Chapter 3 of 46

FUREN BADO Gidan da Ya Karye By ZAINAB IDRIS

ita bata da gadon maita ko tsafi balle ta mutu ta dawo duniya don

kwadayi .

Wanan abin yanawa mama ciwo takai karan inna Asiya har wajen tsohon gidan nasu bata daina mata

wanan kazafin ba hakan ya soma saka damuwa a zuciyar mama a gidan.

Tun wanan lokacin kuma gaba daya gidsn babu armashi a cikinsa don dan zaman lafiya dake akwai

yana neman shima ya gushe a yanzu tsakaninsu .

Don sai a wuni zurr ba maicewa dan uwa kala a cikisu a yadda ta kula ita kanta talatu baki biyu gareta

tana tare da inna asiya a gabata kuma ta nuna mata ai ita ba a wanan hadin kanbda ita.

Idan kin cire shi maigidan dakw cikin walwalanshi a lokacin wanda ko a kwalar riganshi don bai daki

lamarinsu a bakin komai ba.

A yanzu kam inna Asiya ta gama kamo kan maigidan don ba karamar yar duniya bace sabanin mama da

inna talatu da suke tashin kauyesu biyun .

Don haka inna Asiyace lamba taran gidan mai fada aji bayan baba don ko yaran gidan a yanzu duk

shakata sukeyi don take zatai maka sheri a wajen baba kuma ya hau ya zauna ya yanke hukuncin da yaso kan zancen don ya dadada mata rai.

Ranan ma fushi ya tsira da mama din na ba gaira ba dalili don ba zatace ga abinda tayi mashi ba koda

take fada mai zancen ciwon yarta salma sai cewa yayi ai salma yartane takaita asibiti mana.

Yanzu gaba daya baba din ya birkice masu a gidan har inna Asiya din nacine kawai irin na wasu mata ba

gane komai takeyi a wajen mijin nasu ba itama sai taurin rai kawai kada ace gashi.

Amma na mama din yafi yawa a yanzu don gaba daya nunawa yakeyi daga ita har yayanta kamar sun

isheshi a gidan zaman dole kawai yakeyi dasu.

Dole inna ta shirya ta fita da yarta don kaita asibiti a wajen ta hango samarin gidan da suka dawo hutu

a zaune suka fara gaida ita.

Kamal din ke tambaya sai ina haka da yamman nan mama ta soma fadin kemis tayi takai salma ta soma

bashi labarin rashin lafiyan yarinyar.

Kace ta koma gida ta bari mukai yar a dubata Ahmad ya fada yake fada mata tare da karban yarinyar a

hannunta ya rike ta babur din baba Audu da yake hawa idan yana gari yana wajensu tun bayan dawowansu hutu din shi suka hau don kai yarinyar a dubata.

Allah sarki ba zance wanan tausayin tare da mutuntawa da samarin gidan ke nunawa mama din shike

kara tunzura inna Asiya da ita .

Don ita so take da karfi da yaji kowa a gidan mama ta koma kashi ko abin kyama a daina kulata gaba

daya daga ita har yaranta a gidan.

Tayi kuli iri iri a wajen gagga gaggan gidan da take ganin zata shawo kai a dai kula ita mama din amma

abin yaki to mama ta kasance mara ruwa da tsaki ita.

Don ko yarone karami zata fara gaidashi kafin ma ya gaida ita din kinga kuwa ko waye baiga abin fada

da mutum ba a nan shiyasa zaman lafiya yake da dadi ga mutum dan gudun irin hakan.

Sunkai yarinyar an dubata suka dawo da ita tare da sayayya mai yawa irin na yara ai inna Asiya taji

kamar ta kama mama da duka a ranan don kishi.

