Follow us on social media
Showing 18001 words to 21000 words out of 50786 words
Dan Allah Daddy kayi hak'uri ka share hawayen ka kukan ka na k'ara tunzura Samha kukan ka na k'ara karya mata zuciya kai ya kamata ace ka rarrasheta"
Alhaji Nazifi kamar k'aramin yaro ya ringa gyad'a kai da sauri yana goge hawayen da suke k'ara tultulowa
A hankali yafara magana cikin rawar murya
"ALLAH YA JIKANKI NAFEESA ALLAH YA KAI HASKE KABARINKI TUNDA NA AUREKI BAKI TAB'A YARDA NA KWANA DA FUSHINKI BA BAKIDA BURIN DA WUCE KI FARANTA MIN RAI KINYI MIN BIYAYYA NAFEESA KIN BINI SAU DA K'AFA KIN BAWA YARANA TARBIYYA INGANTACIYA KO DAN WANAN INSHA ALLAHU ALJANA CE MAKOMARKI BAZAN TAB'A SAMUN MACE IRIN KI BA NAFEESA NAYI RASHIN DA HAR NA KOMA GA MAHALLICINA BAZAN SAMU WACCE ZATA MAYE GURBINKI BA ALLAH SARKI NAFEESA INA MA ACE NASAN DAREN JIYA ZAKI TAFI KI BARNI INA MA ACE NASAN GANIN K'ARSHE NAKE MIKI DA WLH BAN KWANTA BA DA NA ZAUNA NA NEMI YAFIYARKI NAFEESA ALLAH YA JIKANKI NAFEESA"
Duk inda Alhaji Nazifi yakai Dan ya danne kukan daya taho mishi kasawa yayi sai daya k'wace mishi
Saiam da Samha kuwa mutuwarta ya dawo musu sabo fil aransu suka hau kuka
Kamar Wanda aka mitsina suka ga Alhaji Nazifi ya mik'e yana "Saiam an binneta ne"?
Saiam kanta kawai ta iya gyad'awa
Alhaji Nazifi kuwa yayi sauri ya tuje Karin ruwan da ake mishi a hannun bai damu da jinin dake zuba a hannun shi ba
Yayi hanyar k'ofa da sauri
Saiam da sauri itama tabi bayan shi tare da shan gabansa tana
" Daddy ina zaka je ahaka ?kaga jinin da ke ta zuba a hannunka kuwa?
Alhaji Nazifi da sauri yace " Saiam zanje kabarinta nayi mata addu'a tunda badani aka binneta ba tana buk'atar addu'ata"
Daga haka ya ratsa ta gefen Saiam yayi waje da Sauri
Samha itama Sauk'owa tayi daga kan gadon ta cewa Saiam itama zata tafi gida zaman asibitin ya isheta haka
Babu yanda Saiam ba tayi da Samha akan ta bari ruwan da aka sa mata ya kare ba fir tak'i akan dole Saiam ta kira likita ya Sallamesu
Naila da sauri ta juya tayi waje sakamakon ganin towel d'in da Alhaji Bala ke d'aure dashi a kugunsa ya fad'o k'asa
Alhaji Bala sabida tashin hankali da tsoratar da yayi bai ma San a tsirara yake ba
Hajiya Lubna kuwa itama cikin rawar jiki ta nufi wajen Alhaji Balan daya jik'e da gumi ta d'auki towel d'insa dake k'asa tace
"Alhaji lafiya kuwa mai ya firgita ka haka da har towel d'inka ya bar jikinka Baka sani ba"?
Alhaji Bala sai a lokacin yasan a tsirara yake hannuwansa na rawa ya k'arbi towel d'in daga hannun Hajiya Lubna ya d'aura tare da zama a gefen gado still yana hango Hajiya Nafeesa a tsaye a idonsa
Numfashinsa sai fita yake da Sauri sauri
Hajiya lubna itama zama tayi agefensa Dan tunda take dashi bata tab'a ganinsa acikin irin wanan halin ba
A hankali tace "Alhaji Lafiya mai ya tsorata ka haka ko dai mafarki kayi"?
Alhaji Bala bai ce mata komai ba har lokacin jikinsa bai bar rawa ba
Magana Hajiya Lubna ta k'ara yi
Alhaji Bala ya daka mata wani mugun tsawa yana "dala ki rabu dani Wai meyesa bakida hankaline dolene sai na gaya miki abinda yake damuna"?
