Chapter 7 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

fara ba tare da bata lokaci ba.

"Yabar manya sun soma gabatar da komai yana zaune yana saurarensu wanan dabi,ace ta malam"

"bahaushe bawa manyaka girmansu koda ka fisu da komai kuwa matukar mutum ya girmeka dolene ka mutuntashi don shekarunsa bawai sai musulmam hausawa ke hakan ba a,a mutukar kai dan arewane wanan halin ya zama muna kamar dabi,ace a wajen mu yan arewa."

Saidai su kansu sun kula da kamar hankalisa baya jikinsa a wanan zaman don shi mutum ne da idan

yana waje za a sani don yadda yake da naci akan duk abinda ya saka agaba a harkan cinikaiyansa.

Yayi fice sosai da kaurin suna a wanan jahar don yafi manyan yan kasuwan daya samu sanin hanyar

kasuwanci a yanzu.

Haka ya zamewa wasunsu kashin bakin tukunya don irin haka dole ka samu makiya wa yanda ka

tsonewa ido suke ganin kashige masu gaba a wanan harkan.

Daga karshe duk da baiso magana ba dole shawaran daya bada shi akabi don yana amfani da ilimi da

"basira acikin harkan sabanin su tsofin yan kasuwan dake harkan a kaura da kai ana goggaya da mu,amul a cikin duhun kai."

Amfanin ilimin kena zai taimakawa rayuwa a duk inda bawa ya tsunci kanshi cikin duniyan nan ilimi ko

wace iri makami ga dan adam wurin rayuwa na yau da kullum donshine yanzu da arewa ke yakar jahilci da duhun kai mukai suna da fice a wajen komai.

Din a gaskiya ba finmu fasa ko wayewa akayi ba matsalan mu dayace shine rashin ilimi a baya da

bamayi sosai a arewa yanzu ko ilimin ya zama ruwan dare gama duniya ko wani sako lungu da birni kowa na kokarin yakan jahilci akansa.

A fannin yan matan kuwa sun shige cikin islamiya dama sun makara don tsayawa diban ruwan da

gwaggo Asiya ta sakasu komai nagidan a ranan sun cikashi fam da ruwa kamar ba gobe.

Duk da sun san hakan ba abin mamaki bane kafinsu dawo daga islamiya zasu samu anyi amfani fiye da

rabin ruwan nan wai a aikin gida.

Wanda sunsan ana masu hakan da gaiyace don uwarsu tayi magana ayi mata cin mutunci a gidan idan

ubansu baiyi ba ita gwaggo Asiya din itace zata tsaya a gabansu ba kunya ta zage mahaifiyar tasu tas wanan ba bakon gani bane wajensu ai.

Ranan kamar hadin baki don kuwa a daidai sha biyu da rabi ana harin sallah azahar aka sakosu saman

titi don ko wace ta koma gida ta kimtsa kafin hudu a dawo a sake zama don daukan darasi kuma.

"Duk da hijjabai iri dayane a jikinsu manya da yaransu haka bai hana Rufa,i Ibrahim da abokansa kewa"

"lakane da Alh Rufa,i Ibrahim dasuka mayar da A R wasu kuma sa,oinshi na kiransa da R I duk wanda ka kira amsawa yakeyi acikin mutunci."

Hanyar gidansu yaga sun dosa wanda hakan ke nuni da unguwar rumawa suke kenan idan ba karya

yayiwa kanshi ba don can din suka dosa a lokacin.

Dabarace ta fado mashi inda ya sha gabansu ya tsaya wajen wani mai shago kamar zai sayi abu mai

shagon ya taso da sauri yana fadin Alh Allah me za a kawoma ?

Kai dakata muyi magana dakai kaga wacan yaran su nake son bayani a kansu daga ina suke yayan

waye kuma a unguwar nan.

Kallo mai shagon yakai wa yaran da yake nuna mashi din yace dashi haba kaiko ka kallosu haka gatsau

ai sai a gane dasu mukeyi a nan tsaye abunka da jahilci makin ya tsaya sai kuma ya sake waigawa yana fadin ai su farida ke nan ko ?

