Follow us on social media
Showing 6001 words to 9000 words out of 34548 words
Chapter 3 - IDAN RANA TA FITO by Halima Abdullahi K. Mashi
BINTO ta ce haba?" Na ce, Allah kuwa, ai zan ma biya za ki ji. ADO na zaune kofar gida yana dauke da wani littafi yana nazari, na durkusa na gaishe shi, cikin fara'a ya amsa tare da cewa, kin zo ne? Na ce, eh, ya ce shiga ina zuwa, ban jima ba ya shigo don ya sani lkcn nawa kilalanne, ya ce biya in don ya ji na jiyan. Na yi Bismillah sannan na karanta, ya kara min wani da haka na iya addu'o'i da dama Cikin Haka ne batun auren su BINTO, ya tashi domi kaka ta matso su HINDE ma duk an kawo kudinsu ni kadai ce babu manemi to wa zai so ni, ni ba kyau ba ga kazanta, bugu da kari ga ni baka, su ko na lura samarin kauyanmu in dai kina fara komai muninki za ki samu miji, na lura abn yana damun Babana, ni ko bn damu ba don zancan da ni ke lkcn fa shekaruna 12 an ce ma wai sai watan Mauladi ya kama. ADO yana kwance a shimfidarsa, zuciyarsa tana nazari, ne a kan Jidda yana son taimakon yarinyar sai dai ya rasa me zai yi don ganin ta fita cikin halin da ta ke, gata da kwazo shi dai ya shaku da JIDDA, har ma yana cewa da ya tashi aure ne babu abn da zai hana shi aurenta, Bai damu da so ba ba ya sani suna tare wataran zai so ta. Sama'ila ne ya katse mishi tunanshi da sallama, ya amsa ya tashi zaune dai-dai lkcn da shima ya zauna kan kujerar katakon dakin.... . Sama'ila ya ce, "To Allah ya za6a mana abinda ya fi zama alkairi."Ado ya ce,"Amin. Wata rana da daddare an aike ni kar6o kudin dashi ina tafe da 'yar sandata ina wakar "wayyo Allah na wayya Allah na kalalla6a tashi ga idona kalalla6a, wanda ya cire min kalalla6a, shi ne mijina, sai na ji murayar ADO ya ce Kalalla6a, ya iso gurina. Bayan na tsaya ya dube ni gani zan cire miki, na sunkuyar da kai sannan na ce, "Yaya Ado ai kai Malamina ne." Ya ce, daga ina haka? Na ce amso kudin dashi naje, Ya ce, zo nan dama ina son in yi wata magana da ke. Jingina ya yi daga jikin wata, bishiya da ke nesa dama kadan, hasken farin wata ya haske gurin. Ya zuba min idanunshi, ni ko kaina na kasa ina wasa da kudin hannuna, ya ce, "JIDDA kina jina?" Na ce ina jin ka, sai na ji kalmar saukar aradu, za ki aure ni?" Sai da na yi tamkar zan fadi don firgici, sannan na gyara tsayuwata na ce, "Uhum, Yaya AdO kenan. Yaushe muka sona 'yar tsokana?" Ya ce, "Gaske ni ke magana." Na yi murmushi a zotana ko da wani zaya tsokane ni ban da kai, duk kyawawan 'yanmatan kauyan nan suna burin ko magana ka dinga musy ciki har da yata Hinde duk ba ka ce zaka aure su ba sai ni KAZAMA, MUMMUNA,BAKA, MARAINIYA, MARAR GATA?" Tausayinta ya kuma cika shi, ya uba hannunwanshi cikin aljihu, JIDDA ni ko kin ga wadannan abubuwan da ki ka lissafa sune suka kwadaita min auran ki. Na kalle shi cikin mamaki, sannan na girgiza kai. "Yaya Ado na sani kana dai tausaya min ne amma ba sona ka ke yi ba. Shi aure zama ne ba na kare ba, in ka aure ni zaka yi na dama a gaba." ya ce,"JIDDA