Follow us on social media
Showing 6001 words to 9000 words out of 50786 words
kamar ya harbeshi ya huta
Ogansu kuwa k'ok'awa suka cigaba da yi da Samha Akram ya daka mishi wani irin mugun tsawa yana "ka kyalleta nace"
Ogansu d'agowa yayi yana kallon Akram cikin tsananin mamaki dan bai tab'a mishi haka ba adai dai lokacin da wayar killer ke ringing yana d'agawa yace OK OK
Da sauri ya kalli ogansu da idonsa ya Rine sabida b'acin rai yace "Boss fire ne ya kirani yace yan sanda sun taho inaga makota ne suka kirasu sabida sun ji Harbin bindiga"
Ogansu da sauri ya duro daga kan gadon ya d'auki bindingarsa yace "hurryy up let's live park all our things"
Da sauri su killer suka ringa d'aukar bindigarsu suna yin waje bayan ogansu ya d'auki brief case da akwatin gold d'in yayi waje dukansu da sauri suka ringa ficewa daga d'akin Akram ne a k'arshe sai da yaje bakin k'ofa ya juyo ya zubawa Samha ido dake wani irin kuka kamar ranta zai fita tana kiran mummy
Shima hawaye ne suka k'ara zubo mishi a lokacin data ga Hajiya Nafeesa kwance cikin jini yace "Allah ya jikanki da rahama kanena kuyi hakuri"
Atare suka d'ago suna kallonshi kafin su kai ga tunanin wani Abu ya fice daga d'akin da sauri.......
[2:33PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫
*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝
*A heart touching story*
庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 3*
Da Sauri su lion suka fice daga gidan suka hau motar suka bar Layin aguje
da mota biyu suka je tafiya sukayi mai Nisan gaske kafin su yanki wani daji sukayi ta kutsawa ciki babu gidaje ko d'aya sai bishiyu suke ta wucewa sai da suka kusa minti 20 kafin su isa wani katon gida dake tsakiyar dajin
Cikin zafin nama black da fire suka fito suka bud'e gate d'in gidan
Suke shige da motarsu tunda suka taho babu Wanda yayi magana acikinsu in banda ogansu Dake ta zuba tsaki akai akai
Akram kuwa yana daga bayan motar kansa sai Sara mishi yake har yanzu yana jin ihu da kukansu Samha a kunensa tundazu da suka taho yake hango hajiya Nafeesa a idonsa
Matar da ta tsaya tsayin daka Dan kar wani Abu ya sami 'ya'yanta matar da ta sadaukar da rayuwarta sabida 'ya'yanta take ya ringa hango yanda taringa tsalle tana dambe dasu lion da iya k'arfinta akan kar a ketawa 'ya'yanta haddi sai gashi nan a cikin mintuna da basu wuce Ashirin ba sai gata a kwance a cikin jini rai yayi halinsa lailai duniya ba ma tabbata bace rai ba'a bakin komai yake ba tabbas lokaci yayi daya kamata dubun Alhaji Bala ya cika
Lokaci yayi da mutane ya kamata su San irin sana'ar da yake yi insha Allahu bazai bari ya kuma fita wani operation d'in batare da asirinsa ya Tonu ba da wanan tunanin suka k'araso gidan bayan anyi parking ya fito daga cikin motar bayan dukansu sun shige ciki
A k'aton Palon da babu komai sai rug carpet da one seater guda d'aya suka zazzauna inda ogansu shi kuma ya zauna akan kujerar yana wani muzurai yana karkad'a k'afa ko ba afad'a ba kasan ransa a mutuk'ar b'ace yake
Akram ya zubawa ido a lokacin da yake shigowa shima fuskarsa a d'aure shima waje ya samu ya zauna kusa da fire dukansu suka sunkuyar dakai
Ogansu girgiza Kansa yayi ya d'auko wayarsa daga cikin Aljihu yayi dailing wani number yasaka a handsfree sai da yayi ringing ya kai sau biyar kafin a d'aga wayar cikin wani irin k'ak'ausar murya yace "Kura ya akayi kake kirana da asuba nan"?
