Chapter 27 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

da

mutunci koga iyalinka balle yan waje.

Sosai su mama suka kara lurar da hindu data rike mijinta tunda yana sonta bai kuma boye masu zancen

iyalinshi ba wanan karon sukace tayi hakkuri hakan kaddarantane ta shiga gidansa da zuciya daya.

Taso yan uwamshi da yayanshi ta nuna kaunata akansu fiyema dashi inda hali kuma da zuciya daya

wanan zai saka yayi har abinda bai tashi ba a lokacin zamansu din.

Sannu a hankali aka sakata wajen wajen munirat mai gyaran mata inda zata koyi girki zamantakewa

"tare da mu,amula da jama,a da kuma kishiyoyi har su gyaran gida daki da kuma bayi duk wai sai an koyawa mace zamannin kuma a biya kudi ki dauki darasin hakan a wajenta."

"Wanda iyayyene a baya ke koyawa diyansu wanan dabi,un wanda a yanzu zuwa office da yawan fita"

unguwa ya shagal da uwaye zama da yayansu su fahinci me suke ciki a rayuwansu sai anyi aure a fara samun matsala da mazajen .

Shine wanan boyar Allah tafito da tsarin tana dan samun kudi itama ta wanan hanyar zakiwa yarinya

register kuma karshen wata zaki zube mata kudi haka tsarin yake a yanzu.

Nan mama sharifa takai yayanta dake hutu tare dasu hindu din suna koyon girki da sauran abubuwa

don a huta zaman banza a gida.

"Sau ukku ake zuwa a sati aje goma na safe a taso karfe hudu sana,a iri iri ake koyo a wajen tare da"

lamuran rayuwa na yau da kullum.

"Hakan yasa cikin dan kakanin lokaci hindu din tagoge ta zama macen da kowa yake sha,awa hankalin"

mama dije kuma ya kwanta sosai da auren na hindu yanzu.

Bata da wani fargaba shinganta cikin kishiyoyin a yanzu wanda ta soma yiwa mama sharifa korafi da

farko hakan yasa tayi shawaran kai yaran samun ilimin zamantakewan rayuwa ba cikin takura ba birni ke nan.

"Mama takoma ganin kaf duniya ba wanda yai sa,an samun yan uwa dake kaunar tasu irin yan uwanta"

"da suka tsaya mata ga al,amuranta na rayuwa tare da yayanta."

"ZAINAB IDRIS MAKAWA[12/6, 9:24 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Allah maji rokon bawansa mama ta tsaya ga Allah ya zama mata gata yan uwa kuma sune sanadin da

Allah ya hore mata da zasu zama gatan nata na zahiri.

Don kuwa kawu ya tsaya ya sakewa hindu kayan daki na zamani irin na ko wace yar gata duk da akwai

kalubali a wajen matarsa data nuna abinda yakewa yan uwan nasa yana yawa .

Hakan yasa ya canza sallonsa a yanzu suka hada kai da mama shari suke abinsu a boye ba abaiyane ba

don a zauna lafiya tunda abin yana son kawu matsala tsakaninsa da matansa yanzu.

Wanda hakan yasa mama shari shan alwashin nemawa kawu din mata daidai dashi wace tasan ciwon

kanta tana da shekaru da wayewan kai wace take abin duniya bai rufe mata ido ba.

Kuma ta samu din ta hanyar wata kawarta data kawo mata matan wani mamaci yar nan kaduna wace

mijinta rasuwa yayi a hatsarin mota ya barta da yara ukku maza biyu mata biyu kanana basu girma ba.

Inda aka kai su mama din suka duba matar ba laifi diyan wani malamine sananne a kaduna mutane da

yawa sun sanshi suka dan fada mata irin yanayin kawu din tace indai zai riketa da diyanta ita zata jure duk wani fushi da kishi na mama zuwaira din.