"Ai wa yan nan yan babban gidane zuri,an gidan malam Ali tsohone kaf unguwan nan ansansu ba"

batattatu bane a unguwa Alh.

Wacan nake magana ta tsakiyansu fa ya sake abinda aka hanashi yi waige yace hindu ke nan itace ai

babbansu dakinsu daya su ukkun hindu farida fadila ai dakinsu daya kwarai wallahi.

Dakata don Allah anya tafiyan mu zaiyi daidai dakai kuwa kana abu haka ba natsu na tsani hakan

wallahi ka natsu kabar wanan waigen ka tsaya muyi magana tunda ka gane wanake nufi ko ?

To to to Alh Allah ai a natse yake ka rike fuskata zan dawo zamu tattauna akan zancen su don Allah ina

son kayi min bincke akanta idan bata da matsaya.

Babu don kuwa matsalan dai in akwai shine gaskiya kamar sunfi auren hadi a tsakaninsu saidai yanzu

"sun rage hakan amma har yanzu suna wanan dabi,an na aure gida yasu yasunsu ."

Shine kadai nake ganin barazana a yanzu garesu amma banji ance an masu matsaya ba gaskiya zamuyi

magana karbi wanan ka rika har in dawo mu zauna dakai.

Yana washe baki yana kallon kudin da Alh ke zarowa a lokacin cikin motarahi ya mika hannu ya karba

yana zuba godiya a daidai lokacin suka gilma wajensu aban chewing gun Isah.

Farida ta fada cikin ko in kula ya juya yana fadin ina zuwa farida jeki ce hassan ya baki roban chingun

din ina magana da Alh tukun .

Roban chingun kuma isah in diba iya son raina ke nan ko ku dauka dai ku tafi dashi na baku ta dan ja

tsuki tana fadin shirmen banza kaida ko kwandala baka iya ragawa mutum kaine zaka iya kyautan roban chingun yau.

Ni aban na dari kaji muje mu raba yace Allah ba wasa nakeyi ba jeki karba injini ya fada ita kuma ta

dauka ya rudene don taga iyakarshi taje ta karbi roban a hannun yaronshi din ta juyo tana fadin isah na karba fa ?

To jeki farida a tauna lafiya ya fada yana daga mata hannu hankalishi akan Alh daya ba dariya kan

wanan wasan kwaikwayon da yayi a gabanshi a lokacin.

Ya washe baki yana fadin ai Alh Allah don ka sheda zanma komai tsakani da Allah tunda kazo ta wajena

sai naga abinda ya turewa buzu nadi akan zancen nan .

To nagode isah naji ta kiraka dashi ko ya amsa a washe da hakane Alh sunan nawa ke nan isah mai

shago kaf layin nan ansani ba bace nake ba gaskiya.

Sukai sallama yaja motarshi ya tafi bayan ya dan daga kai yakai karo uku yana karewa tafiyan yaran

kallo zakace yarab irin tashin abuja din nan ne don sai ka rantse ba a katsina suke rayuwa ba kuma a gidan tallakawa .

Su kuma bamgaresu dariya farida kewa isah suna gulma akanshi cewa kila ya rudene wanda ya bashi

jarine yazo karban abinsa yasa ya fita cikin hankalinsa haka baima san abinda yakeyi ba harda kyautan cingun wa yan mata yau.

Sai lokacin hindatu tayi magana tana fadin ki daiyi a hankali kada yazo ya kulla maki sheri kusha dukan

banza a wajen babanmu kindai san halinsa karma har gwaggo Asiya taji kin kade yau a gidan mu.

Ai iya na darina zan dauka in aje mashi sauran har ya waiwayoni mu kwashi tsiya kafin in bashi din sai

na gama garashi zan bashi abinsa.

Ta boye cikin xunbulelen hijab dinta da zasu shiga gida suna kai kofansu sukaji muryan gwaggo Asiya

na tashi farida ke fadin bissimillahi Allah an shiga office ke nan kuma tunda gari ya waye.

Wai ashe abunda takewa fada shine Ahmed ne ya shigo da dinkkakun kayan makaranta guda biyu na

"salma dana sa,id da akace sune basu zuwa school don baba bai sakasu ba."