Ogansu rusuna kansa yayi tamkar yana gabansa yace " Yi hakuri mai gida wani Abu mai mahimmaci yasa na kiraka yanzu Dan na Gaza hakuri"
Daga d'aya b'angaren Wanda yacewa Mai gida ya k'ara cewa "ina jinka"
"Mai Gida agaskiya nagaji da fita operation da Akram babu abinda yake tsinana min sai b'acin rai sau hud'u kenan muna fita dashi bai tab'a yin komai ba sai dai ya tsaya ya kallemu ayau shine har da hanani ciwa manufata agaskiya mai gida ni zan hakura dashi haka zan harbeshi sabida gudun tonuwar Asirina"
Mai gida da sauri yace "kana haukana Ashe Baka da hankali kasan kuwa rashin wanan Akram d'in acikinku shine zai sa asirinku ya tonu da wurwuri Dan ban yarda ma ka karb'e shi ba sai danayi aiki mai k'arfi akansa tauraransa na da kyau na duba nagani shigowarsa cikinku ba k'aramin Alheri bane kuma ta silarsa akwai alherai da yawa da yake tunkaro Ku kamar yanda na fad'a maka kuyi hakuri da halinsa kuringa fita dashi operation karku sake Ku matsa mishi akan abinda bayaso tauraranka Dana shi na da kyau da haske Dan haka ka cigaba da hakuri nan da sati biyu kazo ka sameni akwai abubuwan da zan Baku da kai da yaranka kuyi amfani dashi har shi kansa Akram d'in"
Wani mugun harara ogansu ya wurgawa Akram daya sunkuyar dakai yana jin duk abinda suke cewa aransa yana "nafi k'arfinku wlh da Allah na dogara haka Allah zai cigaba da b'oye muku manufata akanku"
Muryar ogansu ne ya katse masa zancen zucin da yake
"To shikenan mai gida ngd sai na k'ara kiranka babu laifi aikinmu na yau ya Dan yi kyau sai dai abincin da banci"
Mai gida wani mugun dariya yayi yace "gwara da baka ci abincin nan ba Dan zai iya zame maka guba"
Daga haka ya kashe wayarsa
Ogansu zaro ido yayi yabi wayar da kallo yana girgiza kai daga baya ya ajiye wayar hannunsa
Yasa hannu biyu ya d'ora a fuskarsa tare da zaro Mask mai fatar fuskar mutum daga fuskarsa ainihin fuskarsa ya bayyana
Adai-dai lokacin Akram ya d'ago ya zuba mishi ido a ransa yana cewa "this is Alhaji Bala mai kudi known as kura insha Allahu asirinka zai tonu soon mutane zasu San true color d'inka"
Ni kaina sakin baki nayi ina kallonsa Dan ogansu fuska ya saka ayanzu da yacire mask d'in fuskarsa ba bak'i bane wuluk kamar yanda mask d'in yake yana da Dan haske da bajajjen hanci
Brief case d'in ya jawo da kud'in suke ciki ya ringa zaro wrappers din kud'in yana ajiyewa a cinyarsa har sai da ya kwashe tas daga cikin brief case d'in inda a lissafin da yayi brief case d'in million biyar ne a ciki
Mai da kud'in yayi cikin brief case d'in ya ringa zaro wrappers uku uku yana cillawa su lion duk Wanda ya cillawa sai ya chape tare da godiya Akram ya w'ullawa ak'arshe tare da zuba masa harara
Akram kuwa ya saki murmushi yana "thank you boss" adai-dai lokacin da ya chafe kud'in
Ogansu k'ara d'aura fuska yayi adai-dai lokacin daya d'aga hannunsa yana nuna Akram yace "Ak this should be first and last da zaka min abinda kayi min yau u are just lucky mai Gida yace na bika ahankali if not wlh da am done with you since
idan fa muka fita ba wani Abu kake iya tsinana mana ba raka mu kawai kake wai kuma ahaka u are part of us idan muka samo harda kai za'a raba so dan haka babu ruwanka da yanda zamu na operation d'inmu idan zamu kashe dubu muyi raping dubu is non of your business ka zuba ido kawai"
Akram murmushi yayi yace "am sorry boss insha Allahu bazan k'ara ba wanan ma na maka magana ne sabida naga time na tafiya kar gari ya waye azo a kama mu"
Wani mahaukacin dariya ogansu yayi yace "waye zai kama mu kai kasan Rabin 'yan sandan nan ina huld'a dasu koda zan fita operation ina gaya musu shi yasa wani zubin ma idan aka kirasu suke jinkirtawa basu zuwa da wuri sai sun dai dai ci na kusan barin gurin danaje operation ina barin gurin zaka ga sun iso suma ina basu nasu kason hahahahahhaha"
With much interest Akram yace "haba no wonder shi yasa Ashe ba'a tab'a kama mu ba Ashe suma sun d'aure mana gindi boss su wa dawa waye a cikin 'yan sandan"?