Akai musayan waya akan zataji daga garesu bayan sun dawone suka kira kawu suka sheda abinda suka

samo a yau inda tun bai ganta ba yayi murna da hakan .

Har yake fadin komai muninta zai zauna da ita kodon yaran nan da akace tana dasu kanana ya samu

ladan kula da marayun Allah da zaiyi din.

Wasa wasa har zancen yayi karfi cikin sati hudu aka tsayar da maganan aure matar kawu din tana da

kwalinta na degree dinta datayi karatu a waje lokacin da mijinta yana raye suna ghana dashi tayi karatun tasamo kwalin ta na karatun zamani .

A dunkule mama sharifa ke shirin komai ba tare da kowa yasan meke faruwa ba ko yan daurin aure su

ba gaiya akayi ba abune na mutunci wa yanda mahaifinsu yayi hurda dasu abaya a yanzu suke sune matsayin mahaifansu a katsina sune iamar yan uwa iyayye wajensu sai yan uwan mahaifiyarsu daga

malunfashi da sukewa biyayya suma.

Sune sukazo da abokansa su baba Audu su biyar akaje kaduna aka dauro auren wanda dawowansune

uwargidan kawu din ta samu labari don bai fada mata ba.

Tayi karamin haukawa mijin duk da baya gari a lokacin ya fita waje akai komai bata lyaleshi ba har ya

dawo ta fara nuna capacity din mu na mata .

Haka bata bar yan uwanshi ba tace munafukaine dama tasan basu son ta ai dasu aka hada baki akai

mata hakan din a tozartata saboda anga tana juya kambunta yadsa takeso su basu samu hakan ba za ai mata bakin ciki ?

Da mama gambo ta samo a katsina mama gambo kuma irin maman mune bata da rigima masu rigiman

"ke nan mama sharifa sai mama hussaina abokiyar tagwaicin baba hassan da yanzu suna phothercort da mijinta dan kasuwan maine,shi wanda yayi karfi sosai a cikin harkan."

Bata zuwa gida haka ko yaushe yasa ban ambaceta a cikin labarin ba tana da zafi ita sosai don tafi

mama shari zafi halinsu ba daya bane saidai wajen fitana za ace halinsu daya.

"Mijinta da mijin mama Shari kamar yan uwane don zuri,a dayane su a wajen mama hussai yaganta ya"

"aureta lokacin shima a yanzu ya take yazama done a sana,anshi."

Wanan yasa a yanzu sukai karfi suma fiye da yan uwansu su maman mu ke nan amma Alhamdullahi

don a tare ake cin arzikin juna damu din.

Duk da mommy tasan waye mama shari amma haka ta bugo mata waya nacin mutunci da yankar

kauna idonta rufe tanawa mommy din sababi na anhada baki dasu don aga bayanta an samawa kawu mata ?

Dame kike nufi ke an fada maki donke kadau aka halicceshine ko kada yaji dadi don kina tunanen kin

mallakeshi sai abinda kikace yakeyi har iskancinki ya kawo garemu yanzu ?

Barin fada maki zuwaira kinsan dai ban tsoronki to nice nan na nema mashi din kije kiyi duk abinda kike

tunanen zaki iya a kaina Allah ya fiki ?

Mara kunyar banza kawai nasan dama da hannunki ai da wanan mara amfanin a cikin yam uwa dije

dake binku kamar tunkiya.

Aiko data sani da bata fadi hakan ba gaban mama shari don ko ta tsaya ta wanketa tas da zagi duk da

takashe waya ta tura mata text din zagi mai tsayi a waya saida tayi data sanin fadan hakan.

Cikin dan lokaci kuma mama Shari tabi kowa ta fada mai abunda mama zuwaira din ta fada game da

maman mu aiko mama hassana tace gata tafe.

Mata muke jawa kan mu bakin jini wajen samun waje sai mace taso wuce matsayinta ta manta da

aurota akayi a tare ta samu mijinta da yan uwanshi yafi bukatan yan uwanshi busa ga ke ko yaya yake dasu kuwa .