Shine ya dan kula ya dinkawa yaran ya kawo masu wananne abin daya tayar da fadan a lokacin don me

suke nuna bambamci akan diyan gidan yanzu daya kasance da yar Dije ai shine dalilin da aka sakashi dinkawa yaran kaya ya kawo masu.

Ita lokacin data saka diyanta aiba wanda ya tayar dakai ya duba mata ita kadai aka bari tayi wahalanta

da abinta ita ba fakiriya bace dama da zata jira sai an mata an bata tallafi daga wasu.

Jin hakan basu tsaya sauraren iyayyen nasu ba suka shige dakinsu suna rage manyan hijjab dinsu na

islamiya dake jikinsu.

Koshi wanan din gwaggo Larabace ta dinka masu shi ganin wanda suke sakawa yayi masu karami a

lokacin zaman biyayyan dake tsakaninsu da mama Dije yasa take kyautata mata ta bangaren yaran wanda hakan da akeyi yake matukar batawa gwaggo Asiya din rai sosai a gidan .

Gwaggo Asiya da inna hafsatu kishiyar gwaggo balaraba kungiyarsu dayane a cikin gidan tare suke

kashewa su bizzine a tsakaninsu inda suke ganin ita kuma Dije suna biyayya da gwaggo Asiya harda karima amaryan su gwaggo balaraba din.

Wani lokaci tana tare dasu dan tafi dan shigewa hjy balaraba din nasu yafi zuwa daya da inna karima

don rainin wayau hjy hafsatu din.

Inda Amadun kuma danne ga inna hafsatu danta na farko amma rikonshi da komai yana hannun hjy

balaraba don yaron da ita ya bude ido a gidan tana mashi komai har ya taso din nan bata daina ba donshi yayi sabo da ita sosai a cikin kaf matan gidan nasu.

Duk da mahaufiyarshi tabi duk wata hanya da zataga ta raba tsakaninsu amma hakan bai yuyu ba

kinsan da namiji da taurinkai kan abinda yake gani shine daidai a wajenshi.

Da baba Ali yaji zancen dariya yayi yana fadin barsu can da haukansu na banza nasan maganinsu ai

nasan abinda zanyi in kawo karshen wanan mugun zaman a tsakaninsu kowa ya kyalesu dani a gidan nan.

A bangaren A R kuwa yana barin unguwar ya sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idonshi gami da jin

"wani mugun sha,awar yarinyar yana janshi tankar zai fasa mai zuciya."

Haka ya karasa gidansa a dadafe yaransa dake waje suna wasa suna mai sannu da dawowa amma ya

kasa amsawa.

Sai fuska daya hade a wuri daya a cikin damuwa da uwar gidansa Aziza ya soma cin karo tana saye a

cikin rigan data wuni dashi tun jiya a jikinta.

Ga roba ta riko da alaman kitchen zata lokacin ta tsaya tana mai kallon mamaki don yanayin da shigo

din a lokacin gidan.

Dakinshi ya nufa ya bude ya shige yana rufo kofan da karfi a daidai lokacin yaran suka shigo suma a

cikin damuwa suka samu waje suka zauna .

Babban ke fadin ummah meya samu Abba naga Abban ya dawo rashin bace yadda ka ganshi nima haka

naganeshi tabawa yaron amsa a takaice.

Yana shiga dakin gado ya fada ya kwanta rigingine yana tunanen fuskan wanan yarinyar data tafi da

imaninshi haka lokaci guda.

"Yariyar tayi mashi ba laifi irinta yake sha,awan aure yana son mace siririya haka mara jiki fara wanan"

kuma har ta zarce nasashi hasashen don akwai kyau akai baya duk da a hijab take amma a cikin dan kallon dayayi mata ya karewa halittanta kallo a lokacin.

Nabila matarshi ta biyuce ta bude kofan ta shigo ya dan dago yana binta da kallo kanta a baiye yake

yakai kwanaki yana ganinta a hakan ya mutse zani ta dora saman rigan barcin data kwana dashi tashigo tana fadin yaya ashe ka dawo ?