Akram ya tambayeshi Dan yasan sunayen 'yan sandan da ake had'a baki dasu suna wanan ta'asar
Ogansu kuwa wani dariyar ya k'ara k'yalk'yalewa dashi ya hau zayyano mishi sunayen manyan 'yan sandan masu d'auke da babban rank inda Akram jikinsa ya d'au rawa Dan not even in his drm daya tab'a tunanin zasu iya haka amma azahiri kuwa nunawa ogansu murna yake ahaka suka shantake suna hira su lion kuwa suna ta busa sigari sai da gari ya waye wajen 7 ogansu yayi hamma yace zaije ya kwanta Killer ya je ya d'auko masa linder yaci kamar wata abinci suma suje suyi enjoying Kansu anjima zai wuce port Harcourt wajen iyalinsa sai ya kuma jin labarin wani mai kud'in da haka kowa ya watse ya kama gabansa inda Akram ya kwanta a tsakiyar carpet yana tunano halin dasu Samha suke ciki yasan by now suna can suna ta kuka
Wai ni kam waye wanan Alhaji Balan ne sai dai kun biyoni xamuji ko wanene
B'angarensu Saiam kuwa Akram na ficewa Samha ta duro daga kan gado itama tazo kusa da gawar Hajiya Nafeesa tana ta kuka tana "mummy meyesa kika tafi kika barmu ya kikeso muyi rayuwa babu ke mummy kin manta hirar da mu kai dake jiya kince insha Allahu sai kin Goya 'ya'yana mummy amma tun su Aunty Saiam basuyi Aure ba kika tafi y mummy y?
Kuka suka k'ara fashe dashi kamar ta zuga su banda Saiam da ta rungume kan Hajiya Nafeesa tun dazu ta kura wa jinin dake ta zuba ido ko kifta ido bata yi Suhaima ce ta fara ankara da Alhaji Nazifi dake kwance kamar matacce da sauri ta mik'e tayi wajensa tana " Daddy Daddy Daddy" ko motsi Alhaji Nazifi baiyi ba wani mugun ihu Suhaima ta fasa tana "shikenan mun zama cikakkun marayu Daddy shima ya mutu"
Safna da sabida tashin hankali bama tasan babu kaya ajikinta ba da gudu ta tashi tana "AAA Daddy bai mutu ba Suhaima daddy bazai tafi ya barmu ba "
Aguje ta nufi band'aki ta d'ebo ruwa ta watsawa Alhaji Nazifi
Alhaji Nazifi kuwa yaja wani dogon ajiyar zuciya still bai farka ba wani ruwan Safna ta k'ara watsa mishi ahankali ya k'ara Jan wani numfashin kafin ya bud'e idonsa ahankali ya zubawa Suhaima da Safna ido kamar Wanda bai sansu ba
Take maganar Hajiya Nafeesa ya hau amsa kuwaa a kunensa "Alhaji idan wani Abu ya samu yarana wlh bazan tab'a yafe maka ba"
Mik'ewa yayi zumbur yana "Nafeeeesa" tare da nufar wajen da take kwance da gudu inda su Suhaima suka bishi abaya aguje
Zub'e wa yayi akan gwiwarsa yana kallon jinin dake ta zuba akan tiles Sahiba na kwance a k'afar Hajiya Nafeesa Saiam kuma ta rungume kan Hajiya Nafeesa gam ta kurawa waje d'aya ido Samha kuwa ta rik'e hannun Hajiya Nafeesa tana wani irin kuka kamar ranta zai fita majina sai fitowa yake a hancinta
Alhaji Nazifi hawaye ne ya hau gudu a fuskarsa yana " Nafeeeesa karki min haka karki tafi ki barni"
Samha had'iye kukanta tayi tana wa Alhaji Nazifi wani irin kallo tana "Daddy kana ina lokacin da b'arayi suka harbi mummy?Daddy kana ina lokacin da mummy take fad'i tashi akan ta hana a keta mana haddi? Daddy wane k'ok'ari kayi Dan kar ayi mana fyad'e? Daddy wane k'ok'ari kayi Dan kar su kashe mummy? Daddy mummy lost her life because of us she sacrifice her life because of us Daddy kana ina hakan duk ya faru? Daddy ayanzu zaka zo kace kar ta tafi ta barka? Daddy ayanzu kake da bakin magana? Daddy agaban idonka aka ringa k'ok'arin yi mana fyad'e Daddy agaban idonka aka harbi mommy sau uku Daddy sai yanzu zaka zo bayan sun tafi ? Sai yanzu zaka yi kuka Daddy?
