Chapter 30 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

saidai ki zauna katsina.

Murmushi farida tayi tana fadin humm gwaggo har yanzu ai halin yana nan saima abinda ya karu mata

ai.

Ta nufi kayanta da zuman dauko tawul a lokacin faridan ke miko mata sabon tawul din dake nade a leda

tana fadin karbi wanan kinsan ku turaine yanzu komai sai a hankali murmushi kawai tayi ta karba daga hannunta.

Don zuwa lokacin takai gejen magana ta soma gajiya da hayaniya ta shige bayin ba tare data tsaya bada

amsa ba itama din tasan hakan.

Duk cikinsu itace ta kwaso uwarsu sosai da rashin son magana saidai nata din kuma yaso yafi na mama

din a lokacin kafinta fito ta samu an kara gyara dakin an fesa kamshi hakan yayi mata dadi sosai yasa ta dan kimtsa ta saka wani wando da riga ta nemi waje ta kwanta don ta huta saboda gajiya.

Farida farin ciki da ganin yar uwarta ya cikata don haka ta kasa hakkuri ta nemi layin mama ta danna

mata kira tana sheda mata dawowan yarta kasan.

Itama uwar mamaki tayi sosai tana fadin salma fa kikace tazo wallahi yanzu haka tana dakina kwance

tana barcin gajiya.

Ikon Allah mama ta fada tana mamaki tace salma wace irin miskilan yarinyace wai ki shigo kasa haka

babu sanarwa da zakizo a sani a gida ?

Aikin santa mama yanzu haka idan taji na sanar daku zuwanta sai mun kwasa don haka don Allah kada

ki nuna na fada maki zuwanta din mama ba zance mata komai ba ai.

Barci sosai nayi a ranan don gajiya don ma na huta dubai na kwana biyu wajen jiran jirgina da wahalan

yafi min yawa a lokacin.

"Kodana tashi anyi sallah la,asar a lokacin hakan yamin sauki don na iso ina fashin sallah a lokacin duk"

zamana na turai baisa na shagala na daina addinina ba na islama dana taso a cikinsa haka kuma tarbiyana na matsayina diyan hausawa yana nan tare dani ban yarda na biyewa duniya ba inshagala.

Balle idan na tuna yadda tafiyana ya kasance da amanan kaina da mama taban nakanji ko hakan kamar

banwa mama adalci ba idan nayi wani abin.

Don da daman karatun ya samu agareni uncle hassan yazo da zancen iyayyena maza suka tuma sukace

badasu ba wanan akidar nasarane ai akeson a kawo masu.

Da yake Allah ya nufa sai naje da taimakon baba Audu da yaya Ahmed na samu na bar kasan nida dan

wajen uncle hassan din aka turamu karatu a waje.

Ni a lokacin jumping ma mama Shari tayi min don dai kada daman ya wucemu a lokacin inda na zana

waec dina a wanan shekaran da nake aji hudu a FGC na samu na ketara zuwa waje samo ilimi don na taso da irin kokarin yan dakin mu nikecin na daya a ajin mu lokacin.

Abune na yayan manya aka sakani a cikin harkan da yake da rabona yau gashi na samu na kammala

na dawo gida Nageria cikin yan uwana duk da karancin shekaruna ban yarda na shagala da rudin duniya ba a can.

Saidai dan uwan karatuna da muka tafi tare shi nasa karatun ya zamo shiririta a yanzu yama daina

karatun yana wasu harkikonsa a can din yanzu.

Kawune kadai yake zuwa dubamu duk karshen shekara da yake ba waje daya muke karatun ba shine

yasa bai gane matsalan da danshi yake ciki ni a England nake shi kuma yana US a zaune.

Banda surutu balle aji wanan kazamin zancen a bakina son ko a gabana yake harkokinsa sai naga daman

magana zanyi balle ba a waje daya muke zaune ba.

"Zance kaf family din mahaifin,mu dana mama nafi kowa sa,an karatu dana samu nafita kuma na kare a"

karancin shekaru irin nawa a yanzu.

"Banda rigima gaskiya ba wai yabon kai ba don yana da wuya ka ganni a cikin wani sha,ani haka na taro"

don sai ince makaratu idan kin tuna tun farko a haka na taso lake a daki tare da mama ko yaushe.

Koda yaya Farida ta shigo ta duba kona tashi ta samu na falka na kewaya na fito ina zaune bakin gado

kamar me tunane kirarin da suke min tayi min a lokacin.

Tana fadin salman mutanen turai hakan yasa na dan sake murmushi tare da fadin wanan salman kan ba

yar turai bace.

Shiyasa nagudu muna gama karatun mu kafin su rikeni a can balle aishine fa nakance kan alhuda

hudace ke sarkin karatu.

