Chapter 44 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

*BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Kamar yadda baba tsohon nan dai ya saba lafa zance a gidan hakama wanan zancen a ranan ya lafashi

inda yayi tsaye ya kore kowa daga part din mu yan zuwa gulma da zugi.

Inda ya koma ya tsawata da cewa ya kashe wanan magana kada yaji ko ya gani wani daga nan ya tayar

da wanan zance don zai saba ran ko waye yayi hakan kuwa.

Shine mafarin da zancen ya lafa a lokacin inda yasa kowa ya watse tun kan hakan mun riga da mun

koma dakin mu sai yaya farida da zata tafine har take cewa mu bita zuwa gidanta mu kwana mana ?

Kai tsaye na nuna ba zanje ba ina nan gida zan kwana dole sai rakata mukayi ta tafi muka dawo gida

inda muka samu mama na waya wanan yasa bamu zauna ba a lokacin.

Nidai nayi shirin kwanciya na kwanta har barci ya soma daukata naji antyna ta magana a kaina tace

yau karo na farko da naga munzo katsina mama ta karbi girkinta a nan tana can gun baba na rufe kofan mu.

Banga abin wanan maganan ba mata da miji ai sai Allah dama wanan ba zancen mu bane ai take

cigaba da fadin kila yau gwaggo hauka zatayi kafin safe Allah kuwa salma.

Idan munzo tasha bugun gaba tana cewa sai ita guda ba bari ba ta hana tsohuwa walwala da diyanta ai

mutum da malam saidai satan kwana.

Ina jin mama sheri tasa mama zuwa din don tun jiya nake jin tana bugo mata waya baba yace sai mama

tayi girki to ai batayi din ba na bata amsa.

"A,a inna ta karbi kayan girkin ai kafin mu fita ta girka abinci yau shiyasa bataje kamu ba ai kinsan inna"

yar no case ne ita ko tana da case ma dai ta boye abinta ba za a da ita ba ai ace tayi ko ?

Wai kinsan nashiga damuwa a yadda naga dakin inna yau kuwa daki haka kamar zaure antyna wai

dakin mace shi baba wai wani irin mutum ne don Allah dai ?

Kina ganin matan nan kinsan depression zai iya kamata anty time a rayuwanta tace ai yawanci

abindake kashe muna uwaye ke nan a arewa sunnu da bakin cikin mazajesu ke saukar masu.

Ke kina ganin idan su uncle basuyi dabaran cire mama a gidan nan ba da yanzu ba a manta da mama ba

ai sai tarihi tunda lokacin kiris ya rage ta fadi ciwo akace.

Ni ina da wayau ina tuna abubuwan da akayi lokacin wallahi shiyasa kikaga baba bai raina anty kibar

fadin hakana salma shima fa bayin kansa bane juye mashi lissafi akayi ya manta da kowa sai ita sai diyanta Allah kuma bai yarda ba .

Muguwace ta gaske a yadda ake fadi akan kishi suna iya komai a rayuwansu sunansu ya riga ya daga

"ga hakan yan bala,in shige shigen bokaye da malamaine su ai inkin duba kaf dinsu sai tsiraru basu aje"

"komai ba a duniya haka kuma suke tunkahon su ba,a shige masu gaba nace karya dai ai Allah yafisu ko mama basu debi komai gareta ba ai."

Saidai baba on abinsu zai tsaya akan wanda ya kwasosu aida sauki suje suyi ta kwasan zunubinsu can

yau ba gashi kina fadin mama tana gurin baba ba ?

To aikinta baici ba ke nan tunda har akwai ranan da asiri zai karye akai lokacin da basu iya komai kan

mutum ?

Kedai bari ni wanan haukan nasu ai yasa na fara tsoron halisu wallahi ki bar mata mijinta taje tayi ta

kaya da abinta tun yanzu an fara haka inaga sunga an shiga ?

Su ba shigan sukayi ba ai dama sunyi wanan ne don subada tsoro niko wallahi kar nake kallonsu ban

tsoron kowa a cikinsu kafin mu bar garin nan sai na kumsawa matar nan bakin ciki a gidan nan yar iska kawai.