Duk maganar nan da take yi kuka take sosai Alhaji kuwa zuciyarsa ya ringa bugawa da sauri da sauri kansa na juyawa ahankali yakai hannunsa ya ruk'o d'aya hannun Hajiya Nafeesa yana "ki yafemin Nafeesa bazan iya rayuwa babu ke ba Nima biyoki zanyi" daga haka ya rik'e zuciyarsa ahankali ya sulale k'asa
Wani mugun ihu Suhaima ta fasa daya tilastawa mak'ota yar rige rigen shigowa Suna sallati Dan tun dazu suke so su shigo so suke b'arayin suyi nisa adai-dai lokacin da 'yan sanda suka k'ara so gidan suma
Safna da suhaima da sahiba jijjiga Alhaji Nazifi kawai suke yi suna ihun kar shima ya tafi ya barsu
Samha kuwa numfashinta ya ringa fita da sauri da sauri Saiam kuwa tamkar dutse tana nan a kankame da kan Hajiya Nafeesa ta zubawa waje d'aya ido
Sallati mata hud'un da suka shigo da mazajensu suka tayi suna kiran Hajiya Nafeesa sai a lokacin Safna ta Ankara ba kaya ajikinta Dan had'a ido tayi da mijin wani mak'ocinsu yana mata kallon kurilla da sauri ta janyo hijabi tasaka
A adai-dai lokacin da 'yan sanda uku suka shigo da mace d'aya
Da k'yar yan sandan ya tilasta wa matan suyi shiru da su Suhaima Dan su tambayesu duk yanda akayi
Alhaji Nazir dake gefen gidansu Alhaji Nazifi ne yafara cewa bari akai Alhaji Nazifi asibiti Dan yana numfashi kad'an kad'an da sauri suka kinkimeshi sukayi waje
'Yan sandan kuwa suka tsugunna a kusa da gawar Hajiya Nafeesa
macen ta ringa d'aukar gawan hoto da wajen da jinin ke zuba akan tiles d'in kuka suke kamar ransu zai fita
Ahankali macen ta matsa kusa da Saiam Dan tace mata ta sausauta rik'on da tayi wa Hajiya Nafeesa haka sabida ta d'auki fuskarta hoto
Kukansu ne ya d'auke gabad'aya a lokacin da Saiam ta aza d'aya hannun ta abakin ta alamar suyi shiru ssshshhssh tace cikin whisper kamar bata San aji mai take cewa "kuyi shiru karku tashi mummy daga bacci bacci take yi ba mutuwa tayi ba uban waye yace mummy ta mutu to duk Wanda yake wa mummy fatan mutuwa shi zai mutu ba mummy ba dan haka Ku matsa karku tasheta
Mummy ai baki mutu ba ko? ni nasan bacci kike yi ba gobe kika ce zamuje gidan Aunty khadija ba Ni nasan bazaki mutu ba lah mummy kinga wai kuka suke kin mutu"
Wani mugun ihu Safna ta fasa tana tashiga uku ta lalace Aunty Saiam ta haukace su Sahiba kuwa jikinsu ya d'auki rawa suka zubawa Saiam ido dake kwantar da gashin Hajiya Nafeesa
'Yan sandan kuwa hankalinsu ne ya tashi suka hau yimata video still lokacin tana surutu ita kad'ai Samha kuwa zub'ewa tayi ak'asa Dan k'ok'awa take da numfashinta
Ahankali aka fara rarrashin Saiam data k'ara rungume kan Hajiya Nafeesa kamar wacce za'a k'wace ta sai surutu take ita kadai tana yiwa Hajiya Nafeesa rad'a a kunne ganin bama tasan suna yi ba yasa suka fara k'ok'arin b'anb'are hannun Saiam daga kan Hajiya Nafeesa data rungume
Wani mugun ihu ta ringa yi tana kar su tashi mummynta bacci take ba mutuwa tayi ba su rabu da ita kar su tasar mata mummynta..........