kina da hangen nesa, sai dai bana jin hakan ata faru insha Allah, abn da kawai nake so ki amince dani kuma daga yau zan soma zuwa zance gidanku. Na yi 'yar dariya zaka sa Baba Gaje ta kara tsanata kenan, don tana maida ni baya ne saboda kada wani ya nuna yana sona. Ado ya ce, "To ai "IDAN RANA TA FITO TAFIN HANNU BA YA KARE TA, ki je gida sai na zo, ."Na tafi ina waigen shi, anya kuwa ma Ado ne?" Ko dai wani Aljanin ne? Abin da na saka wa a zuciyata kenan. Washe gari muna zaune a tsakar gida, Hinde suna ta cin abincin su da su Jummala ba sa ci da ni ni ko ina can gefe ina cin nawa murfin kwano, hirar samarin suke yi suna min haibaici tare da wakar zanbo wai Allah min tsarin da auran kazama na tashi naje nayo Sallar Isha'i na dawo na zauna, sai ga sallamar Baffa kanin Ado, ya ce, sannunku, suka amsa ya ce wai ana sallama da JIDDA, Hinde ta ce, Jidda kuwa a ka ce, maka?" "Ya ce, "Eh in ji Yaya Ado." Baba Gaje ta ce "Yana ina?" Baffa ya ce gashi nan a waje ta ce to ka ce tana zuwa. Ta kwala wa Hinde kira zo ki je kin ji Ado, yana kiranki, dan nasan ke yake kira ba waccan ba, ina jin su ban ce komai ba. Har da turare Baba Gaje ta ce Hinde ta fesa bayan ta can za kaya. Babana yana kofar dakinshi na je na zauna kusa dashi zuciyata cike da damuwa, domin jiya ne kawai ADO ya gabatar da kanshi gare ni amma ji nake tamkar mun yi shekaru dashi, waton sonsa ne ya shige ni ba na wasa ba, na ce "Baba gurina Ado ya zo, amma Baba Gaje ta ce, Hinde taje.'" Baba ya kama hannuna "Kada ki damu nasan Ado ba zaya can za miki ba, tunda yasan da Hinde ya ce a kira ki. Ita kuwa Hinde lkcn data fita sai ta canza tafiya ta nufi Ado, shi kam lkcn ya shagaltu da tunanin anya za ma abar JIDDA ta fito kuwa? Sai ya ji takun sawu, kanshi yana kasa sai ya ji kamshin turare dan goma ko bai dago ba yasan ba JIDDA ba ce, domin ita in ta kusanto ka sai dai ka ji kaurin hayaki ko warin datti. Ya dube ta lkcn da ta zo ta tsaya gantsartsar a gabn shi, tare da cewa, gani, ya girgiza kai bn kira ba JIDDA nake nema, ta turo baki kai ko ga dan ziza da kai me zaka yi da kucakar mata? Ya yi mata wani duba je ki turo min ita.. . Ya kashe laptop din ya maida shi gidan shi sannan ya sako ta a ma adaninta, ya koma kan gado ya kwanta yana nazarin duk maganganun nasu. Ya jima da zargin cewa haka zata faru shi yasa bai 6ata lkc ba gurin manna wata 'yar mitsitsiyar na'urar daukar magana a duk kan dakunan gidan domin samun rahotannin abnda ke faruwa ko zai faru. Damuwa daya ya shiga dama Basma turo ta aka yi don ta yaudare shi? Lallai ta yi kokari domin yana son ta so mai tsanani duk da ranshi ya sosu da jin batun bai sa sonta ya yi rauni daga zuciyarshi ba, amma zaya cigaba da bin su yaga iyaka gudun ruwansu. Dady ya kalle shi bayan ya kur6i shayi. "Muhammad ya kamata zuwa yanzu a ce wani abu game da aurenka da Basma." M.B ya ce, "Dady ai magana tana gurin ku, ko Hjy?" ta aje cokalin hannunta tare da cewa "Wannan gaskiya ne Muhammad, Dady sai a yunkuro