Chapter 4 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

mijin nasu.

Wai abin haushi tana juye taliyanba lokacin inna talatu halima ke nan ta fito saye da hijab dinta tana

rufe kofa karan rufo kofan yasa mama din dago kai ta dubeta.

Halima dince tana kokarin rufe kofan ga jakka a hannunta cikin mamaki daya baiyana karara a fuskanta

take fadin.

Halima ina zaki haka ?

Inna halima din ta juyo gareta saiga hawaye a fuskanta tana fadin cikin raunin murya gidan mu zani

yaya ban iya tsayawa ganin wanan bakin cikin da malam ke muna kan Asiya.

Fuskan mama ya sauya lokaci guda tasan hakan ba ko wace mace zata iya daure abin ba don da zafi da

ciwo da takaici cikin rudani tace meyasa zaki tafi gida halima ?

Saida ta kallota kamar zatayi magana sai kuma ta juya ta soma tafiya anyi daidai matan lungun yaya

mijinsu Usman tashigo diban wuta ta riski hakan.

Inna halima na niyar ficewa daga gidan mama ta kamo hijjab dinta nan matar baba usman din take

fadin ke kuwa halima me yayi zafi haka kardai ince tun zancen jiya kike riko har yau ?

"Halima din cikin kuka take fadin nikan yaya gidan mu zani na gaji ,,,,,"

Na gaji zaman kuncin nan da mukeyi a cikin gidan nan wallahi kin daiga iya shegen da suka shigo

yanzu suke muna malam ya koma kamar karamin yaro sai tabara da watsewa da yake biyewa Asiya sunayi a gaban kowa bai ko kunyan idon mu balle na yaranshi ?

Ina gani sai me halima dama ai anayine don aji haushi ko gashi ko din munji idan kin tafi kin nuna mun

damu da abin da sukeyi din ke nan.

Don haka ba inda zaki kibar yayanki in mukai hakkuri watarana sai labari.

Ta dan share hawaye tana fadin haba yaya aida za a daina da tuni an daina din amma ka zauna haka

kana hadiyan hakkuri kullum shekaru fa suna ja yaya ?

Ka zauna kai tsakanin ka da mutum babu wani abu duk haihuwa da zakayi sai dai bisa rantsatsen rabi

ni wallahi dai nagaji hakkurina ya kare hakana gaskiya ?

Matar baba usman ta saki tsuki daga gefe data tsaya tana kallonsu tace kema Dije ki kyaketa ta tafi

mana tunda tace ta gaji.

Ko nice wallahi ba zan iya kumsar wanan kayan takaicin bakin ciki ba tunda ba fini da komai ba a siffa.

Dije bata kula da abinda matar baba Usman din take cewa ba sai fadin da takeyi ki daiyi hakkuri ko don

darajan yayanki halima ?

Cikin fushi inna halima din tace yaya ba zasu hana in kwaci yancina don haka gara inje gida in ina da

rana a gidan nan zai gani ai ?

Shike cutan mu mata sai namiji ya gama saka ka haife hajinnka ya tsiro maka da iskanci in kayi yunkurin

daukan mataki ace wai yaya yaya aibadasu kazo ba anan ka samesu.

"A,a matar yaya hakkuri akeba mutum yanzu idan ta tafi yaran nan dasu da marayu kusan dayane gara"

dai din anyi hakkiurin dama shi muka gada mu mata .

Banga zan iya dauriya irin naki ba yaya ko a kalli mace aga mace takai mace gidan nan kaf kowa yasan

kece abin kallo.

Amma lokaci guda an mayar dake da malam kamar Annabi da kafiri kiri kiri kowa ya kasa cetoki ga

hakan har yanzu abin nima ya soma shafana nikan gida nayi wallahi.

To shike nan tunda kin kasa fahintar me nake fada maki danayi hakkuri na zauna a hakan ba ina cikin

yarana ina basu tarbiyan daya dace in basu ba ban bar wata ta basu tarbiyan da bai dace ba ai.