Allah dai ya kai mu gobe lafiya kigani na fada mun dauki lokaci muna hira kafin muka kwanta barci a

makare muka tashi ranan ko ince ni don dai nakai wani lokaci ina barci.

Saida nayi wanka na shirya nafito daga uwar daka mama na samu a falo tana karyawa da koko da kosai

a gabanta mama an tashi lafiya na fada ina kaiwa gurfane yadda mama shari ta koya muna gaisuwa garesu ga baki dayansu sai dole munkai gwiwowin mu kasa mu gaidasu.

Gaisuwan da nayiwa mama din ke nan ta dago tana fadin Auta kin tashi yanzu nake zancen ki a rai in

tayar dake tin masan nan baiyi sanyi ba daga gidan farida aka kawoshi suyane maikyau akai mata tankar masan bauchi don laushi.

Kokon nan nake so yasa ban tsaya cin masan ba don abu mai ruwa kawai nake iya hadewa yanzu

saboda me mama haka na nufin kinyi loosing dandanon bakinki ke nan fa ?

Ta nisa tace ba dole ba auta abu yaki ci yaki karewa matar nan na rasa me take bukata dani a rayuwa

tun ranan da mukazo garin nan nake hakkuri da lamarin Asiya a gidan nan .

Nayi dana sanin zuwa dake ai da kikace in barki dama na barki din a can kaduna da duk wanan fitinan

"ba,ayishi ba kila ?"

Kona zo ko banzo ba indai wanan matarne sai kunyi haka da ita mama kawai maganin irinsu shine a fita

zancen banza kadama mutum ya nuna yasan dasu a waje.

Nishin ciki mama tayi tana fadin wa Asiya asiya ai kadan ke nan haka suke kaf dinsu wallahi baki ganin

yadda hjy laraba ke fama da hafsatu.

Don Allah bar zancenta mama kisha kokonki kada yayi sanyi ki kasa sha ita wanan kamar anyi mata

huduba da karyane ai wajen sababi.

Kedai don Allah rabu masu da dansu suje suyi ta kaya ki samu mijinki waje yafi maki sauki da hakan ina

amfanin badi ba rai haka za aita jidalin nan fa.

"Mama addu,a zaki min Allah yayi min zabi na alheri na fada ina jawo kulan masan gabana wai hira"

akeyi haka da uwa da Auta lalai wani abu sai Auta kuwa mama ?

Fito dai kuci masa ku ajewa Yusuf da yayan ku sauran nasan tana nan tafe yusuf dai mama ita ba gidan

mijinta zata fito ba antyna ta fada.

Kamar mama ba zata bata amsa ba sai can take fadin ai kinsam halinta ko ?

Yanzu datazone zata soma budan kwanonin nan tana tambaya shine bata dafo muna ba ita daga

gidanta son Allah kuci in baku ragewa ina shike nan dai mama ta fada.

Mama yau zan sayawa inna halima katifan kwanciya don jiya dana shiga dakinta kukane kawai banyi ba

wallahi yadda naga dakin nata.

Allah sarki auta dako kin kyauta wallahi ai bana hana alheri ni idan ina dashi danayi mata don halima

mutum ce sosai insha Allah yanzu zan fita in samo mata da yan wasu kayayaki kafin gobe buki a taru daki yana mata kamar zaure haka babu komai a ciki fa mama sai tarkace haba don Allah dai ?

Murmushin manya da mama ta sabayi ko wanan karon shine a fuskanta ta sake tana gyara zama tace

Allah yaba da ikon yi na amsa da amin .

Uwale fa mama na tambaya wata kawar macece dake unguwan mu suna kawance sosai da mama

muna yara mukan kwasa nida yusuf muje gidanta muna kanana ta bamu kankara shine ke kaimu gidanta lokacin kusan yaro da kankara.

Uwale na nan kuwa Auta duk nazo nakanje gidanta ko tazo nan ba mamaki ai gobe wajen bukin nan

kiga ta shigo .