Ita a son samunta har kowa a gidan ya koma a hannunta ga baki daya amma saitaga tana shiri kamar

mama tana walwale mata shirin natane ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"[11/14, 2:45 PM] Mmn Bibo:  FUREN BADO "

ZAINAB IDRIS MAKAWA

"BISSIMILLAHI RAHAMMANIN RAHIM,,,,,,,"

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN

"2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,"

"YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A"

"WAJENKA , , , , , ,"

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA

"YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,"

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI 500

2- FUREN JUJI 500

3- TARKO 500

4- BAMU KADAI BANE... 500

1- SARAUTAR MATA500

2- MURICCIN KAN DUTSE... 500

3- BAHAGON RAYUWA 500

4- KANIN AJALI 500

5- LOKACIN MUKE 500

6- MIJIN BUZUWA 500

7- SARKA...500

8- ABU CIKIN DUHU 500

9- ANA DARA... 500

10- KARAN DAFI... 500

11- TUMFAFIYA... 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI.. 1000

13- JA YA FADO JA YA... 1000

14- MURFIN JALLO 1000

15_ HAWAYEN KADA

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Ba abinda yaciwa mama dije rai sai yadda yarinyar nan ta wahala don abin ya koma mata kyanda a

karshe ance komai da sanadinshi.

Sanadin tsoro yajawa yarinya ciwo sosai don ba karamin jinya tayi a lokacin ba da hankali ya daga

musanman na uwarta da take kwanan wahala da ita duk dare.

Badan yaran nan ba ta tabbatar da sai ta rasa Salma din a lokacin sai gashi yarane kana suka taimaka

mata da sunan zumunta suka dauki dawainiyar yarinyar har Allah ya soma bata lafiya.

Tayi magana da maigidan abinda yayi bai kyauta ba sai cewa yayi ai donshi yaran sukayi tunda diyan

yan uwanshine su ita kuma yarinya jininsune ai ?

Har sai abin yaso ya kawo masu matsala a tsakaninsu inda ta nuna ita dai ta gaji da wanan zaman da ba

dubaiya a tsakani.

Ta dauka zata iya jure duk wani bacin rai da zai nuna mata game da zaman takewan nasu zata iya bashi

lokaci ko Allah zaisa ya gane su daidaita kamar yadda wasu mata kan jeraba hakan .

Amma akan ciwon nan na yarta saita fahinci abon nasa har da gaiya da cin zarafi a cikinsa tunda abu

yakai ya fara nuna bambanci a fili ksn diyan cikinshi haka.

Don kuwa ciwon daga cikin gida ya fara har ya shigo lungun nasu kowa yasan yadda wanan ciwon yake

da zumunci duk inda yara suke idan ba Allah ya gyara ba idan ya shigo gida sai ya ziyarcesu.

Sai gashi ya tsaya tsakar gida yayi wanan fadan da mama washe gari Allah ya jerabi yaran inna Asiya da

wanan laluran .

Tunda farar safiya tasahi gaba kan dole yakaisu asibiti kada yaiwa diyanta illa don gashi yana ta kashe

yara a cikin gari.

Jikina rawa ya kwashi yaran zuwa asibiti sai gashi ya dawo yana fadin an basu gado don gaba daya ya

fitowa babban a jikinshi.

Kamar yadda yasowa salma illa haka shima babban ya kamashi dumu dumu a jikinshi sai ihu da neman

agaji sukeyi tankar dai yadda yaiwa ita na farkon .

Sai rawan jiki yakeyi yana neman kudi don kai yaran asibiti inda yake fadin yabada wasu kaya ba a

kawo kudinsu ba ga kuma wanan laluran daya taso.

Harda sayo abinci lafiyayye yayi ya kawo a dafa don akaiwa masu asibitin abincin ita dai Dije sai kallon

ikon Allah takeyi daga kofanta inda tafito da yarta don iska ya dan kada a jikin nata sosai.

Yaje ya dawo ya samu inna talatu bata karasa ba ya soma fada da ita akan ta faye sanyi jiki koso take

suji yunwa kuma bayan laluran ciwon da suke ciki.

Ya shiga daki can ya fito yana jan tsuki kafin ya juya wajen Dije dakewa yarta fitara yana fadin wai Dije

ba magana nakeyi bane ?

Baki tashi ki saka hannu a girkin nan ayi a gama kinsan halin talatu da sanyi jiki ai sai ta kaimu har

magariba bata kare aikin nan ba.