Ni yanzu inda sabo na saba da hakan gidan nan wani abin don in gani za a fito fili ayishi a gabana don a

tura min bakin ciki in mutu tunda naki kaucewan da akeso inyi.

Nasan ko nayi hakkuri ranan da auren ya kare ba wani tsimi dole in bar gidan nan idan kuma da rabon a

koma daidai sai kiga wata rana kamar ba ayi ba.

Nikan ba dani ba wallahi tsohuwar mace tazo tana min kilaki a mayar dani wata yar gadin gida kawai

nina tafi don nayi niya.

Kyaleta dije tunda tayi niya don da zataji wanan maganan da kika bata a yanzu ya isheta dubawa tayi

nazari a kanshi.

Wata kishiyace zata tsaya tana bawa kishiya hakkuri haka har da shawara a yanzu ?

Wanan zancen da matar baba usman tayi yasa mama bata kara magana ba ita kuma tasa kai ta fice

daga gidan tana sharan kwala a idanunta.

Kin gani Allah ba azzalumin kowa bane ai ta dauka iya kanki abin zai tsaya da farko aida ita aka hada

kai ana cusguna maki yanzu kuma data fahinci amfani akayi da ita a cinma manufa abin ya soma damunta kuma

Matar baba usman din dake diban wuta take wanan maganan cikin takaici ta dago tacigaba da fadin ai

nan cewa suke baki da zuciya an koreki da hali kimki fita.

Itama Asiya din ta jira nata na tafe ai indai namijine na fahinci mazam gidan nan yanzu in dai baka iya

cin mutunci da tonon asiri ba baku zaman lafiya dasu a gidan nan.

Mama kan wani iri taji ta nisa tana fadin Allah ya kyauta ni dai banwa mutum sheri idan yai min kuma

alhakin hakan ba zai barshi ba insha Allahu.

Sa masu ido kawai tsakaninsune reshene ya juye da mujiya aike suka so hakan ya kasance a kanki bai

samu ba yanzu ta waiwayota shine ta kasa hakkurin hakan ko ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/14, 9:05 PM] Zainab Idris Makawa Writer:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Ya kasance ita kadai a gidan bayan fitan halima din da umma Rakiya tayi tunane kala kala lokaci guda

sam bataga laifin abokiyar zaman nata ba kan fitan nata a yau .

Itama tauyewane da Rashin galihu don tasan kota fita sai andawo da ita idan ba auren ya kare ba

tsakaninsu shine kadai zaisa yan uwarta su barta ta zauna gida.

Donshi take faman hadiyan hakkuri tana cinjewa don hakane bata ga laifin ita ummah halima ba din

kan fitan nata.

Karfe daya da rabi ya shigo gidan da kayan cefane a leda ya kawowa halima din don sai yamma zata

fita girki girkin da sunanshi girki kadai ba wani moriya a cikinshi.

Tana jinshi ya tsaya tsakar gida yana kwalawa halima din kira kafin yaja tsuki ya soma fada da mai

bakin yawon tsiya kawai ko ina tashiga.

Ita dai bata leko ba balle ta tanka mashi saima gyara kwanciya da tayi kusa da yarta hakana yasa kai

yafice daga gidan inda tafi kyautata zaton ya tafine duba inna halima din a cikin gida inda yasan tafi zuwa.

Sam.bai kawo haliman zata iya daukan wanan matakin ba data dauka a tsamaninshi ta dawo a lokacin

yasa ya shigo ya gani ko ta gaba girkin a lokacin.

Saidai yana sako kai yayi arba da ledojinshi nam inda ya barsu har rana yazo yabi ta kansu ya tafi don

faduwa duk suna a wajen aje kuda sun gama kwadansu sun barsu wajen.