"Balle wanan zuri,an da kansu yake a hade komai anyinsa a tare kamar tip da taya basu taba yarda a"

gane me dan uwa take ciki.

Don ko matsalan yaso yaso ya shafi auren mummy a lokacin don har mijin saida ya girgizata batayi

zaton zai iya daukan matakin daya dauka ba a lokacin .

Wanan yasa yaya hindun samun kuran fitinan kawu ya sake mata shatara na arziki don kawai kada

mama ta dauki zancen da zafi a ranta.

Part din hindu ya tsaru iya haduwa da saida kishiyoyinta suka razana suma yaso gyarawa farida nata

gidan amma yace ai ba zama zatayi a katsina ba tunda mijinta ya samu aiki Abuja can zasu koma yanzu don har ya kama masu gida a bari sai Allah ya bashi sunyi gina saiya koma ciki.

Sunje umurah da amaryansa da mama da hindu da da yaya fadila da farida tare da yaranshi biyu da

basuyi wani girma ba sosai.

Inda mama Shari tace mu sai zata tafi zata daukemu muje tare da ita a cikin azumi wanan yasa hindu

kara kadari sosai a wajen mijinta da danginshi bata nan amma aka gyara mata dakinta akai komai don data dawo zancen tarewane a wajenta ke nan lokacin.

Sun dawo lafiya wani sati akai shagalin tarewan nata dole katsina mukaje inda za ai bukin hardana

kawu acan din kuma a gidan mu muka sauka inda muka sha mamaki don mun samu an canza fasalin tsarin ginan mu a lokacin.

Wajen mama an gyarashi da kyau an fitar mata da daki ukku falo tsakiya da kitchen ga kujeru an saka

suma su inna an gyara nasu din saidai ba irin na mama ba.

Baban mu kuma kallo daya zakai mai ka fahinci abubuwa sun dan daidaita gareshi yanzu ba irin baya ba

"da zaka ganshi chikwai chikwai da alaman damuwa a yanzu yana shigansa tsab ya fita wajen sana,anshi abinci kuma basu da matsalanshi kamar da can da muke zaune a cakude."

Ankai yaya hindu gidan mijinta washegari kuma amaryan kawu ta iso katsina da tawaganta su mama

shari inda zasu tare a katafaren sabon gidan daya gina a New GRA wanda ake lissafin girman gidan ba a magana.

Don har dasu dinner akayi amaryan tashi yar duba duba da ita mai kyau bata da tsayi sosai saidai

akwai baya gata ba wani shekarune da ita ba kowa yana yabawa da abinda ya gani lokacin shi ake kira da auren debe takaici wanan.

Son tafi mummy komai gaskiya maza na shamtam mata wani lokacin idan sun tashi kara aure sai su

dauko wanda sai mai capacity ta raina kanta ta muzanta.

Duk yadda mummy taso taushe kanta a lokacin ta gaza don saida sukai fada da mama shari da mummy

hussai da dama a jirace suke da ita sukai mata tas basu bari taji da abinda ya sameta ba lokacin.

Aure mun karawa yayan mu zuwaira kije kiyi abinda zakiyi idan zaki zauna lafiya damu a shirye muke

idan baki zama kuma wanan ya rage gareki yanzu kalman da suka fada ke nan daya kasa fita a raina har yau din nan idan na kalli mummy din.

Kar in katse maku zance nasan da yawa suna son ji yadda akayi gidan yaya hindu a lokacin aurenta din

kuwa shine.

"Alh Rufa,i ya kwashi matansa zuwa gidan hjynsu kamar yadda yace zai kawosu din a fada masu zancen"

aurenshi.

Koda suka shigo sun samu hjy da yar uwarta a zaune sai kannesa habiba da Amina dake kitchen suna

girka abinci suka shigo aka gaisa kowana huci a cikinsu saboda rikicin da akayi wajen shiga mota da za a fito.