Yi tayi tankar bata jishi ba a lokacin saboda takaici saida ya kara fadin wai badake nake bane nace ki

tashi ki saka hannu ga aikin nan a samu akarasa shi a cikin lokaci mana.

A cikin takaici ta dago ta soma fadin amma ka ganni da ya ina fama ko kayi min adalci mana malam

don Allah dai ?

Toooo kice min bakin halinkine ya motsa kina ciki bakin ciki da takaicin ashe ban sani ba ina su yan

uwanta basu iya mata fitaranne su ?

Ki tashi ki kama aikin anyi saurin gamawa ko suna gidan nan ba zan taimaka ba tunda baka son hakan a

kan mu ba.

Balle wani saurine talatu batayi ba bayan wanan da takeyi a yanzu kyaleshi yaya don Allah kila so yake

in fada a murhun nima mu dahu tare da abincin don taji dadin kaiwa yar gwal dinshi.

Yanzu kan nagane me kukw nufi bakin ciki da kishine ashe to bari kiji sai dai kuwa ku mutu dashi a

gidan nan indai nine a yanzu duk wace zata iya ta zauna wace taga bata iya zama hanya ai a bude yake ban zaunar da ita dole ba gidan nan.

Ko kuwa kada in kaisu asibiti a dubasu shine dai bakin cikin ku ko nakai su jamil asibiti bankai ita wanan

ba kaita da yan uwana sukayi aiba yan uwanku bane suka kaita ?

Kaidai ka sani malam banbanci kuma kaitayi kunya gareka don kaine zaka taso a shaye bari daya ranan

lahira kowa yasan meka aikata a duniya gidanka ?

Eh dama ance ba komai wajen bakar mace gajera sai sheri da bakar magana na yarda ke talatu banda

aure kaddarace ke baki tunanen yadda kika shigo gidana don Allah ?

Dana shigo gidan naka mena gane banda tarin bakin ciki da takaici da kake kumsawa mutane a kullum

saukin abindai kowa a wajenka banzane har wanda kake kurin kana ji dasu din .

Zakice dije bata gidan a lokacin asalima ta mayar da hankaline kan yarta datake bawa ruwan magani a

lokacin .

Ta fahinci dalilin fadan nasu a lokacin don ita talatu taji haushine kan cewa da yayi bata da lakka

aikima sai an taimaka mata ya fada mata hakane kuma don yana saurin zuwa asibiti ya gyarawa Asiya da yan uwanta rai a lokacin.

Shigowan matan wani lungu gidan nasu suna tambayan meke faruwa zarginta akan talatu ya zama

gaskiya .

Lokacin da talatu ke fadin haba don Allah kan mace daya da yaranta saika rufe ido kana nema kaciwa

kowa mutunci akansu don kawai kana tsoronta ?

Har yakai waje zai fita ya juyo a ciki kunya yana fadin uban tsoro nace abinda yafi tsoro ma zanyi don

in gyarawa Asiya.

Kuje ku mutu yan bakin ciki kada Allah yasa ku dafa abincin marasa mutuncin mutane kawai ya fada ya

fita.

Haba kuko yar uwarku na asibiti da yaro har ku zauna fada akan dafuwan da za akai masu kuma ?

Shiya mayar da zancen fada ai don baizo da lalama ba ta kwashe abinda ya faru ta fada masu indai

hakane shine baida gaskiya balle nasan zai iya aikata hakan sarai.

Yanzu tun bayan maganin da yaran nan suka saiwa yarinyar nan bai sai mata komai ba take tambaya

ina zai saye ba kunya yanzu yazo yana rawan kafa kan yayan mowan gida.

A hankali ta dago kai wanda duk maganan da ake sai a lokacin mama ta samu magana take fadin ai

Allah ya bata lafiya su kuma Allah ya saka masu da alheri.

Kowa yai ta fadan zancenshi tunda ba idon inna Asiya a wajen har suka gaji suka watse don kamsu

dama aiyukansu suka bari suka zo gulma jin inda hayaniya yake fitowa din.

Sai gwaggo Laraba itace taje ta aika aka sayowa Salma kayan marmari su lemo kankana da ayaba ta

aiko dashi abawa salma.