a shiga maganar." Dady ya ce, "Shi kenan, Insha Allah week end zamu shigo Abujan kafin sannan zan yi waya gida sai mu tafi da Sani." Hjy Shuwa ta ta6a baki "kana da son saka 'yan kauye cikin komai naka." Ya dube ta "Ni din dan ina ne?" M.B ya ce, "Kauye Husma ta ce yaya kuma zaya guji kauye Hjy. Dady yana da gaskiya ina son yanda Dady ke son asalinsa." M.B ya jinjina mata hannu, Tsaki Hjyn taja ai nima ban ce ya ki asalinsa ba, amma ka duba zuwa Abuja ba sai ya samu wasu daga abokansa su tafi tare ba? M.B ya ce, "bar shi kawai, Hju gara yaje da danginsa ba don ranta ya so ba ta ce shi kenan Dady ya yi dan murmushi sannan ya ce kamar yanda ni ke daura auren 'ya'yan Sani haka nan shi ne zai auradda nawa." Husna ta ce zamu sha biki fa Bros, Hjy ta ce kai Husna akwai ki da zumud'i, ta ce dole ne nayi zumudi Hjy ba mu fa ta6a yin wani biki namu na kashin kanmu ba cikin gidannan, sai dai in za k yi wani abu na dangan ki." M.B ya ce kina da gaskiya Husna. . Cikin lkc kankani manya suka cikin zancan aka yi sa rana ko in ce baiko, biki sosai aka yi tamkar lkcnnne bikin tare da rabe-raben kyautuka. Hjy kuwa Dubai suka tafi don hado lefe tare tare da kayan da za su ci biki dashi ita kuma Auta ta za6o kayan dakinta irin wadanda take so. Shi kuwa M.B ya yi sallama da su kan cewa za ya tafi kauye don sanar da su Haja. *************** Kimanin kwanaki 4 ne suka shude Ado da Kuluwa ba muga juna ba, sai ranar Lahadi ina dawowa daga talla na biyo ta gefen gonarsu shi ga su shi da Sama'ila, na tsaya turus ina kallonsu, har suka karaso inda nake, waige-waige na shiga yi domin ina tsoron koda akwai wanda zai kaiwa Baba Gaje labarin. "Ado ya ce kwantar da hankalinki JIDDA, babu kowa." Na yi ajiyar zuciya, amma na kasa kallonsu, ya ce kin saida ne? Na ce saura kwano 2, ya ce muje na bi su zuwa cikin gonar, ya kira daya daga cikin mutanan da suke aiki ya ce su dauki abinci karkashin wata bishiya muka zauna, ya ce nasan an dake ki ranar ko? Na ce eh, ta dake ni. Ya ce shi yasa ki ke ta 6oye min har kwanaki 4 ko? Nayi shiru, ya ce kin fasa auran nawa kenan? Na kalle shi sannan na kalli Sama'ila na sunkuyar da kai, na za ci kayi fushi ne game da abinda ta yi maka ka fasa. Sama'ila ya ce, "Allah Sarki, Abokina samun kansa ya yi da kara muradin auranki, kuma insha Allahu ba fashi, sai dai wani iko na Allah, Ado ya ce matsalar daya ce, Jidda na kalle shi gabana na faduwa zuciyata cike da son jin wace matsala ce wannan?" Ya ci gaba zan tafi birni karatu, kuma zan dauki kimanin shekara 3 ya ya ki ke ga za ayi? Nayi shiru ina nazari sannan cikin karaya wato cikin amincewa raina na rasa Ado na ce Allah ya bada sa'a Sama'ila ya ce abinda za ki iya cewa kenan? Na ce to me zan ce? Ado ya ce Jidda shawararki nake son ji game da mokamar auranmu? Na ce Yaya Ado haka kurum na ji a jikina auranmu ba zaya yiwu ba, saboda zai iya kasancewa in ka tafi birni ka manta dani, sannan ga matsalar Baba Gaje in ta gan mu ta ji labari kamar yanda ta