsaya ga dan uwan nasa shi bai fahinci me

yake nufi ba a lokacin yasa yace ita salma ?

Ita dai wanan ya dan bugi kirjinsa da hannu yace zuciyata taki ta barni in hakkura da salma a yanzu idan

ban ganta ba ko naji muryanta har wani hali na soma shiga Ahmed kasan dai ban boye maka komai a rayuwata.

Salma kuma ina kokarin kafa gwaunatina ne a gareta yanzu bana son hadin nan irin na gida

soyayyanta nake nema d9n mu fuskanci irin zaman da zamuyi na rayuwa.

"Dariya abin yaba Ahmed inda yake fadin kayi nisa mutumina Allah ya bada sa,a idan alherine ya amsa"

da insha Allahu hakan alherine garemu baki daya.

Gaskiya akwai cakwakiya a cikin zancen nan don nasan rayuwaka da dama zasu baci akan maganan

nan idan sun baci ai zasu gyaru gaba tunda ubangiji bai hana ba Ahmed.

"Gaskiya mutumina kayi nisa da yawa a zancen nan sai dai addu,a a yanzu insha Allahu ina bayanka don"

ko nace bani bayanka ma karyane don ba za a yarda ba tare muka hada hakan ba dakai.

Koka barni ma ban damu ba Ahmed ni kadai ina iya yakina da kaina dana soma cin gari aiba da

taimakonku na fara ba ko ?

Meyayi zafi ni a fada min bangaren da zanji dashi in soma yakina tun daga yau aiba dan wariyan launi

nake ba balle a wareni daga ciki ?

Dariya abinda Ahmed ya fada ya bashi yace duk wanda yafi sauki ka dauka ka barni da manyan na

shirya tsab tunkan in fito matsalata guda shine ita salma a yanzu.

Salma ba matsala bane matukar farida ta fahince mu abin zai kara zuwa muna da sauki sosai yace da

alaman hakan don kaga a yanzu haka mutum na farko dake ban surpport itace Azizza duk da ban fadi nufina amma naga kamar ta halboni ko ?

Zata iya kasan nazarin dan adam take karatu a kai don haka kota gano ba a mamakin hakan a yanzu

abune da zata gane da sauri.

No wander kuma nasan tana kokarinta a kai don na fahinci salma din ta dan fara saukowa a yadda take

a da sanadin Azizza din .

******* ******* *******

Antynace ta zabo min kayan da zan saka da yamma ta tsaya tayi min dan light makeup a fuskata don

nikan alhamdullahi gaakiya ba wai yabon kai ba komai masha Allah ubangiji yayi halittansa a wajen.

Don kusan dukka danki mu babu munanne a cikin mu duk da gwaggo Asiya ta illanta yaya Fadila hakan

baisa ta nakshe ba don yanzu dan wajen maman hussai da matarshi ta rasu ya auri fadila din suna kuma zaune lafiya kalau a can wajen mama hussai din a nan take aiki taje hutune can warri din yanzu don haihuwa da tayi.

Nayi mamakin ganin canjin da antyna tashigo dashi inda ta cusa min a jakata tana fadin ga canjin

manni nan nayo muna salma ga naki zamu likawa amarene a can nace ba matsala amma nawane in bata abinta take fadin ba matsala bari mu dawo dai yan dari bibiyune sabbi fil dasu a mike cikin leda .

Dagani har Antyna shirinmu ya girgiza gidan don kuwa tun kan mu fita labari ya kai inda ya dace ya kai

din a gidan har