Haka dai tsoho yace min da zan wuce bana manta abubuwan da suka faru a kullum ina ganin kamar

yanzune suke faruwa a idona .

Yaya Ahmed da yaya sulaiman sune farko silan bokona yaya donshine nake son ya zamo mutum na

"farko da zai fara ganin takarduna a duniyan nan don kowa bayansa ya biyo don shine ya sakani school nida Sa,id."

Sai naji tace bawan Allah yana nan ko zuwan nan da mukayi yazo ya rakube a jikin mota nasan kudi

yake so yana kunyar rokon kuma ?

Sai nayi mai hannu yazo nake tambayanshi meye yake min bayani wai kudi yakeso kuma gwaggo Asiya

ta hanashi hakama baba nace kamar nawa yake fadin suna da yawa fa ?

"Nace ya fada min ko nawane wai dubu biyar yana son ya dan soma sana,a yana samun kudi shine na"

bashi dubu goma nace yaje ya soma bakiga irin murnan da yayi ba a lokacin.

"Da yaya ya fito ya ganmu naga dai ya kara mashi kudin ban sani ba ko nawa wallahi Sa,id tausayi yake"

ban gashi duk cikin diyan gwaggo Asiya ya fisu kyau amma shine Allah ya jeraba da nakasa a cikinsu.

To ai yanzu anyi one one tunda muma ta nakasa muna yaya Fadila ko nata da sauki Salma tunda gata

har ta haihu ai don bataso haka ba ai sai Allah ya kawo abinda sauki gareta .

"Sa,id mutuminkine Salma shakuwan ku yasa gwaggo take ganin kece silan kamuwansa da kyamda a"

lokacin har ya samu a sanadin ki.

Haka muka zauna muna hiran yan gidan mu kafin ta mike ta fita taje gyara waje kafin mijinta ya shigo

gidan sai gata ta dawo tare da yaranta da suka dawo daga hadda tana fadin ga mummy salma din ku ganta.

Kallona sukeyi don duk a cikinsu ba wanda ya sanni gaskiya son dai ta haifi na farkon tana da cikin na

biyune muka tafi dole yaran su nuna basu sanni ba sai labewa sukeyi a bayan mahaifiyarsu.

Mun gaisa dai hakana dasu take fada min sunayesu daga ciki harda baba ibrahim yaya yaiwa takwara

da mai sunan gwaggo hafsatu itace mace ita kadai a cikin yayan nata biyar dawowan babansune suka fice daga dakin suka barni inaci gaba da tunanen gida.

Dole in tuna da gida don abubuwan da suka faru a rayuwan mu ba abu bane da zasuyi saurin bacewa

mutum a rai irin haka sai anyi tayi ana tuno da wani abu.

Yau gashi wai yaya Ahmed ne ya mallaki wanan gidan da yara kuma shida Farida auren da haukane

"gwaggo Hafsatu batayi ba a kanshi ba yadda batayi ba wajen ganin ta raba auren nan abin bai yuyu ba gashi a yanzu Allah ya buda masu an koma kamar ba,ayi ba."

Duk da nasan ba dainawa zatayi ba ance hali zanen dutse ga mashi dole ko anbar wani wani na nan ba a

daina ba kam a cikin halin.

Muryan yaya naji shigowa dakin yana fadin lalai salma kin zama baturiya zuwa babu notices dazun fa

ina airport da safe naje daukan pro ya dawo yau din nan .

"Yashigo yana fadin a,a,a salmace nan wai wallahi idan a hanya na ganki ba zance ke bace ai dan"

murmushi na sakw na zamo daga gadon ina gaidashi yace dole kan har da hausan ya koma wani iri kuma a yanzu.

Murmushi kawai nayi don ban iya wasan da yake kokarin yi dani ba matsayina na kaunar matarshi da

akeyi wani lokaci ni sam mazajensu tun ina karama ban iya wanan abin ba.

Tundai mijin yaya hindu dakan so wanan wasan yaita zolayan ka yana da yawan tambaya wanda na

tsani hakan yawan surutunshi nake gani a lokacin.

Wanan yasa ban damu da zuwa gidansu ba a lokacin ko munje katsina yana da wuya tagani gidanta

tunda na fahinci shi me yawan son surutune .

Dole inwa yaya Ahmed bayani nan ya tsaya ya shirishirce a wajena har lokacin sallah yaja ya fita yaya

ta kalloni zata fita tana fadin abinci fa nace bar abincin nan yaya sai gobe kila.

Har zata fita ta dawo tana fadin me zakici kenan tunda kikazo bakici komai bafa salma zanci idan cin

yazo min na fada nace ai nasha drinks dazun ta dan bini da kallo kamar na mamaki sai kuma tajiya ta fita tana fadin dole dai a san abinyi amma baki kwana haka da yunwa ai ?