"Don Nabilace da girki amma sai aziza tayi saurin fitowa ta zauna a gaban mota ita Na,ima kodata fito ta"

samu suna rikici taja ta tsaya a gefe daya ba tare da tankawa kowa a cikinsu ba ?

Shiya fito karshe da yara yasamesu ana wana rikicin komawa yayi ciki ya dauko wani makulin mota

"yacewa Na,ima tazo ta shiga su kuma su zauna baya."

Suka fito suka shiga dole yaja suka tafi wanan yasa har suka kai gidan hjy din yana masu masifa kan

wanan halin da sukeyi a gidan.

Wanan yasa suka isa suna cicika da junansu bayan an gaisane hjy din ta soma magana a cikin hikima

yadda zasu fahinta har inda takai ga fito masu fili da mijinsu ya daura aure da wata kuma zata tare a cikinsu itama.

Aziza da taji zancen kamar daga sama ta dago tana fadin aure fa mama hjy tace kwarai kuwa ya daure

aure da yarinyar da yatashi aure kafin ke Allah baiyi a wancan lokacin ba ya auroki.

Yanzu kuma yarinyar ta fito shine suka daura aure da ita haka yasa nace ya gaiyato min ku don in fada

maku zancen da bakina dukkanku dai kunsan auroku akayi don ana kaunan ku to haka ita wanan ma din da zata shigo yanzu.

Bana son jin wata daga cikinku tayi abin assha da zai hana zaman lafiya a tsakani don matukar kayi

hakkuri komai sai yazowa bawa da sauki a rayuwa.

Amma hjy wani abu yace anyi mai daya kara aure a yanzu bayan ko shekara ban cika ba a gidan wanan

ai ba wani hujja bace hjy ta fada nan ta saka kuka ta mike tabar falon.

"Duk kallo suka bita dashi sai Na,imace tayi karfin halin fadin ko wanan datazo asibiti gaidashi lokacin ?"

Itace kuwa kin gane itace yanzu aka daura aurensu dashi ashe baki manta ba ke nan Amina ke fada

"tace humm,ina zan mata kuwa ?"

Allah ya bamu hakkuri da juna da ya bamu zaman lafiya Allah ya kadar da shedan tsakanin mu kuma ?

Suka amsa da amin Nabila kan sauri aziza ta fita amma kukane bai fito mata ba a lokacin don gaba daya

tun ganin da tayiwa Hindu asibiti da irin kulan da tayi yana matukar son yarinyar hankalinta ya daga da ita.

Shiyasa da aka auro aziza da yake ita bata fita da komai ba na hasken fata bata tayar da hankalinta

kamar yadda ta tayar da zai auri hindu ba ashe kuma duk bata tsira ba daga hakan sai tashigo gidan itama.

A ranan dai hjy tafada masu tana son kwanciyan hankali bata son wani fitina ya biyo bayan hakan ko

waye kuma yasawa danta fitina a gida zata sa a saki maishine a lokacin.

"Dole suna kallo aka fara aikin gyaran part din hindu din dake can daura dana uwargidan Na,ima tana"

kamar tsakiyan su wanda ke nufin tare zasu zauna a part daya da ita ke nan.

Duk da worning din da hjy tayiwa sarakan nata saida Aziza taso tayar da rikici wai idan angama dakin

hindu nan zata koma don dakunan da komai yafi nasu girma shi kuma yace ai ba donta aka gina ba.

Acewanta ita bataga yar da za a kawo ta daga mata hankali ba zai kare rawan kanshi ai ya dawo gareta

tunda tasan ba abin kwarai ya kwaso ba yadda labari yazo mata.

Sai gashi ranan da aka kawo kayan dakin hindu din don a gyara mata waje ta koma fadin ance shiyayi

kayan dakin da komai ita da Nabila suka soma hauka case har gaban hjynshi.