Koba komai yadda yan uwan da yawa a gidan suke nuna kauna ga diyanta hakan yanawa mama dadi a

rai har takan ji dadin tausan zuciyarta akan abubuwan da take gani a gidan wani lokaci.

"Anyi sa,a yarinyar tasha lemo da kankana sosai wanda hakan kamar ya kara mata kuzarine don har"

zama tayi tana bin yan uwa da kallo saidai ba magana wanda hakan yake ba mama din tsoro ga zafin jiki da ciwon kesa yaron wanda mama din take jin hakan har cikin ranta.

"Addu,anta ga Allah shine kamar ko wace uwa da danta ya kamu da wanan mugun ciwon shine kada"

Allah yasa ya nakasa mata ya don inna asiya ta fara furta hakan gareta kafin nata ya sameta a dare daya.

Inda aka wayi gari yaranta dukka ukku sun tashi da wanan laluran hankali tashe a ranan ta hana baba

fita kan akai mata yara a duba kada su salwanta mata a daki.

Inda ba kunya baba din ya kwashesu sai asibiti inda aka kwatar da biyu daya basai an kwantar ba shine

baba yake wanan masifan da matanshi a yanzu kan hakan.

Da dare kuma su gwaggo Laraba da amaryansu sun shigo duba yarinyar da jiki take fadin daga nan

asibiti zasu su duba wa yan can dake kwance din.

Don sauran sun tafi tunda yamma dubosu basu dawo ba yanzu haka nan su mama ke fadin a gaishesu

taba da wani magani abaiwa yarinyar a shafa mata a jiki insha Allahy zasu fito su bi iska.

Suna fita batayi sanya ba ta soma durawa yarinyar maganin tana sha muryan inna ce taji daga bayanta

tana fadin yaya kinji munafukan matan gidan nan sun kwashi jiki zuwa asibiti wai ?

To meye don sunje asibiti komu ai dole muje mu dubasu yau gareka gobe ga dan uwa naso saida safe

muyi sammako sai yaran nan su zauna gida har mu dawo.

To shike nan amma badon malam zan tafi dubiyan nan ba tunda yace bakin ciki mukeyi da yaranshi

halima ina son ki da hakkuri shifa komai na duniyan nan dan hakkurine .

Duk yadda taso suyi zance kan abinda ya faru ranan mama ta kaucewa hakan don sanin hali taki yarda

maganan yayi nisa don tasan halin inna halima da abin duniya za a rudeta ta juya zancen wata rana.

Washegari bayan sun idar da sallah suka fita zuwa asibitin don dubo yaran duk da sun samu yaron a

cikin wani hali haka bai hana inna Asiya nuna halinta ba .

"Don suna cewa ya masu jikin ta soma fadin jikin kan yayi sauki ai duk da ba,aso su mike haka ba Allah"

yayi sun tashi din .

To Allah ya sauwaka inji mama ta mike ta dan duba yaran bata dai karasa kusa dasu ba balle kuma ace

ta shafa masu wani abin tasan sherin inna kamar yunwar cikinta.

Duk da tana son fada masu a dinga basu zuma su lasa don ido da kunne amma taja bakinta tayi shiru

daga fadin hakan garesu.

Sukai masu sallama suka kamo hanyar gida don yara su samu zuwa makaranta inda suka samu yaran

sun shirya suna jiran dawowansu.

Tana daki tana mikawa yaran kudin tara taji muryan inna Asiya zakice tare suka dawo da ita tashigo

gidan tana fadin .

Ato in ma mutum ya buga sakkone yaje ganin kwam zaigani kuwa don miji dai ina can tare dashi

asibitin har yayan mu saidai bakin ciki ya kashe mutum wallahi.

Asibiti ainba gidan buki bane ko wani gidan dadi kun kwana asibiti amma a zaune ko inma wani abin

aka fada maki kika dawo dashi wallahi muna daidai.

Ohh anyi abin kenan kike tsamanin an fada min ai ban zata ba halima ban zaci har dake wajen nuna

bakin ciki akan yaran nan ba ?