Zuwa can ta dawo tana fadin yaya na kirana falo hakan yasa na fito na saka hijjab a kaina na dan tsuke

wuyan na sauko zuwa falon tun kan na karaso ya soma fadin Salma ke waliyace da zakizo tun safe bakici komai ba ?

Shiyasa kike har yanzu ba kiba ai me zakici a fita a samu maki nace ba komai yaya nagode yace haba dai

barin dan fita ki jira in dawo yanzun nan ya mike ya dauki key din motarahi ya fita.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[12/10, 9:58 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Naji dadin barin dakin da yaya Farida tayi min ita da iyalinta wanda yasa na samu yadda nake so watau

zaman kadaici don na samu barci sosai a wanan daren .

Dolenefa inyi ta barci don karatu nayi irin namu na yan Africa da muka sakawa zuciyan mu nacin boko

ka zauna ka bata lokaci kana hadda tare da kwankwance bayanin da takarda ya shafa.

Dan Africa kadai ke wanan karatun wahalan ko ince yan Nageria don akwai mu da kwance abu ya

zauna muna a kai wanan yasa ko gasan me aka hada a duniya matukat dan Nageria yaje wanan gasan ba za a barshi a baya ba komai sonkan mahukuntan abin kuwa sai sun yaba damu a wajen.

Donshine na dawo a galabaice ina bukatan ina bukatan hutu na kuma samu don na dan watsake daga

gajiyan dana debo din a can kofan dakin aka turo wanda haka yasa na motsa don hanin waye ya shigo ?

Yaya Faridace tashigo tana saye da atamfa a jikinta zance tunda nazo sune nake ganinta saye dasu a

jikinta ina kwana mukayi ta dora da fadin nashigo yafi a kirga kina kwance kina barci ai ?

Amsawa nayi da hamma ina mikewa zaune nake fasin dolene yaya na wahala iya wahala don bamson

abinda zai kara zaunar dani wanan kasan kuma yanzu .

Ta dan kalloni cikin mamakin abinda na fada nagane yasa nake fadin ni macece fa yaya dole inba dole

ba bazanso nisa da gida ba irin haka.

Abinda yakaini nayi ai gara in dawo gida cikin ku ko don daran iyayyena dana yan uwa tun ba a samu

abin jifanku dashi ba akaina kuma ?

Wanan ai mun saba inda sabo Salma abinda muka taso a cikinsa anayi tun bamu da wayau har yanzu

"kuma ba,a fasa ba ai."

To Allah ya kyauta na fada ina mika tace yaya ai yana fada wai baki fadawa kowa zancen gama

karatunki ba kinyi komai acan ke daya kamar wace bata da gata haka ?

Gatan ke nan yaya ina amfanin na wahal da mutane yanzu ba gashi Allah ya dawo dani cikin ku lafiya

an huta wani hasaran kudi zuwa kashewa a can din.

Dariya tayi tana fadin ai zaki hadu da yayanki jiya ya barki ki hutane nasan sai yayi maki fadan hakan a

yau.

Murmushi nayi na mike don shiga bayi ta juya ta fita wanka nayi na gyara kaina kafin na fito nan ma na

dan bata lokaci a karshe wando da rigan jeans na saka na dauko after dress na dora a saman kayan kafin nabi da kamshi na fito.

Tun kan in sauko nake jin dan dararakun maza a falin wanda muryan yaya Ahmed da wanine ni dai

kamar in koma har na juya naji yaya na fadin aigatama ta fito ashe ?

Nan na karaso saukowa kasa a falon nasu tun last step nake fadin ina kwana yaya hakan yasa Ya

Ahmed din juyowa yana amsa min da lafiya Salma kin tashi ke nan ya gajiyan hanya kuma ?

Cikin dan muryana karami danake kara makewa kamar dole nake magana na amsa da lafiya yaya ina

kokarin juyawa sama kuma.

"A,a karaso mana ku gaisa da Pro bakiga yayanki Pro bane ko shima kin manta dashi yanzu tunda kun"

dade baku hadu ba ko ?

Cikin son in tuna waye ake kira da pro na karaso ina fadin ina kwana ya amsa yana juyowa tare da aje

cup din dake hannunshi a lokacin.

Tuni zuciyana da ruhi suka tsaya cak saboda arba danay dashi don kuwa mutumin nan cikin jirgi nayi

zaune saman kujera a falonsu yaya.

Dagowa ya sake danyi ya dubeni muka sake hada ido nayi hanzarin kawar da nawa da sauri domin

sunyi rauni a cikin nasa ina sake fadin ina wuni cikin yar murya.

Lafiya ya gajiya ya fada a dakile wai naga kamar baka gane ko waye bafa yaya Ahmed ya fada yana

dubansa itama aida gani bata ganeshi ba yaya Farida ta fada itama.