Cikin mamaki ya karaso ya soma fadin haukan banza da wofi kawai ina halima din tun dazun baki

dauke kayan nan wajen nan ba me kike nufine da hakan ni za a kawowa iya shege kuma yau ?

Halima fa ya fada yana kallon kofan dakinta dake a saye yaran da suka ahigo sun hakada sunyi abinda

zasuyi sun fice zuwa islamiya.

Shirun da yajine yasa ya karasa takawa ya tura kofan kafin ya nufi kofan mama yana fadin dije ke dije

ko baki cikine muryanshi da yake dagawa yasasu tashi ita da yarta ta amsa da alaman barci kafin ta mike ta fito.

Yana tsaye a kofa cikin fusata yabi fuskanta da kallo yana fadin wanan wani urin shashancin banzane

tun daxun na shigo da cefane an barshi a nan wullakance waje.

Ina halima take ya koma tambaya tace bata dawo bane ta jefa mashi tambayan ita yace daga ina tayi

shiru yana sauke mata duba cikin mamaki ina tajene tace kila tana cikin gida ko ?

Banjin hakan toke meye na shigewa daki ki kwanta haka tun safe tun fa daya na kawo cefanan nan

yana gurin nan ajiye ?

Bansan ina ta nufa ba ta kara bashi amsa lokacin ne yarta ta taso tana kuka ta rungume mahaifiyar

nata da hannu biyu gwaunin tausayi bakon dauro din ya fito ko ina a jikinta yamafi na yarancan dake asibiti kwance muni a jikinta ga baki yayi ja jajir alaman kukan da takeyi abin ke damunta lokacin.

Salma meye kin falka bari na dauko maki ruwa kisha kinji ta fada da sautin tausayi a muryanta dan

duban yarinyar yayi yaga yadda take wahala da sauri ya kawar da kai ga kallonsu.

Gwaggo Balaraba ce ta fadon lungun don duba yar dan uwan nata ta samesu tsaye haka tayi sallama

tana fadin ashe kana gida yaya suka gaisa take tambayanshi masu jiki yace sunji dama suna can.

"Ta dora da fadin nima nazone in duba yar nan tana kallon salma din take fadin anyi sa,a duk sun karasa"

fitowa ashe sannu kinji sallama amma ya kamata ace an bata ko dan wani magani da zai kashe mata zafin jikin nata yaya ?

Bansan haka yayi mata ba ai saina fita zan riko mata magani cefane fa nakawo na rasa ina Halima ta

shiga a garin nan haka tun dazun ?

Halima kuma ina ance tun dazun ta kwasa ta fita da kuka gidan nan kan abubuwan da ake mata sunyi

yawa bata iya hakkurin hakan ita ?

Saida gwaggo tagama bayani ya dubota yace ai ta tafi to shike nan idan haka yafi mata alheri take gani

har ya juya kamar zai tafi sai kuma ya juyo yana fadin.

Ke kuma ba zaki gyara ba to abarshi a wajen ya lalace don Allah haba yaya mu rika yiwa kan mu adalci

kada mu manta gobe na tafe garemu fa ?

"Gaskiya yaya ka gyara dabi,un nan daka dauko yanzu a gidanka yaran nan girma sukeyi suna fahintar"

abindake wakana kuma ga uwayensu ?

Fada kikazo min ashe ni gaskiya nake fadama yaya gaban kowa kuma zan iya maimaita abinda na fada

yanzu ka gyara kaje ka dawo da matarka don Allah.

Wa yan nan yaran data fita ta bari wazai rike maka su yaya dakata da ita yayi yana fadin kinga kin

isheni Laraba.

Kinga idan ke zaki je kiyo bikonta ban hanaki ba ai bani na koreta ba bare a matsa min tasan tana da

yaran tasa kai ta fita ta barsu.

Yaja tsaki ya juya bar masu gidan ta daga harshe tana fadin ato mutum dai yaji tsoron Allah kada mace

ta jashi wuta.