Mama meya faru kuma ba yanzu kuka dawo daga asibitin ba anyi wani abin kuma a can ne yarta

babban take tambayan Dije din dake kada kai cikin takaici.

Mama ta dago tana fadin dauke kannenki ku tafi kada ku makara ana tashi kuma ku dawo gidan nan

kada ku tsaya ko ina don Allah.

Yadda uwar ta fada haka sukayi basu tsaya sauraren fadan Asiya din ba saidai suna fita tana tsaye tana

fuskantar dakin mahaifiyar nasu suke gaisheta kamar bata san sunayi ba a lokacin tayi banza dasu a wajen.

Suka fice ransu a bace don sunsan karshe laifin gun mahaifiyarsu zai koma saukin abin mahaifinsu da

baya gida lokacin.

Don da yana nan yanzune zai karbe zancen ya zamo nashi wanan ba bakon abu bane ko yara sunsan

da hakan kuma sun san saboda inna Asiya yake hakan.

A waje suka hadu dashi zai shigo gidan suke gaidashi ya amsa a dakile ya shige cikin gida kai tsaye ba

tare daya tsaya kulasu ba.

Ji yadda baba ke sauri don Allah kamar zai kife yanzu haka fadan nan ba zai kare ba don da alama tun

jiya akeyinshi gidan nan ?

Banjin mama zata tsaya kulasu ai babban hundatu ta fadawa yar uwarta a can cikin gida kuwa yana

shiga ya soma fadin yaya yaya banace dake kada ki tsaya wanan maganan ba idan kinzo ?

"Watau bakiji maganata ba ke nan ta juya gareshi tana fadin abin,ne da takaici malam har da yaro baida"

lafiya sai an nunawa mutum bakin ciki akai ?

Nazo ina magana kuma ita halima tunda tafi kowa baki shine ta saye zancen to zan iya dako waye a

cikin ku don ba tsoro nake ji ba idan mutum ya isa yasa a dawo da yaran gida yau din nan.

Na daice ki bar wanan zancen tunda bada kudin wani nakai yarana asibiti ba balle kuma banga daman

kai salma din ba sai ayi abinda za ayi din mugani.

Har suka gama ba wanda ya koma kansu a lokacin gyaran dakin da yayi kaca kaca don yaran da suka

bata ta fara gyaran dakin nata tana jinsu sama sama har ta fito waje ta gyara duk inda taga ya dace ta gyara din ta koma kitchen don dora ruwan wanka ta watsa.

Tunda salma tayi barci a lokacin tana jin suna yan dararakunsu a dakin wanda bai zama bakon abu a

wajenta ba yanzu saidai taji ta shanye ba don rai baya baci ba kuma ?

Don hakan da daci kaji miji na dariya da kishiya a kullum kaiko sai gani sai hange a tsakanin ku sai kuma

"sa,a idan ba idon kishiya a kusa."

A dadafe dai ta samu ta karasa abinda takeyi din ta kashe wutan ta dauki ruwan a daidai lokacin ya fito

daga dakin na Asiya dauke da kula mai marfi da alama a waje zasu sayo abinci dashi.

Wani kallo ya watsa mata na tsana wanda hakan ya tsaya mata a rai har take jin wani iri kamar zata

fadi a lokacin.

Cikin amincewan ubangiji ta samu tagama shiri har ta dan dafawa yara taliya idan sun dawo suci don

taga halima bata da niyar dora girki a lokacin.

Ba sai an fada ba itama tana daki tana hadiyan nata bakin cikin ke nan a lokacin duk da nata da dan

dama tunda wani lokaci sukayi hakan dashi a dara a danyi wasa sama sama.

Amma ita a yanzu sai tace kusan tun haihuwan wanan yar nata salma tana da cikinta abubuwa suka

juya mata tsakaninta da maigidan wanda ba zatace ga dalilin hakan ba kai tsaye.

Illa iyaka dai da sannu ya tsiro mata wanan halin na tsana tsakaninsu wanda a yanzu gidan kaf har waje

kowa yasan zaman hakkuri takeyi kawai a gidan babu dadin rai tsakaninta da