ce kai kara gurin mahaifin ka ba ka jin akwai matsala? Ya ce don Allah bar zancan wannan Babar taki, zan fa ci gaba da zuwa zancena tunda Babanki ya yarje min kuma kada ki damu kinji na ce to. . Ban damu da su ba na ci gaba da aikina, sai da zan fita muka ci karo da Babana ya dawo zai yi shirin Masallaci, cikin murna ya ce,a'a wa nake gani haka? Kulun majadan, kai amma fa kinyi kyau cancadi." Dadi ya rufe ne, kun san mu2m yana son ya yi gayu a kuranta shi, kuma ban ta6a sa rai wata rana za ta zo da zan ji irin wannan kalmar ba. Na ce "Baba ba ta nan shi ne na saka wannan." Babana ya ce,"Ai ko kin yi kyau, na jima ina son in sai miki kaya in ganki haka tamkar sauran yara, amma hakan ya faskara. Allah ya sakawa Ado da alkhairi, na fita cikin farin ciki, duk wanda ya sanni in ya kalle ni sai ya sake kallona, saboda mamakin kwalliyar da na yi, wasu kuma su ce iyen ba, an ci gayu cikin zuciyata kuwa ba wanda nake so daga ni irin Ado, yau dai ya ganni cikin gayu. Wasu Dattijai suna cikin siyan goro sai na ji muryar Sama'ila yana cewa, "Yammata muna son goro." Na kalle su cikin kunya, bayan an gama sayan goron na rusuna na gaishe su cikin ladabi. Ado ya ce a"a Sama'ila kaga mutuniyar taka ko? Yau kam duk kauyannan kin cinye 'yammata a kyawun kwalliya." Sama'ila ya ce,"Na yarda da kai.' Dadi ne ya rufe ni, na ce "ko dai kuna tsokana ta ne?" Ado ya ce, tunda ki ka fito tsakanin ki da Allah mu kadai ne muka yaba adon naki? Na yi dan murmushi sannan na ce, a'a Baba ma.........
ππππππππ IDAN RANA TA FITO ππππππππ . Book 1 Part 21~30 S auran kalmar ta ki fitowa lokacin da na hango Baba Gaje ita da kawarta Dija suna dawowa daga biki, tuni su Ado suka gano ina cike da fargaba, sannan suka kalli inda nake kallo, ba su san Baba Gaje ba, amma duk sun yanke hukunci cewa ita ce, musamman Ado wanda ya ganta da dare, tana furta kalmar Kuluwa ina ki ka samo wadannan kayan? Cikin mamaki take magana, Ado ya shaidata a muryarta, don haka sai ya ce "Sannu Baba." Ya tsugunna shima Sama'ila sai ya tsugunna bata kalle su ba ni krum ta zuba wa idanu cike da masifa, tana karkada kai. Dija kuma tana fadin "Tabdijam, lallai yarinya ta rika." Ni kuwa tuni tsoro ya cika ni na soma kuka domin ban ta6a ganin fushinta irin na yau ba, don jikinta har 6ari yake, ta ce shin kai Ado ka ke ko wa? Ban ce ka fita hanyar ta ba?" Sama'ila ya ce, "Baba da aure muke sonta don Allah kiyi hakuri." Ta zaburo baki na kumfa "Ban hakura ba, na ce ban hakura ba iskanciin banza da wofi, na ce da ku aure zan mata? Tsinannu kun gama lalata 'yar uban wa zai aure ta?" Ado ya fusata ya kalle ta ya ce, Ni ne zan aureta." Ta kara kusanto shi"kai mara kunya ka fita daga inadunan in rufe ka kiyaye ni bar ganin ubanka ke da gari. Ado ya ce,"Baba insha Allahu sai na aure ta, ki rubuta ki ajiye sai na tsame ta daga wahalar da ki ke bata." Dija ma ta matso "kai dan sara sa'arka ce! ku ji mu da tsagera," Suka mike tsaye, Ado na cewa, "Yi hakuri Jidda, ki daina kuka kukanki