Dan masan da nacine kwara daya na mike zuwa wanke hannu a waje ina sauke kafata daga kofan

mama mukai arba da gwaggo Asiya na kawar da kaina na wanke hannuna na juyo zuwa daki.

A dan wajen inna halima ya shigo kawowa mama leda da suka raba abinda aka basu na bukin jiya din

mama tace ya kaiwa innanshi ta kara da nata nan nakebawa yaron sako yace ana magana da inna din.

Yaron da yaje yake fadin baturiyan nan tace ana magana dake inna ya fada mata sakon mama tace ayi

haka yaya ?

Tamike tazo dakin tana fadin ance baturiya na magana dani a dakin nan na amsa da eeh inna ki shirya

zamu fita unguwane dake don Allah.

Tace ni dinga cabdi jam ni dinga halima yan gayu irin ku na fita da irin mune a gari ke dai shirya kuje din

"ance in kaji kira sa,ane amma banda shirin yan sanda."

"A motan baba karami muka fita wanan karon munyi sa,a munfito shima ya fito ke nan zai fita ya tsaya"

yana tambayan inda zamu muka bashi amsa da kasuwa.

Ina jin wanan ne farkon zuwana kasuwam katsina da wayauna shiya tsaya jiran mu wai mu fito muka

fita antyna na dariya tace wallahi Allah salma kada kisa gida ya fashe da boom shima baba karami kamar ya kyasane fa yana ciki ?

Wane yaro ga manya a waje da taimakonshi muka samu aka dauki mota aka kwaso tarkacen inna don

nakaso mata kudi a ranan har da dan gadonta da wardrobe mota tazo ta aje don sunsan gidan .

Tamu motar na tsayawa matarshi tazo da dariya tana fadin to nima yau hauka zan maku tunda kun fita

min da miji akai wasa da dariya muka shige cikin gida.

Innace ta tsaya aka kwashe mata kaya zuwa cikin gida kaf sai budan baki takeyi tana arziki yau a gareni

ya sauka gidan nan .

Ni nasheda zuwan auta kasan waje a gidan nan taron mata akayo wajen mu ana kallon abin arzikon da

inna ta samu idan an tambaya waya saya mata sai ace auta nan kuma labari ya sake juyawa kaina aka bar zancen maida maganan fadan jiya aka koma fadin ai ba karamin kudi na dawo dashi kasan ba.

Likitace fa a yanzu mai cikkken iko zata iya fida da komai ga mutum idan an kaita asibiti babbace sosai

ko a cikin likitoci don ta samu training a kasan waje inda ake da kayan aiki na kwarai da ake bukata.

Ga wanda yaje gunta ba ai saidai ta gwada fyede kadangaru amma ba mutum ba wanan yar karamar

yarinyarce zata wani fyede mutum ku dai ance maku gwanace kun yarda kawai.

Gwaggo hafsatu data kawo masu maggin da za a zuba a miya take wanan magana ga taron mata dake

hira a gindin iccen tsakar gidan baba Audu din.

Saida ta wuce gwaggo hari ke fadin na rasa wanan irin adawan da ake nunawa yaran nan a gidan nan

inma karyane danta Ahmed ke nan yayi wanan karyan donshi yayi muna bayani ranan.

A haka kuma aka samu wace ta zagaya a wajen take fadawa gwaggo din basu iya bada bashin zance

idan ya shafesu haka suke kamar zawo yasa ta kasa taushe zancen.

Cikin mitane taso yiwa gwaggo hari din cin mutunci ita kuma ta zage take mayar mata da martani sai

hakan kuma ya hada wani hasumi a gidan.

Wajen wanan rikicinne muke ji ai bayan fitan mu anyi zama na manyan gidan tare dasu baba da baba

tsoho an kira sulaiman akan zancen mu.

Gaakiya ba zai yuyu ba haka kawai don rainin hankali ya rasa wace zaice yana so sai salma don ya

rainawa mutane wayau ?