Ke Dije fito ki daure ki gyara kayan nan karsu lalace don Allah ki barsu nasan ko can asibitin indai

Asiyace ba dadinta zai ji ba tunda ba hankaline da ita ba.

Daga daki take fadin zan fito in gyara ai ina bawa Salma dan kunu ne tasha in fito sai hakkuri dije ki

kara daure don Allah ko don yaran nan mata dake gabanki .

Ana makine ki fice ki barsu aji dadin bautar maki dasu yadda ake so amma kina kusa ana ganin idon ki

wani abin zai rage ba kamar baki kusa ba .

Ta dai dan tausheta tare da haska mata hanya sukai sallama ta koma bangarenta ta fito tana gyara

kitchen don dora wutan abinci don wanan kan ya zama na dare ke nan garesu.

Aiki takeyi zuciyanta ba dadi da walwala a lokacin kasatuwar tafiyan abokiyar zaman nata halima koba

komai halima tafi Asiya saukin rayuwa .

Don halima bata da rainin wayau ko izzigili da rashin mutunci ga mutum barta dai da tsegumi da kwadai

irin nata duk inda taga ci tana manne a wajen saita lasa koma maye hankalinta ke kwantawa.

Don ko wanan cafanen da takarba nata take aiki a kansa na dole tasan maigidan nasu yayo shine da

tsigar lalashi a gareta tunda taga har su tantakwahine irin mai kitse din nan.

Yayo hakane da niyar jifan tsuntsu biyu lokaci guda ya dadawa Asiya dake asibiti taga donta akai hakan

nan kuma halima din ta dauka cewa don yana dakintane yayo haka don taci ya samu ya huce a gareta a cikin sauki.

Koda yaran suka dawo sun kamawa mahaifiyarsu aikin duk da Hindu itace babba a dakin a yanzu Farida

tafita zafin nama sosai don ita hindu din tanasa kiuya da izza da shagwaba a lamarinta.

Sai gidan gaba daya ya koma masu ba dadi a ranan idan ka cire shi malam Auwal din dake shaninsa

cikin walwala ta kammala ta aje na asibitin ke nan ta shiga daki tana zaune da yaranta taji muryan Asiya a gidan.

Ta dan jima kafin ta mike ta sameta abinda ya bata mamaki bai wuce girsanta da tayi a dakin tana yan

lakace lakacenmu na mata ba tankar wace zata amshi miji a lokacin.

Itama ta tsargu da ganin da kishiyar tayi mata saidai ta wayance tana fadin au yayace yanzu nake fadi a

raina ko bakiji shigowana bane gidan.

Naji wallahi ina sallah ne aikin ya kaimu darene bansan da nice zanyi ba aidana dora da wuri yaya masu

jikin kuma ta tambaya.

Da dama wallahi yanzuma na dawone indan watsa ruwa in dan kara kimtsa dakin in koma na barsu

dasu umma a can .

Allah ya sauwaka tayi mata ta juya zata tafi suka hade da maigidan daya fito daga dakinshi yana kamshi

shima a take zuciyarta ya shiga zarginsu inda da sauri ta kawar da wanan zaton a zuciyarta.

Wani kallo na tsana suka jefi juna dashi lokaci guda inda ya shige dakin ita kuma ta koma nata wajen

tana saka kafa take jin dariyansu tare da rufo kofansu a lokacin.

Fafffffa kirjin ta ke harbawa lokaci guda inda takw jin kamar zuciyar nata zai fashe a lokacin don

azaban kishi da bakin ciki da zuciyar ke dauka lokaci guda.

Sun jima a cikin dakin kafin kafin taji budewansu suka fito shine ya dauki kayan abuncin data aje a kofan

dakinta din na asibitin suka fita tare daga gidan.

Ya Allah kaiwa mareniyarka gata Allah iya abinda bakinta ya iya furtawa a lokacin ke nan ta fashe da

kukan bakin ciki da takaici meke faruwa da itane haka ?