"Eeh na dawo wani abune ya fada a dakile a cikin haushi da takaicin ganinta hakan a,a dama zancen"

kudin da nayimane nazo in tuna maka naga ka fita baka bani bane ?

Ba zan bayar ba don banga amfanin karban kudi ko yaushe a dinka anko ba tunda ba sakawa kukeyi ba

"wanan dabi,an banza nace bansi kuki ku daina toni zan dauki mataki akan hakan."

Saida ta dan dubeshi kafin takai zaune gefen kafanshi tana fadin akwai kudin ankon daka bamune

bamu dinka ba gidan nan yaya ?

In an dinka din ansa ki duba don Allah tun jiya ko ince shekaran jiya kike yawa haka a yamutse duba

kanki don girman Allah ?

"Wanan wani irin dabi,an banzane haka kukeyi wai ko baki zakayi haka za a zo a sameku a yamutse"

wacan tana fama da wani riga tsami da wari yana tashi a ciki.

Ke kuma ga shiga kamar ta mahaukata kai kamar bukkan mahaukaciya ba gyara kunyi min adalci kenan

a rayuwana ?

Kun sanani zan dauku matakin hakan akanku tunda baku da niyar gyara halinku zan auro wace zata iya

min gyara da kuma abinda nake so .

Wani duban baka isa ba wallahi ta aika mai dashi don haushi da takaici kasa magana tayi a lokacin ta

mike tabar dakin a cikin fushi.

Tsuki yaja a bangarenshi ya dafe kai takaici biyu ya kamashi lokaci guda na rashin karban lamban

wanan mutumin da zai mai hanya akan yarinyar nan duk da mutumin na bukatan lokaci kan binciken daya sashi yin akan ita yarinyar.

Baijin zai dauki lokaci bai leka ba ance karfe da zafinsa ake dukanshi ya lamkwashe irin matan nan ba a

sakaci wajen nemansu sai an kama jiki.

Yarinyace sosai ba wani shekarune da ita don haka yasan a matsayinsa na wanda ke da aure har mata

biyu zai danyi wuya wajen samunta sai gwada bajintarshi da sallon basira irin nasa dole matukar yana son ya mallaketa.

Bai kara fita daga gidan ba yana kwance yana sakawa da walwala ta inda zai fitowa wa wanan yakin da

yanzu ya tunkaroshi.

"Ana sallame magariba da isha,i a inda ya saba sallah matukar yana gari sallah a wanan wajen bai"

wuceshi a daidai wanan lokacin maza da yawa hakan sukewa kansu inkiya don neman sheda suna da inda sukw tsayarwa don gabatar da ibadunsu.

In ba haka ba yanzune gari zai dauka kuwa da cewa wani ai baya sallah a cikin mutane ko kuma ace

baya sallah ma sam a rayuwanshi.

Dan nisa kadan ya tsaya da shagon isah ya fito ya tura yaro ya kira mashi isah din ba a jima ba sai gashi

da saurinsa yana washe baki tare da fadin Alh Allah ashe kaine tafe yanzu ?

Yanzu ko mutumiyar suka shige sun dawo daga islamiya okey yace yana gyara tsayuwa tare da cusa

hannunsa cikin aljihun wandonshi.

Ya soma fadin yaya akwai wani abu daga samo daga bangarenka game da ita bayan wucewana ?

Kwarai kwarai Alh akwai kuwa don ban ma zata zaka dawo haka da wuri ba na dai dan soma bincike

abinda na jiyo shine a halin yanzu gaskiya bata da matsaya kamar yadda na fadama dazun dai.

Saidai matsala shine ance gaskiya basu tsayi da kowa don sai an basu umurni suke fara tsayi da maza

"din akwai wani kakansu dake juya gidan gaba daya haka al,adansu yake dama."

Wanda yake babba shine mai gudanar da komai a cikin family din isah aban taliya da magi muryan

Farida ke fadin hakan daga nisa.

Yar halak kaga kanwarta nan kullum a nan suke sayan kayan masarufi a wajena nasan shi za a sulala

gobe kafin a tafi boko da safe .