Yayan muce take fada lokacin da yaya farida take fadin hakan a cikin fushi kowa dakin ya bita da kallo

inda take fadin aina fadawa salma ta rabu dashi tun wuri kada hakan ya kawo matsala ?

Matsala dawa yayan mu dawa za a samu matsala indai da wa yancan ne wallahi tsab salma zata

gyarawa jamila zama matar da take kamar doluwa da ita.

Na daice kada a soma hakan idan ba matsala ake son samu ba kuma ta rasa manemane da zai wani zo

ya lake mata yana neman bata mata lokaci ga banza.

Ko kudi zaizo ya nunawa mutane shiga mai kudi dole a soshi ko to ba zatayi ba wallahi da sauri yaya

farida tace da ita kibar sa kalman wallahi yayan mu.

"Idan Allah yayi matarshice ita yaya zakiyi kinga rantsuwa ya hau kanki ke nan kuma na dai ce ba,ayi"

wallahi haka kawai son rainin wayau da wullakanci zai wani zo ya tayarwa mutane da zaune tsaye.

"Toni bangane ba da kike fasin ba,ayi kada Allah yasa ki gane farida ta yaya zan auri mutum yanzu kuma"

daga baya yazo yace wai kanwata uwa daya uba daya ita yake so ?

To ai ance Allah bai haramta hakan ba yaya kinga idan tana son shi ai shike nan don shima yace a bari

ya nemi so daga gareta yafi sauki kada a maimaita abin daya faru da farko .

Ke salma ko baki son shine yaya farida ta fada tana kallona duk gaba dayansu suka watso min ido har

mama don wanan tambayan girshi da aka jefo min din a lokaci guda.

Saida na dan gyara zama nace idan halinsa yayi min me zaisa nace banson shi kawai ina da tsarin mijin

da nake so nima idan halinsa haka yake fine me zai hana inyi ko don wanan abun dake faruwa a yanzu.

Ina fadan hakan na koma na fuske kamar banice nayi maganan ba a lokacin dan falon na mama yayi

tsit lokaci guda sai mama data nisa tana fadin.

Fatana dai shine idan hakan alherine gareta damu Allah ya tabbatar da abin idan kuma babu alheri a

cikinsa Allaj yayi gagawan kawar da abin kowama ya huta.

Har lokacin dakin shiru yayi ba mai wani zance a dakin kuma sai mikewa da yayan mu tayi tana kiran

danta daga waje don yaran sun fita suna wasa a tsakar gidanmu.

Sai gata dasu ta riko hannunsu tana hada kayanta yaya farida kuma tace ina zaku kuma yanzu tace gida

zan koma .

Yanzu ta sake tambayanta bata iya bata amsa ba a lokacin sai kokarin hada kayan da takeyi cikin

dakewa ko abinci yaran nan ba suci bafa yayan mu ?

Idan munje gida zasuci ai ta fada tana daukan jakkanta ta juyo tana fadin mama mu zamu wuce mama

din ta dago tace Allah ya tsare hanya ke nan.

Amma banga abin bacin rai a cikin zancen nan ba yaya farida ta mike tana fadan haka zata bita ke

koma zauna ki barta ta tafi din tunda taji abinda na fada ai.

"Ko wa tafi zuciya ana magana nan iya addu,ane kansa yanzu ko so take a fadi abinda ba daidai ba a"

"sabawa shari,a kuma ?"

Nidai ba zan taba son autana da wanan mutane ba tunda nasan abinda ke nan amma ana magana ta

tashi tayi zuciya zata tafi.

Ta dago idanunta dake fidda kwallah ta dan dubesu suma binta sukayi da kallo na tuhuma a lokaci

guda tasa kai ta fice bata kara magana ba.

To aini banga abin jidali ba a cikin zancen nan yanzu tunda ba a ce shi salma zata aura ba antyna ke

fadan hakan mama ta harareta tayi shiru tana dariya tare da min signal da idanu.

Antyna irin yan matan kaduna din nanne da kallo daya zakai masu kasan idonsu a bude yake da

wayewa tsari na kwaliya ko wani jiji da kai duk zaka samu a wajenta shiya a yanzuma take daukata tsara guda da ita bata dauka akwai tazara a tsakanin mu sosai.