No banganeta ba wallahi jirgin mu dai daya da ita tun a england jiyama mun sake hada jirgin still da ita

saidai naga kamar na santa a wani wajen amma bansan ko a ina bane ?

Salmace fa salman mama Dije Autan su farida Salma ya fada da mamaki tare da dago kai yana sake

kara kallona yace kana nufin wanan karamar tasu dai dana sani mai majina ?

Abinda ya fada lokacin yasani murmushin dole yace tabbas itace haba tun a jirgi nake gani kama

wallahi amma hankalina bai kawo cewa ita bace ai ?

Kasan ita a england take tana karatu tun tana da karamin shekaru uncle hassan ya turata kararu baka

gida yasa baka san da zancen tafiyanta ba ai.

Kin ganeshi kuwa salma nace Nope ban ganesa ba gaskiya Sulaimane fa na dan juyo ina duban yaya

nace yaya Sulaiman din yayan mu ?

Tace shi kuwa zakice baki ganeshi ba sai yaya Ahmed yake fadin ke kuwa ina zata ganeshi lokacin yana

kamar a kare ba irin yanzu ba daya kara jiki haka yai lafiya.

"Suka kwashe da dariya lokaci guda a,a yaya duk da yayi kiba a yanzu ai bai kaika ba har yanzu yaya"

farida ta fada jin sun dauko hiran gida yasa na sullace jikina zuwa daki inda na fito.

A fadin duniyan nan tun farko yaya Ahmed da yaya sulaimam shakuwansu harta baci don suna kananu

daya baicin abinci idan daya baya kusa wanan yana cikin dalilin tasowanshi sulaiman din hannun gwaggo hafsatu har yanzu kuma da suka kai haka sun kasa rabuwa da junansu suna tare ko yaushe.

Ina gab da shigewa dakinne naji muryan yaya yana saka min kira ina kuma salma din ai tazo a karya

mana balle yau ga yayanta nan bakin bature irin ta mai kayan shan shayi sai tazo su sha tare ai.

Dole na juyo na dawo falon don ban isa nace ba zan sauko ba yaya ta hadani dashi tace komai baci bafa

tun zuwana dole na juyo na dawo falon inda suke zaune.

Ina saukowa naji yaya farida tana fadin bari na dauko abincin nan tunda kuna nan zaune ta mike da

sauri a lokacin na kawo .

Na tayata kwaso warmers din zuwa gabansu nan na aje masu abincin na koma saman kujera gefe na

zauna ina duban wayata.

Muryan yaya Ahmed naji yana fadin salma ya haka kuma matso mana ki debi abincin gaki kamar kina

bakunta mana ki saki jiki nan gidankine fa koda farida bata gidan nan zaki shigo kiyi duk abinda kikaga dama a gidan nan.

Dago kai nayi ina dan murmushi nakai duba ga abincin inda idona ya sauka ga manakees dakw cikin

bread an nadeshi plate na dauka na dauko guda tare da tsiyaya ruwan shayi take fadin gasu madara da sauran hadi a nan.

"Saina girgiza kai ina fadin Liptop kawai zansha aina fada maki dabi,ansu kusan daya yanzu ."

Ki rabu dasu kawai basu san sanda cikinsu zai bude su fara diban abinci suna afkawa a ciki ba duk

wanan shiririntan jan fatan baya fusheku ai.

Sam na kasa sakin jiki a gabansu ko kadan abubuwa batkatai nake tunane a lokacin ko ince sun daure

min kaima a wajen game da wanan mutum da aka kira da yaya sulaiman tsohon mijin yaya hindun mu ke nan fa ake nufi.

"Wanda shima yayan mune don kusan zuri,an mu ai daya dashi balle a gidan mu ya tashi gaban iyayyen"

"mu da kowa sune muke tsoro kamar me lokacin kurciya nida Sa,id don da mun gashi da gudu muke dawo ahiyan mu mu boye nina tashi da dabi,an rashin son kitso kuma banson hula ko dan kwali wanan nan ne ke hadamu dashi a lokacin."

Gani da suman kai har baya don ma mama na rage min yawanshi saboda baki takan saka almakashi ta

cire bakin gashin ya koma daidai.

Gashin mu yana cikin abinda ke kara muna bakin jini a wajen gwaggo hafsatu da yayanta keda kai

kamar gashin hammata ba suma haka suke kindim dasu kamar maza.

Shiko lokacin kamar akamashi ya kare saboda sirantan da yake dashi irin na fulani ga sogon hanci

sumanshi nanade dakin ganshi dai kinga bufulatani sak.

To wai ya akayi komai ya canza gareshi haka lokaci gudane wai haba salma wanan din ma bai maki

bane kici abinci mana kin kuma saka abincin gaba kina tunane ?

Muryan yaya fadilace take fadan hakan akaina na dan dago kai na sauke kallona gareta ina