Wanan cin fuskan da ake mata ya soma yawa da wuce wuri ko rantsuwa tayi bata kaffara cewa sun

kansance a tarene a lokacin.

Hakan ya zama zalunta ita da girki wata da kwanciya da miji duk da suna halin jinya asibiti amma sai

sun dawo sun ci zalinta a gida wani irin jarabane haka kiri kiri a wanan lokacin baiko gudun yaransu su gano me sukayi a lokacin ?

Don yaran yanzu ba irin na dabane da basu fahintar komai na yanzu sai yaro ya zauna ya fassara abinda

kai babba tunanenka baikai can ba.

Tasan ba zai dawo ba ke nan a ranan tunda taji yana fadawa hindatu data saya gidan idan sun gama da

zai fita haka na nufin ko ranan asibiti zai kwana ke nan wajensu duk daga uwarsu ga mahaifiyarta duk tare da yaran amma sai ya nuna cewa ya damu dasu a fili kowa ya gani.

Washegari ta fito ta sallami yara zuwa makaranta ta gyara gida ta koma ta kwanta da yarta a dakin

bata da niyar girki a ranan ta dai tanadi abinda yara zasuci idan sun dawo kazo ta susuka ta gyara ta wanke ta kife da kwando ta daka kuli kuli dasu magi ta yanka albasa duk ta aje kafin ta shige dakin taja

kofan gida.

Kodaya dawo da safe din bai damu don bai sameta a tsakar gida ba har ya shirya ya fita sai rana ya

dawo da cefane don a girka ya soma nemanta.

Labulen dakin ya daga daga kofa yana fadin ke Dije ga cafene ki girka ayi sauri na samu in kai masu

cikin lokaci .

Tana a yadda take kwance bata dago ba balle ta nuna tasan yana magana a lokacin wanda shi kanshi

hakan ya bashi mamaki matuka don ba halinta bane hakan.

Bakiji bane dake nake magana ga cefane nace ki girka abinci dashi in samu inkai masu asibiti bata bari

ya karasa ba ta soma fadin badai wanan dijen ba ko ?

Don naga kana son mayar dani sakarai a gidan nan zan dauki komai da kake min malam don darajan

aure da diyana amma banda wulakanci da rainin wayau ?

Abinka ya wuce musali malam har ace inyi girki amma ka koma ka dauko macen dake asibiti tana jinya

kazo nan a gabana a gabab kowa ku shige daki da ita.

Amma dai ba karuwa na dauko ba matatace na shige dakin da ita ko balle kice zaki hanani hakan

kwarai kuwa matarkace malam .

Shiya yanzuma naga aika kai mata cefanen ta girka maka tunda dama laluran yaranta girkin zai tare to

gara tazo ta girka din da kanta zaifi.

Zancen banza zancen wofi kawai zaki hana min jin dadi da matanane har abin ashe yakai haka kuma

wallahi baki isa ba Dije ko an haramta min in sakaya da matanane inji ?

Kaje ka sakaya malam amma ka sani idan an shiga hakkina Allah yana gani ta fada Allah ya isa ke nan

kikeja min dije a hankali manira ta mike ta fito ta nufi cikin gida kai tsaye.

Baifi yan mintuna ba sukaji muryan baba Ali a bayansu yana fadin kai maraya meye haka kakeyi kuma

meke faruwa a nan haka wai ?

Kai kenan baka ganin kokarin yarinyar nan a gidan nan baka duban kawaicinta ga kowa daya shafeka

mrya haukankane wai ?

Ka natsu ka dawo cikin hankalinka ka daina wanan shirmen banzan da kakeyi kan mace duk bakin cikin

da kake kumsawa yarinyar nan a kunnena yake sulaiman.

Nasan komai dake faruwa a gidan nan ido nasaka maku daga kai har ita amma ita Dije din taki samuna

ta fada min tsakanin ku yadda yan uwata