Ya rantse da Allah kwadalanshi babu ciki baisan komai ba akai hakana dai sukai ta rikicinsu wanda bai

hana komai sai zubar da kima da hakan zai jawo masu a karshe .

Sai gashi har Allah ya nufa amarya hindu tazo gidan mijinta lafiya sunga abinda yafi karfinsu ba kamar

yadda suke zato bama don hindun can da suka sani a baya daban take data yanzu.

Gaskiya idan akace hali koba kai Allah ya nufa dayin arzikin ba dan uwanka ubangiji yaba matukar baka

nuna hassada ko bakin ciki ga maishi ba kaima sai Allah yayi kaci arzikin nan ta karkashinsa.

Don kuwa mama dai Allah bai mata arziki wanda zata rika da hannunta tace ita ta nema a yau ?

Sai yan uwanta da Allah yaba kuma hakkuri da tawakkalin irin nata yasa ubangiji ya tsaga rabonta yana

fitowa a jikinsu.

Rufin asirin ubangiji ke nan yanawa bawashi duk yadda yaga dama wanan yasa idan ka ganmu saika

zata mu din yayan wani kusan gwaunatine dake fada aji a kasa.

Kaf dinsu suma kishiyoyin baki ya mutu a yanzu don fadan yar tallakawane ya kare kuma tunda yar

tallaka tazo da abinda su yayan masu halin basu dashi.

"Bansan meyasa hakan ba bani kaunan ace za,azo katsina wani sha,ani duk da katsina garinane ta uwa"

ta uba amma sam garin ya fice min a rai .

Watakila don yadda muka bar katsina dinne ta baibai dakuma yadda matan gidanmu sukai muna bayan

tafiyan mama wajen yan uwanta hakan yasa garin ya fita raina.

Ko yanzu din ma ana gama buki na matsu mu koma kaduna din ban sakewa idan anzo katsina din

sabanin yadda yan uwana sukan sake suyi tayi harkokinsu a katsina din idan muje.

Anyi zugan zuwa gidan amarya hindu don aga kwananta a sabon gida wanda daga can zamu wuce

gidan kawu hassan don tarbon amarya da za ayi da yamma kafin a wuce zuwa dinner.

Inda mama da wasu yan gidan mu suka riga da sun tafi gidan kawu din tunda safe irin hjy laraba da inna

halima da gwgg hari sukai su goma fa da suka takawa mama din zuwa can gidan.

Mukuma sai mun biya gidan hindu muga amarya zamu kwashi jiki zuwa gidan mun isa mu sameta a

daki takure saboda bakunta da dole kayi irinsa dama a bakon waje.

Part d8n farko muna jin ana hira muna sallama amma ba a karba muna ba yasa muka shiga na gaba

"mukai sallama wata mata mai dan shekaru zaikai nasu yaya hauwa ta fito tana amsawa da fara,a ."

Muka gaisa tace ku shiga tana ciki muka sakai zuwa part din hindu din wanda ginan gidan gaba daya

sunyiwa babban falon gidan zobene falon yana kallonsu suma part dinsu yana kallon falon.

Tana jin muryan mu ta leko tana fadin sai yanzu har nagaji da jiran ku tun dazun nan aka soma cacan

"baki don tare muke da yaya farida tunda sha,anin bukine an bari ta biyomu a lokacin."

Gefe muke zaune muna jin masu aure suna hiransu ana shewa haka dai suka saka muka bata lokaci a

"wanan gidan kafin mu kwasa zuwa gidan uncle din,mu inda muka samu su mama a can ana hidimar buki ."

Acan naci abinci don hadin ganye da nakeso shi muka sama na zauna naci sosai kafin na mike mukai

sallah sai kwanciya nayi don ba wani aikin da yaro zai tsoma hannu a ciki ko yan aiki daga kaduna mama shari tazo dasu suyi a biyasu.

An daiyi didima sosai a nan kafin a wuce zuwa wajem dinner din ida kowa a nan yaga amaryan dakyau

don