Tau itama yaya banda son kai ai wanan ba abin tashin hankali bane ko abin nan dai Allah bai hana

hakan ba mama for god sake meye akai mata ba daidai ba a nan don Allah dai ?

Tana ganin kamar an hade mata kaine ko wani abu muna goyon bayan salma a yanzu dole mu goya

baya inma hakane kowa fa nason nasa ya huta a yanzu.

Ba baki nayiwa salma ba duk ta kure yaya sulauman a yanzu kamar yadda ita yayan mu ta kure ba lalai

bane a fadin kasan nan ta samu matashi da hutu kamarshi gaskiya ai kowa nason hutu fissabillah ?

Fuska na yatsune gani da murguda baki tankar maganganun nata basu shigeni ba a lokacin nan naji

antyna na fadin ita daice ta tsaya wani jan aji a yanzu garesa danice ai tuni zan bada kai bori ya hau nikam .

"A,a meye laifinta Azizzah ai gara taja aji din don kar ace don kudinsa zata aureshi abune da ko wani bai"

fada ba wani zai fada to me zaisa ba zata ja aji ba kuwa hakan yayi daidai ai .

Nikan Allah ya gani indon ta tawace bani son salma da sulaiman don gudun irin hakan yanzu gashi ita

taki fahintan abinda ku kuke nufi a zancen ai ?

"Wallahi sam bana sha,awan zancen nan kwata kwata a raina saboda tarin matsalolin da hakan zai sake"

jawowa da mutanen nan.

Mama ai tun tan gini tun ran zane mutanen nan ba zasu taba son mu bafa tunda sun san mun fisu da

komai a duniyan nan wanan kuma sun san wani sabon hadine ubangiji ke shirin nuna masu a yanzu.

Ke rufa min baki hakana don Allah ban zaci baki da wayo ba farida sai yau wanan abinda yayanku tayi

yanzu yana nufin matsalan da za a samu tun a dakin nan ne matsala zai fito.

Kin san dai ba a sakewa tuwo suna don sai an lissafa da hindu farko a cikin mantashi kana a kawo kan

ita auta in anyi hakan to meye riban hakan bayan tana raye ba mutuwa tayi ba balle ace an musaya mashine da ita ?

"Mama ai yaya itace ta kishi tun farko nifa bawai ina magana bane don ina son salma ta aureshi a,a"

dacewan yin hakan dai nake duba.

Ko a gidan nan ba iya dakin nan mu kadai ba iyayyen mu maza da yan uwan mu duk zasuso ace yau yar

gidan nan yaya sulaiman yake aure ba yar wani gida ba.

Ki duba yadda ta kwaso muna yan gidansu nan dangin mahauta sukaso su kawo muna iskanci badon

Allah yasa su manira na wajen ba jiya bansan ya za ayi ba ai sai yaran suka nuna masu sun fisu iya iskanci ai.

Ihumm Farida icce tun yana karami ake lankwasashi muddin ya bushr wallahi ba zai lamkwasu ba

saidai ya karye don kuwa anyi nisan da ba a taba shiryawa a tsakani gidan nan .

A take idanunta sukayi ja ga kalaman da zata fada a karshe da alaman mai zafice tace ba kowa ya kara

ja min bakin jini da bacin suna a cikin gidan nan ba sai hindu.

Ido ta runtse yayi da dakin yayi shiru lokaci guda karo na farko ke nan data taba furta zancen mutuwan

auren hindu din da sulaiman tun faruwan abin.

Nice na fara mikewa na bar falon zuwa daki can naji antyna ta fita don inna dake kiranta kafin yayan

mu tabi bayanta akabar mama din da yaran yaya farida a zaune falon.

Duk irin budurin da akeyi a gidan dawakai bakinta bai furta komai ba a zancen sai harkokinta takeyi a

"cikin jama,a."

Tunda buki na dangine ta ko ina bukin ya shafi kowansu kuma haka ta hana gaba daya yaranta