Ka bata katon daya in akwaishi kace nace ta gaida min da ita da sauri isah ya juya yana fadin aike hindu

ina can wajen Alh Allah muna tattaunawane dashi kan hindu yama ce a baki katon kije dashi kinga sai ki bar kudin ku ke nan !

A Kan yaya fa kace a ina ya santa waye shi kuma take tambaya a cikin mamaki in arziki ya tunkaroka ai

ba sallama yake ma ba saidai kayi aune dashi dumu dumu a jikinka.

Gaskiya ba zan karba ba idan na karba karshe dukana za ayi a banza ace ubanwa yace in karbo kayan

maza ?

Keko Farida kada ki min haka zo muje kiganshi da kanki ko zaki yarda Allah saboda itama yazo unguwar

nan yanzu.

Bani dai taliyata in wuce kaji ta sake fada nayi maki kama da dan yankan kaine halan sukaji muryan

"Rufa,i din a bayansu."

Ta dan juyo kamar ta shareshi sai kuma ta juyo tana fadin ina wuni saboda kwarjin da yai mata a

fuskanshi ya amsa da lafiya daga gida kike yanzu ke nan ?

Eh an aikoni in sayo abune gun isah ta fada tare da saya abin don sanin kai da nauyi ayya ainace isah ya

baki koma maye kuke so a dinga aikowa a karba kawai a wajenshi.

"A,a babanmu zai yi fada sosai idan yaji kawai dai angode bani in tafi isah take sake maimaitawa tare da"

kokarin mika mashi kudon hannunta

Ke zaki bari har baba ya ganine kicewa hindu ninace a kawo mata ki boye kawai nan dai yayi dabaran

da saida ta karba dasu maggi din packed ukku tumatur da man turkey tayi sauri tana jan buhun da kyar zuwa gida.

"Tayi sa,a har ta shiga daki dashi ba kowa a wajen gidan sun shiga cikin gida tsegumi da ranan tasha"

kwakwazo wajen gwaggo Asiya.

Suna tsaka da kuskusne mama data kewaya ta shigo tana kallonsu kafin takai kallo akan kayan dake

gefen gado tana fadin wanan fa kayan waye ?

Shi nake tambayanta ai wai wani ya saya mata a wajen isah din yace a kawo min ni kuma wallahi ban

san ko waye ba ?

Farida kayanwa kika karbo don Allah mama din ta fada a cikin raunin murya mai nuna damuwa irin na

uwaye a wani lokaci.

Wallahi mama ban sanshi ba isah dai yace min yazo nan ne saboda yaya ya fada mai bamu fitan dare

tadai fadawa uwar yadda abin ya faru.

Wa kika samu yayi miki wanan sayayyan haka banson daukan magana kin dai san halin gidan nan idan

"ba,a zo nema ba baka tsayawa da mutum kada ki dauko min magana don Allah ?"

Ke yanzu da kika karbo kayan nan baki tsoron wani ya gani a gidan nan kija min magana ?

Tagama fadan suka duba kayan hankalinta bai kwanta ba ta saka hijjab ta fita bangaren baba Audu ta

tafi wajen gwaggo laraba ta kwashe komai ta fada mata hankali tashe.

Gwaggo laraba din ta bata shawara akan a boye kayan ayi amfani dashi kada a bari mahaifinsu ko

abokan zamansu su sani sannan ta turo mata hindu din idan sun dawo makaranta washegari.

Wana ya dansa zuciyar mama di sassautawa don shawaran kwarau hjy laraba din ta bata a lokaci iya

wanda zaka iya bawa mutum tsakani da Allah.

"Ya zama wajibi ta saka ido sosai akan yaran yanzu tasan da suwa suke mu,amula amma wanan ai ba"

komai bane alherine kawai tsakanin yaro da yarinya saidai tunda ya sayo yanzu sai a haneshi don gaba kuma .

Washegari kan yara sun sheda alheri yazo dakinsu daren jiya don kowa saida aka cika mai kula ta

kwashe saura zuwa daki ita da yarta salma dake karama yanzu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/16, 9:33 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO