Chapter 6 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

tafi dashi na baku ta dan ja

tsuki tana fadin shirmen banza kaida ko kwandala baka iya ragawa mutum kaine zaka iya kyautan roban chingun yau.

Ni aban na dari kaji muje mu raba yace Allah ba wasa nakeyi ba jeki karba injini ya fada ita kuma ta

dauka ya rudene don taga iyakarshi taje ta karbi roban a hannun yaronshi din ta juyo tana fadin isah na karba fa ?

To jeki farida a tauna lafiya ya fada yana daga mata hannu hankalishi akan Alh daya ba dariya kan

wanan wasan kwaikwayon da yayi a gabanshi a lokacin.

Ya washe baki yana fadin ai Alh Allah don ka sheda zanma komai tsakani da Allah tunda kazo ta wajena

sai naga abinda ya turewa buzu nadi akan zancen nan .

To nagode isah naji ta kiraka dashi ko ya amsa a washe da hakane Alh sunan nawa ke nan isah mai

shago kaf layin nan ansani ba bace nake ba gaskiya.

Sukai sallama yaja motarshi ya tafi bayan ya dan daga kai yakai karo uku yana karewa tafiyan yaran

kallo zakace yarab irin tashin abuja din nan ne don sai ka rantse ba a katsina suke rayuwa ba kuma a gidan tallakawa .

Su kuma bamgaresu dariya farida kewa isah suna gulma akanshi cewa kila ya rudene wanda ya bashi

jarine yazo karban abinsa yasa ya fita cikin hankalinsa haka baima san abinda yakeyi ba harda kyautan cingun wa yan mata yau.

Sai lokacin hindatu tayi magana tana fadin ki daiyi a hankali kada yazo ya kulla maki sheri kusha dukan

banza a wajen babanmu kindai san halinsa karma har gwaggo Asiya taji kin kade yau a gidan mu.

Ai iya na darina zan dauka in aje mashi sauran har ya waiwayoni mu kwashi tsiya kafin in bashi din sai

na gama garashi zan bashi abinsa.

Ta boye cikin xunbulelen hijab dinta da zasu shiga gida suna kai kofansu sukaji muryan gwaggo Asiya

na tashi farida ke fadin bissimillahi Allah an shiga office ke nan kuma tunda gari ya waye.

Wai ashe abunda takewa fada shine Ahmed ne ya shigo da dinkkakun kayan makaranta guda biyu na

"salma dana sa,id da akace sune basu zuwa school don baba bai sakasu ba."

Shine ya dan kula ya dinkawa yaran ya kawo masu wananne abin daya tayar da fadan a lokacin don me

suke nuna bambamci akan diyan gidan yanzu daya kasance da yar Dije ai shine dalilin da aka sakashi dinkawa yaran kaya ya kawo masu.

Ita lokacin data saka diyanta aiba wanda ya tayar dakai ya duba mata ita kadai aka bari tayi wahalanta

da abinta ita ba fakiriya bace dama da zata jira sai an mata an bata tallafi daga wasu.

Jin hakan basu tsaya sauraren iyayyen nasu ba suka shige dakinsu suna rage manyan hijjab dinsu na

islamiya dake jikinsu.

Koshi wanan din gwaggo Larabace ta dinka masu shi ganin wanda suke sakawa yayi masu karami a

lokacin zaman biyayyan dake tsakaninsu da mama Dije yasa take kyautata mata ta bangaren yaran wanda hakan da akeyi yake matukar batawa gwaggo Asiya din rai sosai a gidan .

Gwaggo Asiya da inna hafsatu kishiyar gwaggo balaraba kungiyarsu dayane a cikin gidan tare suke

kashewa su bizzine a tsakaninsu inda suke ganin ita kuma Dije suna biyayya da gwaggo Asiya harda karima amaryan su gwaggo balaraba din.

Wani lokaci tana tare dasu dan tafi dan shigewa hjy balaraba din nasu yafi zuwa daya da inna karima

don rainin wayau hjy hafsatu din.

Inda Amadun kuma danne ga inna hafsatu danta na farko amma rikonshi da komai yana hannun hjy

balaraba don yaron da ita ya bude ido a gidan tana mashi komai har ya taso din nan bata daina ba donshi yayi sabo da ita sosai a cikin kaf matan gidan nasu.

Duk da mahaufiyarshi tabi duk wata hanya da zataga ta raba tsakaninsu amma hakan bai yuyu ba

kinsan da namiji da taurinkai kan abinda yake gani shine daidai a wajenshi.

Da baba Ali yaji zancen dariya yayi yana fadin barsu can da haukansu na banza nasan maganinsu ai

nasan abinda zanyi in kawo karshen wanan mugun zaman a tsakaninsu kowa ya kyalesu dani a gidan nan.

A bangaren A R kuwa yana barin unguwar ya sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idonshi gami da jin

"wani mugun sha,awar yarinyar yana janshi tankar zai fasa mai zuciya."

Haka ya karasa gidansa a dadafe yaransa dake waje suna wasa suna mai sannu da dawowa amma ya

kasa amsawa.

Sai fuska daya hade a wuri daya a cikin damuwa da uwar gidansa Aziza ya soma cin karo tana saye a

cikin rigan data wuni dashi tun jiya a jikinta.

Ga roba ta riko da alaman kitchen zata lokacin ta tsaya tana mai kallon mamaki don yanayin da shigo

din a lokacin gidan.

Dakinshi ya nufa ya bude ya shige yana rufo kofan da karfi a daidai lokacin yaran suka shigo suma a

cikin damuwa suka samu waje suka zauna .

Babban ke fadin ummah meya samu Abba naga Abban ya dawo rashin bace yadda ka ganshi nima haka

naganeshi tabawa yaron amsa a takaice.

Yana shiga dakin gado ya fada ya kwanta rigingine yana tunanen fuskan wanan yarinyar data tafi da

imaninshi haka lokaci guda.

"Yariyar tayi mashi ba laifi irinta yake sha,awan aure yana son mace siririya haka mara jiki fara wanan"

kuma har ta zarce nasashi hasashen don akwai kyau akai baya duk da a hijab take amma a cikin dan kallon dayayi mata ya karewa halittanta kallo a lokacin.

Nabila matarshi ta biyuce ta bude kofan ta shigo ya dan dago yana binta da kallo kanta a baiye yake

yakai kwanaki yana ganinta a hakan ya mutse zani ta dora saman rigan barcin data kwana dashi tashigo tana fadin yaya ashe ka dawo ?

"Eeh na dawo wani abune ya fada a dakile a cikin haushi da takaicin ganinta hakan a,a dama zancen"

kudin da nayimane nazo in tuna maka naga ka fita baka bani bane ?

Ba zan bayar ba don banga amfanin karban kudi ko yaushe a dinka anko ba tunda ba sakawa kukeyi ba

"wanan dabi,an banza nace bansi kuki ku daina toni zan dauki mataki akan hakan."

Saida ta dan dubeshi kafin takai zaune gefen kafanshi tana fadin akwai kudin ankon daka bamune

bamu dinka ba gidan nan yaya ?

In an dinka din ansa ki duba don Allah tun jiya ko ince shekaran jiya kike yawa haka a yamutse duba

kanki don girman Allah ?

"Wanan wani irin dabi,an banzane haka kukeyi wai ko baki zakayi haka za a zo a sameku a yamutse"

wacan tana fama da wani riga tsami da wari yana tashi a ciki.

Ke kuma ga shiga kamar ta mahaukata kai kamar bukkan mahaukaciya ba gyara kunyi min adalci kenan

a rayuwana ?

Kun sanani zan dauku matakin hakan akanku tunda baku da niyar gyara halinku zan auro wace zata iya

min gyara da kuma abinda nake so .

Wani duban baka isa ba wallahi ta aika mai dashi don haushi da takaici kasa magana tayi a lokacin ta

mike tabar dakin a cikin fushi.

Tsuki yaja a bangarenshi ya dafe kai takaici biyu ya kamashi lokaci guda na rashin karban lamban

wanan mutumin da zai mai hanya akan yarinyar nan duk da mutumin na bukatan lokaci kan binciken daya sashi yin akan ita yarinyar.

Baijin zai dauki lokaci bai leka ba ance karfe da zafinsa ake dukanshi ya lamkwashe irin matan nan ba a

sakaci wajen nemansu sai an kama jiki.

Yarinyace sosai ba wani shekarune da ita don haka yasan a matsayinsa na wanda ke da aure har mata

biyu zai danyi wuya wajen samunta sai gwada bajintarshi da sallon basira irin nasa dole matukar yana son ya mallaketa.

Bai kara fita daga gidan ba yana kwance yana sakawa da walwala ta inda zai fitowa wa wanan yakin da

yanzu ya tunkaroshi.

"Ana sallame magariba da isha,i a inda ya saba sallah matukar yana gari sallah a wanan wajen bai"

wuceshi a daidai wanan lokacin maza da yawa hakan sukewa kansu inkiya don neman sheda suna da inda sukw tsayarwa don gabatar da ibadunsu.

In ba haka ba yanzune gari zai dauka kuwa da cewa wani ai baya sallah a cikin mutane ko kuma ace

baya sallah ma sam a rayuwanshi.

Dan nisa kadan ya tsaya da shagon isah ya fito ya tura yaro ya kira mashi isah din ba a jima ba sai gashi

da saurinsa yana washe baki tare da fadin Alh Allah ashe kaine tafe yanzu ?

Yanzu ko mutumiyar suka shige sun dawo daga islamiya okey yace yana gyara tsayuwa tare da cusa

hannunsa cikin aljihun wandonshi.

Ya soma fadin yaya akwai wani abu daga samo daga bangarenka game da ita bayan wucewana ?

Kwarai kwarai Alh akwai kuwa don ban ma zata zaka dawo haka da wuri ba na dai dan soma bincike

abinda na jiyo shine a halin yanzu gaskiya bata da matsaya kamar yadda na fadama dazun dai.

Saidai matsala shine ance gaskiya basu tsayi da kowa don sai an basu umurni suke fara tsayi da maza

"din akwai wani kakansu dake juya gidan gaba daya haka al,adansu yake dama."

Wanda yake babba shine mai gudanar da komai a cikin family din isah aban taliya da magi muryan

Farida ke fadin hakan daga nisa.

Yar halak kaga kanwarta nan kullum a nan suke sayan kayan masarufi a wajena nasan shi za a sulala

gobe kafin a tafi boko da safe .

Ka bata katon daya in akwaishi kace nace ta gaida min da ita da sauri isah ya juya yana fadin aike hindu

ina can wajen Alh Allah muna tattaunawane dashi kan hindu yama ce a baki katon kije dashi kinga sai ki bar kudin ku ke nan !

A Kan yaya fa kace a ina ya santa waye shi kuma take tambaya a cikin mamaki in arziki ya tunkaroka ai

ba sallama yake ma ba saidai kayi aune dashi dumu dumu a jikinka.

Gaskiya ba zan karba ba idan na karba karshe dukana za ayi a banza ace ubanwa yace in karbo kayan

maza ?

Keko Farida kada ki min haka zo muje kiganshi da kanki ko zaki yarda Allah saboda itama yazo unguwar

nan yanzu.

Bani dai taliyata in wuce kaji ta sake fada nayi maki kama da dan yankan kaine halan sukaji muryan

"Rufa,i din a bayansu."

Ta dan juyo kamar ta shareshi sai kuma ta juyo tana fadin ina wuni saboda kwarjin da yai mata a

fuskanshi ya amsa da lafiya daga gida kike yanzu ke nan ?

Eh an aikoni in sayo abune gun isah ta fada tare da saya abin don sanin kai da nauyi ayya ainace isah ya

baki koma maye kuke so a dinga aikowa a karba kawai a wajenshi.

"A,a babanmu zai yi fada sosai idan yaji kawai dai angode bani in tafi isah take sake maimaitawa tare da"

kokarin mika mashi kudon hannunta

Ke zaki bari har baba ya ganine kicewa hindu ninace a kawo mata ki boye kawai nan dai yayi dabaran

da saida ta karba dasu maggi din packed ukku tumatur da man turkey tayi sauri tana jan buhun da kyar zuwa gida.

"Tayi sa,a har ta shiga daki dashi ba kowa a wajen gidan sun shiga cikin gida tsegumi da ranan tasha"

kwakwazo wajen gwaggo Asiya.

Suna tsaka da kuskusne mama data kewaya ta shigo tana kallonsu kafin takai kallo akan kayan dake

gefen gado tana fadin wanan fa kayan waye ?

Shi nake tambayanta ai wai wani ya saya mata a wajen isah din yace a kawo min ni kuma wallahi ban

san ko waye ba ?

Farida kayanwa kika karbo don Allah mama din ta fada a cikin raunin murya mai nuna damuwa irin na

uwaye a wani lokaci.

Wallahi mama ban sanshi ba isah dai yace min yazo nan ne saboda yaya ya fada mai bamu fitan dare

tadai fadawa uwar yadda abin ya faru.

Wa kika samu yayi miki wanan sayayyan haka banson daukan magana kin dai san halin gidan nan idan

"ba,a zo nema ba baka tsayawa da mutum kada ki dauko min magana don Allah ?"

Ke yanzu da kika karbo kayan nan baki tsoron wani ya gani a gidan nan kija min magana ?

Tagama fadan suka duba kayan hankalinta bai kwanta ba ta saka hijjab ta fita bangaren baba Audu ta

tafi wajen gwaggo laraba ta kwashe komai ta fada mata hankali tashe.

Gwaggo laraba din ta bata shawara akan a boye kayan ayi amfani dashi kada a bari mahaifinsu ko

abokan zamansu su sani sannan ta turo mata hindu din idan sun dawo makaranta washegari.

Wana ya dansa zuciyar mama di sassautawa don shawaran kwarau hjy laraba din ta bata a lokaci iya

wanda zaka iya bawa mutum tsakani da Allah.

"Ya zama wajibi ta saka ido sosai akan yaran yanzu tasan da suwa suke mu,amula amma wanan ai ba"

komai bane alherine kawai tsakanin yaro da yarinya saidai tunda ya sayo yanzu sai a haneshi don gaba kuma .

Washegari kan yara sun sheda alheri yazo dakinsu daren jiya don kowa saida aka cika mai kula ta

kwashe saura zuwa daki ita da yarta salma dake karama yanzu. FUREN BADO 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Tafe yake a motarshi ta zamani mai daukan ido idan kin ganshi zaki rantse ko auren farko baiyi ba sai kin

tambaya zakiji ance matansa biyu ai da yara shidda.

Yarone matashi maijin lokaci daya shigo kasuwa da kafan dama yana kuma damawa a cikin manya don

"a yanzu sana,a bata karbuwa saida ilimi da kuma wayenwan kai."

Yayi karatu gwargwado amma bamai zurfi sosai ba daga haka yacigaba da harkan kasuwancin daya

soma tun yana karaminsa yana bin ubangidansa.

Sai Allah yauwa ubangidan nasa rasuwa haka yasa yayi ta fadi tashi wajen neman inda zai dogara shiga

nan fada nan har ubangiji ya tarfawa garinsa nono ya soma dagowa aka fara harka dashi.

Yanzu yana jin kanshi daidai da ko wani namiji don hakane ya kokarta ya gina sabon mazauni shida

iyalinsa abu daya ya rage mashi a rayuwa shine ya samu sabuwar amarya da zasu tare a wanan gidan a morewa rayuwa a tare.

"Saidai kash duk wanan wadatan ta Rufa,i kamar babushi ga iyalansa don kuwa kullum gasu nan a fige"

ba auki shi kanshi wanan halin na matan nasa yana matukar bakanta mashi rai gashi ba halin daukan mataki a kanshi don umurnin mahaifiyarsa dake kansa kan matan nasa biyu.

Aurene mai kama da gaiya sukai mashi don ba za a kira hakan da gata ba don wanan mahaifinsa yana

"ganin kudi sun fara taso mashi ya dauki yarsa ya bashi aure itace barakha uwargidan Rufa,i din."

Saita biyun ita kuma mahaifiyarsace ta aura mashi ita acewanta gara nata na kusa a dama da ita don

anga yaro ya taso za a dauki yarinya abashi mafarin a mallake matashi ke nan .

Ya zamana iya dangin mahaifinsa kecin moriyansa kadai don haka bata yarda ba itama ta dauko diyar

kanwarta daga kaduna ta aura mashi.

Zance dukkansu ba auren soyayya yayi dasu ba aurene na biyayyan iyayye ya kasance da matayen nasa

donshine a yanzu yake son ya auro zabinsa shima.

Katsinawan dikko kunya hareku badai tsoro ba bakatsinen mutum baya tsoron tara iyali donshine yana

da wuya ka samu gidan da baya cike da mata kuma na mutum daya.

"Alh Rufa,i irin matasan nan ne masu son karya da nuna isa gashi dan gaye don gaskiya yana bawa"

rayuwansa hakkinsa daga sutura abinci kamshi har abin hawa bai tauye kansa da hakan ba yana nema yana samu kuma yanawa rayuwa adalci.

Matsalan AR dayane kamar sauran maza yake shima yana dan taba neman mata da sauran tabara na

"matasan zamani amma ba sosai ba don bayayi a cikin jaharshi sai ya fita bariki wajen sana,anshi yake wanam harkan."

Karfe goma zasu zauna da abokan kasuwancinsa na cikin jaha don su bullowa barazanan hahawan mai

"dake addaban da barazana ga sana,ansu yanzu."

Don haka ya shirya tsab ya fito don kiran daya samu daga Alh hamza akan kusan kowa na wajen taron

a lokacin saura su biyune basu hallaraba.

Ya amsa da yanzun nan zan karaso ina hanya saidai kafin su kashe wayan tsakaninsu yaji bakin AR din

na furta subbahanallahi .

Lafiya yake tambayansa da sauri bai samu bashi amsa ba a lokacin sanadiyan ganin hindu da Farida

dake kyatarowa titi da sauri kafin motar ta fita a galon na saman hanyar unguwan nasu.

Hannunsu rike da juna don hindu din ta kasance matsoraciyace sosai a wanan fanin bata son harkan

hayaniya ko dogon motsi wanan halin mama tayi tayi ta rabata dashi ta kasa dole tasa mata ido dashi duk da har yanzu tana kan tsawatawa yar nata lokaci lokaci data kama jiki ga wanan sanyin halin nata.

Garin amsa wayan da suke damunshi dashine har suka bace mashi ya rasa hanyar da yan matan suka

bi wanda yafi kyautata zaton sun shiga wanan islamiyan dake gefen titine.

Dalili haka ya karasa wajen taron a cikin kuncin rai don kuwa ba shakka wanan yarinyar da hijjab ya

"boye rabin halittan Allah a cikinsa itace kalar matar da yake mafalkin ya aura a baya amma iyayye sukai nasu ikon akanshi yake zaune da wa yan nan marasa ma,anan a matsayin matanshi na aure agidansa."

Haka ya karasa wajen wanan meeting din zuciyarshi a cunkushe yana jin kansa wani iri a lokaci daya.

Wayoyinsa na hannu ya kwaso daga motar ya kulle ya soma tako irin na isa da girma na kasaita gami da

"nunawa jama,a yasan kansa a wajen don kuwa kudi sun gimewa shekaru a wajensa."

Wasan da abokinsa ke masa a lokacin ya kasa mayar da martani hakan ya dai samu wuri ya zauna yana

mai daga hannu alaman gaisuwa ga kowa dake wajen lokacin.

Kwarjininsa da tsatinsa kamar kullum sun hana aga laifinsa na tsayar dasu tsawon wasu mintuna a

zaune inda taro ya