I really felt it wlh Allah ka biya mahaifinmu bukatunsu ka ara musu tsawon rai wayanda suka rasa nasu iyayen Allah ka kai haske kabarinsu alfarmar annabi Muhammad Saw
Ina masoyan Sadnaf masu nemanta ido rufe ga contact din Sadnaf nan da Alphabet 0H0CCGCABCE
Karku manta ishashen lokacin danake dashi shine Friday Saturday Sunday sauran ranakun sai ahankali amma bance bazaku jini ba incase idan ban poster ba working days sai kumin uziri
[2:33PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫
*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝
*A heart touching story*
庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 4*
Ihu Saiam ke yi sosai ta kankame kan Hajiya Nafeesa akan kar atasheta bacci take ba mutuwa tayi ba
Dak'yar matan suka banbare hannunta daga kan gawan Hajiya Nafeesa Saiam kuwa ta hau birgima a k'asa gwanin ban tausayi
Matar Alhaji Nazir mak'ocinsu Alhaji Nazifi ce tafara ankara da halin da Samha take ciki dan kirjinta sama yake sosai
Salatin da tayi da k'arfi ne yasa suka juya suka kalli inda Samha ke kwance cikin mawuyacin hali Sahiba hannu ta d'ora aka tana ta shiga ta uku ta lalace
Da sauri 'yan sandan suka umarci matan da a saka Samha a mota itama tana buk'atar taimakon gaggawa
Mata biyune suka kinkimi Samha sukayi waje da ita inda d'aya daga cikin 'yan sandan ya d'auko wani zani daya gani akan k'ofa ya rufe Hajiya Nafeesa
Kafin ya maida hankalinsa kan Safna da Suhaima dake zaune a kusa da gawan Hajiya Nafeesa sai sheshek'a suke suna jiyo muryar Saiam da aka kulle a dressing room tana su bud'e mata ita mummynta bata mutu ba
Da k'yar Suhaima ta iya basu labarin duk abinda yafaru d'aya d'an sandan yana recording d'ayan kuma yana rubuta statement d'in bayanan ta
K'arfe takwas dai-dai yan uwa da abokanan arziki suka ringa tururuwa cikin gidan suna koke koke familyn Hajiya Nafeesa gabad'aya sai da suka zo ciki kuwa har da mahaifinta da mahaifiyarta
Suna shigowa su Suhaima suka fashe da mugun kuka Safna ta mik'e da gudu taje ta rungume hajiyar su Nafeesa Dan tamkar an tsaga k'ara sabida kamaninsu da Hajiya Nafeesa banbanci kawai ita hajiyar su Nafeesa ta tsufa
Agaban gawan Hajiya Nafeesa ta tsugunna ahankali ta yaye zanin da aka rufe mata fuska dashi
Runtse idonta tayi da k'arfi data ga yanda jini ya wanke fuskarta
Fuskarta ta kumbura tayi suntum
Girgiza kai kawai take hawaye na gudu a fuskarta ahankali ta maida Zanin ta rufe
Ta fara magana cikin wani irin yanayi tana "Nafeesa bazan tab'a yafe wa Wanda ya kasheki ba amatsayina na mahaifiyarki zanta addu'a Allah ya tarwatsa rayuwar Wanda ya kashe ki shi da kwanciyar hankali a duniya sai dai alahira"
Kuka take sosai Wanda yasa duk wayanda ke palon kuka
Mahaifin Hajiya Nafeesa kuwa yana daga nesa ya kurawa Gawan Hajiya Nafeesa ido jikinsa sai rawa yake yana tuno shekaranjiya da ta zo gida tana ta