Chapter 46 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

da wasu yan

uwanta da suka cikia masu gidan yanzu tun zuwansu garin wasuma a nan suke kwana sai ciye ciye sukeyi sai hira.

Jin motsin budan kofanshi yasa ta mike da sauri ta sameshi tana saye da riga da siket na lace dinkin

yayi matukar karban jikinta daidai gwargwado don itama tana da nata haduwan saidai ba irun can din nan ba.

Ta karaso har gabansa tana mai zuba mashi ido don ta karanci yanayinsa don tun faruwancin

mutuncin da sukayi a wajen kamu yazo ya tsawa yake daure mata fuska.

Shima dubanta yayi yana jiran yaji me zatace dashi a lokacin saidai kamar zatayi magana duban

hannunsa tayi taga wayoyinsa har da key din mota tasan ba iya gidan dawakai zai tsaya ba ke nan a lokacin.

Don haka ta dan tabe baki sai kawai ta juya ta koma falon wajen yan uwan nata ta sake zama sai

yaransane suka taso suna mashi magana yayin da yan uwan nata wasu suke gaidashi sama sama shima irin hakan ya amsa masu yasa kai ya nufi dan dogon coridor dake tsakaninsu da hjy inna.

Bin bayasa ta sakeyi tana jan tsuki a cikin takaici to tambayansa zancen naman da yace za a kawo saidai

tana gudun magana tajawa kanta abinda zai iya daga mata hankali kuma.

Balle gashi tasan ganin yan uwan nata haka da yayi a gidan zai iya kawo masu matsala a lokacin ya

mike tana jin wayansa na kara a lokacin ya dauka Ahmed ne ke masa magana yana zancen da take sonyi takasa dashi alokacin.

Har yakai tsakiyan falo bai fasa bayani ba inda yake fasin a kawowa hjy inna nasu nan direct akai

dayawa mama can gida daya a kawowa jamila a part din mu daya kuma ka aikawa wasu Salma a part dinsu.

Kai kai kai mutumina baka baro zancen nan da zafi ba kuwa ya Ahmed ya fada yana dariya don jin

abinda dan uwan nasa ya fada.

Cikin muryansa na kasaita yace meye na boyo a yanzu tunda kowa yasan manufata da ita kayi yadda

nace dakai kawai ayi hakan har drinks indan an kawo ka raba hakana a kai masu nasu na cikin gida a aje wajen tsoho a rabawa kowa sai ka dankawa mama laraba a hannunta yana fadan haka ya kashe wayanshi.

Shikan ya Ahmed yana jin ya kashe wayan nasa ajiyan zuciya ya sauke ya fara neman wayan matarshi

farida.

Tana dauka ya soma fadin kefa Ahmed zance yake so a tafiyan nan ya soma mata bayanin yadda sukayi

da suleiman din.

Yake kuma tambayanta yaya za ayi ke nan farida kina ganin hakan ba zai kara kawo sabon matsala ba

kuma a yau din ?

Yaya kawai kayi yadda yace din matsalan me tunda ba za a zo ace a fito dashi ba komai fitinan mutum

yace to shike nan ni wanan abin ya soma isata wallahi farida.

Kodata kashe wayan bataiwa kowa bayanin komai ba illa iyaka tashiga kimtsa dakin wanda yasa muka

tashi muka tayata gyara waje nida antyna muna gamawa kuma nakoma daki don yayan mu da tashigo lokacin muna gaida ita tankar bata jimu ba nida antyna a lokacin.

Aiko mintuna ashirin basu cika ba drinks aka soma shigowa dashi daga inda mama take take tambaya

daga ina kuma wanan din ko yaya sheri ta isone ?

Daga uban gaiya yace harda dakinki a kawo maki yaya sulaiman ya sayo na buki shine yace kema a

"kawo maki kiba jama,anki nan."

Ke banson shakitanci don Allah ina wanan abin ya fito haka yaran kuma sai ajewa suke faman yi a kofan

mama din.

Gwaggo Asiya daga waje tana tambaya kai wayace ku shigo dashi can sukace yaya Ahmed sai tayi shiru

ta duka tacigaba da aikin da takeyi tana jin zuciyanta na kokarin rufe mata a lokaci guda hakan yasa ta mike daga don kada ta fadi.

Ta koma daki ta zauna kasan zuciyarta tana jin wani ciwo dake taso mata a lokacin yana kokarin kwance

masu a yanzu abubuwa nason dawowa sabo a garesu baki daya.

Wanan matar Dije takai maciya amana mara tsoron Allah don bata da kunya ita da yayanta sunzo gari

suna son su tayar masu ciwo sabo a yanzu.

Bata tashi tsorota ba saida ta hango gicin bankararen naman rago da ake shigowa dashi gidan an nufi

sashen mama Dije dashi wanan kan tsaye ta mike tana kallon ikon Allah lokaci guda.

Wanan tasan ba aikin Ahmed bane saidai Sulaiman me yake nufi da hakan da zai kawo wanan kayan a

tsakiyan buki haka kowa nagani wanan ai ya zama cin fuska a bangaresu koma meye ai zai bari har abin ya tabbata ya soma hakan kiri kiri.

Idanunta suka firfito ta faru ta kare wani sabon masifa kuma ya samesu a yanzu da wanan sabon

zancen daya dauko asali kamar yadda tsoho ya fada.

ZAINAB IDRIS MAKAWA