yana soya raina." Baba Gaje wani tukuki ta ji cikin zuciyarta , ta cije yatsa sannan ta yi gaba fuu. Dija ma ta bita tana cewa, "Gaje gidan su zamu ke kai kashedi." Gaban Maigari suka zube, Baba Gaje ta saki kuka tana fadi "Maigari kun ne masu hukunci ya ya zaka yi da danka Ado wanda ke lalata min yarinya?" Dija ta yi zaraf ta ce, "Har batun cikin da ya yi mata kwanakin baya ki sanar da shi." Nan da na kuwa ta dad rushewa da kuka. Dija dama baki tuno min da wannan ba, Ranka ya dadw kwanaki har ciki ya yi mata cikin zuaran nan naku mai duhu, sai da kyar asibitin Garko suka cire shi, na ji tsoron kawo kara ne don naga ku ne masu garin amma sai naga an ci gaba ni dai ranka ya dade a shiga tsakanin su." Wakilin Maigari ya nuna ta "Ke ba mu son zancan wofi, Ado za ki ma sharri?" Maigari ya daga mishi hannu tare da cewa,"Dakata Wakili." Ya kalle ta "To baiwar Allah, kiyi hakuri zamu yi bincike kuma zan dau mataki. Ta ce, "Na gode, na gode." Ta mike suka tafi. Cikin dakin Baba Gajen suka yada zango sai sheka dariya suke yi, Gaje tana ta zugawa Dija godiya da dabarar da ta kawo mata. Shi ko Maigari Sai ya dubi Wakili da Liman ya ce, Dan yau zaya iya aikata abin da ya fi haka, shi yasa na ce ba zai je karatun nan birni ba, Liman ya ce ni kuma sam ban yarda Ado za ya aikata haka. . 22.......Su kam karkashin wata bishiya suka zauna suna hangen ruwan daga in da suke. M.B yana jefa 'yan kananan dutsuna cikin ruwa, ya kalli Ado ya ce Adamu yarinyar can da ta wuce kamar itama 'yar gidan ku ce. Ado ya ce da ba ka santa ba? M.B ya ce ba duka kannanka na sani ba, 'yanmata da Bintu da Asma'u na sani." Ado ya ce, to ai sune 'yammatan, ita wannan da ka gani da ita zan aura, sai wasu matsaloli suka shigo, kuma ni na yi niyyar auranta ne don na taimaka mata bawai don so ba. Cikin ikon Allah da na sama zuciyata auranta a 'yan kwanakin da muka yi sai na samu kaina da soma sonta nan ya kwashe komai har da tarihin Jidda ya ba wa M.B Nan ya ji ya kara tausayin yarinyar sosai, ya kuma bawa Ado labarin turetan da ya yi dazun na. Bayan sun dawo cikin gari suka sake hangen ta dauke da tiren goro. M.B ya ce wai shin Ado yarinyar can bata da aikin da ya wuce talla ne?" "Kwarai kuwa. "In ji Ado,"Tana talla ne sau 4 a kowacce rana, safe, rana, yamma da kuma dare." Tausayinta ya kuma cika zuciyar M.B kazalika sai gata da daren dauke da tire. Ado ya ce, "In na jin takaicin halin da yarinyar take ciki, lokacin da na yi nufin taimaka mata sai na kara mata damuwa." Ya dubi M.B Muhammad tana zaman zamanta na jawo ta, na kimsa mata sona cikin zuciya, a karshe a ka raba mu don Allah ban zalince ta ba?" M.B ya ce "Ba ka zalince ta ba, kayi nufin taimakonta ne. Zan yi nazari nima na gani wane irin taimako zan mata?" ************* 23..... Komai na bikin M.B suna tafiya dai- dai, yanda Hjy ke rawar kai da ji da Ango tare da fidda kudi daga cikin jakarta take kashe su yana ba wa M.B mamaki, ban da yasan komai game da makarkashiyar da suke kulla