Hajiya Lubna da sauri ta mik'e tayi waje ba tare da ta tsaya bashi hakuri ko taji mai zai cigaba da cewa ba
dan haka take idan taga ransa a b'ace bata tsayawa a wajen barin gurin shi zai fiye mata alheri dan itama akwai zuciya
Naila data yi jugum a Palo tana ganin Hajiya Lubna ta fito ta tareta da sauri tare da tambayarta abinda ya samu Abbanta
Hajiya Lubna da itama ranta a b'ace bata cewa Naila komai ba illa ma hannunta da ta rik'e sukayi hanyar d'akinta
Naila kuwa ganin babu fuska yasa bata k'ara tambayarta ba ta kwanta kamar yanda Hajiya Lubna ta kwanta
Alhaji Bala aranar kwanan zaune yayi a tsorace gani yake ko yaya ya runtse idonsa Zai iya ganin Hajiya Nafeesa
Rayuka nawa ya kashe amma babu wacce ta tab'a masa fatalwa sai Hajiya Nafeesa tunda yake ko mafarkin wayanda ya kakashe bai tab'a yi ba sai Hajiya Nafeesa me hakan ke nufi agaskiya bai ga ta zama ba dole da asuba ya d'au hanyar Maiduguri yaje ya nemi taimakon mai gida
Allah Allah kawai yake gari ya waye
Wajen k'arfe 3:40 yafara gyangyad'i a zaune sai baccin ya kusa sace shi sai yayi firgigit ya zauna ahaka ya ringayi har sai da baccin yaci k'arfin idonsa ya kwanta bacci yayi awon gaba dashi
Mafarki ya fara yi da Hajiya Nafeesa tana ta kuka ga kirjinta na ta zubar da jini sai binshi take da gudu shima yana ta gudu da iya k'arfinsa sai ihu yake yana azo a taimaka mishi amma ina gani yake kamar ba gudu yake ba sabida Hajiya Nafeesa tana dab da k'arasowa inda yake
Hannu ta mik'a da niyyar damk'o shi ya mik'e a firgice yana ihu sabida ba ilimin islama ballantana yayi sallati
Yana zama ya kuma hango hajiya Nafeesa abakin k'ofa atsaye kamar dai yanda ya ganta a mafarki
Wani razannan ihu ya saki da iya k'arfinsa
Hajiya Lubna da Naila suka kwasa aguje sukayi d'akin
Suna bud'e k'ofa Hajiya Nafeesa ta b'ace
Alhaji Bala kuwa ya ringa wani irin k'yarma kamar mai jin sanyi ga wani uban gumi kamar Wanda aka kwarawa ruwa
Naila a bakin k'ofa ta tsaya dan towel d'insa ya kuma yin wani wajen
Hajiya Lubna kuwa fuska a d'aure ta nufi wajensa tana "Alhaji wai me hakane mai yake damunka kake ta mana ihu ka fad'amin ka k'i ka fad'amin abinda yake firgita ka wai mai haka ne dan Allah dan annabi"?
Hajiya Lubna tace tana jefa mishi towel d'insa daya yi gefe
Alhaji Bala ajiyar zuciya Kawai yake yana kalle kalle sai zare ido yake
Hajiya Lubna wadrobe ta nufa ta d'auko mishi wani dogon jallabiya da gajeran wando
Ta cilla mishi adai dai lokacin da Naila ta bar d'akin
Hajiya Lubna kuwa tace " ga kaya nan ka sa tunda abinda yake firgita ka saka yake kayi tsirara agaban 'yarka"
Alhaji Bala da sauri ya zura jallabiyar da gajeran wandon yabi bayan Hajiya Lubna data yi hanyar waje da sauri dan baya jin zai Iya zama a d'akin shi kad'ai
A palo suka zauna gaba d'aya Naila ta hau jerawa Alhaji Bala da jikinsa ke rawa Sannu
Alhaji Bala shi dai kansa a sunkuye yana hango yanda yaga Hajiya Nafeesa a mafarki da zahiri a hankali ya d'aga kai ya kalli agogon dake bangon palon yaga hud'u da minti Arbain an fara ma kiraye kirayen Sallahr asuba
Hajiya Lubna tagumi kawai tayi tana kallon shi aranta tana ta mamakin abinda yake tsorata shi ya fita daga hayyacinsa haka
Alhaji Bala kuwa yana ganin biyar tayi ya mik'e ya d'auko mukullin motarsa a d'aki sai juye juye yake dan duk a tsorace yake
Ko salla bai tsaya yi ba dan dama ba damunsa yayi ba sai yaga dama yake yi
Ko kallon Hajiya Lubna dake ta tambayarshi ina za shi bai yi ba ya fice da sauri dan burinsa bai wuce ya gan shi agaban Mai gida ba
B'angaren Akram kuwa aranar Sam bai runtsa ba da tunaninsu Saiam ya kwana ko yaya ya juya sai ya hango Samha a idonsa tana ta kuka
Wajen k'arfe uku bacci yayi awon gaba dashi atake ya hau mafarki da Hajiya Nafeesa tana ta kuka tana ce mishi ya kular mata da yaranta kar wani Abu ya same su sai kuka take a mafarkin tana had'e hannyenta alamar rok'o
Da Sallati Akram ya farka daga baccin da yake yana ta mamakin Mafarkin da yayi
A hankali ya sauko da k'afarsa daga kan gado ya nufi band'aki dan ya d'aura alwala
Alhaji Bala a zaune yake agaban mai gida yabi ya had'a gumi yana ta kallon K'asan da mai gida yake bugawa shima sai had'a gumi yake sai da ya samu minti Ashirin yana buga k'asa yana gogewa yana kuma zana k'asa sai girgiza kai yake alaman Al amarin babba ne
Alhaji Bala kuwa duk ya matsu ya gaya mishi abinda yake faruwa
A hankali Mai gida ya d'ago tare da sharce gumin dake tsatsafo mishi a goshi ya kalli Alhaji Balan da jikinsa ke rawa dan shi kansa tunda yake bai tab'a ganin mai gida a irin wanan yanayin ba
Mai gida magana ya fara yi yana "Kura akwai matsala matsalar ma kuwa gagaruma dan wanan fad'a ne tsakanin matacce da rayayye matar nan da ka kashe spirit d'inta na da k'arfi sosai wlh haka zata tayi ta bibiyarka har sai ka zamto kamar mahaukaci ka fito duniya ka fad'i hallayenka da kanka da irin sana'ar da kake yi kafin ta rabu dakai kayi kuskure daka bari jininta ya tab'aka"
Hankali a tashe Alhaji Bala yace "mai gida kamar ya jininta ya tab'ani kana nufin babu abinda zaka iya yi akai"?
" emana jininta ya tab'aka ai sabida hular kanta ta cire ta saka a kirjinta sai da ya jike da jini ta jefo ma a fuska ko ba ayi haka ba"?
Da sauri Alhaji Bala yace "anyi haka wlh na d'auka taurin zuciya yasa ta jefo min hular ta ni kuwa na k'arasa kasheta na shiga uku na lalace mai gida yanzu mai abun yi dan Allah ka taimaka min dan ni Dana San matar nan haka take wlh da ban soma ma kasheta ba da iya shegun zan d'ebo na fito"
Alhaji Bala yace cikin rawar murya
Mai gida ajiyar zuciya ya sauke yace "Abu biyu zaka iya yi ta rabu dakai na d'aya ka koma gidan ka d'auko wanan hular nata ka kona shi na biyu kaje gidan ka durk'usa agaban mijinta da yaranta kace su yafe maka idan sun yafe maka to zata rabu dakai amma idan kuwa acikin biyun nan ba'ayi d'aya ba to ni kam babu abinda zan iya yi akai kuma Abubuwa na dab da jagule maka ga rashin kwanciyar hankali da zakayi ta fama dashi"
Hankalin Alhaji Bala idan yayi dubu ya kai kololuwa wajen tashi a firgice ya mik'e yana "mai gida kasan mai kake cewa kuwa ta ina zan iya samo hular da ta cire?ta yaya zan koma gidan a matsayina na Wanda ya kasheta haba maigida ya zaka fad'i abinda ba zai yiwu ba"
Mai gida ce mishi yayi to "iya abinda na duba kenan Wanda zaka yi ta rabu dakai amma bayan shi babu abinda zaka iya yi akai amma dai zan baka wasu Abubuwa idan ka dace ba zata ringa zuwar maka ba"
Da sauri Alhaji Bala ya zauna yana "dan Allah ka taimakeni matar nan ta firgitani har tsirara nayi agaban 'yata bansani ba"
Mai gida wani kwarya ya d'auko Wanda aka nannad'e da jajayen k'yalaye ya mik'a mishi yana
" idan ka tashi ka warware wanan Jan k'yallen ka daura akan goshinka da k'afarka akwai wani kullin magani guda biyu a ciki bak'in jikawa zaka yi ka shafa a jikinka gabad'aya wari ne dashi kamar kashi amma haka zaka d'aure idan gari ya waye sai ka wanke
D'ayan kuma turara d'akinka zaka yi dashi kafin ka kwanta bacci"
Hannu yasa ya d'auko Wasu jajjayen candles ya kuma mik'a mishi yana " ka kashe wutan d'akinka sai ka kunna candles d'in idan dai kaga tazo maka bayan kayi abubuwan nan to babu abinda zan iya yi akai face dai zabin farkon Dana baka"
Alhaji Bala da Sauri yace "insha Allahu ma ba zata kuma zuwar min ba indai nayi yanda kace"
Mai gida girgiza kansa kawai yayi bai ce komai ba ahaka Alhaji Bala ya ajiye mishi makud'an kud'i ya tafi...........
[2:36PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫
*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝
*A heart touching story*
庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*HEA MASOYANA FANS D'INA INA FARINCIKIN SANAR DAKU INA UPDATING NOVEL D'IN BAK'IN DARE A WATTPAD ACAN ZAN RINGA POSTING KAFIN WATSAPP SO PLS IF U ARE REALLY I DIE FAN DONT FORGET TO SEARCH FOR SADNAF FOLLOW AND VOTE ME THERE I WOULD B GREATFUL WEN I START COUNTING YOUR VOTES*馃檹馃檹馃檹
*Page 8*
Wasa wasa sati biyu kenan da Alhaji Bala yaje wajen Mai gida abunda ake cewa kwanciyar hankali Sam Alhaji Bala bashi dashi dan Duk abinda Mai gida yace yayi ya yi amma Kullum sai Hajiya Nafeesa tazo mishi a cikin mafarki ko a zahiri yabi ya zama kamar mai k'aramin tab'in hankali Dan ko yaya yaji motsi sai ya firgita ya zunduma Ihu
Hajiya Lubna da Naila kuwa hankalinsu yayi masifar tashi da halin da suka ga Alhaji Bala a ciki Dan tunda ya fara shafa wani magani mai Warin kashi a jiki ga jajayen candles da yake kunawa duk dare suka fara tsorata da lamarin Alhaji Bala Naila b'uya ma take a d'aki dan ta fara zargin Daddynta yafara samun tab'in hankali kowane lokaci zai iya rufesu da duka dan abun nashi ya kai yanzu har da rana Ihu yake shi kad'ai idan yana zaune a cikin Palo ya kuma k'i gayawa Hajiya Lubna abinda ke faruwa idan ta matsa mishi da tambayoyi sai ya rufeta da fad'a tamkar zai daketa
A haka suka zuba mishi ido suna mishi addu'a samun sauki
B'angaren su Saiam kuwa Addu'a suke babu dare babu rana akan Allah yayi wa Hajiya Nafeesa Rahama ya kuma toni asirin Alhaji Bala har akayi sadakan bakwai bakinsu na d'auke da azumi idan kagansu sai sun masifar baka tausayi dan kowacensu kalar idonta ya koma ja sunyi shak'uwa da mahaifiyarsu fiye da tunanin mai tunani ko abinci basa iya ci ballantana akai ga cikakken bacci ahaka nasu nafila ne akan Alhaji Nazifi tunda danginsu dake tayasu zaman makoki suna dan kwantar musu da hankali sabanin Alhaji Nazifi da ke wuni a d'aki baya fitowa ba um bare uhum uhum haka zai yi tagumi yana kallon Hoton Hajiya Nafeesa lokaci lokaci yana share hawayen dake zubo mishi duk Wanda yazo mishi gaisuwa sai dai ya hakura ya tafi dan Alhaji Nazifi baya ko motsawa daga inda yake kiran Sallah kawai ke sa ya tashi Sallar ma a d'aki yake yinta a k'arshen sujadarsa kuwa kuka yake fashewa dashi yayi ta yiwa Hajiya Nafeesa Addu'ar Rahamar Allah
Sai da akayi Sati biyu da Rasuwar Hajiya Nafeesa Alhaji Nazifi ya d'an fara dawo wa dai-dai a inda ya nemo wani babban Mallami mai tarin ilimi yace ya taya shi da addu'ar Allah ya tonawa azzalumin da ya kashe Hajiya Nafeesa Asiri shi da zaman lafiya har Abada
Mallamin kuwa yace ya kawo kud'in Sadaka ya had'a kan Almajirai ya raba musu ayoyi da addu'oi insha Allahu asirinsa na dab da tonuwa
Makud'an kud'i Alhaji Nazifi ya bashi tare da yi mishi godiya
A Daren ranar suna zaune a Palo gabad'aya kowanensu hannunsa d'auke da carbi yayan Hajiya Nafeesa Alhaji Musa da tun magriba yana gidan kallon Alhaji Nazifi yayi dayake Jan counter kansa a sunkuye yayi yace mishi yanzu sai dai a d'aga Auren Safna da Saiam idan Hajiya Nafeesa tayi Arba'in sai a d'aura musu Auren dan ba dan rasuwarta ba da gobene d'aurin Auren
Saiam juyar da kanta tayi dan ita yanzu Sam Auren bama ya gabanta bata jin zata iya Aure ta rabu dasu Sahiba gwara ta zauna ta kula da kanenta tunda itace Babba
Alhaji Nazifi sai da yafara Sauke ajiyar zuciya kafin ya d'ago yace " A goben za'a d'aura musu Aure insha Allahu babu abinda za'a fasa dan Nafeesa ta rasu bashi zai sa a d'aga daurin Auren ba dan ko an d'aga ba dawowa zatayi ba ni nasan burinta bai wuce taga ranar d'aurin Auren Su ba kuma insha Allahu zan cika mata wanan burin nata dazu na yiwa iyayen mazajen waya akan su zo da shirinsu gobe k'arfe goma sha d'aya za'ayi D'aurin Auren in yaso sa tare idan an kwana biyu"
Tunda Ya fara magana Saiam da Safna suka d'ago arazane suna kallon shi kuka suka fashe dashi kamar had'in baki Saiam tace"Daddy dan Allah kar a d'aura mana Aure gobe mummy satinta biyu da rasuwa yau ya za'ayi a d'aura mana Aure gobe ni wlh na hakura da Auren zan zauna na kula da kanena idan mukayi Aure waye zai kula dasu Daddy Dan Allah mun fasa bama San Auren" Saiam ta karashe maganarta cikin matsanacin kuka
Alhaji Nazifi Da ji yake kamar shima ya fashe da kuka girgiza kai yayi ya mik'e daga kan kujera ya nufi inda suke a zaune
Zama yayi agabansu ya tank'washe k'afafunsa ya kira sunan Saiam da Safna yace "Karku manta ni ina rayye ban mutu ba ni zan kula dasu har zuwa lokacin da suma zan Aurar dasu burin Mahaifiyarku Kullum bai wuce taga ranar Aurenku ba kuma ni nasan a yanzu idan aka d'aga d'aurin Auren nan sabida ita bazata ji dadi ba gwara in cika mata burinta duk da bata Raye idan ta kanenku ne insha Allahu ni zan kula dasu ba wai ana d'aura Auren gobe a goben zaku tare ba sai an d'an kwana biyu haka mun d'an k'ara samun nutsuwa mun k'arasa sauran shirin namu sai Ku tare"
A takaice da k'yar Alhaji Nazifi da Alhaji Musa suka shawo kansu Saiam suka yarda za'a d'aura musu Aure a gobe Su Suhaima kuwa tausayin Kansu ne ya k'ara lullub'esu dan ahaka da suke d'an ganin juna hankalinsu ke kwanciya ayanzu kuma idan Saiam da Safna suka yi Aure gidan girma zai k'ara yi musu
B'angaren Akram kuwa suna nan suna shirye shiryen yanda zasu kama Alhaji Bala cikin Sauki shi da yaransa inda Akram ke kiran su Lion da suka Dade da komawa gidansu dake Daji dan cika Umarnin Alhaji Bala
Akram kuwa karya ya ringa musu da Mahaifiyarshi ce ba lafiya shi yasa bai dawo ba amma kafin ogansu ya dawo zai dawo
Akram ganin anyi sati Biyu Alhaji Bala bai kira shi ba